GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA

YARO DA KUDI

GIMBIYA BALARABA
????????????????
in kana bukatar cigabansi ga numbar nan
08089965176
[04/05, 03:08] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????writting by
BINTA UMAR
Maman Abdul Wahabu

RABBI SHARALI SADARI WAYYASIRLI AMRI WA’ALAL UQUDATUN MIN LISANI YAFQAHU KAULI

????13

Tashi sallau yayi yaje ya dinga buga kyauran dakin ,cikin sigar rashin mutumci ,yana zagin Suwaiba Matar mahaifinshi

Lantana tace” kayi min daidai ni dama nasan zaku share min hawaye Na”

Sallau yaciga ba da ciwa Suwaibah mutumci yace”Tsintacciya wace tafito yawon karuwanci ,Dole sai kin koma garinku ,Na gado mai sifar bararoji nan ba Nijar bace ,kin zo zaki lashe mu mayya kawai”

Suwaiba Na ciki tana kukan wannan cin mutumchi da ,salau ya ke sirfa mata!

Motsi yaji daga waje ,yayi saurin barin kofar ,Suwaibah yaje ya zauna kusa da lantana ,duk a zatonsa malam tanko ne,

Maman ne ya shi go fudun! Fudun! Yadawo daga yawonshi Na gidan kallo
Ya zauna bakin rijiya,yana hamma yace Lantana ina Abinci na?

Ban dashi!! Lantana tafada a zafafe tacigaba da cewa”gantalalle gama yawon Na ka zaka tambaye ni Abinci ai ko ina dashi bazan bayar ba”

Maman yace”to kar ki bayar mana ai nasan in da yake zanje in diba”

Tace”zagina zakayi ne Maman” wato baza ka dai Na yi min rashin kunya ba ko kana gananin Abinda mahaifinku yayi min”

“To me zan miki “yafada babu damuwa a fuskarsa yacigaba da cewa “karkari kawai duk abinda matarshi tayi min ko tayi miki in Zane ta ciki da waje”

Lantana tayi dariya gami da gyara zama tace” yawwa Dan arziqi irin albarka ,dama haka nakeso nasan kuna sona ,sabida haka. Mutaro mu takura mata kamar yadda mukaiwa wa”yancan yaran suka gudu ,har sai tagaji itama ta gudu da kafarta.

Sabida Azabar mu

Tace “kai kuma Sallau kabi dare da rana ka kwashe duk wani Abu da yake taqama dashi mu boye, domin baza mu tashi a tutar babu ba”

Sallau yace ai ba sai kin fada ba Lantana”

Dariya Maman yayi yace”gaskiya Lantana kin San ta kan Mugunta”

Ita ma dariyar ta sheqe da ita tana gyara zama tamkar wata sabuwar mahaukaciya tace” ai duk a gurina kuka koya”

Tace”bara Na kawo muku Abinci “yayan Albarka”

Ta mike tayi kchin tana sambatu kamar tababbiya

Suwaibah Na makale jikin kofarta tana jinsu ,Da duk Abinda suke kullawa,tausayin Malam tanko ya kama ta,sai tace”in sha Allahu Allah bazai Baku iko ba”

Goma da dara bi Tanko ya shi go gidansa,ya kulle gidan ,

Abin mamaki Su Sallau ya gani zaune sun kewaye uwarsu kamar masu Neman gafara

Yayi sallama
Suka Amsa ,ban da Lantana tana can tana kallon Abinda yake hannunsa!

Sallau yace Barka da dare?

“Barka kadai” Tanko yafada yana kokarin shiga dakin Amaryarshi

Sai lantana ta mike taje ta tari hanya ,cikin Neman tashin hankali tace”Malam baka isa ba fa”

Cikin nutsuwa Tanko yake kallonta ,Tamkar mahaukaciya yace”lafiyarki kalau kuwa lantana”

Rasss!! Nake tafada gami da buga cinya!

Tace “bani ledar hannunka ,tafada kamar wata Uwarsa!

Abin yabawa Tanko mamaki ,da yake tanko ba ya son raini ko kadan yace”bazan baki ba Lantana ranki zai yi mummunan baci idan baki kauce kin bani hanya ba”

Ta buga cinya! Cikin rashin mutumci da rashin kunya tace “bacin rai Na yaushe kuma ,Tanko kajima baka bata min ba,har kaje ka daura Aure batare da sanina ba sabida tsabar muna furci da Annamimanci kuma karasa wazaka Aura sai mayya kuma karuwa wacce ba’san daga in da take ba”
To sai dai kazaba ko ni ko ita ihee!!!!

