GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Babu Abunda Moddibo yace, kawai aje wayar yayi gefansa, Balaraba ta kalleshi cikin bacin rai tace”na lura kana mutuk’ar tsoran mutumin nan dubi irin masifar da yake maka a waya tamkar wani mahaifin ka, kayi masa shiru, bakace komai ba, gaskiya ka canza tsari, domin ina gani ko aure ma mukayi duk abunda yace da kai shi zakayi”
ta k’arashe maganar tana zumb’ura baki,
Ajiyar zuciya ya sauke dai-dai lokacin da yake parking d’in motar a bakin hanya, yace”kin kasa gane, Sarki! Gimbiya, na fad’a miki halinshi ne haka, yana da saurin d’aukar zafi ga muskilanci a cikinsa in ban dani babu da wanda yake sakewa, nine shi shine ni, shiyasa nake so ku samu fahimtar juna ke dashi, amma ina neman alfarma a gurinki don Allah”
Ya fad’i maganar yana kallon ta sosai, ya cigaba da cewa”in banda kina da alak’a dani, da yau babu abunda zai hanaki ki kwana a rufe, domin babu abunda Sarki! ya tsana kamar kayi masa tsaki ko yayi magana ka share shi,to duk yadda kuke dashi zai nuna maka kuskuran ka, sabuda shi mutum ne mai mutuk’ar son girma da rashin son wasa, kullum a kame yake,in kika fahimce shi sosai zaku zauna lafiya,a hakane kike ganin kamar d’an wulak’anci ne,shi”
Jin abunda Maddibo yace a kan Sarki! yasa Balaraba ta k’udurta a ranta, zata dunga yi masa domin ta k’untata masa, amma ba zata nuna gabansa ba domin kar yace bata jin magana, yanzu ma kwantar da kai tayi tace”Yusuf ba wai ina gudunshi bane, ni kawai jinane bai had’u da nashi ba, tun ganin farko da nayi masa, amma domin faranta maka rai zanyi k’okarin sashi a zuciya ta”
Murmushi Moddibo yayi yace”yanzu abunda zaki nuna min nasan kin dai na, bari in kira wayarsa ki bashi hak’uri”
Girgiza kai tayi da murmushi a fuskarta tace”shikkenan ka kira shi”
Wayar ya d’auka fuskarshi a sake ya fara kiran Sarki!
Yana ji yak’i dagawa har sai da Moddibo ya kira sau uku,sannan ya d’auka,shiru yayi bece komai ba, jin alamun and’aga wayar yasa shi saurin mik’a mata wayar, kasa-kasa tayi da murya tace”Allah ya baka hakuri”
Wani irin yarrrr! yaji a jikinsa lokacin da yaji sanyayyiyar muryar ta, kashe wayar yayi da sauri, yana da ya sanin d’agawa domin muryarta ta yanzu ta tayar masa da wani mugun tsumi wanda ya dad’e a jikinsa, sam d’azu bai ji wannan yanayin ba sai yanzu, jikinshi ya fara takurewa guri guda,ganin yadda sandar girmanshi ta mik’e sosai abun mamaki, innalilahi yake yaja cikin zuciyarsa, jikinshi ya fara rawa, mik’ewa yayi wayar ta fad’i kasa, ko ta kanta bai bi ba, ya nufi bedroom d’inshi domin duba magani, dama yana ajesu sabuda irin haka wata drowar yq bude ya dauko kwallin maganin ya bud’e ya ciri biyu ya watsa a bakinsa, da sauri ya je ya bud’e firji ya ciro robar ruwa irin na gora ya b’alle murfin ya kora maganin dake bakinsa,sai da ya shanye ruwan tas sannan ya yada robar a gurin ya kwanta kan bed, ruf da ciki,sai mutsu-mutsu yake shi kad’ai yasan halin da yake ciki.
A cikin wannan hali Moddibo ya shigo ya same shi, cikin mamaki ya tsaya yana kallonshi, yana ta murk’ususu kan bed gashi ruf da ciki ya rik’e cikinsa da duk hannuwanshi biyu, k’araso wa yayi kusa dashi yana kiran sunan shi, d’ago kai yayi yana kallonsa da ido jajazir, yace”lafiyan ka k’alau kuwa, dubi yadda ka turme she bedshirt sai kace wani yaro na shigo sai sallama nake kana nan kama mutsu-mutsu”
Harararsa yayi, ya mik’e zaune da k’yar! bai so ya shigo ya same shi cikin wannan halin ba, a tsarge ya mik’e tsaye bai tsaya komai ba ya nufi toilet da sauri dan kar Maddibo ya ga halin da yake ciki.
