GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Allah ya jik’an Yusuf”
Me Martaba ya fad’a,da amin suka amsa.
Sannan yayi shiru na minti biyu kana ya cigaba da cewa”Wato abunda yasa na kira ki, nan gurin shine, ina neman alfarma guda a gurin ki ina fatan zaki bani wannan alfarmar”

A nutse tace”Ai babu abunda zaku nema a gurina in kasa yi muku shi,Allah ya taimake ka”

Me martaba yaji dad’in lafazinta yace”Alhamdulilahi,Allah yayi miki albarka, ina son zan maye miki guribin Yusuf da Almustafa Sarki!kenan, ma’ana zan d’aura muku aure insha Allah rana ita yau, ina fatan ban shiga hakkin ki ba, ko idan ba kya sonsa ki fad’a kar ki rufe min,tamkar “yar cikina kike,domin bazan yi miki dole ba”

Cikin fad’uwar gaba, tace”Duk rin hukuncin da ka yanke a kaina, bani da ja akai domin ka isa dani,saboda haka na amince da zab’in ka”

Albarka me Martaba ya sa mata sosai sannan ya bata umarnin tafiya.

Balaraba ta mik’e a nutse ta bar gurin kai tsaye d’akin da ta futo ta koma.
Tana shiga ta zube kan daddumar da tayi sallah ta fara wani sabon kuka,tana tausayawa kanta,sam takasa cire Moddibo daga zuciyarta, yaya zatayi ta had’a soyyayarsa da ta kowa sam bata jin soyyayar Almustafa cikin zuciyarta,tana ganin bata da babban masoyi. Kamar Moddibo, kuka take sosai,da sosai.

Ganin kukan da yayar tasu take ne yak’i k’arewa yasa Sadiya ta kama hannun Usuman suka futa suna kuka suma.

Babu kowa a falo sai Sarki!dake kwance kan Sofa, yak’i komawa fada, saboda yana buk’atar hutu, sosai kwana biyu sam baya samun ishashan bacci,Moddibo na yawan fad’o masa a rai, mussaman idan ya tuna lokacin da ya had’a hannusa dana Balaraba yana fad’in, d’an uwana ga amana ta nan,wannan magana da Moddibo yayi masa tana tsaye a cikin ransa,

Hangosu yayi sun futo suna share hawaye ya mik’e da sauri yana ware lumsassun idonsa, Sadiya ta k’araso kusa dashi cikin rawar murya tace”Magajin Sarki! ga yayarmu can tana kuka, kuma tak’i taci abunci tun safe take kuka, mu kam munci abunci mun k’oshi abunmu”

Jin da yayi Sadiya tace”Tana kuka sai yayi tunanin maganar da me Martaba ya fad’a matane ta sanya ta kuka, wato tanaso ta nuna masa cewar bata sonsa,amma takasa fad’a gaban me Martaba, ranshi yaji ya b’aci kad’an, cikin zuciyarsa yace “Babu ruwuna da ko tana so ko bata so,insha Allah sai na cikawa d’an uwana burinshi.
Mik’ewa yayi ya rik’e hannunwan su suka nufi d’akin da take ciki, tabbas bazai lamunci zama da yunwa ba
Tana kwance kan daddumar har yanzu kuka take ya k’ofar d’akin ya shiga,da sallama ciki-ciki, sam batasan da shigowarsa ba, yazo ya tsaya kanta,yana k’are mata kallo, inuwar mutum dogo ta gani akanta, tayi sauri d’ago da fuskarta wacce taji jage-jage da hawaye, had’a ido sukayi, yana mata wani kallon kurulla.
Da sauri ta mike zaune tana goge fuskarta da k’asan hijab dinta,hararasa take k’asa-k’asa ta takure jikinta cikin hijab tana sauke ajiyar zuciya.

Yafi minti biyar a tsaye a kanta yana nazarinta, gyaran Murya yayi ya kira sunanta cikin yanayin muryar shi, sunkuyar da kai tayi bata amsa ba.
Tsugunawa yayi kusa da ita ya d’ora gwiwarsa k’asa yana k’okarin d’ago fuskarta,da tafukan hannayensa,a zabure ta matsa gefe tana watsa masa harara,k’asa-k’asa, fuskarsa ya had’e sosai yace”Kukan me kike yi”?

Shiru tayi masa gabanta na faduwa saboda kusancinsu da shi yayi tsanini Wanda har hucin futar nuffashinsa tanaji ga k’amshin turaransa duk ya baibayeta.

Kaurara murya yayi yace”Wannan shine magana take da ta karshe mutuk’ar zan dunga yi miki magana kina raina min hankali, kinajin abunda nake cewa kinyi shiru ko”?

D’ago kanta tayi tana kallansa,cikin dauriya tace”Me ya dame ka da kukana”?

“Saboda ke amana ta ce”
Cikin mamaki ta kalleshi jin abunda ya fad’a.

