GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani k’aramin falo ya wanda zai sada ka da babban falon Mama Fulani,nan ya tarar dasu Mama Fulani Hajiya Kattime Halisa, Hajiya Madabo mahaifiyar Halisa Gimbiya Azima, domin itama tun yammacin jiya tazo sai ta riski abunda yake faruwa, duk suna zazzaune kowa da carbi a hannu,idanunsu sunyi jajazur! bai saurare su ba ya wuce da Balaraba ciki, har bedroom d’in Mama Fulani, kwantar da ita yayi a makeken gadonta,ya nufi k’aramin firji dake d’akin,ruwa ya ciro me sanyi sosai ya bud’e ya fara tuttulawa a jikin Balaraba, wanda yayi dai-dai da shigowar Mama Fulani cikin tashin hankali,tace “Me yasa me ta”?

” Suma take Mama wannan yarinyar amanar Moddibo ne, Mama ki taimaka min kar tabi bayansa”
Yafad’a tamkar wanda baya cikin hanlalinsa, lallai na yarda da ake cewa komai girman mutum a gaban iyayensa Yaro ne.Rarrashin sa take ganin yadda ya tada hankalinsa, ragowar ruwan dake hannunsa ta karb’a ta yayya mata, cikin sa’a Balaraba ta bud’e ido tana sakin wata ajiyar zuciya,, kalle-kalle kawai take yayin da take jin wani irin ciwon kai!
Ajiyar zuciya ya sauke ganin ta dawo hayyacinta yayi saurin futa daga d’akin don kar ta ankara dashi a gurin, yana Futa k’aramin falon ya fad’a musu umarnin da me Martaba ya bayar, mik’ewa sukayi suka futo domin zuwa fada, tsakanin Halisa da Azima harara ce ke had’asu, Halisa wani bak’in kishi ne yake damun ta ganin yadda Habibinta ya rungomo Balaraba a jikinsa,sai kace Wanda ya dauko matarsa, itama Azima nata b’angaran haka abun yake domin kishin da taji lokacin da taganshi da Balaraba har yafi na Azima, kawai daurewa take,dan dai gidan mutuwa tazo.

Gaskiya ina jin dad’in comment d’inku????

ANATARE IYA WUYA
❤❤❤❤❤❤❤❤

Ina taya ku jimami na rashin Moddibo Allah ya bamu hakurin jure rashin sa
[09/08, 17:22] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????


We are here to educate,motivate and entertain aur readers


DIDEGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM

????71

Cikin dauri Hajiya Kattime tsuguna gaban gawar Moddibo tayi masa addu’a sosai gami da nema masa afuwa gurin Allah,A fili tace”Yusuf ni mahaifiyar ka na yafe maka dukkanin abunda kayi min wanda na sani da Wanda ban sani ba,ina fatan Allah ya had’amu a aljanar firdausi”
“Ameen” Ameen”Abunda mutane ke cewa kenan.me Martaba ya aika ai kiran Waziri tun d’azu yak’i zuwa, haka me Martaba ya bada Umarnin d’aukar Moddibo a kai shi gidansa na gaskiya, Sarki!ne ya d’ora makarar gefen kafad’arsa Galadima a gefe sauran mutane suka taya su rikewa a ka futa da Moddibo futa ta har abada, sai bayan futa dashi ne zuciyar Hajiya Kattime ta karye sai ga hawaye na biyo kuncinta,nan jama’ar dake gurin suka dunga tausar zuciyarta,da k’yar dai suka koma Shashen Mama Fulani, inda take zaune gefen Balaraba wacce take ta rusa kuka kamar ranta zai futa, magana take so tayi amma takasa saboda yanda muryarta take sark’ewa, tsabar kukan da take.
Hajiya Kattime ce ta shigo d’akin saboda jikinta na bata wannan yarinyar da Sarki!ya shigo da ita, itace Balaraba.

Kallonta Mama Fulani take har ta k’araso ta zauna gefen gado, tace” Ina kyautata zaton wannan itace yarinyar da ake rigima a kanta ko”?

Mama Fulani tace”Itace kin ganta nan kuka take tak’i jin rarrashi”

Cikin dauriya Hajiya Kattime ta matsa kusa da Balaraba ta rik’e mata hannuwa cikin tausayi da taushin harshe tace”Dole kiyi kukan rashin Moddibo, kiyi hakuri ki barwa Allah ikon shi, nice na haifi Moddibo ina ganin babu wanda zai kai ni jin zafin mutuwarsa, irin wannan ta farar d’aya, to da yake nasan kowa na hakane na hak’ura na barwa Allah mutuwa rigar kowa ce dole inda ya tafi zaki tafi zan tafi haka Mama Fulani zata tafi, saboda haka ina rokon ki ki yi shiru don Allah in ci Albarkacin Moddibo bana son ki jawowa kanki wata lalurar yanzu ke din kece zan dunga kallo a matsayin Yusuf d’ana, kiyi hakuri kiyi masa addu’a domin ita yake bukata a gurin mu”

Cikin kuka Balaraba tace”Mama me yasa Yusuf zai yi min haka? bani da kowa sai shi,Yusuf shine gatana Allah ne gatana,gashi ya tafi ya barni lokaci guda,
Innalilahi wa’inna ilahi rajiun Ya Allah ka kawo min a gaji”
Ta k’arashe maganar tana jin tamkar numfashinta zai d’auke.

