GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin da Moddibo yaje wa da Balaraba zan can halin da ake ciki,ta tsorata sosai da taji cewar me Martaba ne da kansa yake neman ta, jikinta yayi sanyi domin bata san abunda zai je ya dawo ba,tunda yace mata Sallau yana gurin,nan dai Moddibo ya rarrashe ta da ta kwantar da hankalinta insha Allahu k’arshen matsalarsu tazo,haka suka futo tare,da Sadiya da Usuman Balaraba na sanye da dogun hijabi har k’asa,

Yana zaune a inda yake ya hangi sakkowar su daga matattakalar bene, sai yayi sauri d’auke kansa yana jin wani abu a zuciyarsa, dake namiji ne me jarumta kwata-kwata fuskarsa bata nuna ba,

Tsayuwa yayi kusa dashi suna magana, ita kuma taja hannun su Sadiya sukayi gaba,
Bud’e k’ofa tayi suka kusa cin karo da Mariya wato baiwar shi, ta shigo kai a k’asa ta k’arasa inda yake zaune ta zube gwiwa biyu tana gaishe su,sannan tace” Ranka ya dad’e Jakada na waje yana neman iso”

D’aga kai yayi kawai

Mik’ewa tayi ta futa da sauri, ko minti biyu ba ai ba Jakada ya shigi, cikin sallama, ya kwashi gaisuwa sannan ya fad’i sak’on me Martaba.

A nutse yace” A ce masa gani nan zuwa yanzu in sha Allah”

Mik’ewa Jakada yayi yace “A futo lafiya ranka ya dad’e”

Moddibo yace” Nafad’a maka kak’i yarda yanzu dai gashi kaji daga bakinsa ko”

A nutse ya mik’e tsaya ya d’an ya mutse fuskar sa kad’an yace”muje”

Moddibo ne ya bud’e k’ofar suka futa tare,Balaraba na tsaye a wani guri ta hangi futowar su, saurin dauke kanta tayi ganin yadda kyawun Sarki! ya dusashe na Moddibo,wani in rana ta daki fuskarsa yana muuni!sai taga shi wannan wani k’yalli da annuri fuskarsa take, tafiya yake cikin kasaita, tana kallon bakinsa daga inda take yana motsi da alama magana suke da Moddibo, ta lura tunda ya futo bayin da suke gurin suka bar abunda suke suna gaishe shi,

Ganin sun kusa zuwa inda take ne yasa tayi saurin kauda kanta,ta gyara yanayin fuskarta sosai gudun kar ya kawo wargi.

Moddibo yace”Yi hakuri Gimbiya kina tsaye kina jiranmu ko”

Murmushi tayi kawai ta basar, Sarki! kuwa wucewa yayi ya barsu a gurin, sai suka biyo bayansa.

Bayan sun dai-dai ta zamansu gaban me Martaba, ya kalli Balaraba sosai yana nazarin ta,a idonsa yake ganin kamar yasan fuskar, gyara murya yayi kalli Sallau da ya diririce a gurin duk alamun rashin gaskiya sun bayyana,a tare dashi,yace”Wannan itace yarinyar da kake magana akanta”?

Sallau ya d’aga kai cikin tsaguwa Sam yaki kallon gefen da Balaraba take, lokacin k’ankani me Martaba ya fahimci Sallau bashi da gaskiya,girgiza kai kawai yayi ya mayar da idonsa kan Sarki! Yace”Magajin Sarki ya labarin bunkicen da nasa kayi min kan wannan yarinyar dake zaune kusa da kai”

Cikin yanayin maganar sa ya ce”Allah ya baka nasara, a gafarce ni, nayi laifi saboda banzo na fad’a maka komai ba yau tsawon kwana biyu kenan, dama yau nakeso inzo in fad’a maka sai ga shi ka aiko,tuba nake ranka ya dad’e”
Galadima yace”me Martaba ya karb’i uzirin ka”

Moddibo ne ya kalleshi yana masa magiya da ido,dama kafin su futo sai da ya dunga lallab’ashi

Sarki! yayi gyaran murya a nutse yace”Allah ya taimake ka nayi bunkice sosai nagano wannan yarinyar bata da wani aibu yarinya ce me ladabi da biyayya da bin nagaba da ita,nayi bunkice sosai duk wani sharace-sharace da ake mata basu da tushe,anayi ne domin ganin tana futa kullum gurin sana’arta,wannan shine abunda na sani a game da ita,
Ya karasa maganar cikin nutsuwa.

