GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

A jigace Azima ta tashi tana cije bakinta sosai Sarki! Ya gurge ta tunda ya hau kanta bai saurara ba wajan awa guda yake sai da ya samu gamsu, gashi ya d’aga mata k’afafu sama yanzu ji take duk cinyoyinta ciwo ita kama baza ta d’orar da komai ba.

Da k’yar ta samu ta gasa jikinta ta dauro alwala ta futo ta tada sallah, kwanciya tayi kan daddaumar ta kama baccin gajiya mamakin k’arfin Sarki! Take kamar wani doki gaskiya ta gurzu.

Bakwai shaura ya shigo gidan, ya jima a waje yana gaishe-gaishe da jama’a nan ya tarar da Azima tana sharar bacci, girgiza kai kawai yayi ya shiga toilet da kanshi ya had’a ruwa yayi Wanka ya fito daure da towol, tsayuwa yayi dressing mrioow ya fara shirya kanshi,, komai yake a nutse yake, tsaf ya shirya jikinsa cikin wata shadda wagambari ta Asali sky blue duk ya wancin kayan shi sky blue ne,, d’inkin da akai wa shaddar abun kallo ne, wani takalmi mai kyau ya zura a kafar shi ya wai waya yana kallon Azima ko motsi bata yi ba duk da wannnan kusurkusur da yake a d’akin,mamaki yake na irin nauyin bacci irin haka, hannusa yasa ya d’an daki k’afafunta shiru bata motsa ba,,

“Azima”
Sunanta ya kira cikin hosky voice nasa, ina Azima Sam bata San yanayi ba,, sauka k’asa yayi kawai ya k’yaleta yasan dai tayi sallah tunda gata kan dadduma.

Bayin sa ne suke ta kai kawo a falon kowa na aikinsa, yana sakkowa suka dunga barin ayyukan su, suna zuwa suna kwasar gaisuwa,, Mariya baiwar sa kenan Wanda take hidamar gyara mishi bedroom, ta nufi sama, gyaran murya yayi,Mariya ta tsaya kanta a k’asa yace”Ki bar gyara d’akin yanzu wannan ba hurumin ki bane”

Mariya tace “Tuba nake ranka ya dad’e a ya fe ni”

Shiru yayi

Tazo ta wuce kanta a k’asa.



K’arfe goma da rabi na safe Halisa ta futo cikin k’asaitacciyar kwalliya, Mama Fulani na falo a zaune tare da Madabo Jakadiya Lantana Balaraba suna zaune kusa da Mama ana gaiggasawa kamar yarda suka saba.

Madabo na ganin d’iyar ta ta futo cikin shiga ta alfarma ta masu mulki sai wani dad’i ya kamata ita kanta tasan “yar daban take da kowa. Halisa ta zauna kusa da mamanta, tana gaida Mama Fulani, Cikin sakin Fuska ta amsa, Lantana kuwa sai b’arin jiki take tana gaida Halisa, ko kallonta ba tayi ba.

Balaraba ranta ya b’aci ganin yanda take wa mutane kallon banza, Jakadiya tace” Ranki shi dad’e an tashi lafiya”?

Halisa bata duba girman Jakadiya Shafa’atu ba balle ta a gaida ita, sai da ta gama shan k’amshin ta sannan ta amsa mata.

Mama Fulani ta tsani halin Girman kai irin na Halisa ga ta ga “yar uwarta a bokiyar zamanta amma tak’i kallon shashan da take, A nutse tace” Ga “yar Uwar ki nan ko Ku gaisa ya kamata tun yanzu Ku fara had’a kanku domin mijin Ku ya samu nutsuwa da ku”

Balaraba tace”Hakane Mama cikin Siyasa da iya zaman duniya tace”Ranki ya dad’e fatan kin tashi lafiya”?

Halisa kanta ya k’ara girma jin Balaraba na gaishe ta, amsawa tayi fuskarta babu yabo babu fallasa. Ta mik’e tsaya Maddo tace”Yawwa maza je ki Ku gaisa da mijin ki”ki samu lada”

Murmushi Halisa tayi tace”Dama can na nufa Mama.

Mama Fulani ta kalli Madabo da rai a b’ace tana fad’in “Yanzu nayi gyara , kina Neman ki b’ata da Halisa da Balaraba duk d’aya suke a gurina saboda haka idan zaki zartar da hukunci duk su biyun kina da iko dasu a matsayin ki na Uwar su”

Madabo tace”Kim fad’i dai-dai Mama amma kin San ni bana shiga shirgin yara har indai ta mai dani uwarta shikkenan, amma in zata dunga d’aukata a matsayin Uwar kishiyarta , babu ruwana da ita”

Shiru Fulani tayi mata saboda tasan halin ta baud’addiyar macace.

