GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna tafe suke maganar har suka isa shashen nasa Shatima ya zauna kan kujera yana fad’in “Sai yanzu gajiya ta fara damuna kuma”

Shahid yace”Duk ba wannan ba, abunda wannan mutumin ya fad’a fa abun dubawa ne, Tsalle d’aya mutum yake ya fad’a rijiya,Wannan Kalmar a hausance meye ma’anarta”?

Wani k’asaitaccan murmushi Sarki! Yayi yace”Ku rabu dashi don Allah inajin shine zai fad’a rijiyar ya kasa futowa”

Shatima yace”magana ce me harshen damo kuma da gani akwai wani k’ulli

Shahid yace”Nima na lura da haka wallahi tunda muka doso inda suke, suna magana k’asa-k’asa”

Tab’e baki Sarki yayi yana kici-kicin cire babbar rigar dake jikinsa yace”Mugun k’ullinsa zai koma k’ansa ni ina tare da Allah”

“Wannan magana haka take,duk mutumin da yake tare da Allah kuwa to babu abunda wani mutum zai masa ba tare da Allah ya tsare shi”

Su Shatima ne suka fad’i wannan maganar.

Zama yayi kusa da Shahid da gashi sai Singelt da dogwan wando na shaddar dake jikinsa, yana fad’in zafi nake ji wallahi ga yunwa kasan tun jiya da yamma rabona da cin abunci”

Shahid yasa dariya yana fad’in ai zama da yunwa ya k’are me mata hud’u rigis”

Gabansa ne ya fad’i kad’an shi kansa yana tunanin yarda za’ayi ya zauna dasu lokaci guda.

Shatima yace”Mutumina ai jarumi ne, zai iya rik’e su, ni dai INA ja maka kunne da kayi adalci a tsakaninsu”
Shatima ya k’arshe maganar yana dariya

Hararasa yayi yana fad’in “Ank’i ayi adalci me yasa su baza ka fad’a musu suyi min adalci ba sai ni zaku ta damu da maganar adalci, duk wacce tafi kyauta ta min itace Gimbiya ta”

Dariya suke masa,Shahid yace”Maganar haka take duk macan da take kaytata ma kafi jin ta aranka. Ammafa kowa ce mace da irin nata salon wata akwai iya salo da jawo hankalin me gida da iya kwanciya wata kuma iya girki da iya hira wata kuma iya kwalliya da tarairaya duk dai gasu man, idan Allah ya hore maka mace me ibadah fa duk wannan abubuwan Dana fad’a to kayi sa’a a rayuwarka”

Shatima yace”Wannan maganar haka take”

Shiru yayi musu suna ta zubah, mik’ewa yayi ya je ya k’aro k’arfin AC sosai yake jin zafi abunka da wanda be saba ba,ya shiga cikin jama’a ga rana da cukurkud’u kowa naso ya gaisa dashi, shiyasa ya daure ya dunga gaisawa da jama’a domin futa hakkinsu

Shahid ne ya kalle shi yaga yana lumshe ido, yace”Ko a sa a kawo abunci ne”

Bud’e ido yayi yana kallon daining, babu komai a kai, d’aga kai yayi ya mayar da idonsa ya lumshe.

Shahid ya mike yana k’okarin futa, bud’e idonsa yayi a karo na biyu yace”Kasan me”?

Shahid ya tsaya yana kallonsa, shi kuma yace”tea nake so mai kayan kamshi da tafarnu idan nasha shi duk zan daina jin wannan mutuwar jikin”

Shahid yace”Bari in shiga shashan Mama yanzu nasan za’aha da maka”


Wasa farin girgi Shahid na futa yaga jama’ar gidan sun dura sabon buki irin na al’ada sai cashewa suke ana ciye-ciye ga masu kad’an k’warya nan sai bugawa suke “yan mata sun shiga suna ta rawa, gefe kuma wasu maza ne suke wasan wuk’ak’e, kai guri ya hargitse da sawu dukuna kowa na tashi murna, ko da yazo giftawa ta shashen Hajiya Kulu nan kad’e-kad’e ne kawai yake tashi irin na turawa,ta tara k’awayenta suna ta tsula stiyarsu Tsito ma yana zaune cikin mata yana ta busa sigari, duk macan da tayi masa sai daki d’uwawunta yana dariya aikuwa sai su saki shewa suna k’ara rawa da murgud’a d’uwawu” a gurin wasu daga cikinsu suke aikata fasadi batare da damuwar kowa ba.

