GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannuta rik’e da kwandon abuncin ta nufi gurin cin abunci,shi kuma Shahid ya zauna kusa da Sarki! Suna magana k’asa-k’asa.
Mik’ewa yayi yana mik’e duk jikinsa ciwo yake masa, Tashi sukayi suka bi bayan sa.
Tsaf! Ta had’a musu kowa da plate d’insa, ta kalli Shatima da yake satar kallonta sosai yarinyar tayi masa kwarjini da yawa.
A nutse tace”Ina wuni”?
Shatima ya amsa da sauri sai murmushi yake yace”Lafiya lau amaryar mu, yo ke haka ake daga shigowa sai ki fara kuka uhum”?
Shiru tayi tana satar kallon Sarki! Da yake juya abunci da alama yunwa yake ji, tunda yake Neman abunci da kansa, tarasa wani irin mutum ne shi da baka gane gabansa da bayansa fuskarsa a sake take amma ko da wasa yak’i kallon inda take, abuncin sa yake ci kawai, su Shatima sun rik’eta da suturutu ita kuma tana ta k’okarin yaya za’ayi ta gudu domin mutuminta da yayi mata wani mugun kwarjini gashi tana so ta gaidashi amma babu fuska. Da k’yar dai tace” Barka da yamma”?
Shiru gurin yayi su Shahid suna kallonsa sun san da shi ake”
Lumshe idonsa yayi ya cigaba da cin abuncin sa, bai amsa ba. Shatima yace”Ana magana fa”
Da gefen ido ya kalleta ya d’an tab’e bakinsa yace” Naji ai bazan amsa ba, tunda duk sai da ta gama wulak’ancin ta sannan”
Shatima yace”Amarya ce fa kasan amarya bata laifi komai tayi dai-dai ne”
Wani irin kallo yayi mata me d’auke da ma’anoni daban-daban yayi wani murmushi irin na gefan baki,yace”Ai ba ita kad’ai gare ni ba, Anjima kad’an nasan Halisa nan tafe,kaga kuwa ai bazan damu ba”
Balaraba sarkin d’aukar zafi! Fuska ta turb’une duk idanta ya rufe,wani kallo ta watsa masa,suka had’a ido dashi, tsaya wa yayi yana mamakinta, wani irin Abu tayi da idonta ta kalli su Shatima muryar ta a cunkushe tace”Ni zan wuce ku tashi lafiya”
Sauka tayi daga kan step d’in ta fara tafiya a nutse zuciyarta duk babu dad’i ta lura Sarki! Zuma ne shi ga zak’i ga harbi,dubi yadda kwana ki ya dunga lallab’ata har tana yi masa d’aukar mutum me saukin hali a she ba haka bane,wannan halin nasa nan, halin wulaknci da raina mutum,yo ita ina ruwanta ko mata dubo zai aura a rana d’aya ba damuwar ta b’ace,shine bai sani ba ita tafi sha’awar zamanta a haka tunda tayi rashin babban masoyinta Modiibo.
Shatima yace”Allah ya huci zuciyar gimbiyar mata, ai dukaninsu kin sha gaban su, kar ki manta ke fa amanrmu muce,bayan haka kuma kina da babban matsayi a zuciyarmu ki kwantar da hankalin ki.
Ko waigo wa batayi ba, ta bud’e Kofa tai fucewarta Rahila na tsaye na jiran futuwar ta sai ta take mata baya.
Shahid yace”Lallai addu’a ta ta karb’u, wannan yarinyar ba itace wannan yarinyar da sukayi saukar alk’urni shekaru biyu da suka wuce ba”?
D’aga kansa yayi kawai.
Shahid yace”Allah sarki Moddibo Lallai na yarda zuciyoyinku d’aya duk abunda kuke so iri d’aya ne,Allah bai hukunta zai aure ta,ba sai ya kawo maka ita har gida”
Shatima yace”Ni wallahi abunda kayi mata ne ya bani haushi da alama yarinyar tana da hankali da nutsuwa,kawai sai ka ci mata fuska, kasan dole taji babu dad’i a zuciyarta.
????????????????????????????????????????????????
_*GIMBIYA BALARABA*_
????????????????????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
LOODING......
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate,motivate and entertain aur Reades
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????91
Balaraba tayi k’asa da idanunta domin baza ta iya jurar had’a ido dashi saboda kwarjini da Allah yayi masa.
Niyar koma dakin take, yayi gyaran murya tsayuwa tayi. Ta d’an waiwayo suka had’a ido lumshe nasa yayi ya bud’e baki a hankali yace”Jimana”
Sak tayi jin abunda yace wai jimana! Sai kace Wanda bai san sunanta ba.
