GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Me Martaba yace”Yarinyar nan ai tana gurinki ko”
Mama Fulani tace”Tana cikin d’aki ita da “yan uwanta,gaskiya ina tausayawa rayuwarsu wallahi”
“Dole ai abun tausayi ne, shi yasa na yanke shawarar d’aura mata aure da Magajin Sarki tunda ta rasa miji me nagarta kamar Yusuf ina ganin shi Almustafa zai iya rik’eta amana”
Murmushi Mama tayi cikin k’arfin hali tace”Wannan hukuncin naka yayi Allah ya tabbatar da alkairi, amma ina hasashen rigimar da zataje ta dawo kasan dai rigimar k’anwarku Madabo ko”?
Me Martaba yayi gyaran murya a nutse yace”Barta wannan duk rigimar ta a bayan fage take kuma batayi a gabana sai bayan idona,na riga na yanke hukunci Almustafa zai Auri matar Yusuf Balaraba kenan zai kuma auri Halisa d’iyar k’anwata Madabo”
Duk irin maganganun da suke wakana tsakanin iyayen nasa yana ji yayi lamfu, shi kad’ai yasan abunda yake sak’awa a zuciyarsa
Bud’e ido yayi kad’an yana kallon iyayen nasa ya mik’e zaune, a nutse yace”Allah ya taimake ka maganar Azima fa”
Shiru Martaba yayi daga bisani yace”Maganar Azima tananan itama za’ayi tunda an yiwa mahaifinta Alk’awari kar ka damu, Zamu aika masa da wasik’a cewar ranar juma’a me zuwa za’a d’aura auran sai su shigo da shirinsu insha Allahu zaka had’a mata uku rana d’aya ina maka addu’a da fatan alkairi,insha Allahu zaka samu nasara a rayuwarka”
Godiya Sarki yayi yana girmama al’amarin mahaifin nasa,shi da kansa yake addu’ar Allah ya bashi ikon yin adalci tsakanin matansa,
Me martaba yace”Kaje ka kiramin ita yarinyar,ina so mu zauna da ita gaka gata gani ga mahaifiyar ka, domin in fad’a mata irin hukuncin da na yanke a kanku, bazan yi mata dole ba, a rayuwarta”
Mik’ewa yayi a nutse Mama tace”Tana cikin uwar d’aki takasa sakewa har yanzu”
Kai tsaye d’akin ya nufa, yana taka k’asa kamar me tausayinta.
[15/08, 05:41] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYARNana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba
ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????
We are here to educate,motivate and entertain aur readers
DIDEGATED
TORAHAMA ALIYU
????????????????
BANI BANE????????
????????
(Zargina ake)
~BY: MAMA QUEEN~
????DA BAZAR MU WRITER’S ASSOCIATION????
NOTE
Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark’akiya,rikitarwa dad’i sauransu…..
_Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_
Whatsap numbar
07061553385
Karku bari abaku labari
BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM
INA MIK’O GAISUWA TA GAMI DA FATAN ALKAIRI GARE KA
Adimin Haruna H Umar
Beneficial writers fan’s
INA MAKA ADDU'A DA ALLAH YA BAKA MACE TA GARI????
????74
A nutse ya bud’e k’ofar ya shiga bakinsa d’auke da sallama.
Wata irin fad’uwar gaba taji lokacin data tsinkayi muryarshi tana daga cikin toilet tana d’auro alwala, lokaci guda taji duk jikinta yayi sanyi wasu hawaye masu zafi suka fara zubuwa a idonta, cikin zuciyarta tace”Shikkenan yanzu zai zo ya dawo min da damuwa ta baya,wayyo Allan Moddibo, hawaye ne ya ke kwarara sosai a idonta mutuwar Moddibo ta dawo mata sabuwa dal!tunda taji muryar d’an uwansa Sarki!sai take ganin kamar zata ga Moddibo.
Jikin bangon band’akin ta jin gina tana share hawaye sai k’okarin dai-dai ta kanta take, amma ina dole fuskarta ta nuna alamun anyi kuka.
Murmushin k’asaita
ya saki lokacin da suka had’a ido da Sadiya dake zaune kan gado,tana wasa da wasu awarwaron Balaraba da ta cire ta aje kan drowar duk wani kwalliye-kwalliye ta daina sai kace me takaba kullum da hijab a jikinta da carbi,kai hatta da d’an kunne ta cire ta aje,gani take itama rayuwarta tazo k’arshe babu Yusuf Moddibo rayuwarta ba zatayi dad’i ba.
