GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk wad’annan maganganun da Sallau yayi kamar a gaban Sarki! yayi su dan yaji komai, haka Shamsiyya.
Muje zuwa
Comeent vote and Share
[19/07, 22:49] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????
Bisimillahir-rahamanir-rashim
????54
Sai surutu Shamsiyya take masa, kanshi a k’asa sam baya k’aunar ya kalli fuskar ta, haka Sallau ya same su, jiki na rawa yace”barka da zuwa”
D’ago kansa yayi a nutse ya kalli Sallau hannu ya mik’a masa yace”barka kadai Baba”
Washe baki Sallau yayi yace”yan samari nayi mamaki jin cewar nayi bak’o,gashi bangane fuskar ka ba”
Shamsiyya tana tsaye tana dariya tace”aikuwa nima nace bangane shi ba”
Shiru yayi na minti biyu ya kalli Shamsiyya a ya mutse yace”d’an bamu guri, zamuyi magana ne”
Yak’e tayi tana “yar dariya takama hanya zata huce Sallau yace” ai “yata ce in taji babu komai” bana buk’atar taji”
yafad’a babu walawala a fuskar shi, wani kwarjini yayi wa Sallau sabuda haka sai ya kalli Shamsiyya yace ki shiga gida” Ko kunya babu ta shiga gida, sai ta mak’ale a soron gidan ta kasa kunne tana so taji, abunda ya kawo wannan guy addu’a take Allah yasa cewa zaiyi yana sonta,
A nutse Sarki! yace”wani abokina ne yaga “yar gidan nan shine muke bukince a kanta, ance mana kaine mahaifinta”
Washe hak’ura Sallau yayi yace”Eh duk “yayana ne, wacce kakw nufi a cikinsu”?
” Balaraba”
yafad’a kai tsaye
Murtuke fuska Sallau yayi yace”wannan lalatacciyar yarinyar kake nufi, yanzu nan ta futa yawon bariki, ai inaji ma ka ganta wata gansamemiyar mara kunya”
“Eh naga wata yarinya yanzu ta futa ko ita ce”?
” Babu shakka itace, shawarar da zan baka shine kaje ka fad’awa abokinka ya janye maganar auran ta domin ba d’iyar arzik’i bace, ni ne wan mahaifin ta, na santa ciki da waje jiya nan ta yankewa d’an uwanta ya tsa da wuk’a, sabuda haka in mata yake so yazo zan bashi d’aya daga cikin “yayana masu hankali da tarbiya”
Yafi minti biyar yana nazarin maganganun da Sallau ya fad’a masa, daga bisani yace”shikkenan dama abunda ya kawo ni kenan”
Sallau yace”to madallah, ka gayawa Abokinka cewar yazo ya duba d’aya daga cikin “yayana zan bashi, amma ya rabo da wannan yarinyar,in ba haka ba sai ta kashe shi”
Sarki! yace”za’afad’a masa, hannu ya zura cikin aljihun jins d’in dake jikinsa ya ciro kud’i kimanin dubo goma ya mik’a masa,
jiki na kyarma! ya warce kamar zai had’a da hannusa, saura k’adan ya tsuguna sabuda tsabar godiya da rawar jiki, nan Sarki! ya wuce ya barshi yana sambatu daf, da zai futa daga lungun sukayi karo da Balaraba, fad’uwa ta kusa yi yayi saurin rik’o hannuta, yana kallonta ta cikim gilashin dake idonsa, kallon kallo sukeyi da ita, fuskarta a had’e ta fuzge hannunta tana hararasa, tare da zabga tsaki tayi gaba, ji yayi bazai iya jurewa ba yasa ya tarota ta hanyar fuzgota ta dawo gabanshi, ya rik’e mata kafad’u da duk hannuwan shi sannan ya mannata da bango fuskarsa daf da tata yace”wai ke dame kike tak’ama ne, mara kunya, dan ma kin samu zaki fad’i na taimake ki shine zakiyi min tsaki” a tsiwan ce tace”anyi maka d’i… bata karasa ba ya rik’e bakin da ya tsunsa biyu ya murd’e leb’ubunan fuskarshi babu walwala yace”wai me kike da suna”? Balaraba kome? d’azu kafin ki futa kin min tsak’i yanzu ma haka, daga kawai an miki tambaya, zakina wa mutane, tsaki, wai ke kina tak’ama da kyau,ko dame kike tak’ama ne”? yafad’a yana zura hannun shi ta bayanta in da ya shafo tudun mazaunan ta a hannunsa, cikin sigar duniyan ci, yace “ko da wannan kike tak’ama ne”?
