GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da Labari ya iski Lantana gurin daurin Auren tafito tamkar mahaukaciya tariqa dure duren Ashar
Da kyar su Sallau suka jata suka mayar da ita gida.
Tace”Yanzu Sallau Abinda Malam zai yimin kenan ,ya muna furce ni ,Ashe Aure zai yi ban sani ba niko mai zan yiwa Malam in wuce bakin cikin da ya kunsa min”
Sai ta fashe da kuka har dasu fyatar majina.
Sallau yace”ki rabu dashi Lantana,mune maganin Matar tasa wallahi ,tunda tasa ki zubar da hawaye Sai mun hanata zaman lafiya”
Maman yace “kwarai kuwa sai mun daukar miki fansa a kanta”
Sai tai ta shi musu Albarka ,tace”ai dama nasan zaku share min hawaye shi kuma Malam din zai shigo ya same ni wallahi”
Lantana babu irin cin mutumchin da bata yiwa Malam Tanko ba ,ya share ta ,kawai bai kulata ba ya cigaba da hidimarsa,
Gidan Malam Ilayisu nan a ka kai Atika,sosai Tanko yayi mata kayan daki babu laifi ,nan ma da labari ya iski lantana ,tai ta zuba ruwan bala’i a gidan ,tana cewa Tanko ya kwashe dukiyar “yayanta yayiwa wata banza kayan daki ,ai “yaya maza sune “yaya
A takaice dai ranar Lantana bata barsu sun rintsa ba.
Ashe Abu Na gaba,
Sabida kayan dakin Amaryar Malam Tanko iri daya ne da Na Atika ,da Alama duk shi yayi musu.
Wata makociyarsu tazo tana tsoguntawa Lantana ,Aikuwa “yan jeran nafita ,suka shiga dakin Amaryar ita dasu Sallau ,duka wargitsa shi,gami da debo kwata suka yaba jikin gadon da tsakiyar dakin ,sannan suka dinga kuza ruwa a tsakiyar gadon da dakin,sai da suka jiqa katifar jagab sannan suka futa daga dakin ,gami da barinshi a bude.
Ko da “yan kawo Amarya suka zo Lantana Na kuryar dakinta ta tasa redio tana ji ,tana jin shigowarsu sai ta rage redio n tayi lif tana jiran me zai faru.
Abin Mamaki gami da daure kai dak in suka gani a bude ,suna San ya kafafunsu ciki suka ga Abin mamaki ,Komai a fashe ga katifa jagab dakin yana ta warin kwata,
Matar Liman ,ta ce”innalilahi wa’ina ilayi rajiun”! Ai ba haka muka bar dakin nan ba,kai! Jama’a wai kishi hauka ne?
Lantana Na jiyo Abinda take cewa sai tafito a fusace tana gyara daurin zaninta ,Dan kwali a hannu,
Ta nuna Matar liman da hannu tace”ke Shattu bana son munafurci da kankanba ,ehe! Duk wata kutun gwila da kuka hada naji labari da sanya hannuku gurin bawa Malam ,waccan Mutsiyaciyar yarinyar tsintaciyya wacce ba’a San daga in da take ba ,wato ni za ai wa rufa rufa ,an lullube kura da fatar Akuya ,an dauko Mayya an kawo min gida salon tazo ta leshe ni da “yaya Na,to wallahi baza ta sabu ba ehe!! Tafada tana buga cinya cike da neman tashin hankali!
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN
08089965176
[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????writting by
BINTA UMAR
Maman Abdul Wahabu
Up
up
up
BINTA UMAR FAN’S
INA MUGUN YINKU SOSAI DA SOSAI INA JIN DADIN YADDA KUKE KAUNAR NOVELS DINA ,NAGODE DA GOYAN BAYANKU DARI BISA DARI
HAKIKA BANI DA BAKIN DA ZAN YI AMFANI DA SHI GURIN GODE MUKU ,SAI DAI IN CE ALLAH YABARMU TARE ,ALLAH YABAR KAUNA TA DAN ALLAH
❤
“YAN QUNGIYAR ZAMANI WRTERS ASSOCIATION
INA YINKU OVER ,MUSSAMAN ,RAEL SHAXXI ,HUSAIN 8K “YAR MUTAN ARKALLAH ,HAFSAT SISI ,HALINKU YANA BURGE NI HALINKU ABIN KOYI NE
ALLAH YAQARA DAUKAKA ZAMANI
????11
Shattu tace”kinga lantana mu ba tashin hankali ne ya kawo mu ba Alkairi ne ya kawo mu duk dai wannan da yayi nagari kan shi,” takarashe magana tana kama hannun Amaryar Malam Tanko
Da nufin shigar dai ita cikin dak in’
Mutanen dake ciki suna ta faman tsane ruwan dake kwance gurin ,suka ce “Aa shattu yanzu in kinshigo da ita nan ina guri ,ki kai ta makota tukkuna mugama gyara gurin.
