GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Abunda sukaji d’an bori Tsito yana fad’a kenan.
Waziri yace”Allah ya ja zamanin ka, tabbas kaine ka gaji mulki gaba da baya, ko a cikin jinsun Ku,ma zuriarku daban take,da kowa muna fata wahalarmu tazo k’arshe”
“Ihuhuhuhuhu! Aljani Mak’asudu yayi,ya kyalkyale da dariya,yana Fad’in ” Kasamu mulki ka gama, gobe ka kwana da shirin hawa kujerar sarauta,domin zan b’atar da d’an uwanka a duniya jininsa zan shanye tass!! Wannan mataki na farko, bayan na shanye jinin d’an uwanka, zaka bani jini bil’adamu k’afa shida bakwai kenan,,,wannan shine sakamako na”
Waziri yace”Duk za’ayi maka daga yau zuwa gobe zan kawo maka,bil’adamu kasa jini ka k’oshi.
Gyad’a kai Aljani Mak’asudu yayi, ya kalli Hajiya Kulu yace”Ke ma kije buk’atar ki ta biya, zamu sa, a tsugunar miki dashi wannan yaron da ya tsaya miki a zuciya, zakiyi yadda kike so ke da yaran ki, itama Uwar tasa duk wani abu da take ji dashi, zamu sauke mata shi,amma dole mubi a sannu saboda tsarin da yake jikinta,a shekarun baya mahaifinta ya bamu wahala sosai, dan haka dole mu d’auki fansa a kan jininsa”
Hajiya Kulu tace”Kar kaji komai Ubana, ka fad’i bukatar ka ni kuma zan baka abunda kake nema”
Aljani Mak’asudu yace”Ke ma zaki bani K’afa Uku shine muradi na”
Hajiya Kulu tace”Angama Ubana, duk Wanda. Kaga yayi maka cikin gidan nan mace ko namiji ko a cikin “yayana ne,kana iya shanye masa jini na baka”
Waziri shima yace”Wannan haka yake, nima ka zab’i Wanda kakeso cikin “yayana da bayina na baka, kasha jini yadda kake so”
Aljani Mak’asudu yace”Ku tashi ku tafi buk’atarku ta biya ta duniya”
Tashi sukayi suka futa da baya-baya.
Tun a daran Aljani Mak’asudu ya fara gudanar da kinsa, takan me Martaba ya fara, jininsa ya shanye tas,a ka wayi gari babu shi,a duniya.
Innalillahi wainnailaiyi raji’un
Gida ya kacame da ihu da tashin hankali na mutuwar me Martaba sarki Almustafa mutuwar ka tsaham, yayi sallama da kowa lafiya lou ya shiga turakarsa, Liman na jira ya futo sallah asubah, shiru abunda bai tab’a faruwa ba, Sarki! Ne ya shiga shashen Mamansa, domin nan me Martaba yake, suka had’u da ita a babban falo itama ta futo, cikin wasi wasi da damuwa suka nufi d’akin da yake.
Kwance suka ganshi kamar me bacci, idonsa a rufe, Sarki! Ya zauna gefansa yana tattab’a jikinsa, sanyi k’alau d’aga hannunsa yayi yaga ya koma ya kwanta yaraf!! Shi ba yaro bane yasan mecece mutuwa, Mama Fulani ta zube gurin a sume.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate, motivate and entertain aur Reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM
????84
Cikin damuwa da tashin hankali Sarki! Ya futa daga d’akin, Jakadiya Shafa’atu na tsaye a falon tana gyare-gyare taga futowarsa,a gigice, tace”Allah ya taimake ka lafiya”?
Sarki! Yace”Babu lafiya Jakadija, Allah yayi wa me Martaba rasuwa, Mama ta suma a d’aki,innalallahi wa’ina ilahi raji’un”
Futa yayi bai san Inda yake saka k’afar sa, lokacin gari ya soma haske, kai tsaye masalaci ya nufa domin ya shaidawa liman abunda yake faruwa.
Jakadiya Shafa’atu kuwa kasa shiga d’akin tayi, saboda tsoro da sauri ta nufi b’angaran Waziri domin ta kirawo Hajiya Kattime.
Lokacin da liman ya sanar da rasuwar me Martaba mutane da dama sai suka dunga k’aryatawa kafin kace kwabo kowa ya futo daga shashinsa,har Waziri,,, ya nufi shashen Mama Fulani domin ya tabbatar. Babu Wanda ya hanashi shiga,saboda me Martaba bashi da wani d’an uwa shak’ik’i kamarsa,duk da sun san cewar babu jituwa a tsakaninsu kwana biyu.