“Anyway,nasan abunda yasa kike kuka saboda ance dake ki aure ni ne,shine dalili, ko”?
Yafad’a cikin sigar tambaya.

Shiru tayi tana takure jikinta,so take ya tashi daga kusa da ita duk a takure take.

Wani murmushi yayi yana d’an girgiza kansa cikin damuwa abubuwan da suka da meshi yace” Tabbas kinyi rashin masoyi, mu kuma munyi rashin d’an uwa managarci hak’ika Moddibo ya taka muhimiyar rawa a rayuwar ki, tabbas duk abunda ya tafi ya bari a doran duniyar nan dole in d’ora daga inda ya tsaya, ko da me Martaba be yanke wannan hukuncin ba, ni ina da wannan kudirin na auranki araina saboda wasiyar da d’an uwana ya tafi da ita” Nuffashi ya sauke yayi shiru,gami da tsura mata ido, kana ya cigaba da cewa, mutuk’ar kikaga ba’ayi wannan auran ba,to sai dai in ke kika bujere,wa buk’atar mu,saboda haka, inason ki kwantar da hankalin ki a kaina ni ba,bak’on zafi bane duk irin zaman da kike so muyi ni dake haka zamuyi”

Tsitt!! D’akin yayi bakajin komai sai k’arar AC da sautin nuffashinsu, da k’yar ta d’ago kanta tana kallonsa,bata tab’a tsammanin ya iya kyawawan lafazai irin wannan, wani irin kwarjini yayi mata,wanda yasa tayi saurin kauda da kanta daga kansa, muryarta na rawa tace” Ka matsa daga kusa dani”

Girgiza kai yayi kawai yana sakin murmushi,yace”Sadiya tace”tun safe baki ci abunci ba,hakane”?

D’akin take bi da kallo tana neman su Sadiya,basa nan, gabanta ya fad’i ta zaci suna d’akin a tunaninta ko Sarki!yayi niyyar yi mata wani abu ganinsu zai sa ya fasa.
[17/08, 15:30] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
GIMBIYA BALARABA
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
????????????????????????????????

                _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR
Nana Khadija
Yaro Da kud'i
Gimbiya Balaraba

ZAMANI WRITERS
ASSOCIATION????????


We are here to educate,motivate and entertain aur readers


DIDEGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM

????76

Ganin yadda take rarraba ido yasa ya mik’e tsaye cikin nutsuwa yace”Ki futo falo kici abunci,ki sake da mutane, sannan ki cigaba da walwalarki,wannan zaman da kike cikin d’aki ke kad’ai duk bashi ne mafuta ba,a gareki, ita rayuwa ta duniyanan bata tabbata, ki sanya tawakkali a cikin zuciyarki, kisa a zuciyar ki cewa inda Moddibo ya tafi kema zaki tafi,domin can d’in shine tabbas,a garemu”
Yana gama maganar sa ya futa daga d’akin,a nutse.

Balaraba tayi mamakinsa mutuk’a sam bata tab’a tunanin mutum ne shi mai sauk’in kai haka ba,ga Ilimi da ikilashi,ta lura mutuwar Moddibo batasa ya furgice ba,duk da shak’uwarsu amma yana cikin nutsuwarshi, haka ake son mutum me tawakkali.

Wannan Nasiha da Sarki!yayi mata ta k’arfafa mata jiki sosai tanaji a zuciyarta cewa itama hakane idon lokacinta yayi dole tatafi babu tsumi babu dabara.

Allah kasa mu dace.

A nutse ta furo falo, taga su Sadiya na zaune kan wata k’atuwar dadduma suna cin “yayan itatuwa shi kuma yana kwance kan Sofa kamar d’azu idansa a lumshe,da alama bacci yake ji,

Babu kuzari a jikinta ta nufi wani keb’antaccan guri wanda aka tana da domin cin abunci ta zauna a nutse ta had’a dai-dai cikinta tayi bissimilah ta fara ci, duk abunda take yana kallonta ta k’asan idonsa dake mutum ne shi mai yalwar gashin ido shiyasa in ya lumshe idonsa sai kayi tunanin a rufe yake.

Mama ce ta futo daga wani d’aki cikin shiri tana sanye da wata lafiyyar lifaya wacce tayi mata kyau sosai, had’a ido sukayi da Balaraba tayi saurin yin k’asa da kanta, Mama Fulani tayi murmushi kunyar yarinyar tana burgeta sosai,tace” Yawwa ko kefa ai gwara da kika fito amma kin zauna cikin d’aki babu ci babu sha”
Sunkuyar da kai tayi cikin jin nauyi.
Ta kalli su Sadiya sun sake suna wasa,Usuman ta kira tace”Zo muje ka rakani wani guri”
Da sauri yaron ya tafi gurinta.Mama ta kalli Balaraba tace”Zamu shiga shashen Hajiya Kattime yanzu”
“To Mama a futo lafiya”
Balaraba tafad’a cikin girmamawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button