GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fuskarta d’auke da k’ayataccan murmushi ta sauko k’asa gami da sunkuyar da kai, tace ” lafiya kalau na tashi Ina fatan kai ma ka tashi lafiya”?

“lafiya k’alau, ya kwanan bak’unta kuma”?

Shuru tayi kawai har yanzu da murmushi a fuskarta, yace” sakko muje k’asa Ku gaisa da mutumin ki”

B’ata fuska tayi, tace”ba Kaine kake gaba dashi ba,ai shine ya kamata yazo ya gaishe ni”

“Duk da nine nake gaba dashi amma girman shi yafi nawa, kuma a matsayin ki na matata uwar ” yayana ya kamata ki d’aukeshi a matsayan magaji na tunda shak’ik’ina neshi, duk ranar da bana nan,shine zai mar miki uwa uba”

K’walla ce ta taro a idonta tace” wannan wace irin magana ce kake Yusufu ni dai ka daina min don Allah”
Kamar zata fashe da kuka ta k’arashe maganar.

Rarrashin ta ya fara yi cikin taushin murya har sai da yaga ta mayar da k’wallar sannan hankalinsa ya kwanta ya kalli su Sadiya gami da shafa kan Usuman yace”kun tashi lafiya”?

Kai a sunkuye Sadiya tace”Yaya Yusuf Ina kwana”?

Amsa yayi fuskarsa a sake, Usuman ma ya agaidashi a nutse ya amsa, Balaraba tace”Sadiya ai da zazzab’i ta kwana mybe ko b’akonta ne”

Hankalin sa a tashe ya jawo yarinyar yana tambayar ta, jikin nata, tace” Yaya Yusuf naji sauk’i abokinka wannan me kyau d’in yana da kirki shine ya bani magani nasha cikin dare”
Moddibo yace”sunanshi Sark! Ko ce masa Magajin Sarki! nasan zaiyi fiye da haka ma, saboda yana tausayi”

Kicin-kicin da fuska Balaraba tayi tace”ka gafarce ni Yusuf, ko maganar da zanyi maka zata b’ata maka rai, gaskiya kayi masa magana jiya cikin dare ya shigo d’akin nan, gaskiya ni ban yadda ba”

Wani iri yaji a zuciyar sa, jin abunda tace”me ya kawo Sarki! d’akin, ya san halin d’an uwanshi ba mane min mata bane,kuma bazai ci amanarsa ba, Sadiya tayi Sauri tace”A’a Yayarmu ya ganni a wajan d’akine shine ya bani magani nasha ya rakoni na kwanta yace kuma in daina futowa cikin dare”

Moddibo yace”yanzu naji,zance, kiyi hakuri Gimbiya babu abunda zai faru sai alkairi ba halin Sarki! bane abunda kike nufi”

d’an tab’e baki tayi kawai tayi shiru yace”Ku tashi mu sauka k’asa Ku gaisa sai Ku karya”
M’ikewa sukayi duka suka nufi k’ofa.

Karo sukaci dashi zai hau saman shima, ratse masa sukayi a baranda har ya k’arasa hawowa Mariya baiwarsa ce take bayansa da’alama gyare-gyare zatai masa Wanda takeyi kusan kullum duk safiya, murmushi ya sakarwa Sadiya, sam ! baki kalli inda Balaraba take tsaye ba, ciki-ciki tace”Ina kwana”?
yaci albarkacin Yusuf Moddibo.
A dak’ile ya amsa, ya mik’awa Sadiya hannu, yarinya mai sauk’in kai da wayewa sai ta sanya hannuta cikin nasa tana yar dariya tace” Magajin Sarki ina kwana”?
Cikin mamaki yake kallonta sai kuma ya kalli Moddibo cikin tuhuma yasan shine zai fad’a mata wannan sunan, saboda ba kowa ne ya ke kiransa dashi ba,

Murmushi Moddibo yayi, shi kuma ya tab’e baki kawai yaja hannun Sadiya suka nufi d’akinsa, Sakin baki Balaraba tayi kawai tana kallon ikon Allah, shi kuma yana sane ya sakarwa yarinyar fuska duk Dan ya muzgunawa zuciyarta, saboda yana bala’in jin ciwon zargin da take masa a kan yarinyar,baya ga haka ma, yarinyar ta kwanta masa,tana da hankali da nutsuwa ba kamar yayar ta ba.

Comments Vote and Share
????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM

????62

K’asa suka sauka zuciyarta tana mata sak’e-sak’e kan zak’ewar da taga mutumin nata yayi kan Sadiya,sam bata yadda dashi ba, ganin yadda yake wa mutane wani irin kallo, kullum ido a lumshe kamar munafuki.

Ko da suka sauka k’asa hadimai ne su wajan biyar maza biyu mata biyu suna aikin gyara falon,kowa da inda yake gyarawa, jikinsu sanye da wasu kaya iri d’aya masu kamar Uniform, wani k’amshi ne mai dad’i ya cika hancinta, wani ku-ku ne ya futo daga kchin hannusa dauke da wani tank’asheshan faranti cike da abubuwan ci, Balaraba tayi saurin kauda kanta domin bata so tayi k’auyanci irin na jiya, hannun Usuman ta kama suka ni bayan Moddibo,inda ya nufi
Wani k’ebantaccan guri a falon, yace da Usuman ya zauna, yaron ya zauna cikin wata k’aramar kujera mai taushi, zama tayi itama tana bin gurin da kallo gaskiya k’ayatuwar gurin ya burgeta sosai dagani gurin hutawa ne,

D’aya daga cikin hadiman dake aiki a gurin ne ya k’araso ya zube gaban Moddibo yace”ranka ya dad’e a kwai abunda za’ayi ne”?

