GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka sukai ta tsallake shirgin gurin Kafin su shiga cikin gidan da babu kofar arziqi duk ta lauye ko tsayuwa batayi da kafarta sai an kare da dotse ko kujera,Kawu sai zage zage take yi kafin ya shiga gidan fadi yake shegu tsinannu “yayan Allah bani duk sun zo sun cika mana layi da kayan sata “yan iskan yara kawai”
Wani kallo Balaraba taiwa Kawun Mai kama da Harara tace”Haba Kawu wannan zage zagen bashi da Amfani Shiyasa suka rai naka ina ruwanka dasu ,sai La’antarsu kake yi ta’ina zasuyi Albarka kar ka Manta fa harda su Babaye da Walidi cikinsu shikkenan tunda ka hadasu ka zage babu ta yadda zasuyi Albarka ,Neman halak dinsu sukeyi yafi suje su dauki Na wani ” ta qarashe maganar Cikin bacin rai!
Gyaran Murya yayi ko kunya babu domin shi yanzu lallaba Balaraban yakeyi so yake ya kwace mata duk Abinda ta samu gurin saukar.
Yace”Rabu dasu diyar Albarka kinji ko shige muje ciki Ae ke kaman Dan Uwana yayi sa’ar Haihuwa ba wa”yannan “yan iskan ba”
Yaran dake gurin suka kwashe da dariya suna nunashi da hannu domin dai dama yaran duk sun rai nashi sakamakon zubar da Mutunchin shi da yakeyi gurin in sunje gwangwan dinsu sun dawo yabi yana kar6e musu kudi.
Balaraba taja tsaki ta shige ta barshi gurin tace”ae kaga Abinda nake gudar maka nan gashinan sun mai da kai mahaukaci”
Walidi ne yafito a guje su ka ci karo da Balaraba yayi mata wata bangaza tamkar zai yadda ita kasa,yayi gaba ko saurararta bai yi ba.
Da sauri ta jawo hannunsa ta zabga Masa Marika hagu da dama tace” Dan Uwarka ni sa’arka ce zaka bangaje ni ka huce ko kallo ban isheka ba ko ka ga INA shiga sabgarku ne”?
Kuka Walidi yafashe dashi yayi cikin gida da gudu yana cewa”Allah ya isa ban yafe ba Shegiya “yar Karuwa”
Wani Bacin rai! Ya dirar wa Balaraba tayi cikin gidan A fusace yau sai taga da Wanda walidi yake taqama Lallai yau za’ayi rigima gidan nan domin tagaji da irin cin zarafin da yaran suke mata.
Da sauri Kawu yabi bayansu yana zagin Walidi ta Uwa ta Uwa ba
Uwa” Na zaune kan kujera “yar tsuguno tana wanki dake sana’ar tace kenan wankau Walidi ya shigo yana burara ihu tamkar Wanda a ka yanka ,Sai tambayarsa take menene da qyar yace waccan “yar karuwar ce ra mareni hagu da dama inaji ma ido na yafashe yafada tana rintse ido daya cikin sharri
Cikin Sababi! Da tashin Hankali! Uwa ta Mike tana gyara daurin zaninta tace “Lallai Yau zaci kambu a gidan nan Wallahi tallahi bazan lamunci wata “yar iska ta riqa dakar Min “yaya ba bara ta shigo inji meye dalil……kafin ta karasa tajiyo Muryar Kawu yana ta Surfawa Walidi zagi!
Abin Mamaki!
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????????
[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????writting by
Binta Umar
MAMAN ABUDL WAHABU
MRS AHAMAD GWADABE
WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN
????8
“Yau kuma da Abinda kashigo da shi kenan Malam me walidi yayi maka kake ta surfa masa zagi haka? Kar dai a ce tarewa mutsiyaciyar yarinyar nan kake Balaraba”
Tafada tana nuna Balaraba dake jikin rijiya tana kallonta.
Kawu ya gyara tsayuwa gami da riqe Abubuwan dake hannunsa da kyau ,ya kalli “Uwa yace”Laifi ne Dan Na tare mata Yarinyar kirki haka ka wai kin bata yaranki kin sangar tasu basa ganin kowa da mutumchi a gidan nan yanzu a ce kamar Balaraba ita Walidi zai zage yayi ta zagi kina kallonshi kice in yi shiru”
Mugun Mamaki ne ya kama Uwa jin Abinda Kawu yake fada Lallai a kwai lauje cikin nadi kawun da yake zama a zagi Balaraba da ita da iyayenta da qannenta yau shine yake tare mata fada.
