GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin tausasawa tace”Yau da alama dai nan zaka kwana,ko”?

Shiru na minti biyu,yace”Mama yau wani irin kad’aci nake ji wallahi,ki barni inyi kwanciyata nan,ina jin motsin ki”

Murmushi tayi cike da tausayinsa tace”Yau yarinyar tar ce kuma ta motsa maka”

Murmushi yayi wanda har sai da sukaji sautinsa,Balaraba taji wani yarrrrr! A jikinta. Yace”Dama ni kullum yaro ne,a gurin ki, tunda har yanzu banyi auran fari ba,kuma ban haihu ba”

Shiru Mama tayi,kunya duk ta isheta Mama Fulani maca ce mai mutukar kunya a rayuwarta,

Jakadiya Shafa’atu tayi murmushi tana k’okarin mik’ewa tsaye tace”Lallai Uban d’akina dole kasa Fulani tayi shiru,saboda ka tab’o abunda baza ta iya magana akai ba,saboda kunya, kana maganar auran fari,kai kasha kurumin ka, mata uku zaka aura me yafi wannan dad’i”

Miskilin murmushi yayi iya leb’anshi yana satar kallon Balaraba shi yana ganin fuskarta sosai,itace takasa gano fuskarsa,sai dai zatinsa,

Jakadiya ta runk’umfa tana fad’in A tashi lafiya Uwar d’akina”

Mama tace”Allah ya bamu alkairi”

Sarki!ta kalla kanta a k’asa tace”Yallab’ai a tashi lafiya”

Hannu kawai ya d’aga mata,maganar tana masa wahala,dama zuwa-zuwa ce, in yaga dama wataran haka zai ta hira,mussaman da Moddibo ko Mamansa
Balaraba ma mik’ewa tayi ,tai wa Mama sallama, Mama tace”Har zaki shiga Balaraba, ko dan kinga Jakadiya ta tashi”

Girgiza kai tayi cikin jin nauyi tace”Ba haka bane Mama,ina so in d’an kwanta ne, naji kaina na ciwo kad’an watak’ila bacci ne”

“Ayya, to ki tabbatar kin sha magani kafin ki kwanta kinji ko”
Tafad’a cikin kulawa.

Balaraba tace”Insha Allah Mama, Allah ya bamu alkairi”

Mama tace”Ameeen

Balaraba ta wuce d’akinta a nutse, Idansa a k’asa sai ka rantse da cewar bacci yake saboda yadda ya lumshe su, amma duk wani motsin Balaraba yana gani har ta shige d’aki.

Ajiyar zuciya ya saki,yanayin jikinsa na sauyawa, ya rasa abunda yasa yake jin wani irin sauyi a jikinsa mutukar zai ga gilmawar ta,sai sha’awarsa ta motsa,yasan yanzu idan ba’ai wasa ba,kwana zaiyi yana mafarkai, shi kansa yasan mutum ne mai mutuk’ar Sha’awa, yana daurewa kawai,amma abun mamaki idan yana tare da Halisa baya shiga irin wannan yanayi

Shi kad’ai a kabari a k’aton falon, domin Mama ma ta shiga ciki, rage haske futular yayi ya gyara kwanciyarsa,bacci ya d’aukeshi, mai cike da mafarkai, mafarkin da ya dad’e bai yi ba,yau yayi Balaraba ya gani, tare da wannan matar suna cikin farin ciki da annushuwa,suka zo gurinsa, kamar kullum, matar ta kama hannusa dana Balaraba ta had’a guri guda, ta tafi tana waiwayensu, fuskarta cike da farin ciki har suka daina ganinta.

Balaraba ya kalla sai yaga tanai masa wani k’ayataccen murmushi, gashi ta rik’e hannunsa sosai, taja hankalinsa cikin mafarkin, wanda yayi sanadin da yakasa daurewa ya rungume ta sosai yana kiss d’inta, ji yake kamar gaske, jikinsa duk ya shiga babu abunda yake buk’ata lokacin sai Jima’i, sai da ya kai k’ololowa sannan ya farka cikin wani mugun yanayi jikinsa duk ya b’aci, still kamar yadda yake ganin girmansa cikin mafarkin haka take a fili, ta mik’e tsaye! Tana jiran hakkinta .

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????81

Ya dad’e yana jin wani irin yanayi a jikinsa, wanda bai tab’a jin irinsa ba, da k’yar ya samu ya mik’e a jigace, futa yayi daga shashen gaba d’aya, ya nufi nasa, lokacin ana kiraye-kirayen sallahr asubah, a gurguje yayi wanka gami da tsarkake jikinsa, ya futo ya zura jallabiya me yankakken hannu, wani takalmi mai kyau ya zura a k’afarsa ya futa, da nufin zuwa massalaci, domin gabatar da sallahr asubah.