Wasu hawaye Mama Fulani ta goge na tausayin Balaraba sosai yarinyar ta bata tausayi.

Hajiya Kattime tace”Kar kiyi sab’o kinji ko, lokacinsa ne yayi dole ya amsa kiran da a kai masa”

Mama Fulani tace”Ki daina kukan rashin iyaye kinji ko mu zamu zame miki uwa da uba Insha Allah ba zaki maraici ba”

Cikin kuka da damuwa Balaraba tace”Nagode sosai kamar yadda kika fad’a Mama nima zan muku biyyaya dai-dai gwargwado tamkar Ku ne kuka haife ni”

Hajiya Kattime tace”Yanzu ina “yan uwan naki”?

Sai sannan ta tuna dasu Sadiya,k’okarin saukowa take daga gadon cikin faduwar gaba, tabarsu su kad’ai bata san wane hali suke ciki ba.

Hajiya Kattime ta rik’eta tace” Bari aje a d’auko su,kinji ko kar ki futa cikin wannan halin”

Muryar ta na karkarwa tace”Suna can Shashen Sarki!nan muka kwana”

“Shikkenan bari in tura Mariya taje ta dauko su ki kwantar da hankalin ki”
Hajiya Kattime ta mike ta futa.

Mama Kuwa k’ara kwantar wa da Balaraba hankali take,tana d’an yi mata tambayoyi cikin hikima,irin tasu ta manya,nan ta fuskanci yaran sun sha wahalar rayuwa kuma sun taso cikin maraici, lokaci guda taji sun shiga zuciyarta zata iyayin komai a Kansu.

Har akaje a ka dawo Waziri bai futo ba,yana shashen sa yana sak’e-sak’e mugun abu a zuciyarsa.

Cikin “yan Uwan Moddibo kuwa babu wanda ya futo aka zauna dashi sai Ishak duk shauran basu fito ba, suna can suna goyan bayan mahaifinsu,Wanda har aka share makoki babu shi babu dalilinsa.

Yau kwana takwas kenan da rasuwar Moddibo me Martaba yayi shirin zaman Fada, Hajiya Kulu me d’akin kudu tana kusa dashi, da yake yana shashenta, k’orafi kawai take masa na shashanci, duk wannan abunda take masa bashi ne a gabansa yana mamakin da har aka share makoki bata tab’a bud’ar baki tayi masa ta’aziyyar rasuwar Moddibo ba. Gyaran murya yayi yace” Duk wannan k’orafin naki bai karb’u ba a gurina saboda ke babbar me laifi ce,kinayi kamar baki San abunda yake faruwa ba a gidan, ke indai ba Matsalar “yayan ki bace babu matsalar da ta dame Ki, kina a matsayin matata Uwar ” yayana na farko, kin tsaya kina rashin hankali, ya kamata ace kin nutsu kin San abunda kikeyi a rayuwar ki,saboda haka kar ki k’ara kawo min maganar Na’ja’atu nan saboda ban ga dalilin da zai sa kice dole in d’ebi kud’i masu nauyi har million uku in bata da sunan zata ja jari, Wanda nasan k’arya take, babu wani jari da zata ja zuwa zatayi ta b’arnatar dasu, ke da ita kuje ku sanja tuni”
Ya k’arasa maganar yana k’okarin mik’ewa da niyar futa.
Mik’ewa tayi itama da sauri tace”Allah ya ja zamanin Sarki, a duba maganar nan tawa, tunda kayiwa Na’ajatu aure bata tab’a zuwa tazo ta nemi alfarma a gurin ka ba sai wannan lokacin,kullum kana nuna min “yayana kamar ba kaine ka haifesu ba”

Wannan magana da Hajiya Kulu ta fad’a ta d’agawa me Martaba hankali,sosai tsayawa yayi yana kallonta da ransa a b’ace yace”Kar ki k’ara yi min magana makamanciyar wannan, duk sanda kika k’ara ranki sai ya b’aci, sosai daka ke har “yayan naki da kike ganin kamar bani ne na haife su ba”
Sunkuyar da kai tayi ranta yana suya sosai tace”Allah ya huci zuciyarka” Shiru yayi mata na minti biyu ya cigaba da cewa”Duk cikin “yayan naki wacece tazo tai min gaisuwar Moddibo, ko da yake ai ban isa ba,tunda bani da Iko dake dasu,sai abunda kika tsara musu shi zasuyi ai kun kyauta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button