GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Baki na rawa Halisa tace”Wai Yallab’ai me nake gani ne haka? Me ya kawo wannan gurin ka da safiyar nan,ai idan za’a bi yadda tsarin al’ada yake nice zan fara kwana da kai kafin ta, ni dai gaskiya an shiga hakki na”
Ta k’arashe maganar da murya a kaurare domin kishi ya rufe mata ido yasa ta manta da wa take magana.
Zaunar da Azima yayi kan kujera bai ce komai ba, ya zauna gefan ta shima, ita kuwa sai wani mar-mar take da idonta ita gata wanda miji ya kwana da ita.
Sarki tsabar haushin Halisa bai sa ya kalle ta ba, ya kalli Balaraba da fuska a had’e yace”Tsayuwar me kuke min anan ko kema kina da abunda zakice a kan hakan”
Gabanta ya fad’i jin abunda yace, Yo ita me zatace don ya kwanta da matarshi ta sunna kiji d’an neman rigima ita wacce tayi masa bai sauke fushin nasa a kanta ba sai ita da bata ji ba bata gani ba” Babu yabo babu fallasa ta d’an risina ta rage tsawon ta tace”Ina kwana fatan ka tashi lafiya”?
Sai da ya gama ya mutse ya mutsen shi sannan ya amsa ciki-ciki.
A zuciyarta tace”Dube shi don Allah wai mu zai nad’ewa tabarmar kunya da hauka.
Juyawa tayi da niyar tafiya ya kalle ta a fakaice ya d’auke kansa ganin yadda mazaunan ta suke juyawa gwanin ban sha’awa”Jimana” Zuciyarta ta tsinke tasan da ita yake inda yayi mata wannan kiran tasan wata tsirfar ce.
Juyowa tayi tana kallonsa yayi saurin d’auke kansa, yace”Ke je ki had’ama abun kari, ita wannan babu lafiya” yana nuna Azima da baki
Wannan hukuncin da ya yanke yayi mata tsauri da yawa ita kam bata ga inda aka tab’a haka ba, wacce ta kwana da miji daban me kula dashi daban,, zuba abunci kawai za’ace baza ta iya ba, Ba tace komai ba ta nufi daining area cikin yanayin tafiyarta,dama abunda yake so kenan kallo ya bita dashi babu ko kunyar su Halisa da Azima da take fafar tana tare dashi hankalinsa da tunaninsa nacan gurin kallon rausayar Balaraba da tsarin jiki me kyau da Allah ya hore mata, duk namijin da ya d’ora idonsa a kanta sai ya kyasa balle kuma mace “yar uwarta.
Halisa ta k’ara cika tayi fam-fam tamkar ta fashe da kuka haka take jin zuciyarta ita a ganinta ita aka takewa hakkin ta.
Yana sane yak’i kallon gurin da take tsaye domin ba k’aramin haushi ta bashi ba da kan maganar da tafad’a.
Jiki a sanyaye ta je ta zauna kusa da shi suka sashi a tsakiya, Azima cikin barikan ci da iya duniyan ci, ta mak’e murya irin me jin jikin nan, tace” Barka da safiya Uwargidan mu”
Ko kallonta ba tayi ba,, hankalinta na kansa Wanda ya d’auke kansa tamkar bai san akwai ta a gurin ba,
Murya a sanyaye tace”Ina magana fa ka share ni”
Kallonta yayi yace”Ki je ki koyo yanda ake magana tunda ke kin ki kiyi hankali har yanzu”
K’walla ta taro a idonta Lallai yau bata futo a sa’a ba komai a kanta ya k’are gara ma wacan wahalalliyar ita ya kula ta, cikin rashin abun yi tace”Ina kwana
Kallonta yayi kamar yasa dariya domin ta bashi ita sosai, wai Ina kwana, fuskarshi ya kara had’ewa yana fad’in”Bazan amsa ba, sai kinje kin koyo yanda ake lafazi”
Azima burinta ya cika jin yadda ake dizga Halisa sai wani lumshe ido take na jin dad’i.
Halisa hakurin ta ya soma zuwa k’arshe da Jan ido ta kalle shi tana fad’in “Wai me yasa kake min haka hubby naga dai ni dakai auran soyayya mukayi ba auran had’i ba, kuma ba wani ne ya mutu akayi maka madadi da ni ba, kana sona ina sonka,to me yasa zaka dunga wulakanta ni a gaban Wanda basu isa ba”
Kowa yayi zagi yasan da wanda yake,, Ba Azima ba har Balaraba sun gane habaici Halisa take musu”
Shi ko Sarki! Kallonta yake gwanin ban haushi har da goge hawaye, shi kam bai ga abunda yayi mata ba da har take kuka idan laifi ne itace tayi,dole ne kuwa ya koya mata zamantakewa domin baya son rashin zaman lafiya a gidan shi.