Ahankali ta taka ta k’arasa inda yake zaune, mik’ewa yayi yana gyara zaman sa,idanunsa a kanta, ita kuma tana tsaye gefansa duk jin ta take a takure, sai gyara fuskarta take.
“Zauna zamuyi magana dake”
Cikin k’asaita gami da jan’aji ta zaune kujerar gefansa.
Cikin bada umarni yace”Ki dawo wannan domin maganar da zamuyi dake tanada muhimanci”
Kujerar da yake nuna mata ta kalla, ita fa bataso tana had’a ido dashi domin. Idanunsa suna mutukar kashe mata jiki. Dakewa tayi tace”Duk maganar da zamuyi muyi ta anan da can da nan duk d’aya ne”
Shiru yayi na minti biyu, yace”Na fi so ina kallon fuskarki maganar zata fi armashi”
Tab’e baki tayi tana d’an hararsa, minti biyu da maganar tasa ta mike a nutse taje ta zauna kujerar da ya nuna mata, zama tayi irin Wanda ake Dora kafa d’aya kai d’aya.
Kallonta yayi yana mamakin zaman k’asaitar da tayi, babu Wanda ya isa yayi irin Wannan zaman a gabansa, ba tare da ya karb’i hukunci ba, amma da yake ya san halinta sai ya share kawai ya gyara fuskarsa sosai idanunsa ya zuba mata babu wasa yace”Inaso ki yi min bayanin Asalinki dana mahaifiyar ki, domin inajin a jikina akwai wani al’amari a game dake, bazan b’oye miki ba, nafi k’arfin shekara goma shabiyar ina mafarki dake tare da wata mata da alama mahaifiyar ki CE,tunda kullum tare nake ganinku kuna zuwan min cikin mafarkina, wannan mafarkin babu Wanda yasan dashi sai ni sai ke, yanzu Dana fad’a miki”
A kori kura guda biyu aka cika da kayan masarufi, su Shatima suka nufi gidan su Balaraba inda suka samu rakiyar daga Bubu direba tunda shi kadai ne yasan gidan.
Sosai Shahid yayi mamakin inda mahaifar Balaraba take,ashe dama ‘yar talakawa ce tilis, Lallai so babu ruwanshi ko a mafarki bai tab’a tunanin zai iya zuwa irin wannan gurin ba, Soyayar da Moddibo yakewa Balaraba ta gaske CE. Tabbas yayi mamaki da ya kalli yanayin jikinta da fatar ta, idan zata kwana tana rantsuwar babu Wanda zai CE a cikin irin wannan guri take rayuwa.
Yara ne suka fara taruwa a gurin suna tsale suna d’ane mota sai su ruga da gudu, hankalin Samar in dake can tsallake ya dawo Kansu da sauri suka k’araso gurin, Buba Direba ya bud’e mota da sauri ya futo ya bud’e wa su Shahid suka futo, ganinsu cikin kayan sarauta yasa yara zurawa da gudu zuwa gidajansu suna ihu! Suna fad’in ga sarki! Sarki ga sarki! Mutane suka fara lekowa daga gidajansu. Da sauri Shahid ya umarci matasan nan dake tsaye a gurin yace su fara d’ibar kayan nan suna shiga dashi, lungun su Balaraba, Buba yayi gaba, sukuma suka koma cikin motar saboda hayaniyar jama’a, yuuuuuu!! Jama’ar dake gurin yara da manya suka rufa musu baya domin ganin ina za a shiga da wannan uban kayan masarufi.
Lantana ta sawo Kai kenan zata futo daga cikin gidan suka buga karo da Sauri ta koma da baya tana masifa!
Abokin Walidi yace”Lantana ina zakije ne”?
D’ago kai tayi a fusace za tayi masa masifa”Aik.. Idonta ya sauka kan k’aton buhun shinkafar dake kansa ta bud’e baki kenan za tayi magana, sai ta hango matasa hud’u kowanne kansa da buhun shinkafa irin na kan Abokin Walidi kuma da alama suma gidan zasu kaita,, Zanin jikinta ne ya sabule garin sauri ta buge da kyaure bata damu ba, da sauri ta tsugans ta dauki zaninta da ya fad’i k’asa tana tafiya tana d’aura wa gami da k’walawa Maburuka kira.
A nutse take kallonsa tace”Bangane kullum kana mafarkina ba, a ina kasan ni ka san uwata da har zaka dunga mafarkin mu”?
Ta karashe maganar cikin mamaki.
“Duk ba wannan na tambaye ki ba,duk wata maganar ki ki aje ta gefe guda ki fara bani amsa ta tunda nine na tambaye ki”