GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani hawayen ya kuma zubo mata,ba tare data goge ba tace”Yusuf inajin wani abu a zuciyarta a game da wannan al’amari, don Allah ka nemi afuwa gurin Baba Waziri, kan dukkanin abunda yazo maka dashi”
Damk’e hannunta yayi sosai cikin nasa, da murmushi a fuskarsa yace” Insha Allahu komai zai zo da sauki, yanzu abunda zakiyi shine, kici abunci ki bawa su Sadiya suci su kwanta, ke kuma sai kiyi alwala kiyi sallah raka’a biyu ta nafila domin ki nema mana zab’i na Allah, yanzu zanje in dawo muyi hira me dad’i irin ta Ango da Amarya”
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta.Ya mik’e tsaye da murmushi a fuskarsa,ya kamo fuskarta ya manna mata kiss, rufe ido Balaraba tayi cikin jin kunya, fuskar ya saki, ya nufi hanyar futa yana waiwayenta, har ya bud’e kofa zai futa,ya tsaya yace”Gimbiya sai na dawo”
Bud’e ido tayi da sauri tana kallon kofar futa ko rigarsa bata gani ba,ya fuce.
Jiki a sanyaye ta mik’e ta nufi toilet ta dauro alwala tazo ta shimfid’a dadduma ta tada sallah kamar yadda Moddibo ya umarce ta.
Sosai ta yi addu’oi tana kuka tana rokan Allah, bacci ne ya ci k’arfinta nan kan daddumar ta b’ingire bacci me nauyi ya d’auke ta,ba tare da taci komai ba,hakanan su Sadiya basu ci komai ba suma bacci ya kwashe su,
Humm baccin asara kenan baccin da Balaraba bata tab’a irinsa ba, ko sallahr asubah ba tayi ba, a tak’aice dai Balaraba bata da labarin rasuwar Moddibo domin bata tashi farkawa ba sai k’arfe bakwai da kwata na safe.
[08/08, 04:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYARNana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba
ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????
We are here to educate,motivate and entertain aur readers
DIDEGATED
TORAHAMA ALIYU
BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM
????70
Bugun k’ofar Sarki! ne ya tashe ta,ta mik’e zaune jikinta duk a mace,da k’yar ta mik’e tsaye ta nufi, K’ofa domin bud’ewa duk a tunaninta ko Moddobo ne, tayi mamakin baccin da ya kwashe ta,me cike da tarin mafarkai marasa kyau.Bud’e kofar tayi tana koma wa ciki ba tare da ta kalli me shigowa ba, shiga yayi d’akin sosai yana bin su da kallo daga ita har su Sadiya
Sai da ta zauna gefen gado tana kallon sa, gabanta ne ya fad’i lokacin da suka had’a ido da Sarki! Mutum me fararan idanu taga k’wayar idonsa ta rine tayi jajazur!
K’asa tayi da kanta,gabanta na dukan uku-uku! A nutse yace”Kinyi sallah”
Cikin wani irin yanayi ta kalleshi tana girgiza kai.
Alamun batai ba.
Ajiyar zuciya ya sauke k’asa-k’asa yace” Kiyi sallama ki sauko k’asa ki same ni, ina jiran ki”
Cikin k’arfin hali tace”Ina Moddibo”?
Yana k’okarin futa daga d’akin yace”Yana k’asa,zaki sauko ki same shi”
Futa yayi ba tare da ya saurari abunda zata ce ba.
Mamaki take me ya kawo shi d’akin ina Moddibo yake?,shine ya kamata ya shigo gurin ta ba Sarki! ba,bayan haka kuma taga kamar a kwai alamun rashin nutsuwa a tattare da Sarki!
Sauri-sauri tayi alwala ta futo ta tada sallah.Bayan ta idar tai addu’oi yanda ya sauwak’a ta mik’e har zata futa ta dawo tana duba su Usuman dake ta faman bacci, Ajiyar zuciya tayi ta tashi Sadiya domin tayi sallah,sai da taga Sadiya ta shiga toilet sannan ta futa daga d’akin.
Yana tsaye tsakiyar falon hannunshi goye a bayansa hankalinsa na sama ita kawai yake jira ta sauko, had’a ido sukayi a karo na biyu lokacin da take saukowa dukkaninsu suka d’auke kai,sai kace wasu surukai, bai jira sun jera ba, ya kama hanya zai futa, ita kuma sai ta tsaya a tana kallon sa,yace tazo kasa ta same shi zai futa kuma ina Moddibo yake?
