GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wa d’annan yaran fa?
a sharad’in mu dama a zata zo min da yara ne”?
yafad’a yana binsu Sadiya da kallo.
Moddibo yace” Yan uwanta ne,itace uwarsu itace ubansu,zata zauna tare dasu insha Allah ko aure mukai muna tare dasu.
Tab’e baki yayi ya mayar da kansa k’asa yana duba littafin hannunsa.
Da k’yar Moddibo ya rarrashe ta,tare ta bishi sama, tare da sharad’in gobe zai canza mata gurin zama, sai da ya tabbatar da ya kwantar mata da hankali sannan ya sauko k’asa cikin sauri ya nufi k’ofar futa, ko kallon Sarki! baiyi ba, saboda ya bashi haushi d’azu abunda yayiwa Gimbiyarsa bai dace ba,
Tab’e baki yayi kawai ya cigaba da abunda yake, yananan zaune Moddibo ya dawo hannusa nik’i-nik’i da manya-manyan ledoji, kamar yadda ya futa bai kulashi ba, haka da ya dawo kai tsaye sama ya nufa, inda Balaraba take.
Wajan minti ashirin ya sakko, yazo ya zauna kusa dashi ya dafe kansa da hannu guda yana sauke ajiyar zuciya,
Shareshi yayi shima tsawon minti goma babu wanda yace da d’an uwansa k’ala, Cikin jan nuffashi Moddibo yace”wallahi narasa wane irin hali ne da kai, kafin in kawo yarinyar nan sai da nafad’a maka kuma ka amunce, kan me yasa zaka ci mata mutumci, kowa ai da koyo ya iya,gaskiya banji dad’in abunda kayi mata ba”
Kamar da dotse yake magana yana jinsa yayi shiru.
K’wafa yayi kawai yana duba agogon hannusa yace”yanzu dai gata can babu abunda zata nema,komai na siyo mata in tsautsayi yasa ta sakko don Allah babu ruwanka da ita”
Hankalinsa na kan littafin hannunsa yace”sai ka fad’a mata nima babu ruwanta dani, haka kawai ni da gidana anzo ana kafa min doka”
” In dan ta ita ne sai ku shekara bata shiga harkar ka ba, nasan halin kowa a cikinku”
Aje littafin yayi yana wani murmushi mai d’auke da ma’anoni daban-daban ya fuskaci Moddibon sosai yace”wai dakata malam har tsawon wane lokaci ka d’auka zatayi anan, inaji fa kayi mata alk’awarin gobe zaka canza mata guri, kazama me baki biyu kenan”?
” Wannan kuma kai za’a tambaya tunda wuk’a da nama na hannunka, dole ne in kadamu kaje ka k’arasa bunkice a kanta idan kuma ka gama shikkenan sai kaje kasanar da me Martaba halin da ake ciki”
” Ni tuntuni nagama bunkice na a kanta kuma nafad’a maka, amma tunda kace haka insha Allahu gobe zan sanar masa da halin da ake ciki”
yafad’a yana d’an jan numfashi sannan ya cigaba da cewa” Yanzu wane amsa zaka bawa me Martaba in ya aika gidansu yarinyar nema maka auranta, a kaji cewar tana hannunka ka b’oye kana da amsar da zaka kare kanka”?
“Duk wannan me sauk’i nr tunda kafin in d’auko su sai da naje na sanar da me gari, yasan halin da ake ciki, kuma a ranar yace zai aika a kira masa shi me unguwar da aka had’a baki dashi da wan mahaifin nata Sallau, wata k’ila kana iya ganinsu gobe a fadar Sarki”
“Shikkenan Allah yasa haka shi yafi alkari, Allah ya baku zaman lafiya”
“Ameen ameen”
Moddibo yace cikin jin dad’in addu’ar da d’an uwan nasa yayi masa, hira suke sosai irin tasu, Sarki! yace”gobe da misalin k’arfe hud’u na yamma Gimbiya Azima zata kawo min ziyara”
Murmushi Moddibo yayi yace”kace muna da manyan bak’i”
Ya mutse fuska yayi kawai bai ce komai ba.
Moddibo yace”wai Halisa tasan halin da ake ciki kuwa? ma’ana tasan su biyu zaka aura lokaci guda”
Wani murmushi ya saki cikin k’asaita yace d’azunan muka gama rigima da ita anan,sai da nayi mata fata-fata sannan ta shiga hankalin ta kasan halina sarai bana son shirme”
Cikin dariya Moddibo yace”gaskiya ne, rigimar Halisa babu mai iyawa da ita sai kai, wai don Allah yanzu ka fara sonta kuwa, na lura kai sam ba’a gane cikinka ko kana son abu baka nunawa wai saboda me”?
