GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nagode muku masu bina domin jin abunda ya dakatar dani kwana biyu Hak’ika kun cika masoya na na hak’ika, ina mugun sonku iya wuya ana tare????
Ku k’ara yawan comments ku ga redemore goma idan kunk’iyi na tafi hutu, wannan shine magana☺______________
Husaini Atk 80k
Allah shine abun godiya ina taya d’an uwanmu Husaini Atk 80k murna da samun nasara daga abokan adawa,ina fatan Allah ya k’ara muku nasara a rayuwarku
????86
Azima na shigowa Halisa ta sha kunu, kallon banza tayi mata tana hararata k’asa-k’asa tsaki taja tayi saurin zama kusa dashi har jikinsu na had’uwa.
Azima ta k’araso kusa dashi cikin nata salon tace”Allah ya taimake ka, tuntuni nake so in samu mu zauna dakai Allah bai nufa ba, yau sati na biyu a gidan nan, ban keb’e dakai ba, tun mutuwar Moddibo komai ya hautsi ne,Allah me yadda yaso a sanda yaso,gashi ya d’auke mana ubanmu maganin kukanmu, ina mik’a ta’aziyata a gurin ka bisa rashin da mukayi gaba d’ayanmu”
Azima ta k’arashe maganar tata tana sharar hawaye.
Wannan kalamai da Azima tayi sun k’ara mata martaba a idonsa, tabbas tanan Azima tafi Halisa hankali da sanin ya kamata shi a ganinsa, don haka sai ya maida hankalinsa kanta yana amsa mata maganar ta, cikin sakin jiki, yace ta zauna a d’aya gefan nasa.
Azima ta samu guri ta zauna tana k’ara lauya muryarta duk dan tayi dad’i ganin wacce tayi amfani da ita d’azu tayi tasiri a gurinsa.
Tace” Wallahi mutuwar me Martaba bakai kad’ai akai wa ba,har damu domin munyi rashin suruki nagari,hakik’a har abada baza mu daina yi masa addu’a ba”
Sarki! Gyad’a kai kawai idanunsa a lumshe suke yana jin duk irin rarrashin da Azima take masa,dama abunda yake buk’ata kenan,zuciyarsa ce ta fara yin sanyi, ya bud’e idonsa duka ya sauke su kanta, muryarshi k’asa-k’asa yace”Je ki d’auko min abunci naci”
Azima ta mik’e jiki na kyarma, ta girgiza jiki da gayya ta gallawa Halisa harara ganin ta samu nasara, abincin ta d’auko cikin wani irin fulas mai uban kyau da k’yalk’ali.
A fusace Halisa ta mik’e saura kad’an ta fad’i tana kumbure-kumbure ta futa daga d’akin.
Kallo d’aya yayi mata ya kauda kansa.
Azima ta had’a masa abuncin ta zauna kusa dashi yana ci tanai masa hira mai dad’i sai gashi yaci da yawa babu laifi.
Da kanta ta zuba masa ruwa ya wanke hannusa cikin wani abu mai kyau, ta yago masa abun goge baki ya goge bakinsa,ya mik’e ya koma kan gadon ya zauna yana kallon ta,har ta gyara gurin tazo ta tsaya kusa dashi,cikin nata sallon tace”To zanje in kwanta Allah ya taimaka ka,Don Allah kayi bacci karkayi tunani kaji ko”
Kallonta yayi na minti biyu yace”Karki damu, kije ki kwanta Allah ya bamu alkairi”
Azima ta juya da niyar futa daga d’akin, tana wata irin tafiya domin ta d’auke masa hankali
Allah Sarki! Azima ai bai san ma tanayi ba,domin tana juyawa ya kwanta kan gadon rigingine ya lumshe idonsa,,,D’an juyowa tayi a sace taga ko yana kallonta,ganinsa tayi a kwance da ido a rufe, bud’e k’ofar tayi ta futa jiki a sanyaye, ta wani gefan kuma murna take k’untatawa Halisa ita da Mahaifiyarta Madabo,, sauranta Balaraba, Azima na futowa falo ta ga su Halisa da mahaifiyarta a zaune suna magana k’asa-k’asa, d’auke kanta tayi ta shiga wani d’aki harda bugo k’ofa.
Mama Fulani da Balaraba dama tuntuni sun bar falon.
Madabo ce tak’i tafiya wai Lallai sai taga futuwar “yarta Halisa.