B’angaran Mama ma buki suke sosai irin na al’ada “yan uwa da abokan arziki sun cika mata falo kowa yazo taya ta murna, tana zaune cikin shiga ta alfarma ta fuskarta cike da walwala, Gimbiya Halisa tare da Mahaifiyarta Madabo suma nan suke hidimar bukin tare da Mama Halisa taci uban ado gwal ko ta ina alkyabar dake jikinta ma abar dubawa ce sai sheki take, jama’a sai kallonta suke ita kuma kanta yana kara girma dama so take ace tayi kyau , Taso Balaraba ta futo amma fafur tak’i futowa tana kulle a cikin d’aki kunya take ji sosai ita baza ta rashin kunyar da Halisa take ba, Lantana kuwa ai ta saje cikin mutane ta zama ” yar gari sai kutsawa take tana shigshigi ga jama’a,,

Tana sanye da wani irin material me kyau da tsada Multi color ne jikinsa duk stone anyi mata wani irin d’inki bubu wuyan rigar yaji stone work sosai tayi kyau kamar ka sace ka gudu d’aurin d’ankwalin da tayi ya k’yatar sosai Sam babu wani tarkacan kwaliyya a fuskarta, tana zaune gefan gado tana sak’awa da kwance wa su Sadiya kuwa Duk suna waje tun safiya.

Da k’yar Shahid ya ganin Mama Fulani yayi mata bayanin abunda ya kawo shi, tace”Bari yanzu za’a had’o akawo muku in yaso d’aya daga cikin matan nasa sao tazo ta had’a muku abunci”

Godiya yayi ya futa ta k’ofar baya,

Ita kuwa Gimbiya Azima dama can shashen Waziri ta sauka da jama’arta nan suke shagalinsu, don haka ko da ta shirya ta futa tare da wasu bayinta da ta tawo dasu suna take mata baya, kai tsaye shashen Sarki! Ta nufa domin da zafi-zafi ake bugun k’arfe a ganinta wannan kwaliyyar da tayi baza ta tashi a tutar babu ba, dole Wanda akayi domin shi ya gani.

Jakadiya Shafa’atu ce ta had’a musu duk abun buk’ata ta sanya baiwa Mariya wacce take shige da fuce shashen Sarki! Ta d’auko kayan abunci ta dunga kai wa can. Mama ta bi falon da kallo tana neman Halisa babu ita da alama ta futa, wasu k’wayenta ne suka zo, Sadiya ta kira Yarinyar tazo ta duk’usa Mama tace”Je ki kira Yayarku kice tazo inji ni”
Domin tasan idan ba haka akace ba Balaraba tana iya k’in zuwa.

Tana zaune taji sallama Sadiya kallonta take har ta k’araso kusa da ita tace”Yayarmu ka zo inji Mama”

Balaraba tayi shiru tana tunani Sam bataso ta futa mutane suyi ta kallon ka”

“Jeki ce gani nan zuwa”

Sadiya ta futa cike da walwala.

Mik’ewa tayi ta d’auki wani mayafi me kyau ta ya yafa har fuskarta sai da ta kusa rufewa, kanta a k’asa ta futa, kallonta kawai jama’ar dake gurin suke.

Har ta k’arasa kusa da Mama ta tsuguna tana fad’in ‘Mana gani”

Shafa kanta tayi tace”Allah yayi miki albarka Balaraba ya albarkaci auranku,, Allah ya baku “yaya nagari”

Duk jama’ar dake gurin suka amsa da “Ameen”

Mama tace”An kai kayan abunci shashen me mijinku kije ki had’a musu shida abokansa”

Gabanta ne ya fadi jin abunda Mama tace, a nutse tace ‘To Mama” mik’ewa tayi a nutsu take tafiya k’afafunta duk suna hardewa tasan idanun mutane dake gurin suna kanta, tana futa, kowa ya fara fad’ar albarkacin bakinsa a kanta.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????95

Da sallama a bakinta ta shiga falon.

Kujerar da yake zaune tana kallon k’ofar shigowa karaf suka had’a ido, kasa d’auke idonsa yayi daga kanta, ta k’araso cikin falon a nutse su Shatima suna amsa mata sallamarta.

Daining area ta tuna cikin yanayin tafiyar ta me d’aukar hankali, kallonta yake a sace har Shahid ya lura dashi sai ya tab’o Shatima yana nuna masa,suka dariya.

Wayancewa yayi ya kalle su yana ya mutse fuskarsa yace”Dariyar meye wannan”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button