GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Can fada kuwa komai yana tafiya dai-dai kana kallon Sallau kasan yana cikin wani mugun hali na d’imuwa yayi yunk’urin mik’ewa ya kasa saboda yadda yake jin jikinsa na rawa ji yake kamar kafarsa ba a jikin jikinsa take ba, nan me Martaba ya sallami kowa, mutanan da suka rage a ciki sune makusantan sa, sai Sallau da me gari Halilu da Walidi, kyautar ban girma me Martaba yayi wa Walidi, wanda tasa shi kusan sumewa a gurin ya dunga godiya, me Martaba yaja kunnen Sallau sosai, da sosai, sannan ya gargad’i me gari Halilu kan kar ya kuma aikata abu maka mancin haka, me gari Halilu ya bada hakuri kuma ya nemi afuwa, shi ko Sallau bud’ar bakinsa,sai yace”ranka ya dad’e maganar sauran yaran wato Sadiya da Usuman ina so abani su mu koma gida”
Sarki!! Ya d’ago da kansa cikin fushi! yace”Sadiya da Usuman zasu zauna gurin “yar uwarsu,kai ka tafi ka kad’ai”
Wani bafade ya kalli Sallau da jajayen idonsa yace”gyara kintsi dai!!! kayi na d’aya kayi na biyu kar ka sake kayi na uku,anan zan tub’e ka in zane maka jiki,ko zaka nunawa me Martaba abunda ya dace ne.”
Girgiza kai Sallau yayi jikinsa na kyarma! cikin tsawa wannan bafade yace”ka nemi afuwar gurin me Martaba”
Jiki na rawa Sallau yace”Allah shi gafarta maka ina neman afuwa”
Saura kad’an Walidi ya saki dariya saboda yadda ya ga jikin mahaifin nasa yana rawa, murmushi me Martaba yayi yace”Allah yayi mana afuwa baki d’aya, wato malam Sallau maganar wad’annan yaran naka Sadiya da Usuman kayi hakuri kabar su gurin “yar uwarsu kaji ko, duk lokacin da kukayi sha’awar ganinsu za’a kawo muku su har gida,idan kuna sha’awar zuwa gurin su k’ofa a bud’e take muna maraba da ku baki d’aya”
me gari Halilu yace”godiya yake ranka ya dad’e”
Ganin babu yadda zai yi ne yasa ya fara yak’en dole yana godiya ga me Martaba, amma in zaka tona zuciyarsa a lokacin tafi garwashi zafi da turiri.
Nan me Martaba ya bada Umarni a kaisu gida tare da kayayyakin abinci buhu-buhu mota guda a ka had’a musu na kayan masa rufi,Walidi kuwa in ya tuno da kyautarsa da akayi masa sai yaji kamar babu wanda ya fishi sa’a a rayuwa,gobe i yanzu yana cikin kasuwar sha tambaya yafara gudanar da kasuwancin sa.
Cikin tsananin b’acin rai! Waziri Zayyanu ya shiga b’angaran sa,sai a kayi sa’a duk “yayan shi maza na zaune a falo suna hira, nan suka ga shigowar mahaifin su hankalin sa a tashe, Khalifa ne yace” Allah yasa lafiya dai na ganka kana faman gumi!
Zama yayi cikin kujera yana cire rawanin dake nannad’e a kansa,yace”je ka kira min mahaifiyar ka”
Tafiya yayi kiranta, ya kalli sauran yaransa da kumfar baki yace” in dai nine na haife ku daga yau na rabaku da Moddibo har abada babu ni babu shi hakanan kuma babu ku babu shi”
Cikin rashin fahimta Ishak yace”ban fahimci me kake nufi ba Baba”
Zuwan mahaifiyar tasu ne ya dakatar da maganar da yake tazo ta zauna kusa da mijin nata,tana kallon fuskarsa tasan lallai yau an tab’oshi”
“Lafiya ranka ya dad’e”?
Ta fad’a cikin sigar tambaya.
Waziri yace” zaki ce min baki san abunda yake faruwa bane? kun had’a kai da d’anki kun munafurce ni, yaje ya d’auko yarinya da suka gama lalacewa da ita a waje ya kawo wa wannan mak’iyin nawa ya d’aura masa aure da ita”
“Duk maganar da kakeyi ban fahimce ka ba,domin kuwa ni ban San abunda yake faruwa ba”
Girgiza kai yayi kawai ya umarci d’aya daga cikin yaran dake zaune a gurin yaje ya kira Moddibo.
Hankalin kowa ya tashi a gurin saboda sun san halin mahaifin nasu bai iya b’acin rai ba.
Mintuna goma tsakani Moddibo suka shigo tare da Ishak d’an uwansa
Ko zama Waziri Zayyanu bai bari yayi ba,yace”Umarni na ne ni ne nasa a kira ka, saboda dalilai masu k’arfi,yanzu-yanzu nake so ka furta cewar ka saki wannan yarinyar da kasa aka d’aura maka aure da ita,idan kuma kak’i ni yanzu zan saki taka Uwar,saboda haka zab’i ya rage naka.”
Muje zuwa
Comment Vote and Share
[05/08, 20:08] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYARNana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba
ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????