Ta gyara tsayuwa gami da gyara daurin dankwalinta ta kalli kawun tace Au! Ashe kai ma tafara baka cin hanci cewa zakayi kafara cin kudin zina da sata
Tafada tana wani girgiza jiki cike da Neman fitina,
Kifta mata ido Kawu yayi ganin har ta hasala
Duk Balaraba Na kallonshi.
Aiko dake “Uwa tasan Halin Mijinta nan da nan ta dago Abinda yake nufi kifta mata idon da yayi
[04/05, 02:54] +234 808 996 5176: ????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????writting By
Binta Umar
MAMAN ABDUL WAHABU
????9
“Ke kuwa Uwa wane irin Abu mai muni yarinyar nan tayi miki ? Kike jifan ta da Mummunan Al’kaba’i haka me yayi zafi kema fa kin haifa”
Iya take fada bayan fitowarta daga dakin ta tana tsaye ruqe da ha6a tana kallon Uwa cikin Mamaki
Kafin Uwa tace komai sai gasu Mabaruka sun shigo a guje ko wanne hannushi ruqe da Farin botiki Wanda suke zuba Awarar da suke Siyarwa da kwai suna kaiwa kasuwanni
Sai wasan banza suke suna dariya kamar wasu shashashai ko wacce taci janbaki gami da wani katon A cuci a kawunansu.
Sai suka tsaya ganin Iyayen nasu a tsaye dagani Fada a keyi.
Uwa tace “Yawwa “yayan Albarka dama tunda naji shiru nace Lallai yau Awara zata qare Allah dai yayi muku Albarka Ya Baku miji nagari duk Dan bakinciki sai ya mutu ehe!!
Tafada tana kallon gefan da Iya ke tsaye tana kallonsu,
Shamsiyya tace”wai meye ne ? Naga duk kunyi wani cirko cirko tafada tanawa Balaraba Wani Dan iskan kallo.
Uwa tace”Wannan mai ido a tsakar kan ce take zagina bay an ta mari Walidi shine babanku yake cewa wai laifin walidi ne kan nayi mata magana Shine yar Ubanta tafito zata tare mata .
Tafada gami da zama kan kujerar da tatashi ta ciga da wankinta tana sakin habaici ga Iya.
Mabaruka ta kalli Kawu sallau Mahaifinsu ,Cikin Raini da rashin kunya tace “Haba Kawu yanzu har ka fi son bare da Jininka yanzu a gabanka wannan jakar! Take zagin Maihafiyarmu baka ce komai iyi!? Kawai sai ta aje botikin Awarar a Fusace tayi kan Balaraba gadan gadan!
Dama sun saba dambe Dan su Shamsiyya basu da Hankali in dai Abu ya hadaka dasu Abu kadan sai a fara dambatuwa.
Balaraba tayi saurin kaucewa daga jikin rijiya ta tari Shamsiyya tun kafin ta karaso suka kacame da kokawa Abin Mamaki!!
Mabaruka tafara daukar Abubuwa tana dukan Balarabar dashi ganin ta kayar da Shamsiyya tana duka .
Sai dura mata Ashar Mabaruka take ta Uwa ta Uba.
Iya ta shiga tsakani tana rabawa gami da ruqe Balaraba Amma Ina!! Balaraba taqi rukuwa domin dama in tai zuciya fadanta baya rabuwa.
Shiko Kawu sallau barin gurin yayi yana tsitstsinewa su Shamsiyya a zuciyarsa domin babu Halin yayi a fili sabida tsoran Masifar Uwa.
Uwa dataga Ana cutar “yarta sai kawai ta daga ruwan daudar da take wanki dashi cikin roba ta kwararawa Balaraba a jiki tundaga tsakiyar kanta har zuwa qafarta tana ta zabga Mata zagi gami da mugun fata!!
Da kyar Iya ta janye Balaraba daga kan shamsiyya tana bata hakuri gami da yi mata Fada,
Shamsiyya da tasamu ta mike sai taciga ba da zagin Balaraba tana jin fan ta da kwanonisu Na cin Abinci Wanda suke gefe Dan qazanta har yanzu ba’a wanke ba qudaje sai bi suke gami da ruwan wanki da Uwa ! take kwara musu
Har tasamu nasar jifanta a kanta gurin ya tasa ,cewa”take Wallahi sai naga bayanki Dan Uwarki karuwa Uwar tamu zaki dinga zagi shegiya wacce ba’a san Asalinta ba”
Bakinci tamkar ya kashe Balaraba sai tafashe da kuka, a gurin su Sadiya da Shamsu kannanta suna taya dawowarsu kenan daga makarantar Allo,yara duk sun cika gidan,