GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin sauri tace”Allah ya gafarta maka, duk babu wanda be zo ba a cikinsu,duk sunje sun yiwa Waziri gaisuwa,ko wacce ta tafi gidanta gudun fad’an ka”
“Saboda haka kika tsara musu cewar Waziri ne Uban Yusuf bani bane shiyasa bani da matsayin da zasu zo su gaishe ni balle suyi min gaisuwa, sun kyauta”
Ya karashe maganar cikin b’acin rai!
“Allah ya huci zuciyar ka”
Tafad’a muryarta na rawa ganin kwab’arta tana so tayi ruwa.
Har ya wuce zai tafi yaja ya tsaya yana kallonta yace”Nasan duk akan wa kike wannan abun wanda har kike nema ki sheganta min “yayana, duk cikin ” yayan da na haifa babu wanda na ware nace shi nafi so kowa ina sonshi tunda nine na haife shi, Almansur Sarki!shine d’ana namiji guda shine kuma magaji na insha Allahu,saboda haka in zaki kwantar da hankalin ki ki kwantar da hankalin ki”
Yana gama fad’ar maganar shi ya futa a nutse.
Hajiya Kulu zaman durshen tayi kan kilishin dake malale tsakiyar d’akin wasu zafafen hawaye yana zubo mata, wai me yasa bata haifi d’a namiji bane?wai me yasa duk “yayanta suka zamo ” yaya mata,? Ita kad’ai take tambayar zuciyarta, yanzu ta tabbata kenan Mama Fulani tayi nasara a kanta,tunda har ta haifi d’a namiji kuma takasa nasara akansa da ita kanta Mama Fulani, wata wawar ajiyar zuciya ta sauke ta mik’e zumbur!tana surutai falonta ta futa inda Hadiman ta ke zaune,suna jiran futowar ta, daga bakin Kofa ta tsaya ta kira Jakadiyarta me suna Ladi, suka shiga d’aki tare, wani irin zama tayi kan wani tuntu tace”Ladi duk wani shiru da k’uli da mukayi shekara da shekaru ina ganin duk sun karye,dole ne yanzu mu sake sabon lale,me zafi!domin inaji ina gani zamu zama “yan kallo a gidan nan dani da ” yayana”
Muje zuwa
Comment Vote and Share
[13/08, 19:27] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYARNana KhadijaYaro Da kud'iGimbiya Balaraba
ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????
We are here to educate,motivate and entertain aur readers
DIDEGATED
TORAHAMA ALIYU
Alhamdulilahi, Ina taya d’aukacin alummar musulmi murna za gayowar wannan wata me albarka,ina fatan Allah ya nuna mana na shekarun gaba, ubangiji Allah ya shafe mana zunuban mu
????????♂????????♂BANI BANE????????♂????????♂
(Zargina ake)
~BY: MAMA QUEEN~
????DA BAZAR MU WRITER’S ASSOCIATION????
NOTE
Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark’akiya,rikitarwa dad’i sauransu…..
_Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_
Whatsap numbar
07061553385
Karku bari abaku labari
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????72
Jakadiya Ladi ta gyara zama sosai gaban uwar gijiyarta cikin sigar munafurci da iya kitifi tace”Allah ya taimaki uwar d’akina,dama abunda nake taso ki gane kin kasa fahimta,ai tuntuni ni na riga nasan abunda kikayi ya daina tasiri kan me Martaba,amma yanzu ga shawara”
Gyara zama Kulu tayi tace”Ina sauraranki tabbas nasan shawarar ki me kyau ce”
K’asa-k’asa Ladi tace”Me zai hana yanzu mu dawo kan shi d’an nasa wanda ya k’wallafawa rai,tunda dai,asiri baya cin mahaifiyat tasa kuma baya cin me Martaba, ina ganin haka shine abunda ya dace muyi”
Kulu ta sauke ajiyar zuciya tace “Wannan shawarar taki itace abunyi, ni in san samu ne ma dukaninsu inga basa motsi a duniyar nan,saboda basu da wani amfani”
Jakadiya Ladi tayi wani munafukin murmushi tace”Wannan aiki naki da kika d’auko me girma ne uwar d’akina,amma duk bazai gagara ba, a kwai wani d’an bori dake can lakwaja,shi zanje in d’auko zai yi miki aiki sosai,amma gaskiya dole za’a bawa aljanunsa me k’afa biyu sannan aiki zai ci”
Cikin gadara Kulu tace”Ko me k’afa hud’u suke so za’a nemo abashi indai bukata zata biya”
Ladi tace”Allah ya taimake ki kin san me ake nufi da me k’afa biyu kuwa”
Girgiza kai Kulu tayi cikin izgili!