We are here to educate,motivate and entertain aur readers
DIDEGATED
TORAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????68
Dukaninsu sun furgita da jin furucin da mahaifin nasu yayi, ita kanta mahaifiyar tasu ta girgiza da furucin da mijin nata yayi,kuma tafi kowa sanin halinsa zai iya aikata duk abunda ya fad’a.
Modibbo ya shiga, tsaka me wuya bai tab’a tsammanin hukuncin da mahaifin nasa zai yanke ba kenan,iya tunanin sa yana ganin zaiyi fushi dashi daga baya ya sakko shi kuma sai ya nemi afuwar sa, tabbas Uwa-Uwa ce, babu ta yadda za’ayi ta sanadiyar sa ya rushe auran da aka d’aurashi sama da shekara talatin da wani abu,dole duk son da yake wa Balaraba ya rabu da ita ko da hakan zai yi sanadiyar rasa rayuwarsa, a kan mahaifiyar sa babu abunda ba zai iya ba.
Khalifa ne mara kunya sosai ya cikinsu yace”Mu baza ka jawo mana b’acin rai!ba a cikin gida saboda haka kabi umarnin da a ka baka, idan ba haka ba zamu b’ata maka rai kuma zamu hana matar taka daka aura jin dad’in duniya,a kan mahaifiyar mu,babu abunda baza muyi ba”
Jin furcin da Khalifa yayi yasa Waziri umartar sa da yaje ya d’auko takarda sa biro, aikuwa da sauri ya tafi, ita kuwa Hajiya Kattime tana zaune tana kallon ikon Allah bakinta ya mutu, takasa fahimtar komai, a wannan badak’alar da take faruwa.
Khalifa ya dawo hannusa rik’e da farar takarda da biro ya zo ya mik’awa Moddibo, guda d’aya, d’ayar kuma yaje ya kai wa mahaifin nasu ganin Waziri ya d’ora biro jikin takkada yasa Moddibo saurin dakatar dashi, da hannu jikinshi na kyarma! yayin da gumi yake zuba a jikinsa, ya d’ora biyu jikin farar takarda yayi rubutu kayi biyu,kamar haka.
Ni Yusuf Moddibo na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki d’aya kacal, kan wani dalili guda d’aya, ina fatan Allah ya had’amu da ita a aljanar Firdausi
Yana gama rubutuwa ya ninke takadar, zuciyarsa tana wani bugawa fatt!!fatt!fatt! Waziri Zaiyyanu ya mik’a masa hannu yana nufin ya bashi takardar, a hankali ya karasa inda yake zaune ya mik’a masa, bud’e takardar yayi ya karanta ya mayar ya ninke ta ya aje ta gefe,wani takarda ya kara cirowa ya mik’awa Moddibo cikin bada Umarni yace”Saki uku zaka rubuta mata,saboda nasan halin wancan mutsiyacin zai iya turasasa ka ka mayar da ita,don haka ban yarda da saki d’aya ba”
Cikin tsantsar b’acin rai Hajiya Kattime tace”Wannan abunda kake tsantsar jahilci ne da son kai, Allah da kansa shi ya hallici saki,kuma ya umarci da ayi shi,amma kuma baya son ayi din,saboda haka tunda ka tursashi ya rubuta saki d’aya saboda son zuciyar ka to ka kyaleshi haka, ba lallai sai an saki mace saki uku ba take sakuwa,saki d’aya ma ya hallata”
Cikin tsawa Waziri yace”Zakayi abunda na saka ko sai ka gama jin hudubar da mahaifiyar taka take maka”
Ganin Moddibo ya tsaya yayi shiru da takarda a hannu yasa Waziri ya d’ora biron dake hannusa a jikin takarda ya fara rubutu.
Moddibo ya rik’e hannunsa jikinsa zafi rad’au! muryasa a shak’e yace”Baba Waziri ka gafarce ni, idan nayi maka,laifi, ni Yusuf Moddibo na saki Matata Balaraba saki uku”
“Innalilahi wa inna ilaihi rajiun”
Shine abunda Kattime take fad’a zuciyarta kamar tayi bunduga tarasa wane irin bakar zuciya ne da mijin nata.
Mik’a masa takardar yayi a karo na uku yace”rubuta min da hannun ka”
Ganin babu abunda yayi saura yasa Moddibo ya rubuta ya mik’a masa, ya bud’e ya karanta tsaf, cikin bada Umarni yace”Ka tafi da kanka kaje ka kaiwa wanda ya d’aura maka auran” Moddibo ya karb’i takardar ya kama hanya, yana tafiya yana had’a hanya jiri yana kwasar sa,Allah yasa bangaran babu ma’aikata sosai, sai da ya futa harabar gidan sarautar sannan ya dai-dai ta nutsuwar shi,amma duk da haka duk Wanda ya kalleshi a lokacin yasan yana cikin tsananin damuwa, haka ya isa fada, lokacin ana shirye-shirye kiran sallaar magariba
me Martaba ya futo kenan domin shiga gida suka ci karo da Moddibo, yana kallonsa ya gane da akwai matsala, kafin yace komai Moddibo ya mik’a masa takardar hannunsa, da sauri maga takarda ya karb’a ya bud’e ya fara karantawa kamar haka.