Mutumin dake take masa baya ne yace”Allah ya kara miki lafiya, ai bayansa zaki ni, me Martaba ne yake neman ki”
Jin abunda yace yasa fad’uwar gabanta ya tsananta, babu kuzari tabi bayansa, kanta a k’asa
Tayi mamaki da ta dunga ganin mutane a harabar gidan kuma kowa ta kalli fuskarsa babu walwala gashi wasu daga ciki sai kallonta da k’yar dai suka isa fada, Sarki!ya tub’e takalmin sa ya shiga,ita kam tsayuwa tayi bakin Kofa sai da akai mata iso sannan,ita babban abunda ya d’aga mata hankali shine dandazon mutanan da ta gani shiya furgitata.
Me Martaba ne kad’ai cikin fadar sai gawar Moddibo dake cikin makara a killace, Balaraba na sanya k’afarta ciki taci karo da makara, fad’uwa ta kusa yi saboda tsorata da tayi,bango ta dafa da hannunta miyau din bakinta ya bushe tass!tamkar ba’a tab’a hallitarsa ba,a bakinta har wani shak’ewa take, zubewa tayi bakin k’ofa, tana shashsheka,shikkenan mafarkin da tayi kan Moddibo ya tabbata babu tamtama wannan Moddibo ne cikin makara,kamar yadda ta ganshi jiya cikin baccin ta, kamar zautacciya ta k’arasa kusa da Moddibo da rarrafe,ta sanya hannu ta d’aga mayafin da aka lullub’e masa fuska dashi, Silalewa tayi ta fad’i a gurin ta suma.
Da sauri Sarki!ya mik’e yaje ya janye makarar,cikin tashin hankali yake tunanin yaya zai da ita
Me Martaba,ne ya mik’o masa ruwa irin na gora,ragowa ne wanda ya sha ya rage yana aje a gefe, jikinshi na kyarma!ya karb’a ya gumtsa a bakinsa ya fesa mata a fuska, ta bud’e idonta zumbur zata mik’e a gigice!Sarki!ya dafe,hannunta dake rawa,karr!-karr! muryasa bata futa sosai ya kalli mahaifin nasa yace”Allah ya taimake ka, ya kamata a futa da Moddibo domin wannan kwata-kwata babu abunda zata iya yi masa na addu’a tunda bata cikin hayyacin ta,ina ganin zan shiga da ita gida gurin Mama dole sai tasa ido a kanta zata iya futa bata sani ba”
Me Martaba yace”Wannan shawarar taka itace shawara, kai ta cikin gida, idan ka shiga kai kiro min Hajiya Kattime da Mahaifiyar ka, su futo suyi bankwana da Yusufu domin za’akaishi gidansa na gaskiya”
“In sha Allah”
Sarki ya fad’a lokacin da yake mik’ewa yana rik’e hannun Balaraba da ta zama kamar wata zautacciya, yayi da ya sanin zuwan ta gurin, mik’ewa tayi tsaye kafafunta na rawa, sai kace me koyan tafiya,haka ta kuma komawa ta zube gurin,Suma ta k’ara yi a karo na biyu,wannan karon hankalin Sarki!ya tashi,sosai da sauri ya d’auko gorar ruwan a karo na biyu,ya gumtsa a bakinsa ya fesawa fuskarta babu alamun zata farfad’o kuma fesa mata yayi a karo na uku na shiru, mik’ewa yayi har yana kusa tuntub’e da k’afarta, hanyar futa ya nufa, cikin sauri, Shamaki na tsaye bakin k’ofar shigowa yaga futowar Sarki! da sauri yazo ya rissina Sarki! yace” Yanzu ka umarci jama’ar dake bakin hanya su matsa zan futo ya zuwa shashen Mama Fulani”
Shamaki yace”Angama ranka ya dad’e”
Minti uku Shamaki ya dawo yace”ranka ya dad’e zaka iya futowa”
Hannu kawai ya d’aga masa ya koma ciki,
Balabara dake kwance ya hau tattaro wa da niyar d’aukar ta me Martaba na kallonsa, ya ciccib’eta cikin jarumta ya nufi k’ofar futa da ita kana ganinsa kasan yana cikin tsantsar damuwa dan dai shi mutum ne me tawakkali da mik’ewa Allah lamarinsa, cikin nutsuwa yake tafiya da ita,tana hannunsa yayi mata d’aukar jarirai, duk tsayin tazarar dake tsakanin fada da b’angaran Mama Fulani,bai damu ba, shi ko ya gaji ji yake maka tamkar yarinya k’arama ya d’auka,duk da cewar Balaraba tana da girman jiki kuma bata da rama, a jikinta.
Yana tafiya yana kallon fuskarta, wani irin tausayinta na ratsa masa zuciya, haka ya isa shashen mahaifiyar tashi, mutan dake gurin sam basu dame shi ba, burinsa kawai ya kai Balaraba gurin Mamanshi domin yana jin tsoron amanar Moddibo ta samu matsala, ganin shine yasa bayi dake shashen suka dunga sunkuyar da kansu har sai ya wuce sannan zasu d’ago Kansu