GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Balaraba na cikin d’aki shiru, zuciyarta duk babu dad’i gasu Sadiya masu d’ebe mata kewa suna can falo har yanzu basu shigo ba. Mik’ewa tayi a nutse ta futa daga d’akin.

Can ta hango su, wani keb’antaccan guri suna wasa babu abunda ya dame su

Kwata-kwata bata kalli inda suke zaune ba, ta nufi inda su Sadiya suke, tunda ta futo yake satar kallonta ta kasan idonsa, har Halisa ta fahimta,ranta ya b’aci amma ta danne, kawai bata nuna ba.
Mik’ewa yayi shima ya d’an kalli a gogon hannunsa bakwai shaura, Yace”Lokacin sallah yayi ya kamata, kije kiyi sallah ko” Halisa ta mik’e tsaye tana gyara zaman rigarta, tace”Idan nayi sallah zan dawo mu cigaba da hira, yau naji dadin hiraramu,babu fad’a bare hantara”

A kasalance yace”Baki da abunyi ne,shiyasa kike wannan maganar, hirar haka ta isa, gobe ma bance kizo ba, domin nasan halinki”

Cikin shagwab’a tace”Me yasa”?

“Ba ranar ki bace gobe,zan zauna da Azima kamar yanda na zauna dake yau”

Tab’e baki tayi,amma bata yarda ya gani ba,tayi shiru da bakinta kawai bata sake magana ba.

Tsakaninsa da Balaraba ido ne,ko da tazo ta wuce su bata ce masa komai ba shima haka haka suka shige d’aki ita dasu Sadiya, su kuma suka futa tare.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
。。。。。。。。。。。。。。。
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

               _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA

Zamani writers Association


We are her to educate motivate and entertain aur Reades


DIDEGATED
to
RAHAMA ALIYU

????????????????????????????
Soyayyar gaskiya
????????????????????????????

Jin jina gare ki marubuciyar wannan littafin,( Mugirat Musa 66) Nagode da addu’ar ki a gare ni, Ina miki fatan alkairi a rayuwar ki,Ubangiji Allah ya biya miki buk’atanki na alkairi damu kanmu al’umar musulmi baki d’aya.

BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM

????80

Sai bayan sallahr Magariba Mama ta shigo, sun sha hira da Hajiya Kattime sosai,taji dadin ziyarar da Mama ta kaima ta,domin ta d’ebe mata kewa sosai, ko da Waziri ya futo daga turakarsa ya ganta,shan kunu yayi ya fucewarsa ba tare da ya amsa mata gaisuwarta ba, inda akwai wacce ya tsana a duniya,bai wuce Mama Fulani, da d’anta ba,wato Sarki! Ko da ya futa babu inda ya nufa sai sashen Hajiya Kulu me d’akin kudu wato Uwar gidan me Martaba kenan.


Tana hakimce kan wata kujera me cin mutum d’aya k’afarta d’aya kan d’aya bayi ne zagaye da ita suna fadanci, ita kuma sai zuba mulki take, Waziri yayi sallama ya shiga d’akin.

D’aya bayan d’ayan bayin da suka futa,bayan sun kwashi gaisuwa gurinsa.

Guri ya nema ya zauna yana fuskantar Hajiya Kulu sosai, suka gaisa cikin barkwanci kamar yarda suka saba, yace magana ce, nake tafe da ita”

Hajiya Kulu ta gyara zamanta tana kallonsa,tace”Ai tunda na ganka nasan akwai magana a bakin ka, kasan abokin kuka shi ake fad’awa mutuwa, nima dama ina neman ka”

Girgiza kai yayi, yaja wata ajiyar zuciya me zafi, yace”Mijinki yana samun nasara akaina ta ko wane hali,to wannan karon nayi rantsuwar sai dai ayi mutuwar kasko, ko ni ko shi,wallahi tallahi, mulki sai ya dawo hannu na,domin inaji ina gani, bazai bawa d’anshi mulki ba,ni ina zaune ban hau kurarar naji yaya take ba, ajiyar zuciya ya sauke,ya cigaba da cewa”Ina me tabbatar miki da cewar wannan karon idan ya tsananta to zan kawar dashi, daga duniyar nan,sai dai yaga ana mulki a k’iyama,idan yaje can”
Ya k’arashe maganar bakinsa na kumfa”

Hajiya Kulu,tace”Wannan maganar da kake tafe da ita,nima a kanta nake,a kintse nake,a shirye nake,zan mara maka baya gurin ganin burinmu ya cika,akansa ko d’ansa,domin kwata-kwata bana sha’awar mulki ya koma hannun wancan d’an shegiyar,ina me tabbatar maka da cewa kashinmu ya bushe”

