GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Banyan sun d’an yi nisa da tafiya Sarki! ya kalleshi yaga duk a furgice! yace”kayi shiru wai menene”

“Balaraba za’ai wa aure”
yafad’a kamar zai rushe da kuka!

Wata dariya ce ta kama Sarki! ya dara yace”shine zakayi kuka lallai Moddibo yarinyar nan zata zautaka, sai me in anyi mata aure,? dama can Allah ya nufa ba matar ka bace”
Cikin damuwa da b’acin rai Moddibo yace” ba nafad’a maka damuwa ta bane domin ka b’ata min rai ba, na fad’a maka ne domin ka nema min mafuta”

“Ok toum yanzu me zanyi maka, dama ni bana son ka aureta sabuda haka babu wani mafuta da zan nema maka”

A nutse Moddibo ya juyo yana kallonsa yace”alfarma d’aya nake nema a gurin shine ka amunce min in kawo Balaraba shashen ka in b’oyeta kafin ka gama bunkice a kanta, dan girman Allah kaga daga mungama bunkice a kanta sai muje mu samu me Martaba mu fad’a masa halin da ake ciki,amma yanzu in muka bari a ka daura mata aure rayuwarta tana cikin ha tsari, nima zaku iya rasani, domin zuciyata zata iya mutuwa”

Comment Vote and Share
[23/07, 16:23] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????

MARUBUCIYAR
Nana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba

DEDIGATED
TO
{RAHAMA ALIYU}

ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????

Bisimillahir-rahamanir-rashim

????58

Cikin mamaki yace”ban fahimci abunda kake nufi ba, kana nufin ka kawo min ita shashena ka aje, min kan wane dalili zaka had’ani da mace baliga irin wannan”

Cikin kwantar da kai Moddibo yace” ai a k’asa zata zauna, kai kana sama, duk abunda kake buk’ata da a kwai a saman ka,nasan in ba neman magana ba babu abunda zai sakko da kai k’asa”

“Shikkenan sabuda buk’atar ka sai in dai na zaman farlo sabuda ka aje ” yar gwal,sai in takure kaina,kasan abunda bazai yi hu bane”
Ya k’arashe maganar yana masa wani kallo a d’age!
“Shikkenan to ka bata aron d’aki a saman mai d’auke da toilet, ni zan dinga kawo mata abunci,da komai na buk’ata,banaso ma ta futo balle masu yi maka hidima su ganta su zargi wani abun”
Ganin yadda Moddibo ya wani sukurkuce yasa yace”shikkenan” sakin fuska Moddibo yayi yace”nagode d’an uwana,na baka amanar ta ka kula min da ita don Allah”
Cikin shank’amshi yace”ban karb’i amana ba, gaskiya ga guri nan da ta zauna”

“Shikkenan hakama nagode”
Moddibo ya fad’a cikin farin ciki, ya cigaba da cewa yanzu, in mun dawo me zai hana mu tsaya a gidan nasu ko”?

Girgiza kai yayi kawai yayi shiru, hakan ya nunawa Moddibo bai yadda ba, shiru yayi bai sake maganar ba yana jin tsoron kar ya botsare masa, yasan halin kayansa.


Sai bayan sallahr la’asar suka dawo gida, Moddibo ko zama baiyi ba, ya k’ara futa shi kad’ai a mota,

Balaraba suna zaune ita da Bushira suna jiran zuwan Moddibo domin yayi mata waya yace gashi nan kan hanya, “yan kayanta ta had’a a k’aramar a kwatu, ta had’a nasu Sadiya da Usuman tanayi tana kukan bakin ciki da halin damuwar da take ciki, Bushira sai tausar zuciyarta take, Lantana ce yi sallama ta shigo d’akin tayi musu wani irin kallo,na raini da wulak’anci tace” Au kuka kikeyi, dan mugun hali, in ceko “yan gulma sun fad’a miki d’aurin auran ki da d’an uwanki ne,shine kike koke-koke banza,to ko kukan jini zakiyi sai dai kiyi munafuka kawai,ai da wannan lalatar da kike gwara ayi miki aure kar ki jawo mana abun kunya a gari”

Haka Lantana ta k’araci zage-zagenta ta futa, basu ce mata komai ba, suna jiyo shewarsu Uwa da “yayanta a tsakar gida, sai zaginta suke, Iro ne ya shigo shima ya zauna anayi dashi,

Wayarta ce tayi k’ara Moddibo ne, ta d’aga wayar gami da karata a kunne, cikin sanyin murya tace” Yusuf, ka zo ne”?

