GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

A daddafe yayi Wanka ya dauro towol dinshi ya futo yana goge jikinsa had’a ido sukayi da ita ta cikin mudubi, dukaninsu suka d’auke kai a tare,,, Murmushi ya saki Mara sauti cikin zuciyarsa yake cewa yarinyar nan fa bata da juriya da gani romance kawai ya labdatar da ita,, Lallai ya gano lagonta.
Tana kallon shi yana shirya wa cikin kaya irin nasu na sarauta sai k’ak’ale yake turare kamar yayi magana ya fesa yafi kala bakwai a jikinsa d’akin Duk ya gauraye da kamshi,,,
Cikin k’asaita ya nufo inda take tsaye yana k’araso wa ya rik’e hannuta ya bud’e k’ofar suka futa daga dakin, babu Wanda ya kula kowa a cikinsu har suka sauka k’asa.
Shatima yace”Ai da mu muna cewa kawai mu tafi amarya ta rik’e maka wuya,, Shiru yayi musu yana kallon Azima da tayi kicin kicin da fuska kamar ta kurma ihu ganinshi rik’e da hannun Balaraba sai annuri suke futarwa.
Shahid dariya kawai yake kunshewa ganin abokinsa yayi shar da shi yasan halin mutumin sa sai da ya d’ana abun,ganin Duk yanayin Balaraba da alama bata cikin nutsuwa domin Sam taki had’a ido dasu Zama yayi cikin kujera,, Har yanzu hankalinsa na kan Azima, ita kuma sai cunkushe fuska take.
Ganin haka yasa Balaraba ta yi hanyar futa daga falon tanai wa su Shahid sallama. Domin tasan halin dabbacin su Azima yanzu sai ta hau hauka da surutai Wanda ita kuma tana ji tana gani baza tabari su zageta ba,
Kallo ya bita dashi har ta futa,yw sauke ajiyar zuciya me zafi, duk suna kallonsa wata kibiyar kishi ce tazo ta tokarewa Azima makogwaro wai dame wannan yarinyar tafisu ne? Ta lura fa Sarki! yana sonta tunda gashi ya kasa b’oye son yana nunawa a zahiri.
Yanayin fuskarta ta gyara domin bata so tayi masa magana cikin b’acin rai! taga alama dole sai ta had’a da kissa da shiyasa, tace”Yallab’ai ina ta sauri inzo in nuna maka adona ashe ban sani ba “yar uwata ta rigani,fatan dai ta kula da kai yarda kake buk’ata idan kana bukatar wani Abu ta b’angare na ka fad’a yanzu in tashi in aiwatar maka dashi,domin duk mu du muna karkashin ka ne”
Lumshe idonsa yayi ya bud’e a hankali har yanzu yana tunano abunda ya faru shi da Balaraba na d’azu, a hankali ya bud’e baki yace”Itama bani na kirata ba, Balle kiyi min wata fassara,maganar bukatar abu ta b’angaran ki, sai ki Bari sai da daddare kizo ina neman ki”
Shahid dai da Shatima mik’ewa sukai suka nufi gurin cin abunci suka bar Shi da Azima.
Wani k’asaitaccan murmushi tayi tace”Godiya nake ranka ya dad’e ai dole in amsa kiranka,da kamar k’arfe nawa zanzo”? Ta k’arasa maganar tana karkad’a idanuwan ta.
Abunda takeyi ya bashi dariya sosai, dakewa yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa yace” Kizo ko da wane lokaci”
Azima taji dadin wannan abu tana ganin idan Sarki! Ya d’and’ana zumarta a farko, dole ya susuce domin ba k’aramin gyara tayiwa kanta ba, Mik’ewa yayi ya nufi gurin cin abunci, itama ta mike ta bishi a baya,, k’are masa kallo take a zuciyarta tana cewa Allah yayi hallita anan gurin,,, gaskiya yanzu sonshi da kaunarshi tsakani da Allah take, Sam baza ta yadda da auran sharad’i ba, yanzu ta gane dalilin da yasa Mahaifinta da Waziri suke son auranta dashi,saboda wata manufa tasu.
Lokacin da sak’o Mama ya isa gurin su Uwa! da Sallau cewar ga direba nan na jiransu su shirya “yan uwa da abokan arzki kai da duk me ra’ayin zuwa gidan sarauta ya shirya ga mota tazo daukarsu har gida, domin. Suje su kalli shagalin bukin Sarki! Tare da matayen sa uku.