Wani bacin rai ne ya turnike Tanko ,wai shi Lantana take zagi a gaban yaransa da matarsa,kawai sai ya fidda hannu ya tsinka mata mari ,ya hankade ta ,tafadi a gurin ya shige dakin Amaryarshi ya mai da kofa ya rufe gamma!!

Kuka Lantana ta rusa tana dukan kofar dakin da kafarta gami da zagin suwaibah ta uwa ta uba,makota Na jinta,

Sallau ya taso yana kokarin janye ta daga gurin tana fincikewa tace”sallau kaga yadda Malam ya fasa min hanci jini Na zuba ko”

Da sauri sallau ya lalubi Cocilan din shi da yake yawo da ita a Aljihu yana haska fuskar Mahaifiyar tashi

Ai kuwa ya sata habo gurin marin gashinan jini yana zuba a hancinta.

Da sauri yace”Maman zo kaga n”

Maman ya taso a fusace ya karaso gurin.yana dubawa

Tabbas jini ne yake fita a hancin mahaifiyar tasu,

Ganin yadda Maman yake huci yasa Lantana kara lanjarewa tana kuka sabida ta San halin Maman da bakar zuciya!

Suka janye ta daga bakin kofar suna rarrashinta ,nan suka yi mata Alkwarin daukar mata fansa a kan Suwaibah tunda duk a dalilinta Malam tanko ya zubar mata da jini ,Abinda bai taba faruwa ba ,
To suma sun dauki Alkwarin sai sun zubarwa da Suwaibah Joni


Tun daga ranar Su Sallau suka matsawa Suwaibah in har suna gidan bata isa ta fito ba sai su hau jifanta ko su sanya mata kafa tafadi ,ko du zuba karkashi kofar dakinta da ta fito tafadi kasa,
Su kuma Na gefe Na faman kyalkyala mata dariya

Ko idan tayi girgi ,suje su kwashe su cinye tai magana su zageta

Ranar Sallau ya dauki cokali mai ya tsu ya kai mata jifa a goshin ta,bayan ta fito daga ban daki,ai kuwa kan kace kwabo jini ya tsinke sai ta saki butar hannunta,ta dafe gurin tana jin wani mugun zafi

Lantana dake zaune kan kujera “yar tsuguno tana tsintar shinkafa ta kyalkyale da dariya,tace kayi min daidai Sallau!!

BINTA UMAR ABBALE

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????
in kana bukatar cigabanshi ga number nan
08089965176
[04/05, 03:09] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀
????GIMBIYA BALARABA????
????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀????‍♀

✍????Writting by
BINTA UMAR
MAMAN ABDUL WAHABU

BISSIMILLAHI RAHAMANIR RAHIM

????14

Suwibah ta dago kai tana kallon Sallau ,dake tsaye , zuba mata ido yana jiran ta tanka masa ,yayi mata wankin babban bargo!
Tafi minti biyar tana kallonshi ta gaza furta ko kalma daya,sabida tana tunin yin magana ,a yadda suke su kadai a gidan zasu iya yi mata duka,

Sai kawai ta wuce shi ta nufi dakinta jini Na diga a goshinta,

Suka kwashe da dariya suna nuna ta da hannu Lantana kamar ta tuntsira kasa Dan dariya
Tace “in kin sa kiyi magana mana”
Maman yace”wallahi Na dauka ma ramawa zatayi da naga tana kallonka.
Sallau ya zabura! Yace ta rama? Lallai da ta tarowa kanta Masifa tana cikin gidan Uban nawa”

Lantana tace “duk Ku rabu da ita a kwai Abinda zamu kulla mata idan an kwana biya”
“Zo kaji” tafada tana yafito sallau da hannunta

Rada tayi masa wacce ko Maman dake gurin a zaune bai jiba.
Su LA fashe da dariya murya kasa kasa ,Sallau yace”gaskiya Lantana dole a Sara miki’
Lantana tace ba dole ba! ai ni duk Wanda yaci tuwo miya ya sha dani

Ko da Malam tanko ya dawo yaga goshin suwaibah a fashe yayi tambayar duniya yaya haka tafaru taqi fada masa,sai ya rabu da ita kawai ya samo mata magani ,ta sha ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta,kwananan tana yawan yin bacci tarasa meye dalili.


To haka rayuwa tai ta tafiya har cikin suwaibah ya fito ,lantana ta daga hankalinta,sosai Amma da ta tuno Abinda suka shiryawa cikn ita da sallau sai hankalinta ya kwanta.

Cikin suwaibah Na da wata tara tana dab da haihuwa ko yau ko gobe, ta fito zata ban daki ,da kyar take taka kasa sabida tsabar nauyin da cikin yayi mata bayan haka kuma Mararta Na mata ciwo

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button