GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL


Sati biyu da rasuwar su Fiddausi, su Latifa da Iklas sauran “yan matan dake gaban Kulu kenan,suka fara rigimar dole a raba musu gado suna so su fara kasuwanci,nan Hajiya Kulu tasa ai mata kiran Sarki! kan buk’atar ” yayanta.

Bayan Sarki! Ya gama sauraron maganganun Hajiya Kulu kan rabon gado,sai yace mata ta kwantar da hankalin ta insha Allah za’a raba a cikin satin nan, yayi mata sallama ya tafi, yarasa me yasa idan yana gabanta baya iyayin katab’us.

Limamai da shedu ya Tara kan rabon gadon akayi shi cikin adalci inda Sarki! Ya tashi da kusan rabin dukiyar me Martaba had’e da kadarorinsa, a matsayinsa na Namiji matan ma aka basu abunda Allah ya sharanta,, bak’in ciki kamar ya kashe Hajiya Kulu dan haka a daran ranar ta nufi gurin Tsito domin ta nemi shawarar yaya za’ayi.

Tana zuwa Tsito ya bushe da dariya yana fad’in dama nasan kina tafe ai”

Kulu ta zauna tana sauke nuffashi tace”Dole inzo gurinka domin ka had’ani da Mak’asudu yanzu anyi rabon gado komai yaron nan ya kwashe mu mun tashi a tutar babu”

Tsito ya kece da wata mahaukaciyar dariya yana fad’in gaskiya Hajiya kina dan son kud’i sosai, Mak’asudu na jin ki kuma yanzu zan had’aki dashi”

Ai kuwa Kulu ta gyara zamanta Mak’asudu ya hauro ya fara magana kamar haka” Kinzo kan wannan yaron Wanda ya tsaya miki a zuciya ko”?

Kulu ta d’aga kai, yace”Kije kawai zaki samu yanda kike so akansa ko yau kuka karar da dukiyarku, daga zarar kin tambaye shi kud’i zai baki jikinsa na rawa”

Kulu ta dunga godiya sosai Aljani Mak’asudu yace”Ki kawo min k’wai d’anye goma sha d’aya yanzu zan sha”

Kulu ta mik’e da niyar tafiya tana fad’in “Yawwa yanzu kuwa zan aiko Ladi dashi, godiya nake Ubana”


Ina labarin su Shamsiyya ne?

Satin Shamsiyya d’aya a gurin Arrama kullum ta Allah zai bata wannan rubutu yace ta shafa jikinta, sai yaga ta b’ingire yazo ya kwashi gara, ya wani murmure saboda yana samun biyan buk’ata yadda ya kamata yanzu tunaninsa yaya za’ayi ya kafe Shamsiyya s gidan,Ku kuma ta dunga kawo kanta gurinsa dole sai yayi aiki a kanta.

Shamsiyya duk ta rame ta figale sai uban nonowa da suka cika k’irji ta futo daga k’aramin d’akin cikin shirin tafiya tunda dama tun daran jiya yace aiki ya fara ci, saboda haka zai sallame ta amma ta dunga zuwa lokaci zuwa lokaci domin a dunga dubawa.

Godiya sosai take masa, yace”Kinanan zaune zai zo gurinki yace ke yake son aura ba waccan ba”

Cikin rashin dabara da wayo Shamsiyya taita zabga godiya tayi masa sallama ta tafi, tana cike da farin ciki ganin bukatat ta takusa biya


Lantana ce ta tafi mak’abarta da kanta
Ta samo k’asar sabon kabari ta kawo aka had’a maganin kamar yadda Arrama ya bada umarni, suna sauraron dawowar Shamsiyya

Shamsiyya ta dawo gida cike da farin ciki da annushuwa domin ta gazgata maganar Arrama gani take kamar ta auri Sarki! ta gama, Uwa! Taga duk ta rame ba kamar ranar da suka tafi ba, amma labarin da Shamsiyya ta bata na samun nasara yasa bata wani damu ba, suka cigaba da kulla yadda al’amarin zai kasance.

Sun yanke shawarar cewar Lantana ce zataje can gidan me Martaba domin ta gabatar da aikin nata,, Shamsiyya tace” Ai naji dad’in mutuwar me Martab wallahi ko babu komai zan sake kuma ina sa ran zan auri Sarki! Domin na san d’anshi ne zai gaje shi”

“Bari ke dai ” yar nan, ai bake kad’ai ce kikayi farin ciki ba har damu mun kusa hutawa dai da talauci mutukar kika auri Sarki! Ai kakarmu ta yanke sak’a”

Shamsiyya ta washe baki cike da farin ciki tace”Lantana ke zan fara kaiwa aikin hajji,domin ina ganin in bata dalilina ba,har ki mutu baza kije maka ba”

Lantana tace”Aikuwa dai ni kaina nakan fad’i haka,wallahi wannan bak’in talaucin namu ya ishe ni”

Dariya Shamsiyya tasa,, tana fad’in wai ina Babanmu ne”?

