GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Girgiza kai tayi cikin tsoro tace” Yayarmu fad’a suke yi da wannan da tazo gun ka”

Falon yake bi da kallo, cikin mamaki, ina Neman Halisa,

M’ikewa yayi kawai ya rik’e hannun Sadiya suka nufi sama,
Yana tura k’ofar yaga abun mamaki da d’aure kai, Balaraba ce, rik’e da wuyan Halisa ta mak’ure a bango,ita kuma Halisa duk tayi wujiga-wujiga,sai k’okarin k’watar kanta take,ta kasa,idanunta duk sun firfito waje, k’arasawa yayi ciki har inda suke, batare da yace,komai ba ya fara, k’okarin b’anb’are hannun Balaraba dake wuyan Halisa, sanyi da taushin Hannunsa,suka sa ta dawo hayyacin ta, kallonsa tayi da idonta wanda suka kad’a saboda b’acin rai!

Hannunta ya matse cikin nasa,shima ya zuba mata idonsa,kamar yarda tayi masa, dafin! dake nasa idon ya fi nata,dole tasa, ta risinar da idonta, ta zare hannuta daga nasa ta koma gefe guda tana huci!
Halisa kuwa zubewa tayi a gurin tana nufarfashi,na wahala! Dariya ce take cinsa ganin yadda Halisa tayi wurjanjan, cikin yanayin maganar sa yace”Halisa,da ilimin ki da komai kike kokawa sai kace a jahiliyya,in ita ta saba da dambe,ke sai ki biye mata,gwara ma da tayi miki duka”
Yafad’a babu damuwa a tare da shi.

Hawayen b’akin ciki ne ya fara zubowa Halisa,tace”abunda zaka ce kenan ko”?

“To me zan ce miki me ya kawo ki gurin ta,ko na aiko ne”?

Mik’ewa tayi tana gyara alkyabar jikinta,tace” zaka ce na fad’a maka wannan k’ask’antacciyar bata isa ta dake ni a banza,ba tana a matsayin baiwa ta,wallahi sai na wulak’antata”

Siririn murmushi ya saki iya leb’anshi ya d’an kalli Balaraba kad’an sai kuma ya kauda kansa,ganin ta babu hula,ga botiran rigar jikinta duk sun zube, saboda fad’a duk saman k’irjinta a waje, Ki yayi yanayin jikinsa na sauyawa, Matsalar shi kenan shi mutuk’ar zai ga wani shashe na jikin “ya mace shikkenan sai sha’awarsa ta motsa, ya cije leb’anshi na k’asa kad’an yace” Wannan tafi k’arfi ki Halisa,kika tab’a ta kin tab’a zuciyar Moddibo,ki bari zan mishi magana ya ja mata kunne”
Hannunta ya rik’e suka fara tafiya, domin barin d’akin,tace”wato ni ba zuciyar ka bace,kenan har zaka kasa d’aukar mataki a kanta dubi irin dukan da tayi min”
Kamar zai yi dariya, yace”muje k’asa in rarrashe ki, ko” mamaki sosai yake na k’arfin halin Balaraba, kizo har gida kina fad’a da masu gida, da alama dai yarinyar tana da aljanu.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM

????64

Da harara Balaraba ta bisu dashi,har suka futa, Sadiya ta matso kusa da “yar uwarta tana wasa da hannuta tace” don Allah yayarmu ki daina fad’a da ita baki ga ita “yar Sarki bace,kar ki jawo a kulle mu,kinji tana cewa sai ta d’aure ki”
Ta k’arashe maganar tana sharar hawaye

Tsawa! ta buga mata tace”rufe min baki,duk bake kika jawo ba, wallahi duk sanda na k’ara ganin kinje gurin wancan mutumin sai ranki ya b’aci,ki ko kiranki yayi kar kije”

Kwanciya tayi kan gadon tana kuka,Usuman yana taya ta,ita kuma Balaraba sai fad’a take mata.

Ko da Sarki! suka sauka k’asa da Halisa, zamansa yayi a inda ya tashi,ta k’araci k’orafe-k’orafen ta,bai ce mata komai ba, haka ta mik’e tana niyyar tafiya ranta duk a b’ace! ya d’ago kai a tsanake yace”koma ki zauna zamuyi magana”

Komawa tayi ta zauna, ya aje littafin dake hannusa,fuskarsa babu yabo babu fallasa yace”kin san Gimbiya Azima,”yar Sarkin Yalwa”?

Gabanta ya fad’i! jin sunan wacce ya fad’a ita kuwa tasan Gimbiya Azima,domin abokiyar fad’anta ce, basa shiri ko k’adan dalili kowa yana ji da izza! gami da tak’ama.