A nutse Moddibo yace”ka kawo abun kari na mutum hud’u”

Cikin bin umarni ya mik’e daga gurin.

Cikin nutsuwa ta kalli Moddibo tace”ya kamata fa ka kira Sadiya haka”

” Yanzu zai sauko ai wanka ya hau yayi”
Shiru tayi kawai tana d’an ya mutse fuskar ta, tace”tsarin gurin nan ya burgeni Yusuf ina so abu White coulor” Murmushi yayi yace”lallai tsarin ku d’aya da mutum min in kin lura ai duk adon falon nasa white ne”
Shiru tayi tana da tasanin fad’ar maganar, minti biyu tsakani yace”zan shirya miki falon ki da wannan colour”

“Nagode”
Abunda tace kenan,tayi shiru kanta a kasa tana wasa da hannuta

Tsura mata ido yayi,kurum yana kallo, ta d’ago kai tana kallonsa suka sakarwa juna murmushi, tace”wannan kallon fa,Yusuf”?

Da murmushi a fuskar sa yace”kallon soyyaya ne Gimbiya zuciyata tana fad’a min akwai wani babban al’amari da zai faru a tsakanina dake”

Itama Murmushin take,tace”babban al’amari ai bai wuce na aure na da kai ba, dama ina so in tambaye ka a wace matsaya muka tsaya,nifa zama anan kamar a kan k’aya nake”

” Karki damu insha Allahu yanxu in na tashi daga nan gurin me Martaba zan wuce, za’ayi komai a gama cikin kwanciyar hankali”

Ajiyar zuciya ta sauke,ya cigaba da cewa”maganar gurin sai da abuncin ki ki bar wa su Hauwa’u su cigaba da samu a ciki, in sha Allahu xaki fara business in munyi aure”

Cikin murna da farin ciki take masa godiya,a bisa karamcin sa a gareta, tanaji a yanzu bata da babban masoyi kamar sa, zata dunga k’okarin danne damuwar ta duk Dan ta kwantr masa da hankali, Salmanu ne, ya k’araso gurin hannunsa d’auke da wani faranti me fad’i ya aje a tsakiyar su, Moddibo yace”jeka abunka kaji” godiya Salmanu yayi ya bar gurin, Sauri-sauri yake ya gama abunda yake yaje ya fesawa abokinshi Dauda labari,shi Dauda yana b’angaran uwar gidan Sarki wato, Kulu,mai d’akin kudu, kenan Mama Kulu kenan,

A nutse suke karyawa ita dashi, kana ganinsu kasan masoyan asali ne,Wanda suka yarda da Kansu, Usuman na gefe yana karyawa shima.

Cikin nutsuwa yake sakkowa daga sama step by step hannunsa na rik’e dana Sadiya, yana sanye da wasu kaya na alfarma, masu tafe da wata alkyabba, kafarshi sanye da wani takalim me gidan ya tsa, babu nad’i a Kansa, duk da cewar shigar dake jikinsa ta nad’in ce amma bai yi ba, cewarshi ya gaji da kayan nauyi, sumarshi ya gyara,sosai da gemunshi, sai sheki yake,d’an k’aramin bakinsa mai d’auke da siraran lips Wanda suka d’an yi duhu kad’an, yayi Kyau kwantaccan gashi ya kewaye shi, as’usul idanunshi a lumshe kamar ko da yaushe,sai k’amshi yake zubawa, yana sakkowa masu hidima a gurin suna zubewa suna kwasar gaisuwa, ko wanne munafurci fall a abakinsa saboda ganinsa da k’aramar yarinya “yar shekara goma, cikin yanayin tafiyarsa ya nufi, daining teble d’insa Wanda yake cike da abubuwan ci, dai-dai inda suke zaune yazo ya gifta Balaraba taji gabanta yana fad’uwa duk da cewar ba ta kalli fuskarsa ba,gefansa ta kalla, Yanayin kwarjinsa da yadda yake tafiya cikin k’asaita ya furgitata ko ba’afad’a an San d’an mulki ne shi saboda abun a jinsa yake, jin kamshin turaran sa yasa Moddibo saurin waiwayo wa sai yaga yana k’okarin zama kan kujerar daining d’in, ga Sadiya ta zauna itama, ku-ku shi na tsaye gefe,yana jira ya dai-dai ta zamansa yafara had’a masa,abin kari.
Mik’ewa yayi ya bar Balaraba a gurin ya nufi inda Sarki! yake zaune, sukai yi magana sama-sama,batajin abunda suke cewa, saboda a kwai tazara a tsaksninsu can ta hango,Sadiya ta zage sai kwasar girki take, babu wani kamun kai sosai yarinyar ta bata haushi, Moddibo ne ya k’araso inda take,tayi saurin kauda kanta saboda wani lokacin shima haushinsa takeji in taga yana wa Sarki!rawar jiki.
“Gimbiya zanje in gaisa da mutan gida,zuwa yamma zan shigo sai muk’arasa maganar mu, don Allah ki cire fargar ba komai a ranki”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button