Cikin yanayin maganar shi yace”kowa an fad’a maka irinka ne, da kake haukacewa kan mace, duba don Allah shiriritar da kake kan wannan kidahumar yarinyar wacce ko hankalin ki kirki bata dashi, ka zubar da girman ka ta gani, d’azu dakana bata hak’uri ji nayi kamar in tsinka maka mari dan haushi wallahi”
Dariya kawai Moddibo yake kyak’yatawa yace”malam bakasan dad’in soyyaya bane shiya kake wannan maganar, ina ganin in kane kuka ma sai kayi da dai ban san halinka bane shiyasa nake tambayar ka yaya kakejin Halisa a zuciyarka, dan gaskiya ni ina mutukar son Gimbiya ina tunanim zan iya rayuwa da ita ita kad’ai”
Sarki! yayi masa wani kallo a d’age yace”wannan tsarin ka ne, malam ni babu wata “ya mace da zanyi wa kuka a kan me, me zata bani? wallahi kuna bani mamaki, wai me kukeji ne in kuna rawar jiki akan mata, soyyayar banza duk shirme ce ni aganina”
Girgiza kai Moddibo yayi yace”gwara da kace kai a ganin ka, amma ina nan ina addu’ar Allah ya nuna min lokacin da zan ganka kanai wa mace “yar murya ni nasan komai daran dad’ewa wannan lokaci sai yazo
Turka!Turka
WAI SARKI!! NE?
KOMODDIBO NE?
Muje zuwa
Comment Vote anda Share
[25/07, 16:36] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^°
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®{REAL BINTU BATULA}????
MARUBUCIYARNana khadija
Yaro da kudi
Gimbiya Balaraba
DEDIGATED
TO{RAHAMA ALIYU}
ZAMANI WRITES
ASSOCIATION????????
Bisimillahir-rahamanir-rashim
????60
“Lallai kuwa ashe zaka sha zama in har zaka tsaya jiran wannan lokacin da kake, fad’a, aini ko ina son mace bata isa in nuna mata ba, zahiri sai dai ta gani a ai kace, kai dai da kaga zaga iya kaje kayi”
Moddibo ya mik’e tsaye da niyyar tafiya, da murmushi a fuskar sa yace”wannan ciki bakin naka yana bani mamaki, amma dai zamu gani ai”
Hannu ya bashi sukayi sallama, ya futa.
Shi kuma kusan rabin kwana yayi a farlon nasa yana karance karance sai wajan uku shaura ya mik’e ya haura sama, toilet ya nufa ya d’auro alwala yayi nafila kamar yadda ya saba, yayi addu’oin sa, sai jingina jikin bed d’insa yana jsn carbi, bacci ya soma fuzgarsa, cikin bacci ya dinga jin motsi, kad’an-kad’an a bardar saman sa, mik’ewa yayi a nutse ya bud’e window yana duba gurin, Sadiya ce a takure a k’ofar d’akin da suke ciki ta bud’e ta futo ta tsuguna ta takure kanta cikin gwiwa jikinta sai rawa yake.
A nutse ya bud’e k’ofar d’akin nasa ya futo yazo ya tsaya kan yarinyar, sam bata san ma yazo gurin ba, kallon cikin d’akin yayi haske tarr! da yake basu kashe futila ba, can ya hango Balaraba kan bed tana ta bacci abunta, gashin kanta duk ya hargitse, ga sharab’ar ta duk a waje, kasancewar riga da wando ne a jikinta irin cotton d’in nan rigar me dogon hannu ce tana da botora shi kuna wandon iya gwiwa ne, shiya duk wasu sassan jikin nata suke waje, sauri d’auke kansa yayi yana d’an ya mutse fuskarsa, ya mayar da idonsa kan Sadiya, cikin murya mai sanyi yace “Kee”
Da sauri yarinyar ta d’ago kanta tana kallonsa a furgice zata ruga da gudu cikin d’akin, sai yayi saurin damk’e hannunta, inda yaji zafi rad’au, da alama zazzab’i yarinyar take, k’okarin fuzge hannuta take cikin tsoro, yayi k’asa da murya sosai yace”me yasa kika futo nan uhumm”?
Shiru Sadiya tayi tana kuka, “Baki da lafiya ne”?
D’aga kai tayi tana zubar da hawaye
” ina yayar taki”?
yafad’a k’asa-k’asa
“Bacci take yi, na tashe ta tak’i tashi gashi ni tsoran d’akin nake yayi girma da yawa”
Bai ce komai ba, ya kama hannun yarinyar suka shiga d’akinshi ya futo da maganin zazzab’i ya ciro biyu yace”kinji abunci da zaki kwanta”? d’aga kai tayi, ruwa ya ciro mara sanyi ya mik’a mata maganin yace”maza sha kinji ko, yanzu za ki daina jin ciwon insha Allah”