GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Misalin hud’u da rabi na yamma Balaraba na zaune gefan gado tana duba wani k’aramin littafi irin na addu’oi, tana sanye da wata doguwar riga mai uban kyau da tsada rigar taji stone masu shek’i wuyanta da hannuta tayi amfani da k’aramin hijab irin me hulan nan fari k’al dashi, dai-dai kafad’arta ya tsaya, fuskarta tayi fayau sai annuri ne yake sauka, dama can ita wannan kwaliye-kwaliyen bai dame ta ba,ko Wanka tayi k’ark’ari ta shafa mai sai hoda,da kwalli sun ishe ta, amma fa akwai son k’amshi jidin jikinta na k’amshin turare.
Sadiya ce ta shigo da saurinta tana fad’in “Yayarmu kizo inji Mama,wai zaki kaiwa Magajin Sarki! Abunci yana zazzab’i”
Balaraba gabanta ya fad’i jin abunda Sadiya tace, tace”Wai ke ba na hanaki rashin kamun kai ba, don Allah dube ki sai wani rawar jiki kike yi”
Sadiya ta sunkuyar da kanta tana jin tsoran fad’an yayar tata.
“Karki k’ara shigowa babu sallama kuma ki daina wannan gudun da kikeyi”
Sadiya tace “To”
Ajiye littafin tayi kan gadon ta mike tsaye tana gyara zaman hijab din nata,tace”Yana ina ne Magajin Sarkin”?
“Yana shashensa tare da abokansa,muma bamu dad’e da dawowa ba ni da Usuman tun d’azu muna can”
Ita fa bata son zuwa shashensa gudun abunda ka iya zuwa ya dawo ta lura wani irin mutum ne shi, me saurin tab’a jikin mace ko haka yakewa sauran matan oho shi dai ya sani, amma dole zata kiyaye ta daina sakar masa jikinta.
Niko nace Balaraba kenan maganar sakin jiki ta k’are tunda an kusa d’aura aure
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate, motivate and entertain aur Reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM
Tsokaci
Tun farkon farawa na fad’a cewa ban rubuta littafin Gimbiya Balaraba domin in ci zarafin wani ko wata ba, ku wani jinsi mutum me k’iba ko siriri, wannan labarin k’agaggene daga ni, Binta banga dalilin da zaisa kawai in ci mutum cin wani jinsi ba,kamar yadda wata “yar uwa ta fad’a min, Asali ma, wannan jinsin mutane da take magana akan su ina cikinsu to kun gani idan naci musu fuska har dani a cikinsu, Allah da kan shi ya hallici d’an Adam kuma ya karrama shi, duk a cikin hallitunsa ni Wacece da zanyi ciwa hallitar Allah fuska,, labari ne kawai saboda haka don Allah mu San abunda zamu dunga fad’a akan ” yan uwanmu
????89
Mama Fulani na zaune a falo ita da Jakadiya Shafa’atu suna hirarsu cikin mutun ta juna.Balaraba ta futo a nutse ta k’araso inda suke ta tsuguna tana gaishe da Fulani.
Cikin “yar fara’a Mama Fulani ta amsa, tace” Dama nace Sadiya ta kira ki kaima Mutumin ki abunci yana can shashensa tare da abokansa su Shahid,watak’ila ya fi maida hankali yaci abuncin, tunda bashi kad’ai bane”
Cikin jin nauyi gami da kunya Balaraba tace”Mama Sadiya tace bashi da lafiya yana zazzab’i”?
“Ba wai bane, da gaske ne, yau ya tashi da zazzab’i amma dai yanzu nasan jikin da sauk’i tunda d’azu ma ya shigo mungaisa”
Balaraba ta mik’e tana fad’in Allah ya sawak’e, Mama ina abuncin yake”?
Can wani katafaran gurin cin abunci ta nuna mata tace “Kije ki had’a masa,amma yace nacin mutum uku za’a had’o in yaso in kika gama sai ki kira d’aya daga cikin ” yan matan dake aiki a waje ta d’aukar miki’
Balaraba tace”To ta mik’e ta nufi gurin cin abincin.
A nutse ta had’a masa komai yadda yace d’in, Mama tasa Sadiya ta kira wata baiwa me suna Lahira ita tazo ta d’auki kwandon abincin suka futa tare da Balaraba.
Tun washe garin rasuwar Maddibo rabonta da b’angaransa shiyasa yanzu da ta shigo taji gabanta yana fad’uwa tunowa da tayi da rayuwarsu da Moddibo wasu hawaye ne masu zafi suke k’okarin zubo mata, ta fara k’okarin mai dasu,,.