Shiru na minti biyu me Martaba yayi gyaran murya hankali kwance yace” Nayi farin cikin jin wannan abu, wannan yarinyar tun kafin in ganta hankali na ya kwanta da ita,in sha Allahu tana tare damu ita da “yan uwanta, ni ne zan shige mata gaba,kan lamarinta, a yanzu yanzu zan d’aura mata aure da Yusuf Moddibo, saboda na yaba da nagartarsa gami da jajircewar sa kan lamarin ta, wannan shine hukuncin da na yanke”

“Alhamdulilahi-Alhamdulilahi, Abunda Moddibo yake ta fad’a kenan cikin zuciyarsa, Balaraba ma taji dad’in yadda abubuwa suka zo da sauk’i haka, duk wanda yake zaune a fadar yayi murna da wannan abu,in ka cire mutum biyu wato Sallau da Waziri Zayyanu,

Nan me Martaba ya umarci maga takarda da ya futa ya sanar a cikin gida,sannan ya tawo da goro da Alawa domin, cika al’k’awarin da ya d’auka.

Shiru fada tayi bayan futar maga takarda,kowa da abunda yake sak’awa cikin zuciyarsa,kawai sai sukaji muryar Waziri Zayyanu cikin fushi!yace” wannan hukunci da me Martaba ya yanke bai yi ba, domin ni ne nake da hakki a kan yaronan don haka ban amunce ya auri wannan yarinyar ba,in ko ya aureta zai had’u sa fushina!

Tofaaaaaa!

Fans kuna ina ne wa ya dace Balaraba ta aura, shin me zai biyo baya in me Martaba ya d’aura auran Moddibo da Balaraba, shin wane irin rikici ne zai faru kan hakan, yaya su Lantana zasuji jin cewar Balaraba tayi aure gidan sarauta, shine wanene mijin Balaraba???

SARKI! NE KO MODDIBO?
[05/08, 00:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????


We are here to educate,motivate and entertain aur readers


DIDEGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????67

Shiru fada tayi ana kallon kallo abunda Waziri ya fad’a ya girgiza jama’ar dake gurin. me Martaba bai tab’a yanke hukunci ba, a samu wani wanda zai ce be yi dai-dai ba, kowa yana jiran yaji abunda me Martaba zai ce, shiru yayi kawai yana jin damuwa da b’acin rai a zuciyarsa yau Waziri ya nuna masa cewar d’anshi Moddibo bashi da iko a kansa aure tunda ya riga ya yi niyyar d’aura shi a yanzu sai ya d’aura shi, saboda haka duk abunda Waziri yaga zaiyi yayi, yanzu yana sauraron dawowar maga takarda ne.

Mik’ewa Waziri yayi ya futa, ba tare da ya yiwa kowa sallama ba, me Martaba yaji ciwon abunda d’an uwansa yayi masa,amma sai yayi shiru kawai.

Mintuna goma da futar Waziri sai ga maga takarda nan ya dawo, yana tare da wani bawa a bayan shi, yana d’auke da d’aurin goro da kwalin alawa, Galadima ne ya matso ya kwance d’aurin goron da alawa, kansa a kasa yace”Allah ya taimake ka, Waziri tuba yake yayi abisa kuskure a gafarce shi”

Murmushi kawai me Martaba yayi ya kalli Sarki! dake zaune kanshi a k’asa yana jini b’acin rain abunda Waziri yayi wa mahaifin sa.

Kafin me Martaba yace wani abu Sarki! Ya fahimci abunda yake nufi, kamar ya sani kawai ya zura hannu cikin rigarsa ta ciki ya futo da kud’i zasu kai duba talatin ko sama da haka, mik’ewa Moddibo yayi ya rik’e a hannusa, kasa-kasa yace”ka rik’e a hannuka ana d’aurawa sai ka bata sadakin ta”

Moddibo ya k’arba fuskar sa d’auke da murmushi kana ganinsa kasan na farin ciki ne.

Kafin kace kwabo fada ta cika da mutane, nan me Martaba ya Umarci babban limami a fara d’aura aure.

Alhamdulilahi-Alhamdulilahi an d’aura auran Moddibo da Balaraba kan sadaki dubu arb’ain da biyu, nan maga takarda ya fara rabon alawa da goro me Martaba ya Umarci Moddibo ya d’auke Balaraba su futa, haka kuwa a kayi, suka futa,suka bar Sarki! suna ta gaishe-gaishe da mutane

Jiki a sanyaye Balaraba ta dunga tafiya har suka isa shashen Sarki! gabanta sai fad’uwa yake tana jin kamar a kwai wani abu da zai faru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button