Duk abinda mutum yayi kansa.
Shatu tace “to bara muje gidan Baba Laraba I Dan kun gama sai kuzo Ku fada,
Da sauri Lantana ta tare hanya tana buga cinyarta tace”Ahayye nanaye Akin bur in ji tusa ,dole Dan ace da Mijin iya baba ni warki CE daidai da qungun kowace shegiya,ihe! Muna fukar Banza kawai!
Shattu tace”wai Lantana Lafiyarki kalau kuwa kishi fa ba hauka bane”A tunani Na zaki dauki Suwaibah a matsayin “yarki tunda kin San kome ya faru da rayuwarta”
“Ke!! Dakata shatu” Lantana tafada ta na turo dauri gaban go shi
Tace”dadin baki zaki yi min Dan bake a kaiwa kishiyar ba.
Baki San yanda zafin Abin yake bane shiyasa kike shishshigi a kan Maganar,
Nafada Na kara fada ni Lantana,in dai ina raye babu macan da ita sa in zauna da ita ,ko wacece kuwa”
Ta karashe maganar tana buga cinya.
Shatu kawai sai taja hannu Suwaiba ,wacce take ta kuka tsora ya cika ta,dama tuntuni take jin labarin matar a bakin mutan gari.
Lantana ta koma ta zauna ,gami da kunne redion ta tasaka kasat din wakokin bar mana coge tana ta zubda habaici a gidan,jira kawai take su tanka ayi wace za’ayi
Su dai sukayi mata shiru suna Aikinsu,
Bayan da suka gama ne daya ta tafi domin Kiran shattu ta shigo da Amarya dakinta.
To can kuwa gwaggo laraba ta sanya Suwaibah a gaba tana ta yi mata fada tace”duk Abinda lantana zatayi babu ruwanki da’ita idan mijinku ya fita kine mi izinin zuwa nan gudun fitinar laraba ,sai miyi zamanmu idan ya dawo sai ki koma,
Kinji ko?
Suwaibah ta daga kai tana zubar da hawaye gami da tuno Dan ginta da “yan Uwanta ,Rayuwa kenan
Kafin su watse sai da shatu takara yi mata fada sosai San nan tafito ta tafi
Lantana Na zaune tsakar gida tana jiran shigowar ,malam Tanko ,Domin yau ko me za’ayi sai dai ayi taci Alwaashin bazai kwana da Amaryarsa ba tunda ya munafurce ta,
Sallau ya shigo fudun! Fudun! Dashi kayan jikinsa duk datti tsabar kazanta jikinshi in banda tsami babu Abinda yake yi
Ya zauna kusa da Babarta sa gami da cewa”lantana me kikeyi har yanzu baki je kin kwanta ba ,goma fa ta wuce yanzu”
Tace”INA jiran babanku ya shi go Ayi wacce za’ayi”
Yace”to Ina Abinci Na”?
Lantana tace “kaga sallau !!wane irin Abinci kuma ,zan baka? Da girmanka da komai ,ni yau ban yi girki ba,ka kyale ni inji da Abinda ,ya dame ni”
“Gaskiya dole in yi Aure nima nagaji da wannan Abin da a ke mana a gidan nan Abinci ma sai a hanaka”
Dubi Yunusa dake shi Ubanshi yana sonshi ai yayi masa Aure ya bashi Abin yi da gurin zama,Amma mu muna zaune, gaskiya da sake ,bari Baban ya shigo yasan wacce zaiyi, shikkenan sai mu zauna muna kallonshi yana Aure Aure ,duk kudinshi su kare ta nan gurin. Sai bayan ya mutu mu tashi a tutar babu”
Lantana ta gyara zama tace”Yo dama ai tuntuni nake fada muku Ku San Abin yi wallahi domin Malam baya tataku ,kaima kaje ka nemo matar Aure ,ihe! Duk in da kudi suke yafito dasu yai maka kuma dole ya baka jari da gurin Zama”
Sallau yace “ai Abinda zan yi keanan kuma zan fara binkicen a dakarsa ta waccan dakin nasa da baya son Abude nasan da a kwai Abubuwansa a ciki masu Amfani ,zan bi dare Na sacesu ,a kan ya Qarar dasu a banza ba mu mori ko kwabo ba”
Wata dariya Lantana ta fara yi cike da Farin ciki tace”shiyasa nake son ka Sallau ,ai kai ne maganainsa wallahi”
Sallau tace”wai har an kawo masa Amaryar ne”?
Dakin Suwaiba lantana ta kalla tana zabgawa harara ,tamkar da mutum take tace”tana ciki tana jinka munafukar banza!
BINTA UMAR ABBALE