Kafin kace kwabo unguwa ta hautsine kowa na shiri babu Wanda yake so a barshi a baya,wad’anda basu sani ba, sukaita mamaki jin cewar Balaraba d’iyar Ayuba ita tw auri Sarki! Almansur,, lallai kowa ne dan Adam da lokacinsa.
Uwa! Kuwa kuka wiwi! Ta dunga yi mutan unguwa sun cika gidan suna kallonta wasu na bata baki wasu kuwa mamaki sukeyi kukan me takeyi wasu daga cikinsu kuwa dariya suke mata sun San bakin ciki ne yake d’akinta,Sadiya matar Kawu farin ciki ya cika mata zuciya tabbas yau Allah ya nunawa Uwa! Ita ba komai bace a rayuwa , yarinyar da take rainawa ta hau wani matsayin da babu Wanda ya isa ya kaita kansa sai Ubangiji makagin baiwa.
Cikin farin ciki ta kulle d’akinta ta tsallake Uwa! Dake durkushe a tsakar gida tana gunjin kuka mutane sunyi dafifi a kanta suna bata hakuri, a zuciyarta tace” Kune wahallalu munafukai kawai, d’akin Iya ta nufa.
Tare suka futo da Iya sukayi fucewarsu, suka bi a yari zuwa gidan Sarki!
Duk wannan wainar da ake toyawa Shamsiyya da Maburuka basa gida. Shamsiyya dai, gurin Arrama ta tafi, ita kuwa Mabaruka wani sabon saurayin ta ne yazo ya d’auke ta a mota suka futa.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate, motivate and entertain aur Reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM
????97
Buki aka gudanar irin na al’adar masarautar ,matasan samari suka shirya kilisa, duk suka shirya dokunan su da ado me k’ayatarwa suka futa, yayin da masu busa da k’ida irin na gidan sarauta suka rufa musu baya suna aikin su.
A gaskiya shagalin buki ya k’ayatar ya kuma ni shad’antar, jama’ar unguwar su Balaraba, kafun su tafi sai da suka sa a kai musu iso gurin ta, suka gaisa sosai sunai mata fatan alkairi, Iya ta bata shawarwari sosai, Sadiya matar Kawu ta kalli Lantana wacce tayi kicin-kicin da fuskar ta, so take kawai su tafi gida, domin ita gani take kamar zasu ce zasu zauna kamar yanda tayi.
Tace”Lantana ai sai ki taso mu tafi haka tunda dai an gama shagalin buki ko”
Wata k’atuwar harara ta Dan k’ara mata tace”Ai sai kizo ki ja ni ki kai ni gida munafuka, ai ni naga gurin zama, kuje Ku k’arata da iskancin ku”
Cikin mamaki Sadiya tace”Lantana daga magana kuma sai ki fad’a min me zafi”?
“Ke kika jawo ehe! masu gidan ma basu gaji dani ba balle ke karan k’ada miya”
Girgiza kai tayi cike da mamaki tace”Ai gaskiya ce,Lantana ke da ya kamata kiyi wa wani fada kece kike aikatawa”
“To bana son gaskiyar, nace bana son gaskiyar, gaskiya ko munafurci dai”
Ta k’arashe maganar a fusace!
Iya ta kama hannun Sadiya suka wuce, tana fad’in “Ke ma dai kin tsaya Ki na daka ta Lantana kamar bakinsan halinta ba, yanzu sai tasa mu raba abun kunya ba damuwarta bane”
Akwai In da Mama Fulani take suka nufa, sukayi mata sallama gami da godiyar abun alkairin da a kai musu,, har wajan mota Balaraba ta rako su tare dasu Sadiya suna ji kamar su bisu gida, Balaraba ma idanunta duk ya tara kwalla haka dai sukayi sallama suka tafi, kamar yarda aka d’auko su a mota haka aka mai dasu gidajan su, kowan ne kana kallonsa kasan yana cike da farin ciki.
Bayan sallah isha ne, masu karatun al’kur’ani suka zauna farfajiyar gidan suka fara karatunsu, saukar alkur’ani me girma zasu yi.
Arrama yana ganin Shamsiyya afujajan, yasan da akwai matsala, tana zama ta fashe masa da kuka wiwi! Murmushi yayi yana mata wani irin kallo yace”Da kwai matsala kenan malama Shamsiyya”
D’aga kai tayi domin kuka yaci k’arfin ta kasa maganar.
“Shiga ciki ganinan zuwa”
Ya fad’a mata yayin da ya ke zane-zane cikin yashin dake gabansa.
Wuff Shamsiyya ta shige d’an a kurkin d’akin tana goge hawayen ta domin ita gani take tazo inda za’a share mata hawaye.