K’wafa! Madabo tayi tace” Zanyi maganin ki ne yarinyar banza kawai tana fama rama sai kace jemage babu k’irjin arzik’i, ai da ni wata me fad’a aji ce a wannan gida,dana hana auran nan wallahi”
Halisa tace” Don. Allah Mamana kiyi masa magana gobe ya hanye maganar auran,ko da ya kuntatawa Baba Waziri , kamar yadda ya k’untatawa mahaifinsa”
Madabo tace”Rabu dashi gobe idan Allah ya kaimu zan masa magana ai yana jin magana ta”
Halisa tace”Allah yasa ya d’auki maganar taki Mamana”
Madabo tace”Ameen ke dai”
A ranar Azima kwanan farin ciki tayi yayin da Halisa ta kwana bak’in cikin abunda Azima tayi mata.
Bacci mai cike da rud’ani da mafarkai shi Balaraba tayi a ranar, Asubar fari,ta farka jikinta.yayi sharkar da gumi tamkar babu Ac a d’akin,wani irin nauyi kanta yayi mata, ta dad’e kan gadon tana sak’awa da kwance wa,wani irin mafarki tayi mai tsananin rud’u da tashin hankali,abun mamaki kuma so take ta tuno ko menene takasa tunowa gashi dai tasan tayi, k’arfin addu’a ne ya tada ita tsaye, toilet ta nufa domin yin wanka da alwala .
Bayan idar da sallahr Asubah ne. Suna k’okarin futowa daga masallacin wani bawa ya k’araso gurin da sauri, ya zube gaban Sarki! Muryarshi na sark’ewa yace”Ranka ya dad’e babu lafiya shashen Uwar gida Hajiya Kulu, yanzu-yanzu Naja’atu da Fiddausi suka fad’i kwata-kwata sun daina numfashi sai wani abu dake futa daga bakinsu”
Hankali a tashe Waziri da Galadima suka nufi shashen Kulu. Shi kuwa Sarki! Abun ne ya fara bashi mamaki, da kuzari a jikinsa shima ya nufi shashan,sauran mutanen dake gurin suka rufa masa baya,, Yanayin yadda yake tafiya cike da jamurta yasa har yazo ya Tatar dasu,bai saurare su ba,ya kutsa kai cikin falon..
Fiddausi da Naja’atu ne kwance a k’asan tayal sun mik’e samb’al basa nuffashi, Kulu ta tasasu agaba tanata kwarma ihu! Kamar gaske.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate, motivate and entertain aur Reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM
????87
Jakadiya Ladi ce ta k’araso gurin hannuta d’auke robar ruwa me sanyin gaske, bud’ewa tayi zata zuba musu, Galadima ya buga mata tsawa yana fad’in “Kar ki zuba musu ruwa, gawa ba a zuba mata ruwa”
Ihu! Kulu ta kurma ta mik’e tsaye a zabure! tace”Au! Ashe da gaske sun mutu? Wayyo na shiga uku na lalace ni Hauwa Kulu”
Waziri ya tsuguna yana duba gawar su Fiddausi cikin zuciyarsa yana tunanin shi kuma a cikin “yayansa ko suwa Aljani Mak’asudu zai tsotsewa jini oho.
Ihu kawai kake ji a b’angaran Hajiya Kulu babu me salati a cikin mutanan ta, lokacin k’ank’ani mutuwar su Fiddausi ta watsu a gidan, Ihun da Hajiya Kulu take ne ya b’atawa Sarki! rai kawai sai ya fuce daga shashan cike da b’akin ciki da damuwa.
Wannan al’amari ya tayarwa da kowa hankali, Mussaman Sarki!, Cike da damuwa a kai wa su Fiddausi suttura aka kaisu makwancin su, bayan an dawo daga makabarta Waziri ya shige fada ya zauna kan kujera tare da jama’rshi,, kafin kace kwabo “yan zaman makoki suka fara gulma,har da masu zuwa inda Sarki! Yake zaune suna fad’a masa ga Waziri can a fada bayan kuma Governor yace” Kujerar ta shi ce.
Sarki! Yace”Suyi hakuri su kyaleshi tukkuna a kwana biyu komai zai dai-dai ta, dama shi Galadima baya goyan bayan Waziri shiyasa basa shiri sosai, yanzu ma yana kusa da Sarki! Suna karb’ar gaisuwa.
Bayan sadakar uku Hajiya Kulu Duniya sabuwa saboda a yanzu kud’i baya yanke mata motsi kad’an zata sa a kira mata Sarki! Tace zata ciri kud’i dole ya bata, ko yak’i ko ya so, watarana in ta umarshi da yayi Abu baya sab’awa umarnin ta,, Mama Fulani kuwa duk dan a zauna lafiya take k’ara tursasahi idan ya bujirewa bukatar Kulu wataran.