“Ke Halisa tsaya Ku tafi tare da ” yar uwarki, insha Allahu zan zauna daku anjima”

Halisa taji haushin hukuncin da Mama ta yanke, babu yadda ta iya dole tabi umarni.

Fulani tace”Balaraba tashi kuje Ku gaisa da mijin Ku”
[9/15, 9:31 AM] Akwai Citta????????????: A nutse ta mik’e tana gyara zaman hijab din ta, yau ma tana cikin dugowar riga ash color tayi amfani da irin hijab d’in nan na larabawa e had’e da hula tayi kyau sosai sai da rigar ta d’an matse ta sharp d’inta ya futo sosai,, Halisa tayi mata wani irin kallo ta watsa a kwandon shara.

Tafiya sukeyi babu Wanda ya kula kowa dake safiya CE, babu mutane sosai a farfajiyar gidan, dab da zasu shiga shashen Sarki! Ne motar Shukura ta danno kai cikin gidan.

Halisa ta tsaya tana murmushi domin Shukura mutuniyar ta ce, Shuruwa yarinyar Hajiya Kulu ce ta dawo daga yawace-yawacen ta na dare domin bata kwana ma a gida ba.

Ganin sun tsaya suna hira yasa Balaraba wuce wa, Shukura ta bita da wani mayen kallo babu abunda ya rikita ta sai tsarin zubin halittar ta,Balaraba a kwai jiki me kyau.

Tace”Wacece wacan ne”

Halisa ta tab’e baki tana fad’in Balaraba kenan wacce akayi madadi da ita tsohuwar matar Moddibo Yanzu kuma matar Sarki! Ta uku”

Shukura ta sauke ajiyar zuciya tana fad’in ‘Gaskiya ta had’u iya haduwa wallahi”

Wani kallo Halisa tayi mata tana Jan tsaki. Dariya Shukura tasa tana bin Halisa da kallo tana fad’in “A Gaskiya CE dole In fad’a”

Ko kula ta bata yi ba tabi bayan Balaraba wacce take dab da shiga cikin gidan.


Har yanzu yana zaune a falo yana duba littafin zadi zaujen, littafin dake kunshe da zamantakewa irin ta aure. Yaji motsi da alama shigowa za’ayi kafin ya an kara, Balaraba ta shigo cikin sallama”

Muryar ta da yaji ita tasa yayi saurin dago kanshi yana kallon bakin bak’in k’ofa.

Lumshe idonsa yayi lokacin da suka had’a ido da ita ya mai da kansa k’asa tare da amsa mata sallamar ciki-ciki, a hankali take takawa domin ta k’araso kusa dashi.

Halisa ta shigo ita da sallama, abun ya bashi mamaki sosai ya amsa mata ita, itakam fuskar ta ta saki sosai tazo ta wuce Balaraba kai tsaye kujerar da yake zaune ta nufa.

Hankalin su ne ya koma can idan da suka ji motsin bud’e k’ofa duk su ukun,Sarki! Shaf ya manta da cewar Azima na d’akin shi a kwance,, da sauri ya mik’e ya nufi in da take, ganin tana k’okarin saukowa daga sama tana shirin fad’uwa kana kallonta kasan tana cikin wani yanayi na wahala.

Duf-duf-duf! Gaban Halisa ya dunga bugawa, kar dai wannan a nan ta kwana”?
Tambayar kanta takeyi.

Balaraba ma taji wani abu cikin ranta amma da yake tana da wayo da dabara bata nuna ba, ammafa zuciyarta babu dad’i.

Halisa kuwa rashin hakuri lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya da mugun b’acin rai Lallai yau dole ayi ta domin tana gani an shiga hakkinta baza yadda ba.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????99

sai ya rik’e Azima a jikinshi suka soma saukowa a hankali daga k’afar bene, sai yanzu ya tabbatar da cewar ba k’aramin jigata Azima tayi ba,domin har fuskarta ta fad’a idanunta duk sun shige loko. Ganin ya rirrik’e ta ne yasa ta k’ara lanjarewa a jikinsa tana k’ara kwanciya a faffad’an k’irjinsa,, sai wani lumshe ido take duk dan ta k’untatawa su Balaraba. Aikuwa zuciyoyin su tamkar su babbake dan rad’ad’in zafi kai kishi masifa ne, mussaman akan wanda kake so,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button