Wasu k’yatattun takalma ta gani a bakin k’ofar shiga falon, kuma tana d’an jin magana a ciki, sai ta gyara yanayin ta,ta koma Balaraban ta ta asali, cike da jarumta tayi sallama ta shiga falon, Rahila na biye da bayanta.
Yana kishin gid’e cikin wata shirgegiyar kujera,me kamar k’aramin gado da wasu k’ananun fililluka a kai, daga shi sai boxar da k’aramar shart me k’aramin hannu,abunda yasa yayi wannan shigar saboda jin jikinsa ya d’auko zafi gumi sai zuba yake,dalili yasha maganin zazzab’i shikkenan gumi sai karyo masa yake ko ta ina,shine fa yayi Wanka ya sanya k’ananun kaya,yazo ya ware AC har suna rigima da Shatima saboda k’arfin AC d’in yayi yawa,shi kuma yace ya rabu dashi haka yake so.
Hira suke irin ta abokai Sarki! Yana daga kishin gid’e yake sa musu baki, zumbur! Ya mik’e da sauri ya nufi tv memory ya zura jikin DVD ya kuna sai gasu shida Maddibo sun bayyana jikin faskekiyar TV plasma dake manne jikin bango, suna zaune cikin makaranta a can america new york, can sukai karatunsu, wani abokinsu ne me yawan yi musu photo da vidio, ranar dai Sarki! Ya samu memori ya bashi yace duk sanda suke zaune shida Moddibo suna karatu ko suna wani abun Ku suna hurawa to kawai ya dunga d’aukar su a hota ko yayi musu video aiko Ashir baya gajiya mutuk’ar yana kusa idan yagansu sun keb’e kawai sai ya ciro memori a zura a wayarsa yayi tai musu hotuna had’e da video.
Shahid da Shatima duk sun rud’e ganin Moddibo jikin tv kamar kayi masa magana ya amsa,kai wannan duniyar abar tsoro ce.
Balaraba na shigowa idanunta suka sauka akan fuskar tv Moddibo tayi tozali dashi yanai wa Sarki! Magana yana dariya
Kwandon da yake hannuta ta saki ta k’wala k’ara jikinta ya fara k’arkarwa, “Inallahi wa’ina ilahi raji’un”
Jin gina tayi da bango tana sauke a jiyar zuciya bakinta sai motsi yake.
Dukaninsu kallon ta suke sosai saboda ba suji lokacin da ta shigo ba, sai ihunta da sukaji Shahid ya zubawa fuskarta ido yana tunanin a ina yasan fuskar tabbas yasan me wannan fuskar
Shatima kuwa gulma yake son yayiwa Sarki! Sai ya lura babu fuska yaja bakinsa yayi shiru,amma fa bakinsa da akwai magana, domin yana kokwanton anya ba wannan ce,Balaraba da yaji Mama tana yawan ambatar sunanta ba.
Tv take kallo babu k’iftawa wasu hawaye masu zafi suna biyo kumatunta. Maddibo ne yake magana tamkar ta kirashi ya amsa mata.
In banda sautin kukan Balaraba babu abunda yake tashi a falon, Tsura mata ido yayi babu k’iftawa, wato har yanzu yarinyar nan bata far kukan mutuwar Moddibo ba kenan,a ganinsa ta shigo musu babu sallama kuma tazo tanai musu kuka babu gaira babu dalili.
Shatima ne da ya fuskanci kukan me take ya tashi da sauri yaje ya kashe tv d’in ya dawo ya zauna yana mamakin ta.
Shahid ne ya mik’e ya k’arasa inda take tsaya ya fara rarrashinta da kalmomi masu sanyaya zuciya, ya jima yana tausar zuciyarta sannan tayi shiru tana share hawayen ta, k’okarin futa take ba tare da tace musu komai ba.
Shahid yace”Ranki ya dad’e ai baki bamu abuncin ba, zaki futa kuma bamu gaisa ba, ya kamata kizo ki duba mutumin naki kafun ki futa”
Shahid yana da k’ima da mutumci a idonta, ta lura yasan abunda yake, kallonsa tayi babu yabo babu fallasa ta gaishe ya amsa fuskarsa a sake, tare suka jera suna tafiya har cikin falon.
D’auke kansa yayi daga kansu, yarinyar yau tayi masa kyau sosai tamkar wata balarabiyar k’asar saudia shigar tayi mata kyau, yana so ya ga mace na suturce jikinta.