Tab’e baki Uwa! Tayi tace”Gashi can a kwance yau da lafiya gobe babu, sai kace me cutar farfad’iya kullum fad’uwa miyau na zuba”

Shamsiyya ta lek’a d’akin da Sallau yake kwance ta ganshi kan tabarma ko fulo babu,miyau sai dulala yake. Yana ganin ta ya d’ago mata hannu wai tazo,Shamsiyya ta mak’e kafad’a tana fad’in “Wallahi bazan zo ba Tabb! Ji wani zarni da d’akin yake,aini yau bazan kwana a d’akin nan ba, d’akin Wacan shegiyar zan bud’e in shiga in kwanciya ta”

Uwa!tace”Yo ba dole kiji zarni ba idan iskancin sa ya tashi nan yake sakar min futsari ke har guntin kashi sai ki gani a jikin wandonsa sai kace wani k’aramin yaro,duk yabi ya sakwarkwace aikin banza kawai”

Dariya sosai Shamsiyya take harda hawaye tana fad’in Lallai ba, tsufan ka da kallo tabdijam harka fara kashi da futsari aiko zan hayo masu jinya, domin ni bazan yi aikin kashi ba”

Uwa! Taja tsaki tana watsawa Sallau harara yana cikin daki yana kallon ta yana kuma jin duk abunda suke cewa bakin ciki kamar ya kashe shi,Uwa! Ta cigaba da cewa”Ai na kunshi takaici wallahi. da kike ji daga ni ko a gado wancan uban naku babu abunda yake iya tsinana min sai dai inyi kid’ana inyi rawa ta, solob’iyo kawai,, in banda shan taba babu abunda yasa a gaba”

Cikin dariya Shamsiyya tace”Tab!! Uwa! A lokacin ki kin tsula tsiyar ki. yarda kike so,ai daga ni babu sauk’i waiiii”

Uwa tayi shewa tana fad’in “Ke rabu dani dan ubanki, ko yanzu garau nake ji na,zan iya da d’an shekara goma sha bakwai ma”

Shamsiyya ta zare ido tace”Kice kawai Babanmu ya wulla kawai ki sha shagalin ki”

Duka Uwa! Ta kai mata suka sa dariya tamkar wasu k’awaye,Allah yasa lokacin da suke wannan zancan Lantana ta tafi siyo kalanzir d’in futalar ta.

Shamsiyya ta mik’e tana fad’in bari inje in kwanta wallahi duk jikina ciwo yake yi”

Ganin tayi hanyar d’akin Balaraba na da yasa gaban Uwa! Ya fad’i tace”Ashe zakuyi rigima da Walidi domin wannan d’akin da kike k’okarin shiga ya dawo nasa.

Shamsiyya tayi mata wani irin kallo tana fad’in aikuwa bai isa wallahi domin bazan iya shiga cikin zarni da warin kashi in kwana a ciki ba”

Uwa! Tace”Mu da muke kwana a ciki me ya cimu, kin san halin Walidi sarai ba saurara miki zai ba”

Shamsiyya ta juya tana bud’e Kofa tana fad’in “Sai kiyi kuma”

Uwa! Tsoran fushin Walidi take domin yanzu kusan shine yake d’aukar nauyin gidan,Saboda ita yanzu duk jarinta babu ta karar dashi gurin Arrama, da siyawa Sallau magani, Sai Mabaruka ta dawo daga yawon tallanta watarar suke cin abunci da d’an abunda ta samo.

Shamsiyya na bud’e d’akin Walidi ya shigo gidan cikin sallama……
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU


Gaisuwar Ku daban ce, mutanan kirki, a gaskiya inajin dad’in addu’oin da kuke min Wallahi nagode sosai da sosai,Allah ya kara zumunci


Takwara ta: Hajiya Binta Shitu

Hajiya Indo Amadu

Wannan pege d’in naku ne, kuyi yadda kuke so dashi, nice taku Binta Umar Abbale????????


BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????88

Da sallama a bakinsa ya shigo gidan, ganin Shamsiyya yayi a k’ofar d’akinsa tana k’okarin bud’ewa. Da sauri ya k’arasa gurin yana fad’in “Ke mai zaki min a d’akina ne,? sai kace wacce kika bani ajiya zaki bud’e min d’aki,wai ni garin yaya akai ma na tafi na bar d’akin a bud’e?
Ya k’arasa maganar tasa yana kallon Uwa! Cikin tuhuma.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button