“Bar wannan maganar Hajiya,domin in kina yin ta jikina har wani d’aukar zafi yake,yanzu ke wace shawarar kika yanke kan al’amarin domin inji shirinki,nasan kema dai ba daga baya ba gurin shirya mugunta”

Hajiya Kulu ta gyara zams sosai,ta kwashe masa duk abunda ta tsara,har da zuwan d’an bori, me suna Tsito, Waziri ya girgiza kai, gami da cewa”In yazo nine zan bashi masauki ina fatan dai ya iya aiki”

Hajiya Kulu tace”Idan kaji aiki ma d’aya kenan,Tsito k’arshe ne,duk wani aljani dakake ji da gani, yana aiki dashu,kuma in ka nemi kayi magana dasu zai kirasu kuyi magana, babu wata shirka da tsubbu da bai iya ba,mutuk’ar zaka’aje masa kayan aiki,zaka ga aiki da cikawa”

Gyad’a kai Waziri yayi cikin jin d’adi yace”Hak’ika wannan shine irin Wanda nake so, na samu,na lura yanda kike k’warzanta shi,har kashe mutum zai iya yi ko”?

Hajiya Kulu tayi dariya, har da dukan hannun kujerar da take kai, cikin annushuwa tace”K’aramin aiki kenan,ai nake fad’a maka,yanda nake jin labarinsa gurin Jakadiya tace,a rana in yasa kansa,zai iya bawa aljanunsa k’afa masu goma,su sha jini su k’oshi”

Waziri yayi murmushi yana ji a jikinsa buk’atarsa ta kusa biya, yace”Yaushe kika ce zai zo ne”?

“Gobe Jakadiya za taje ta d’aukoshi”

“Allah ya kaimu”
Waziri ya fad’a ya cigaba da cewa”Tabbas idan yayi mana aiki me kyau,zan yi masa muhimiyar kyauta,ta ban mamaki”

Hajiya Kulu tace”Kai dai kaje ka kwantar da hankalin ka kawai,ai buk’atarmu kamar ta biya ne”

Waziri ya mik’e tsaye, da niyyar tafiya, gaskiya yana cike da farin ciki, tabbas yasan Hajiya Kulu ba tun yau ba,makirar maca ce kuma muguwa ce,ta inna niha,duk hanyar mugunta,ta sani,sallama sukayi,ko wanne zuciyarsa fara tas, suna Allah-Allah gobe tayi D’an bori Tsito ya dura,a gidan, domin ya fara aiwatar da aikinsa.


Bayan sallahr Isha’i Mama ta aika Jakadiya Shafa’atu domin ta kira mata, Balaraba a cewar ta zaman kad’acin da Balaraba take,zai iya haddasa mata wani ciwon, babu yadda ta iya, ta mik’e ta bi bayan Jakadiya,domin baza ta iya sab’awa umarnin Mama ba,lokacin su Sadiya sunyi bacci.

Sosai Mama take hira da ita tana dan janta a jiki,duk domin ta sake,tasa Jakadajiya tana basu labarai na ban dariya,sai ga Balaraba,ta saki jiki sosai har tana dariya. duk abunda bata gane ba,a game da labarin da Jakadiya Shafa’atu take bayarwa sai ta tambaye ta,ita kuma ta fad’a mata, k’arshe dai Mama Fulani tayi musu shiru kawai tana kallonsu da murmushi a fuskarta,taji dad’in sakin fuskar da Balaraba tayi.

Yana kwance, cikin Sofa yayi lif kai baka ce a kwai mutum cikin d’akin ba,duk wannan abunda yake faruwa yana ji,tun futowar Balaraba, ya nemi nutsuwarsa ya rasa hatta baccin da ya rufe masa ido nemansa yayi ya rasa,ya lumshe ido kawai yana sauraron muryarta wacce ta kashe masa jiki, ashe haka yarinyar take da surutu,muryarta nada dad’i,abunda yake fad’a kenan cikin zuciyarsa.

Mama Fulani ce kawai tasan yana gurin,domin da futo ta ganshi a kwance har tayi masa maganar tafiya shashensa yace”Sai ad’an jima zai tafi”

Yanzu ma murya ta d’an daga kad’an tace”Magajin Sarki!”

Da sauri Balaraba ta kalli inda Mama take kallo,gabanta na fad’uwa yanzu da yana gurin ta saki jiki take,dariya sai kace wata shashahsa, k’asa tayi da idonta lokacin da ta hangi inuwarsa kwance kan kujera, dake gurin da yake babu wadataccen haske,ya k’ashe k’wai shiyasa lokacin da ta futo bata ganshi ba,

Jin muryar Mamansa yasa yayi gyaran murya,yana daga kwancen yace”Na’am Mamana”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button