Da gudu Sadiya taje ta rungume shi tana dariya tace”Magajin Sarki!yau kwanana bakwai ban gan ka ba,wai ina ka shiga ne?ina Yusuf kullum yayarmu sai tayi kuka idan na tambayeta sai tace babu komai”
Lokaci guda duk tayi masa wannan tambayoyin.
Hannunta ya kama suka zauna cikin wata kujera ya d’ora Usuman a cinyarsa, yana shafa kan yaron cikin tausayi,yace”Na fuskanci Halimatu kina da surutu da yawa, Ok kina son in sanya ki a makaranta ko”?
Cike da farin ciki ta d’aga kai, murmushi yayi kawai yana girgiza kai,yace”Kar ki damu insha’Allah a satin nan zaku fara zuwa school ke da d’an uwanki”
Tsalle ta buga na murna cike da farin ciki tace “Mun gode Magajin Sarki,Allah yasa kazama Sarkin mu”
Murmushi yake sosai yace”Ameen,in dai na zama Sarki kece Gimbiya ta” tsalle Sadiya take tana murna cike da k’uruciya Usuman sai taya ta yake,
Wata tsawa taji wacce tasa tayi saurin shiga taitayin ta d’akin yayi shiru, Balaraba ce ta futo daga toilet taga shashancin da Sadiya take ranta ya b’aci sosai, ta lura shi kuma sai biye mata yake,tana jinta ko gaida shi batayi ba saboda rashin hankali.
Fad’a sosai takewa yarinyar kamar zata kai mata duka Sadiya har ta soma hawaye, ganin hawayen ne yasa ransa ya b’aci ina dalili ita ba’a hakura mata ba,ita zata takurawa wata.
Cikin wani irin voice me kashe jiki yace” Ya isa Malama”
Kallonsa tayi ta gefen ido tayi saurin kauda kanta, kasa-k’asa tace da Sadiyar taje ta gaida shi,
Simi-simi Sadiya taje ta tsuguna tana gaishe shi,ya amsa sama-sama suk hankalinsa na kan Balaraba dake k’okarin ta da sallah,
Rarrashin Sadiya yake har Balaraba ta idar da sallahr ta d’an waigo kad’an bata yarda sun had’a ido ba tace”Ina wuni”
Shiru yayi kawai yana rikitata da mayun idanunwansa masu sa kasala.
Jin bai amsa ba, ta kara maimaita gaisuwar.
Gyaran murya yayi a nutse yace”Lafiya, nake, yayi shiru na minti biyu kana ya cigaba da cewa”Me Martaba na neman ki yanzu”
Cikin fad’uwar gaba ta mik’e tsaye da sauri har tana k’okarin faduwa ta dalilin dogon hijab din dake jikinta
Bakinta na rawa tace”Allah yasa ba wani laifin nayi ba”
Shiru yayi mata yana binta da kallo ganin jikinta na tawa.
Had’e fuska yayi yace”Ji mana, kinga ki nutsu ba wani abun bane,naga kina ta wani rawar jiki, yawwa bayan nan kuma, Wad’an nan yaran da suke gaban ki ki bar ganin k’annan ki ne, to in kika cucesu sai Allah ya saka musu, na fad’a miki”
Yana gama maganar sa ya mik’e ya futa a nutse, bai tsaya kallonta ba balle ya saurari abunda zata ce,ita kuwa binsa tayi da kallo har ya fuce tana mamakin yanda yake mata magana cikin isa!da gadara, lallai ruwa ya daki babban zakara,
[16/08, 14:28] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYARNana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba
ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????
We are here to educate,motivate and entertain aur readers
DIDEGATED
TORAHAMA ALIYU
????????????????
BANI BANE????????
????????
(Zargina ake)
~BY: MAMA QUEEN~
????DA BAZAR MU WRITER’S ASSOCIATION????
NOTE
Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark’akiya,rikitarwa dad’i sauransu…..
_Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_
Whatsap numbar
07061553385
Karku bari abaku labari
BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????75
Cikin nutsuwa, tabi bayansa, Yana gaba tana baya zuciyarta sai wani d’ar-d’ar take, me Martaba yana bala’in yi mata kwarjini don haka suna had’a idoshi ta sunkuyar da kanta a k’asa,gami da zubewa k’asan k’afafun Mama Fulani tana gaishe shi.
Cikin sakin fuska ya amsa yace”Sannu kinji ya k’okari,ya mukaji da rashin Moddibo kuma”?
Cikin rawar murya tace”Alhamdulilahi”