GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Diriricewa Uwa! tayi, baki na rawa tace” Yo in banda ka fad’a ma yanzu ni bansan a bud’e ka bar d’akin ba”

Tsaki yaja ya juya yana kallon Shamsiyya cikin sigar rashin mutumci yace”Kinje kin gama yawon barbad’ar ki kin dawo gida zaki cigaba dai mana sace-sacen da kika fara ko”

A hasale Shamsiyya ta juya kamar zata kai masa duka tace”Kayi k’arya in maka sata wallahi, Yo ina abun yake banza shashasha kawai Kai har wani kud’i ne da kai wanda za a sata d’aki duk kud’in cizo da kwarkwasa”

“Kya k’araci sharrin ki dai ki matsa ki bamu guri banzaye masu mugun b’akin jini, duk sai an aurar da ” yan matan unguwar nan kuna zaune a gida,saboda mugun bak’in halin ku”

Tsabar bak’in ciki yasa Shamsiyya fashe da kuka tana kallon Uwa!tace”Kinajin irin cin mutuncin da yake min ko,kin ja bakin ki kinyi shiru”

Uwa! Tace” Me zan ce miki ai na fad’a miki tun kafin ki tunkari k’ofar d’akin, kin san halin Walidi farin sani”

Buge hannun ta yayi daga jikin k’ofar ya bud’e abunsa ya shiga yana fad’in, Balaraba dai ta huta da bala’in ku shegu sai ku k’araci bak’in cikin ku mutu”

Rashin abunyi yasa Shamsiyya ta dunga k’unduma masa ashar! sai kace “yar maguzawa,yana jin ta yayi mata banza,ita kuwa sai sake fad’i take Cewar wallahi duk ranar da tayi aure Walidi yazo yace ya santa sai tasa and’aure shi, yana daga cikin d’akin yana mata dariya,domin shi yanzu d’aukar mahaukata yake musu ita da Mabaruka,ganin har yanzu sun kasa gane gaskiya, dama shi Iro ba’a sashi cikin lissafin mutane masu nagarta.

Nan suka zauna har aka kira sallahar magariba mutan gidan suka fara dawo wa, Iya ta dawo daga gidan jikarta domin yanzu can take wuni saboda haihuwar da tayi,dake gidan babu nisa dasu.

Ita kuma Sadiya Matar Kawu Maman, tana zuwa nany ne wata makaranta pravite tana d’aukar albashinta me tsoka, shiyasa bata da damuwa ta wanke goma ta tsoma biyar babu abunda ya dame ta.

Uwa! Tayi tayi ta raba Sadiya da gurin aikinta Allah baiyi ba, ta k’ulla munafurcin da Sharrin duk Allah bai amsa ba,haka dai ta hakura amma tana bala’in jin haushin ace k’arshen wata yayi Sadiya ta shigo da kud’in ta, tayi cefane me kyau suci su sha ita da mijinta, ta zubo ko babu yawa ta kaiwa Lantana. Ita kuwa tai ya murna baki zai sauya abinci.

Sai wajan goma da rabi Mabaruka ta dawo gidan hannunta nik’i-nik’e da manya-manyan ledoji, cike da fara’a ta zauna kusa da mahaifiyar tasu, wacce take ta washe baki tana k’okarin bud’e ledojin kana ganinta kasan tana cike da farin ciki yau zasuci kayan dad’i da alama Shamsiyya tayi sabon saurayi”

Jin motsin Leda yayi yawa a tsakar gidan,yasa Lantana rarrafowa ta futo, domin taji sallamar Maburuka tabbas tasan ta kawo kayan dad’i, ilai kuwa tana futowa tayi arba da wata k’undumeniyar kaza gasashiya taji k’uli-kuli da tumatur da albasa,Uwa sai k’okarin kaiwa bakinta take. Lantana ta dunga washe baki tana fad’in Allah yasa banyi bacci kam,tun d’azu bacci yake so ya kwashe ni,Allah bai nufa ba”

Zam tayi gefan Maburaka tana tai mata banbad’anci Mabaruka ta ciro cinya da hak’arkari ta bata, sannan ta bata robar yoghot guda d’aya, tace”Shikkenan na sallame. Ki tashi kije ki kwanta”

Lantana ta mike tana. Fad’in “Ai ko baki fad’a ‘yan nan, Allah ya bamu alkari”

Babu wanda ya kulata a cikinsu duk suna can suna rubibin cin gasashiyar kaza me maik’o☺

Sai da suka kusa cinyewa sannan suka tuna da Sallau, Uwa! Tace”Wannan ragowar k’ashushuwan sai ku barwa babanku ki”?

Shamsiyya tace”Wallahi ni har na manta ma dashi”

Tab’e baki Uwa! Tayi ta mike tsaye tana niyar shiga d’akin take fad’in kin manta dashi ko na manta dashi, ummm”.