Bakinta na rawa tace”Eh nasanta”

“Yawwa itace zata zama abokiyar zaman ki in Allah ya yarda”

Wani irin yarrrr! ta ji ajikinta lokacin da taji abunda yace mak’ogaron ta ya bushe k’amas, tace”ban fahimci abunda kake nufi ba”

Wani irin kallo yayi mata yace”kin San bana magana biyu, kije kiyi tunanin maganar dana fad’a miki”

Kuka ta fashe! dashi kamar wacce a ka aiko mata cewar uwarta ta mutu, tace”yaushe har a k’ulla wannan al’amarin ban sani ba,kuma mahaifiyata bata sani ba,Dan anga cewar ita macace shiyasa har ake abu batare da saninta ba,wannan ai yaudara ce”
Cikin kuka ta k’arashe maganar.

Ransa a mugun b’ace ya d’ago Kansa ya zuba mata idonsa,masu kwarjini,tuni tayi k’asa da kanta tana sharar hawaye
Yace”dukanin ku ke da ita Azimar babu zab’ina a ciki, ke kin kasance zab’in Mamana,ita ta kasance zab’in Waziri, duk zan aure ku ne ba dan inaso ba,sai dai n in cika umarnin magaba tana”
Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa na fad’a miki ne saboda ki sani kuma ki shirya, saboda kin fi kowa sanin halina bani da munafurci kuma bana san hayaniya, da fitina,wanda na lura ke haka halin ki yake tada zaune tsaye, idan anjima zata zo nan domin ta kawo min ziyara zan tara Ku guri guda dake da ita,ku fahimci junanku, kar wata b’araka ta futo daga gare ki, nasan halinki, in xaki kwantar da hankalin ki ki kwantar domin ke da ita ba da ku kad’ai zan zauna ba,kin fi kowa sanin yaya tsarin masaraurmu yake”

Kuka mara sauti Halisa take,lallai tana cikin tsaka mai wuya, yanzu ta tabbatar da cewar Baba Waziri baya k’aunarta tunda har ya had’a “yar abokinsa aure da masoyin ta, ita da take burin taci lokacinta ita dashi kafin ya kawo wata,tasan ta more kuma sunsha soyyaya, yanzu ko auran a kayi tilas su raba kwana ita da Azima.

Tunda ya gama maganar shi,ya kishin gid’e kan kujerar ya lumshe idonsa Allah kad’ai yasan abunda yake damunwa, yana jin kukan Halisa yak’i k’arewa ya bud’e idonsa wanda suka d’an yi ja kad’an, yace” kin cika min kunne fa da gunjin kuka, kije ki tambayi Baba Waziri yadda a kai haka ta faru tunda na lura ke baki da kunya, har kina cewa an yaudare ku”
Yadda ya fad’i maganar da yanayin b’acin rai! yasa ta gane tayi kuskure domin Sarki! mutum ne wanda baya saurin nuna b’acin ransa da wuri, in ransa ya b’aci a yanayin maganar sa zaka gane, mik’ewa tayi ta nufi kujerar da yake zaune, ta rab’a jikinta a jikinta harda langwab’e kai, ta rik’e hannusa guda, d’aya, tayi k’asa da murya ta sosai tace” Allah ya huci zuciyar Habibi na, zuciya tana azabtuwa da so da k’aunar ka, shiyasa na rasa tunani na,lokacin da naji wannan maganar,ina kishin ka,mutuk’a bana k’aunar ko wace mace ta rab’eka sai ni,amma ina ganin burina bazai cika ba, Habibi nasan Azima ciki da waje,zata aure ka ne da wata manufa,a zuciyarta, gaskiya banso Azima zata kasance matarka ba, amma tunda haka Allah ya hukunta mama zan cigaba da tayaka addu’a”

Yanayin yadda tayi masa magana a nutse yasa yaji ta bashi tausayi, gyaran murya yayi gami da d’an gyara zaman sa,a nutse yace”ki koma inda kike mana, na hanaki irin wannan”
Muryar shi bata futa sosai yayi maganar,
Mik’ewa tsaye tayi tana gyara alkyabarta tace”tafiya ma zanyi,yanzu sai anjima zan shigo,da kamar k’arfe nawa zata zo”?
Tafad’a cikin sigar tambaya.

“Hud’u zuwa biyar na yamma”

“Shikkenan to”
Tafad’a a sab’ule jikinta babu kuzari ta futa daga falon
To,can gidansu Balaraba kuwa,babu wanda ya damu da rashin dawowar ta gida da wuri har wajan k’arfe tara da rabi na dare bata shigo gida ba, Iya hankalinta ya tashi ta futo ta nufi d’akin Sadiya matar Kawu suna maganar,can sai ga Sallau nan ya shigo fud’un-fud’un yana sab’a babbar riga, Iya ta tare shi cikin damuwa tace”Sallau har yanzu Balaraba bata shigo ba,babu ita babu yaran”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button