Dariya Moddibo yasa yana binsa da kallo, a fili yace” Yo me zaka b’oye min naga komai, sai anyi magana kace,kai mace bata gabanka har da ciki kuri wai zaka iya zama da babu aure, da wataran sai dai azo a d’auki gawar ka”
Sarki! yana jinsa yayi masa banza, jikinsa babu kuzari sosai ya had’a ruwan sanyi da zafi ya dunga kurmawa kansa, wai ko zaiji dad’i ya jima a toilet d’in sannan ya futo yana shan kunu dan kar Moddibo ya k’ara wata maganar a zuciyarsa kuwa ya k’udurta gobe zai tashi da azimi tunda abun hakane.
Wasu riga da wando ya d’auko irin na shan iska ya sanya a jikinsa, ya fesa turaren shi mai k’amshi, sannan yaje ya zauna, har yanzu fuskarshi babu walwala ya kalli Moddibo yana ya tsine fuska yace”sai yanzu ka ga damar zuwa kenan? kana can tana hure maka kunne ko mijin tace”
Zama Moddibo yayi kusa dashi yana wata dariya cikin jin dad’i yace”wallahi kamar ka sani kuwa yanzu ma da kyar! na tawo domin na kasa gajiya da kallon kyakykyawar fuskarta”
Wani irin kallo yayi masa yana jin kamar ya gaura masa mari, ya tsani yaga namiji na zumud’i a kan mace, cikin gatse yace”me yasa baka kwana a can ba”
” Yo kwana nawa ne”?
Maddibo yafad’a yana wani lumshe ido.
Wani iri Sarki! yaji a zuciyarsa jin abunda Moddibo yace, gyara fuska yayi yana d’an tab’e baki yace” bayan kak’i ka bada had’in kai,kana can tana hure maka kunne, tuntuni nake neman ka, in fad’a maka abunda na bunkito a kanta”
Gyara zama Moddibo yayi yace”ina sauraronka nasan dai duk abunda zaka bunkito to na alkairi ne,domin nasan Balaraba bata da aibu, wanda zai hanani auranta”
Comment Vote and Share
[22/07, 20:34] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????
Bisimillahir-rahamanir-rashim
????57
” Yarinyar da kake son ka aura “yar daba ce”
Sarki! yafad’a kai tsaye
Sakin baki Moddibo yayi cikin mamaki yace”ban fahimci abunda kake nufi ba, “yar daba kamar yaya”?
” Ina nufi tana yawo da wuk’ak’e a jikinta tana sukan wanda ta gadama, a yanda na samu labari cewar ta cirewa d’an uwanta d’an ya tsa”
wani mugun b’acin rai ne ya ziyarci zuciyar Moddibo idanunsa suka k’ank’ance yace” yanzu kai bakaji kunyar fad’ar wannan kalmar ba,akan yarinya kamila irin Balaraba”
“Wace irin kunya kuma,ana maka maganar gaskiya wannan maganar ta futo ne daga bakin Ubanta k’arewa ma”
ya karasa maganar yana d’aga kafad’a alamun abun bai dame shi.
” Duk abunda a ka fad’a maka a kan Balaraba k’arya ne, mak’iyanta ne, kawai masu neman suga bayanta”
ya karashe maganar cikin jin haushi
Murmushin k’asaita yayi yace”shikkenan in anjima da daddare ka shirya muje unguwar tasu ka k’ara tambaya kaji, da kunnen ka”
“Ko bak fad’aba dama yau zani gurinta, nifa duk abunda za’a fad’a kan yarinyar nan sai dai a fad’a sai na aureta insha Allahu”
Ya mutse fuska yayi yace”Allah ya sanya alkairi”
nasan dai ni ake fad’awa magana”
Mik’iwa Moddibo yayi yana k’okarin futa yace”ai duk kai ka jawo kana nuna tsananin k’inka a kan yarinyar, ko d’azu da tayi maka tsak’i nace ta baka hakuri duk dan ku fahimci juna”
yana gama fad’ar maganarsa ya fuce daga d’akin, hakan da yayi ya tabbatar wa da Sarki! yayi fushi dashi, Moddib mutum ne mai tsananin hak’uri da kauda kai, ganin fushinsa sai an shirya sabuda zakai tayi masa abu yana hak’uri, amma in yayi fushi ana dad’ewa kafin a shawo kansa,
Balaraba kuwa can gidan da takama haya taje,ta tarar yaran da tasa suyi mata aiki sun gama suna k’okarin kulle gidan, ta k’arb’i mukulin ta sallame su,