GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sallama ya shigo, falon Suka fara rige-rigen gaishe shi,da yi masa gaisuwa,amsawa yayi sama-sama ya shige turakar mahaifinsa.

Ko da ya shiga kwanciya yayi kan gadon me Martaba,ya d’auki rigarsa da ya rasu da ita a jikinsa,ya rungume ta,k’am wasu zafafan hawaye suka fara zubo masa.

Shikkenan Moddibo ya tafi me Martaba ya tafi,sun barshi shi kad’ai hakika duniya abar tsoro ce,hakama abun jikinta

Kuka Sarki! Yake sosai,kukan da bai tab’a yin irinsa ba, hak’ika yanzu yana buk’atar me rarrashinsa domin ji yake zuciyarsa zata iyayin bunduga, shi musulmi ne, dole ya yarda da mutawa da rayuwa yasan mutuwar wannan mutane biyu, babu wani mahaluki da ya isa ya tare ta sai,Allah domin shine ya hallice su, amma ya karb’i abunsa, shima kuma na hakane, yanzu kawai addu’arshi itace Allah ya sanya masa dauriya da jarumunta a zuciyarsa.

Kamar a mafarki yaji muryarta a kansa,tana kiran sunan sa.

Bud’e idonsa yayi dukansu ya sauke a kanta

Wani irin yarrrr taji lokacin da suka had’a ido ganin yadda k’war idonsa ta koma wata kala,tayi jazur kamar Jan gauta.

Wani irin tausayinsa ne ya tsirga mata,itama sai taji hawaye yana k’okarin zubo mata,daurewa tayi kawai,a zuciyarta tace”Maraici babu k’arya a cikinsa,komai girma komai dukiyarka, ka rasa iyaye kayi babban rashi,yanzu zai fara jin irin ciwon da take ji a zuciyarta na rashin iyaye.

Lumshe idonsa yayi yana jin tamkar ya kamo ta ya rungume a jikinsa ko ya samu sassaucin abunda yake ji a zuciyarsa,hak’ik’anin gaskiya yanzu Wanda zai rarrashe shi yake nema.

Cikin taushin Murya tace”Ka tashi inji Mama kaci abunci,tace inyi k’okari in baka kaci kafin ka kwanta”

Yana jinta yayi shiru abunsa, wani sanyi irin na zazzab’i yana k’ara ziyartarsa.
Ta kure jikinsa yake yana neman bargo domin ya lullub’e jikinsa.

Duk tana kallon abunda yake yi, muryar ta na rawa tace”Don Allah ka tashi kaci abunci kaji ko, bana son abunda zai damu Mama,ina tausaya mata da halin da take ciki,kar ka k’ara sanya mata wata damuwar tunda kasan rashin cin abuncin ka zai d’aga mata hankali, ba kai kad’ai kayi rashi ba,har damu,ni ina ganin kamar ni akayiwa mutawar ma”
Ta k’arshe maganar tana goge hawaye da suka zubo mata.

Yana lullub’e cikin bargo yace”A k’oshe nake,ko na tashi babu abunda zan iya ci, kiyi tafiyar ki kawai nagode”

Girgiza kai tayi kamar zatayi kuka ta zauna gefan gadon ba tare da wani tunani ba ta kama bargon tana k’okarin cirewa daga jikinsa, bargon ya rik’e ya had’a da hannunta, yana girgiza kai,alamar ta sakar masa

Girgiza kanta tayi itama kamar yadda yayi mata, komawa yayi ya kwanta kawai ya rufe idonsa,

Kallonsa tayi taga yadda kwarmin idonsa suka zurma ciki sai girman k’war idon,sai kace Wanda yayi wata yana lalura, ba tasan sanda hawaye ya fara zuba daga idonta ba,wannan tausayi ta rasa daga ina yake zuwa, babu komai a zuciyarta face tsagwaron tausayin Sarki!Almansor.

Sheshshek’ar kukanta yaji yasa ya bud’e idonsa da Sauri, yana kallonta,tayi saurin kauda kanta,tana k’okarin mik’ewa daga kusa dashi, ya ruk’ota da Sauri ya rungumeta tsam-tsam yana wata zafaffafiyar ajiyar zuciya!
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU


????????????????????????
NAMIJIN DUNIYA
????????????????????????

Story & writing

        *By*

Aunty Mamie


Ina masoya wannan novel d’in, Aunty Mamie na gaida ku, kuma tana muku fatan alkairi, gaba d’ayan Ku, wannan novel d’in mai suna Namijin duniya ya koma na kud’i dan haka duk me buk’atar ci gaba da karanta shi sai ya tuntub’i wannan numbar
08166526167


????85

K’okarin k’wace kanta take daga jikinsa, ya rik’e ta tsam a k’irjinsa,sai sauke ajiyar zuciya yake,zuwa can taji d’igar wani abu me d’umi a bayanta, hannuta tasa ta shafo,taji ruwa, Wannan ya tabbatar mata da cewar hawaye ne, tunda take dashi bata tab’a ganin kukunsa ba sai yau, itama zuciyarta sai ta karye,babban mutum kamar Sarki! yana kuka lallai tashin hankalin ya kai inda ya kai.