Uwa! da Shamsiyya ne zaune gaban wani mutumi zaune a kan wani buzu, da wasu manya-manyan carbuna, gami da alluna irin na k’arfe a jijjigine a bango, yana sanye da riga da wando na wani yadi bulu, wanda akai wa d’inki “yar shara. Gabansa wani fefe ne k’aton gaske cike da yashi, yana zane-zane a ciki, shi kad’ai ya san abunda yake zanawa.

Yana ganinsu ya saki fuskarsa, sannu da zuwa kawai yake musu.

Suka nemi guri suka zauna suna gaisawa, amsawa yake, hankalinsa na kan Shamsiyya.

Yashin, da yake gabansa ya hau zanawa, tsawon minti biyar, ya d’ago kansa yana kallonsu yace” Na duba naga abunda yake tafe daku, ina fatan dukanin abunda aka umarce ku dashi zakuyi batare da kun bamu wahala ba”

Uwa! ta gyara zamanta sosai, tace”Allah ya gafarta maka, duk abunda aka umarce mu muyi zamu yi mutuk’ar buk’atarmu zata biya”

“To Masha Allah”
Arrama ya fad’a yana kallon Shamsiyya sai sid’e leb’e yake.

Gayan murya yayi, yace”Naga wata yarinya buduwar wa,gata anan”
Yafad’a yana nuna wani zane da yayi jikin yashin.

Uwa! ta k’walalo ido tana son ganin budurwar da ya fad’a

Murmushi yayi yace”Ai baza ki ganta ba, wannan aikinmu ne”

Uwa! tayi yak’e tace” Allah ya taimake ka”

Arrama ya cigaba da cewa “Wannan yarinyar da nagani, naganta kewaye da wasu taurari masu haske da d’aukaka, kuma na fahimci akanta kuka zo”

Shamsiyya ta gyad’a kai tana fad’in “Hakane Arrama, Balaraba sunanta.

Murmushi yayi, ya sid’i leb’ansa a karo na biyu yace” Itace Balaraba, gatanan cikin gidan sarauta, kewaye da dawakai da bayi, gatanan cikin shigar alfarma, kuma zata haifi “yaya maza sosai a gidan, ciki kuwa harda Sarki!”
Arrama ya k’arasa maganarsa yana duba ya shin dake gabansa.

Uwa! saura kad’an ta saki futsari saboda jin abunda Arrama yace, bakinta na rawa tace” Yanzu Allah ya taimake ka babu yadda za’ayi a rusa mata rayuwa,a sabauta mata rayuwa ta haukace, a maye gurbinta da Shamsiyya, gata a gabanka”
Ta k’arasa magana tana nuna masa Shamsiyya

Arrama, yayi wani bazawarin murmushi, yace”Akwai yadda za’ayi mana mutuk’ar zaku bi umarni kamar yadda na fad’a muku tun farkon zuwanku nan”. Shamsiyya tace”Insha Allah zamu bi umarni”

Arrama yace”To yanzu abunda za’ayi, ke zaki zauna a gurina tsawon kwana bakwai zan fara yi miki wankan magani, ke kuma”
Yafad’a yana kallon Uwa! yace”Ke kuma zan had’a miki wasu magunguna da zakuje kuyi amfani dashi duk rintsi kar ku wuce kwana bakwai ba Ku gabatar dasu ba, har indai kuka bi abunda nace muku, to buk’atarku zata biya”

Babu fargabar komai Uwa! tace”Ai dama mu domin buk’atarmu ta biya yasa muka zo gurin ka, zamu bi dokikin aiki insha Allah”

Malam ya janyo wata k’warya k’autawar gaske tana cike da d’aurikan magani, yw ciro k’ulli uku ya mayar da murfi ya rufe.

Kulli d’aya ya mik’a mata yace”Wannan duk yadda za’ayi aje a samu k’asar kabari Wanda aka bunne sabuwar gawa,a d’ebo damtsa uku, a had’a da wannan garin magani, aje har inda wannan yarinya Balaraba take, a barbad’a a hanyar ta ta wucewa, mutuk’ar ta tsallaka to zata had’u da ciwon me wahalar gaske, babu wanda ya san makarin wannan abu sai ni, zata dunga lalura a kasa gane kanta,da gidinta k’arshe ta haukace kowa ya huta”

Uwa! Ta karb’a tana hamdala, ya mik’a mata sauran d’auri kan maganin yace”Su kuma wannan a abunci ko abunsha za’a bata taci, sunansa shashatau,mutuk’ar taci zata mance wacece ita”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button