D’akin ta shiga,Mabaruka ta mik’e da Sauri,jiri yasa ta dafe bango sai da tayi minti biyu sannan ta d’an dawo dai-dai, cikin yanayin maye ta k’arasa bakin rijiya ta ja ruwa ta zuba a buta ta shiga band’aki.

Lokacin da suka gama alfashansu da saurayin batayi wanka ba,ko da yake a cikin motarsa suka yi komai, babu gurin wanka dole sai ta dawo gida.


Yau sati biyu da rasuwar su Fiddausi mutuwar me Martaba kuma ta kasance sati uku,, Waziri ya saki jiki sosai kullum yana zama a fada sai dare yake tashi sosai ya jinjinawa Mak’asudu domin da yarjewarsa ya samu nasara, tun bayan mutuwar su Fiddausi Mak’asudu bai k’ara tsotsewa wani jini ba,ya bari ne k’ura ta lafa, amma yana sane da iya adadin mutanan da akai masa alk’awari.

Komai yana tafiya dai-dai ta b’angaran Hajiya Kulu ita da yaranta, biyu daga cikinsu ma sun kaso auransu sun dawo gida, kullum sai su shirya su futa basa dawowa gida sai dare can,wani lokacin ma a can suke kwana. Hajiya Kulu kuwa kullum tana tare da k’awayenta “yan duniya sosai suke shek’e ayarsu Hajiya Kulu ta zama k’umgurmar ” yar lesbian, sosai take jin dad’in harkar shiyasa take ganin babu wani dalili da zai sa ta tadaina more rayuwarta yanzu ta fara, k’awarta Hajiya ta Masu, itace take kawo mata “yan mata zuguda-zuguda. Sai ta biya ta kudi masu tsoka.

Kuma duk abunda ta tacewa Sarki! Ya aikata sai ya aikata shi,domin baya tsallakewa umarnin ta.


Yau saura kwana uku d’aurin auran Sarki! shine dalilin da yasa gidan ya hautsine da shirye-shirye b’angaran Mama Fulani ma haka bayi sai shige da fuce sukeyi, Mama Fulani taso Sarki! Ya d’aga lokacin d’aurin auran sai bayan futarta daga takaba. Yace tayi hakuri kawai a d’aura yanzu burinsa kawai a d’aura auran ya wuce gurin domin sunyi magana da governor maganar zama a fada yace sai bayan auransa wannan zai fara zama domin shine cikar mutum, wannan magana da Sarki! Yayi itace ta kashe masa jiki, yasa ya hak’ura kawai,amma sam baya kaunar ganin Waziri kan kujerar mulki domin sam bata dace dashi ba.

Halisa na keb’e a wani guri, a cikin gidan dai, Madabo da sauran ” yan uwansu suna kula da ita tare da gyara mata jikinta sosai domin Madabo tace “yar baza tayi boranci ba,dole sai tafi sauran matan da zai aura shiyasa tasa ake had’a ta sosai

To itama Azima tunda aka fara hidamar bukin ta tafi garinsu domin ta shirya tsaf, duk da yake ita kullum cikin shiri take Mamanta ma ba a zaune take ba.

Su Shahid da Shatima ne suke fad’i tashi tare da shige da fuce, ganin ko wacce a bata hakkinta a kwatuna iri d’aya suka siyo irin me sha biyu nan, duk a bubuwan dake cikin d’aya a kwai a cikin d’aya,Kai dai-dai da kayan bacci iri d’aya suka zuba musu, takalma mayafai gasu nan birjik,gaskiya sun had’a musu kaya kamar hauka.

Mama taji dad’in k’okarin dasu Shahid sukeyi domin in ta Sarki! Ne sai dai a d’aura auran babu lefe sam taga bashi ne a gabansa ba.

” Yan uwa da abokan arzik’i Mama ta kira suka mik’awa ko wacce nata Balaraba dai nata suna gaban Mama,inda tayi-tayi da ita tazo ta duba kuma ta d’ibi wanda take so a d’inka mata Balaraba kunya duk ta hanata, haka Mama ta hak’ura ta kira Jakadiya Shafa’atu ta d’ibar mata atamfofi da lesuka masu kyau da tsada a ka kaiwa masu d’inki.

Yanzu Balaraba bata futowa falo sosai, kullum tana d’aki a kulle indai ba Mama CE take kiranta ba bata futowa saboda wata irin kunyar ta da take ji,Su Sadiya kuwa ai sun zama “yan gari sun saba da Mama sosai hakanan Jakadiya Shafa’atu in zata wani guri sai ta tafi dasu domin suga gari.

Shi kansa Sarki! Ya kwana biyu bai sanya ta a idonsa ba, daurewa kawai yake amma kwanakin nan yana yawan jin fad’uwar gaba idan ya tuna da ita,kasancewar shi mutum ne Wanda baka ganin damuwarsa sai ta kai ta kawo shiyasa lokaci guda baza ka fahimci halin da yake ciki ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button