Tsallake Mama Fulani yayi ya nufi gawar me Martaba,yana dubawa, hamdala yayi a fili yace”Taka ta k’are Mustafah sai mun had’u, acan,
Lillab’e gawar yayi ya futo yana share hawaye kamar gaske,nan ya k’ara tabbatar wa da jama’a cewar me Martaba ya amsa kiran ubangijinsa.
Da k’yar Mama Fulani ta farfad’o ana tai mata fiffita, duk bata cikin hayyacin ta, Hajiya Kattime ta rungume ta a jikinta.
Balaraba a gefenta tana share mata hawaye Mama takasa cewa komai, tunda ta farfad’o bakinta sai motsi yake,babu abunda take fad’a sai Kalmar innalillahi wa’inna ilahi raji’un”
Balaraba hawaye kawai yake sharewa tana addu’a Allah ya yaye musu wannan masifa da ta tun karo su,gani take kamar k’arya ne me Martaba bai mutu ba, sai data an futo dashi cikin suttura za’a kaishi makomarsa sannan ta gasgata,fad’uwa tayi a gurin ta suma,Mama Fulani kuwa rirrik’eta akayi domin itama saura kad’an ta fad’i da k’yar! ta samu tayi masa addu’a wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, Waziri ya tasa gawar a gaba yana kuka kamar wani k’aramin yaro. Sarki! Kuwa wani mugun haushinsa yake ji,ganin yadda ya babba ke gaban gawar, ya hana mutane suyi masa addu’a, sai da aka sauke alk’urini me girma sannan aka sallaci gawar me Martaba ya samu jama’a sama da k’asa ko ina,haka aka d’auke shi aka kaishi makwancinsa na gaskiya.
B’angaran Hajiya Kulu da yaranta kuwa duniya sabuwa suka bud’e sun cika suna ciye-ciye da kalle-kalle tamkar ba mahaifinsu ne ya rasu ba, babu abunda ya dame su,Naja’atu ce me cewa,lokacin su yayi,za tayi facaka da kud’i, son ranta
Sarki! Kuwa wani irin zazzab’i ne yake damunsa tun bayan dawowarsu daga mak’abarta,daurewa kawai yakeyi ya zauna yana karb’ar gaisuwa gurin “yan uwa da mutan gari,suna kokawa da rashin da akayi, kowa sha’awa yakeyi Almansor ya maye gurbin mahaifinsa,hatta da su Galadima ma burinsu kenan,Governor da yazo gurin gaisuwar a bunda ya fad’a kenan,Waziri yayi tsagal yace” Ba haka al’adar sarautarmu yake ba,nine k’anin me mutuwa nine zan gaje shi,kafin “Yayanmu saboda haka tunda ina raye,ban mutuba ni zan zauna kan kujerar mulki” Governor yace”Wannan ba sarin mulkin k’asa bane, nine shugaba,dole nine zan zab’i sarkin gari na, saboda haka baza mubi tsarinka ba,Dan kar kace ba’ayi maka adalci ba,za muyi k’uri’a bayan sadakar uku wanda ya fi jama’a shine zai zauna kujerar mulki”
Waziri ya baza babbar rigarsa cikin bak’in ciki da b’acin rai yace”Lallai kam kun jawo masifa,domin rashin zaman lafiya zai tabbatar a masarautar nan, tunda iyayenmu da kakanimu suke mulki basu tab’a wata k’uri’a ba sai yanzu, mu baza’a rusa mana tsarinmu ba”
Yana gama fad’in maganganunsa ya mik’e ya futa daga fadar,ranshi a b’ace, yana ganin wannan Governor zai kawo masa matsala fa, yayin da buk’atarsa ta kusa cika
Sunyi mamakin abunda Waziri yayi,zahiri ya nuna mulki yake so,Sam mutuwar d’an uwansa ba itace a gabansa, wannan ya k’ara bawa Sarki! K’warin gwiwa da son sha’awar mulki abunda bai dame shi ba,a da yana so yanzu su fafata da Waziri, Allah yaba mai rabo sa’a.
Sai bayan sallahr isha’i Sarki! Ya shiga gida kai tsaye shashen Mamansa ya nufa,yana tafiya cikin sanyi jiki, ji yake duk duniyar tayi masa zafi, Lallai d’an adamu ba abakin komai yake ba,dubi irin hukuncin ubangiji,wata guda yayi rashin mutane biyu da bazai tab’a mantawa dasu ba a tarin rayuwarsa.
Balaraba da Mama Fulani da tare da Madabo,da Halisa,da Azima da wasu mata biyu, sai jakadiya Shafa’atu wacce take kusa da Mama Fulani tana b’are mata lemon zak’i,domin ta kasa cin komai, wani irin d’aci take ji a bakinta, da k’yar ta dunga shan lemon har tasha guda uku.