Zabura! Balaraba tayi tana mutso-mutso, gashi har yanzu bai sakar mata baki ba, wani munafukin murmushi ya saki, yace” yarinya ko dame kike tak’ama bai dame ni ba, babu abunki wanda zai rud’ani kamar yadda yake rud’a wasu mazan, yanzu “yar uwarki tafad’a min wai inyi taka tsan-tsan dake, bata sani ba ni ko a k’afa aka d’aura min ke sai na kwance,na gudu”
yana gama fad’ar maganarshi ya sake tayi taga-taga zata fad’i sabuda rashin k’arfin jiki, shi kuma kamar walkiya ya b’ace daga gurin.
Kamar ta d’ora hannu aka haka takejin wani mugun d’aci a zuciyar ta, gabanta ne ya fad’i lokacin da ta tuno muryarsa sai taji kamar tasan mai irinta, tsugunawa tayi a gurin tana cusa fuskarta tsakanin k’afafunta tafashe da kuka wurjanjan! babban bak’in cikinta yadda wannan guy d’in ya samu nasara a kanta, gashi ta kasa gane fuskarsa duk da haske futula, tunda take a duniya babu namiji da ya tab’a kusantar ta kamar haka,sai shi har yayi nasarar tab’a mata jiki, bayan shi sai Sarki! ranar da suka zo tare da Moddibo, shima kuma bai yi a banza ba sai ta d’auki fansar abunda yayi mata, ta dad’e tana kuka a tsugune a gurun, daga bisani ta mik’e ta shiga gida, duk suna zaune a tsakar gida Sallau yana mayar musu da magana abunda ya faru, amma k’iri-k’iri yak’i futo da k’udin, tanaji Uwa! tana cewa”ai yadda Shamsiyya take f’adamin mutumin da yazo yayi mata, sabuda haka ko ya sake dawo wa ka had’ashi da ita kawai, amma me za’ayi da waccan mutsiyaciyar yarinyar, nan sukai ta zagin Balaraba, gami da mata mugun baki, duk tana jinsu a d’aki, abunda ya hanata kwana a gidan da ta kama haya shine, babu fenti babu shara, yanzu futar da tayi ma kenan, domin tasa yara su share mata gidan, tunda anyi fenti da yamma, haka ta kwanta tasa su Sadiya da Usuman a gaba tana kuka tunda take bata tab’a kukan maraici ba sai yau
Comeent Vote and Share
[21/07, 06:17] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????
Bisimillahir-rahamanir-rashim
????55
Da wuri ta tashi tayi shirye-shiryen ta, tsaf ta shiryasu Usuman cikin kayan makaranta, ta had’a musu shayi, suka sha, itama ta had’a tasha, tana zaune gefan katifa, wayarta tafara k’ara tana dubawa taga Moddibo ne, sai ta kusa katsewa ta d’auka, ajiyar zuciya taji yana saukewa,sai ya bata tausayi , sallama tayi cikin muryar ta mai dad’in sauraro, yace”Gimbiya kin tashi lafiya”?
“Lafiya k’alau, kai fa”?
” Nima k’alau na tashi, jiya nai ta kiran wayar ki tun safe a kashe, gashi baki futo kasuwa ba”
Cikin nutsuwa tace”wallahi kuwa na kashe ne sabuda ina da uziri,nagode sosai”
” Wane uziri ne wannan, da alama kina cikin damuwa”
yafad’a da cikin tausayin ta gami da so da k’auna
A jiyar zuciya ta sauke, tace” yanzu zan fito zan kira sai muhad’u domin maganar ta wuce a fad’eta a waya”
“Ok toum in sha Allahu yanzu zan futo sai mu had’u, amma kicire damuwar komai a ranka kinji ko”
K’walla da take k’okarin zubo mata take k’okarin mayarwa tace” nagode Yusuf sai mun had’u”
kashe wayar tayi ta aje gefan katifa, ta cigaba da kurb’ar ruwan shayin ta, sha takeyi kawai amma zuciyarta babu dad’i,, tana jiyo hayaniyar mutan gidan a tsakar gida,, Uwa sai cinikin awara take babu abunda ya dameta