“Eh ina cikin unguwarku, na bari ay sallahr Magariba duhu yayi sai in zo”

“Yawwa dama abunda nakeso ince kenan” tafad’a tana kokarin kashewar jin alamun za’a shigo d’akin, Iro ne ya shigo yana wani lasar baki, idonshi tar! a kan Balaraba, yace”amaryata ya akai ne”?
K’okarin tsallake Bushira yake yi yaje kusa da Balaraba yw zauna, Bushira tayi saurin janye k’afarta hakan yasa ya fad’i k’asa kamar wani soko, dama ga jiki babu k’wari ya mik’e yana layi yace”ke tashi ki futa zani magana da amarya ta”Wari ne ya cika d’akin na tsamin hamta da warin ganye, zuciayarta taji tana wani irin tashi, Balaraba kuwa tuni ta toshe hancin ta, Bushira tace”kai in banda abunka Iro ai kamata yayi kai da zakazo gurin amaryar ka kaci kwalliya kazo kana k’amshi, ba wari ba, yanzu abunda za’ayi kaje kayi wanka kasa kaya masu kyau ka fesa turare in kanaso amaryar taka ta saurareka, jin abunda Bushira tace, yasa ya washe baki yana kallonta yace”kina nufin ta yanzu ta amunce dani”?
“Sosai kuwa”
Balaraba tanai masa murmushi kamar gaske
Futa yayi daga d’akin yana fad’in yanzu zanje kuwa in shek’awa amaryata kwalliya”

Yana futa suka fara dariya kasa-kasa Bushira tace”wannan ya kasance a mijinka ai ka shiga uku da wari da tsamin hammata”

Cikin takaici da damuwa Balaraba tace”rabu da shashasha mahaukaci kawai”
Dariya kawai Bushira take mata.

Sai bayan sallahr isha’i sannan Moddibo yazo, yana zaune cikin mota yana tunani,sai yaga gilmawar Walidi, ya sauke glass d’in mota yana kiransa, dawowa Walidi yayi ya tsaya, ganin fuskar Moddibo yasa ya washe baki yace”yallabai barka da zuwa”

“Barka kadai abokina”
Moddibo ya fad’a ya cigaba da cewa” kaje ka kiramin Gimbiya”

Da sauri Walidi ya tafi, lokacin duk sun watse a tsakar gidan babu kowa, sabuda haka da sauri ya shiga d’akin Balaraba tace”yawwa dama kai nake nema d’auki wannan a kwatun ka futa dashi, zakaga wani mutum da mota a bakin lungu” Walidi yace”ai shine ya aiko ni ma yanzu” “Ok yi sauri ka kai masa” hannu biyu yasa ya d’auka ya futa da sauri,su kuma suka mik’e suna yafa mayafansu, Bushira ta rik’e hannun Sadiya, Balaraba ta rik’e hannun Usuman a haka suka futa daga gidan, lokacin babu mutane sosai a waje, sai yara k’ananu, sabuda haka basu fuskanci komai ba, nan Walidi ya bud’e bayan motar ya zura jakar ya mayar ya rufe ya tsaya yana hangowar zuwansu Balaraba, Moddibo yana ganin tawowar su ya bude mata kofa, su Sadiya tafara sakawa, ta tsaya suna sallama da Bushira Moddibo ya zuro kanshi suna gaisawa da Bushira, kud’i ya ciro wanda bai san adadinsu ba, ya mik’a mata, ya k’ara ciro wasu ya mik’awa Walidi dake ta washe baki, yace “ina neman alfarma a gareku da ku rufe wannan abu a tsakanin mu, in kukayi haka kunyi jahadi,bayan komai ya lafa zan muku kyauta ta mussaman”

Bushira tace”Babu komai Yallab’ai”

Godiya yayi musu ya kunna motar cikin sauri yaja motar, su kuma suka bar gurin cikin mamaki kyautar kud’in da yayi musu.

Shiru cikin motar babu wanda yace komai sai da suka hau titi sosai sannan Moddibo ya juyo fuskarasa d’auke da murmushi yace”Gimbiya wannan ce Sadiyar”?

A hankali tace”Eh”

“Kai masha Allah kuna kama da ita amma ba sosai ba”

Murmushi tayi kad’an da damuwa a fuskarta tace”Yusuf ina ka shirya a jeni ne”?

Fuskarshi ya gyara yana kallonta ta cikin mudubin motar,yace”gidan mu mana amma kina keb’antaccan guri,wanda babu wanda zai san dake a gurin”

Ajiyar zuciya ta sauke hankalinta ya kwanta tace” nagode Yusuf Allah ya kara mana so da k’auna”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button