GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Iya ta janye Balaraba ta kai ta dakinta tana rarrashi tace”ko da yaushe ina fada miki ki daina Daka ta tasu Mabaruka su ba hankali garesu ba gashi yau a cikin farin ciki kike kinyi saukar Alku’ani mai girma Amma zaki bata wayonki Dan Allah ki daina kulasu.
Cikin kuka tace”iya kinajin zagin da suke min fa wai mai Na tsarewa Uwa ita da yaranta suka tsane ni ,nifa basa bani ci basa bani sha komai bi nakewa kaina ni nake fita in nema in ciyar da kaina da kannena to gaskiya nagaji zan siyar da gado Na kawai in bar musu gidan gwara inje in kama haya sai yafi min”
“Aa Balaraba kina nufin zaman kanki zakiyi bazai yihuba dama yaya Lafiyar kura kullum cikin yi miki sharri suke duk Wanda yaji cewar kin gama daki shikkenan sai zancensu ya tabbata ,ki kara hakuri kinji ko kwana nawane zaki yi Aurenki .
“Aa Iya ki kyaleni kawai “tafada tana share hawaye.
Iya tace”Aiko bazan kyaleki ba Balaraba yin hakan yana nuna cewar cin Amanar Dan Uwana Ayuba ,Sam baicancanci haka ba bayan haka kuma zumunchi bai CE haka ba
Share hawaye tayi ta kalli su Sadiya da shamsu Wanda suke zaune sun zuba mata ido suma suna share hawaye,tace “kunci Abinci”?
Girgiza kai sukai Alamun A’a.
Mikewa tayi ta karbi mukullin dakinta gurin iya tace”Ku taso Ku je Ku siyo indomee sai in dafa muku kafin in daura girki”
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????
08089965176
[04/05, 03:04] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????writting by
Binta Umar
MAMAN ABDUL WAHABU
~MRS AHAMAD GWADABE~
????10
Dakinsu Na gado ,ta bude musu ,suka shiga ,tana jin su Mabaruka da Shamsiyya ,sai zaginta sukeyi har yanzu ,sai tayi musu banza,
Tafito da kudi gudar Dari biyar Sabuwa dal! Tabawa Sadiya ,dake tafi Isyaku ,wayo ,tace maza taje ta siyo musu indome guda hudu ,sai ta dafa musu kafin ta Dora musu Abincin dare.
Cikin Farin ciki Sadiya ta kar6a ,ta tafi kantin Abbah ,dake bakin layinsu siyowa Sai Murna takeyi dake yarinyar ,tana son. Indomee sosai ,shiyasa kullum said tayiwa Aunty tasu Addu’a in tayi Sallah,sabida duk Abinda suke Nema tana musu .
wannan kenan
ASALIN LABARIN
Malam Tanko Makeri
Shine Ai nihin sunasa ,Wanda jama’a suke kuranshi dashi ,Amma A salin sunansa dayyabu ” to tun yana yaro Mahaifinshi ya sanya masa Tanko kasancewar sunan Mahaifinshi ne dashi
Shiyasa sunan ya buya idan ba Tanko Makeri kace ba babu Wanda zai gane.
Mutum ne shi Wanda Allah yayi masa baiwa da Fasa ta qere qere duk Abinda ya kalla sau daya to in sha Allahu nan take zai qera makashi ,tamkar daga kamfani
Shi kadai Mahaifinshi ya haifa ya koma ga Allah.
Shi kuma tun tasowarsa mutum ne mai Auri saki ,Matarshi ta Farko Lantana itace Uwarsu Kawu Sallau da Kawu Maman ,Matarshi ta biyu “yayanta duk mata ne su biyar ,haka ta zubesu gaban Lantana ,tayi tafiyarta ,Lokacin da Auran ya Mutu.
Lantana wata irin mace ce mai zuciyar kafurai bata da imani ko miskala zarratin,ita ke daura yaranta a kan mumun dabi’a
Idan Tanko ya fita sana’arsa sai ta daurawa “yayan kishiyarta ,mata talla ,tace duk inda zasuje suje su siyar mata tallah har da daddare daura musu take ,idan suka qi kuwa tasa Sallau ya Zane su.
Tun Tanko bai Sani ba har yazo ya sani ,yayi tai mata fada,budar bakinta sai cewa tayi itafa baza ta zauna da gurda gurda “yan mata gida daya ba batare da ta more su ba idan baya so ta daura musu tallata to yayi musu Aure,
Dake Tanko Jan wuya ne a gidanshi ,ya tsawar mata ,yace “gidansa takyale masa yara suyi karatu ,tukkuna idan Miji ya fito ai za’ai musu Auran.