Jakadija Ladi tace”Me k’afa biyu yana nufin mutum kamar ni da ke”
Babu wata fargaba Kulu tace”Ai shine nace miki ko k’afa hud’u suka nema ni zan basu domin buk’ata ta biya”
Ladi tace”Allah ya taimake ki nasan zaki iya ai,gobe idan Allah ya kaimu zan tafi in zo miki dashi, saboda haka sai a ta nadar masa masauki”
Kulu tace”Babu damuwa duk wannan tunda a kwai d’akuna nan b’angaran yanzu babban k’alubalen shine yadda za’ayi ya shigo gidan”
“Ranki ya dad’e zan bashi tufafi irin na hadimai na gidan nan sai ya sanya kawai in ya shigo su saje”
“Yawwa wannan shawarar taki tayi”
Kulu tafad’a tana gyara zamanta.
Nan suka zauna suna kullu yadda abun zai kasance .
Lokacin da me Martaba ya shiga fada ta cika sosai abun mamaki Sarki! Ya gani zaune gefen Galadima yaji dad’i sosai d’aya gefen ya kalla yana laluben Waziri babu shi babu Alamarsa.
[14/08, 14:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYARNana KhadijaYaro Da kud'iGimbiya Balaraba
ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????
We are here to educate,motivate and entertain aur readers
DIDEGATED
TORAHAMA ALIYU
????????♂????????♂BANI BANE????????♂????????♂
(Zargina ake)
~BY: MAMA QUEEN~
????DA BAZAR MU WRITER’S ASSOCIATION????
NOTE
Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark’akiya,rikitarwa dad’i sauransu…..
_Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_
Whatsap numbar
07061553385
Karku bari abaku labari
BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????73
Zama yayi kan kujerarsa, suka fara gaisawa da jama’ar dake zaune a fadar,bayan angama gaishe-gaishen ne, me Martaba ya umarci jakada ya je ya kira Waziri,cikin sauri ya tafi, wajan minti goma sai gashi ya dawo,ya zube gaban me Martaba kansa a sunkuye yana jin nauyin fad’a masa abunda Waziri yace”Sai da ya nisa tukkuna yace”Allah ya taimake ka yace”Ace maka bazai zo ba”
Shiru na minti goma me Martaba be ce komai ba, kawai a kafara gudanar da al’amuran da suka dace, kwata-kwata Sarki! baya jin dad’in zaman fadar saboda b’acin rai da damuwa da yake ciki,gashi ya fuskanci mahaifin nasa ma yana cikin damuwa ko ga yanayin fuskarsa ma,ta nuna alamu, haka dai ya d’aure
har lokacin sallah azuhar yayi kowa ya mik’e domin yin sallah, tare suka fito daga massalaci da me Martaba, kai tsaye Shashen Mama Fulani suka nufa, suna tattauna,wasu muhimin abu da ya shafesu.
Mama Fulani na zaune a farlo ita da Jakadiya Shafa’atu, Sarkin k’ofa ne ya shigo ya sanar mata da shigowar me Martaba, kafin kace kwabo bayin dake gurin kowa yayi nasa guri,har Jakadiya Shafa’atu.
A nutse suka shigo Mama Fulani ta gyara masa gurin zama tanai masa barka da shigowa zama yayi sosai da murmushi a fuskarsa suka gaisa,duk b’acin ran da yake ciki idan yazo gareta sai yaji wata sa’ida a ransa.
Sarki!ya gaida mahaifiyar tasa a nutse, tace”Kai kuma sai yau ka shigo ko, kazo ka aje amanar taka baka zuwa dubata haka ake rik’e amana”
Sosa kai yayi irin na sabo yace”Afuwa Mama ni kaina bana cikin nutsuwa bani da lafiya”
Me Martaba yace”Dole ne kayi Magajin Sarki wannan rayuwar bata da tabbas babu komai a cikinta sai rud’u da tashin hankali”
Sarki!ya sauke ajiyar zuciya yace”Allah ka jik’an Moddibo”
Tare suka amsa da “Ameen”
Mik’ewa yayi yaje ya kwanta kan wata katuwar Sofa, ya lumshe idonsa wani irin bacci yake ji.