Sunfi minti biyar rungume da juna, sai da taji jikinsa yayi sanyi sannan ta zare jikinta daga nasa,tana kallon fuskarsa, lumshe idonsa yake amma ba bacci yake ba, tana kallon yadda yake cije bakinsa,kamar wanda yaji ciwo me zafi. Jikinta a sanyaye ta futa daga d’akin.

Tana zama Mama Fulani tace”Ina fatan kin bashi abunci yaci ya k’oshi”?

Balaraba bata iya k’arya ba,dan haka kawai sai ta girgiza kai alamar A’a.

Tace”Mama nayi-nayi ya tashi yaci yace a k’oshe yake Wallahi”

Mama Fulani tace”Nasan dama abunda zai ce kenan, sam baya son cin abunci, tun safe a ce mutum babu abunci a cikinka, sai damuwa Allah ya kyauta”

Balaraba dai Shiru tayi tana tunanin abunda ya faru tsakaninta dashi.

Halisa ce ta mik’e da sauri tana kallon Mama Fulani tace”Bari inje in gwada bashi ko zai ci”

Mama tace”Aikuwa da kin kyauta”

Madabo tayi murmushi, tace”Ai dama ko wace mace da irin hikimar ta,da kin sani tun farko ita kika tura ba waccan ba, ita har yaushe ma suka shak’u da shi”

Mama ta gane magana Madabo ta fad’a mata, tabbas Madabo baza ta canza halinta ba, na fad’ar maganganu da habaici.

Halisa ta shige d’akin da Sarki yake cikin gadara.

Azima kuwa tana zaune tamkar ta d’ora hannu aka, ta lura babu Wanda yake sonta, Balaraba tana da fada,gurin Mama Fulani, Halisa kuma “yar uwarsa CE, ga uwarta a tsaye a kanta, itama dole ne ta zage damtse gurin ganin ta kafa gwamnatin ta.

Mik’ewa tayi itama tana shan. k’amshi ta kalli Mama Fulani tace” Bari in shiga in duba jikin nasa”

Mama Fulani tace”A fito lafiya, kuyi k’okarin bashi abunci dai”

Azima tace”Insha Allah Mama” Wucewa tayi ko kallon inda Madobo take batayi ba.

Balaraba kuwa a manakinsu take in taga suna wani rawar jiki a kansa,abunda baza ta tab’a iya wa ba kenan, shi kuma dasuke domin shi, baya wani damunsa gwara ma Halisa yana sauraranta.

Halisa na zaune kusa da k’afafunsa, tana masa magana k’asa-k’asa,yana jinta yayi mata shiru, hannunsa ta rik’o tana fad’in “Yallabai ka tashi kaci abunci don Allah kar ka kwanta da yunwa”

Ranshi a b’ace ya bud’e idonsa ya mik’e zaune yana hararata, saurin sakar masa hannu tayi, yace”Wai ni yaro k’arami ne da zaku dame ni da in tashi in ci abunci, ita tazo ke kinzo to me kuke nufi ne”?

Halisa tana jin tsoran masifarsa tace”Umarnin Mama ne”

Hararata yayi yace” Ko dai umarnin ki, nasan dai “yar aike ta farko da izinin Mama ta shigo, ke nasan neman maganar ki, dan haka ki tashi ki bani guri in inajin yunwa ai baku san sanda zan nemi abuncin ba”

Halisa ta bud’e baki zatayi magana kenan Azima ta shigo d’akin.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM


Attention⚠⚠


Akwai masu kirana a waya suyi min zancan banza, kusani baku kuka aje ni ba,,,, ban san wulak’anci ba,saboda ba halina bane,cikin Ku masoya babu wanda na ware nace dashi nake,mutukar kika turo min sak’o kikaga ban baki amsa ba,to ki min uzuri, kar ki bini ta pravite ki gayamun magana littafin gimbiya balaraba dai nawa ne, mallakina ne,nake rubuta muku da basirar da Allah ya hore min,ina fatan Allah yasa sak’ona ya isa, Hak’ika abunda wata baiwar Allah taimin ya bani haushi wallahi, ta sanadin haka ma na janye typing kwana biyu, saboda haka duk wacce tasan ba maganar arzik’i zatai min ba,to kar ta kirani a waya, idan Gimbiya balaraba take so ta nema a groups,wannan shine magana

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button