Lantana taqi ji ,Tanko yana sa kafa yana fita zata fafaki yaran da faratin tallah ,suna kuka suke tafiya,
Karshe Suka yanke shawarar guduwa gurin Uwarsu,
Aiko ranar da Asubah suka fito dukkaninsu suna labewa suna jiran babansu ya fita sallah su gudu
Tanko ya fito kamar yadda ya saba ,ya tsaya shagon su Sallau ,domin tashinsu ,suje massalaci ,daga bakin kofa ya tsaya gami da bubbuga kyauran ,ya wucewarsa
Su sallau ko sunajinsa ,da suka fahimci ya kauce daga gurin sai suka cigaba da baccinsu ,dakin sai tsami ne yake tashi ,sabida ,dama bawata tsaftace dasu ba ,sai su fi sati basiyi wanka ba.
Su Atika kuwa bayan sun tabbatar da wucewar babansu ,sai suka fito sadaf sadaf zasu gudu.
Abin Mamaki ! Sukayi gware da Tanko ya dawo domin daukar chazbah ,
Sai ya kara haske fitilar dake hannunsa yana kallonsu daya bayan daya,ga Atika riqe da katuwar jaka.
Yace”INA zakuje ne”?
Sai suka fashe da kuka dikanninsu ,
Kukan da yayi sanadiyar Farkawar Lantana daga Barci duk da tana cikin Uwar dakinta,
Tafito da sauri jin kukan da soro ,tana Addu’a Allah yasa ba daya daga cikin “yayanta bane ya mutu ,kanta ko Dan kwali babu.
Me za ta gani su Atika ne tsaye riqe da jaka suna zabga kuka ,ga babansu a tsay”
Tace”Malam Lafiya dai in ce ko “? Wa”yan nan shashashan yaran sun tashe ni daga bacci”
Ko sauraronta bai yi ba ,ya cigaba da tambayar su Atika ina zasuje da Asubar nan.
Atika tace “babah mungaji da Azabar da ake gana mana ,zamu tafi gurin babarmu,
Lantana tayi salati kamar gaske tace”Au!sharri zaku kullamin gurin Ubanku “ooo ! Ni Lantana Na hadu da “yayan zamani,
Sai ta hau kwala Sallau kira.
“Sallau” Sallaau!! Sallau”!!
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????
in kana bukatar cigabansi ga number nan
08089965176
[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????writting by
Binta Umar
MAMAN ABDUL WAHABU
Bissimillahi _Rahamanir rahim
????11
Sallau ya taso a fusace Sallau ,yafito gami da cewa “wai menene kin tashe ni ina bacci”
Sai tafashe da kuka tana nuna su Atika da hannu tace”ga sunan suna kulla min sharri a gurin Ubanku ,har da zagina”
Ai ko sallau ya yi tsalle ya gaurawa Atika Mari yana zaginta ta Uwa ta Uba,kwata kwata bai lura da Malam Tanko dake tsaye a gurin ba.
Tanko yace”yanzu Lantana yaushe yaran nan suka zage ki Dan sharri” to tunda Abin ya zama haka zan dauke yaran nan daga hannunki ,ya mai da idonsa kan Sallau dake tsaye yace”kaji kunya sallau ,da zaka din ga biyewa Uwarka da duk Abinda tace da kai , Allah ya shirye ka,ya mai da idonsa kan su Atika yace su koma ciki ,kafin yadawo daga masallaci.
Yana fita Sallau ya riqa zaginsu shi da Lantana,sukayi masu shiru ,Lantana tace baza su koma ba cikin gidan ba tunda suka fito sun fito kenan ,sai subari Ubansu mai daure musu gindi ya dawo sannan.
Bayan Sun fito daga Massalaci Tanko ya tsaya shida Amininsa yake fada masa halin da a ke ciki.
Budar bakin Malam iliyasu yace”mai zai hana muha da Atika da Yunusa mana ina ganin hakan zaifi.
Malam Tanko yaji dadi hakan ,ai nan suka tsayar da Magana.
Bayan sun karya da kansa ya fita dasu yasa su a mota ban da Atika domin yafada halin da ake ciki.
Tana kuka suka rabu da “yan Uwanta.
Lantana kamar ta mutu jin cewar Atika zata Auri yunusa Dan gidan Malam iliyasi ,ita San samunta yaran suyi tazama babu Aure sabida tsabar qiyyaya.
Ranar daurin Aure Abin sai yabawa jama’ar dake gurin Mamaki jin ana daurawa Uba da “ya Aure.