Yace”Kin shigo kina kallonmu d’ai-d’ai ke ga Gimbiya matar Sarki, ko? Bayan nan kin zo kina min wata maganar banza da bata da tushe balle makama, Eh na kwanta da Azima jiya kwanciya ya aure laifi ne, ke me ya hana ki kawo kanki tunda kina tak’amar da cewa kece Uwar gida wacce a ka fara d’aura min aure da ita” shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa”Bari ki abunda baki sani ba, Dan an d’aura maka aure da mata uku ko hudu a rana to bai addini bane kace Lallai sai da wacce aka fara d’aura maka aure sannan zakayi tara da ita ba, alhalin basu tare ba, ita ta kawo kanta gurina sai me ai itama matata CE,don haka ya rage naku yanzu Ku tsara yaya zaku raba kwana kamar yadda addini ya tanadar”
Sosai Halisa take kuka taji zalin fad’an da yayi mata ahalin yanzu babu wata kalma da zata kara futowa daga bakinta bayan ya gama wulakanta gaban kishiyoyin ta.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate, motivate and entertain aur Reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM
????100
Tashi tayi jikinta a mugun sanyaye ta nufi k’ofar futa daga falon, ko kallo bata ishe shi ba balle ya hanata tafiya.
Balaraba ma cikin k’warin jiki tayi saurin had’a duk abun buk’ata kan daining d’in ta jera komai gwanin sha’awa, cikin nutsuwa ta baro gurin, kanta a k’asa ta tsaya nesa dasu tace”An kammala komai”
Yana jinta sarai ya share tamkar bai ji ta ba,, d’ago kai tayi suka had’a ido, gaskiya ta tsani kallo wallahi ta lura kuma kamar d’abi’arshi ce,abunda Balaraba bata sani ba kuwa kallon kurulla ba hallin Sarki! Bane mutuk’ar ya damu Abu da kallo to tabbas abun yayi masa kuma ya k’yatar dashi,, Kishin Balaraba kamar ya kashe Azima domin ita ma ta lura da irin kallon da yake mata.
Gyaran murya yayi k’asa-k’asa yace”Sauran ki d’akina ki hau ki gyara min, ita wannan bata da lafiya “
Ya k’ara maimaita mata maganar da yayi mata akaro na farko.
Farko yace mata ta had’a musu abunci yanzu kuma yace mata ta gyara masa d’aki wato yana nufin ta gyara inda suka b’ata ko yana so ya nuna mata Lallai yayi rayuwar aure da Azima ita a ganinta ba sai ya nuna mata komai ta gane sarai, b’ata fuska tayi kamar tace baza tayi ba, kuma sai ta tuno karamcin Fulani a gareta, kai tsaya ta juya da niyar hawa saman bene inda d’akunan baccin sa yake.
Wannan kallon dai ya bita dashi, yana sauke wata sihirtacciyar ajiyar zuciya,, Azima ta d’ago kanta dake jikinsa tana kallonsa sai taga kwata-kwata ma hankalinsa baya kanta, bak’in ciki kamar tayi yaya, murya a sanyaye tace”Yallab’ai ya kamata muje kaci abunci zan wuce b’angaran da na sauka a kwai “yan uwanmu nacan na jira na da yawa daga cikinsu yau zasu tafi”
Babu abunda yace mata, ya mike a tsanake ya nufi daining mik’ewa tayi da kuzari ba kamar d’azu ba ta bi bayansa
Balaraba na shiga d’akin ta tadda bed d’in duk a hargitse duk nauyin bedshirt d’in dake shimfid’e a bed d’in ya hautsine da alama ba k’amin dirama aka sha jiya ba, wani mugun b’acin rai ne ya turnuk’o mata zuciyarta tamkar ta tarwarshe haka take jin wani matsananci kishinsa yana damunta, wai ya akayi ne ta yarda mutumin nan ya raina ta, Wannan fa ba sara bace, yasan dole zata gani kuma zataji ciwo shine zai ce ta gyara masa d’akin,me yasa bai sa Halisa ba saboda yasan baza tayi ba kenan, don dai ita yasan komai yace tayi tanayi shine zai sanya ta wannan aikin gaskiya ta canza shawara baza tayi ba,ita wacce aka kwanta da ita tazo ta gyara abunta, wallahi ya mugun raina mata hankali ma, tana ganin zata dawo masa da ainihin kalar ta, gudun irin wannan rainin, rai a b’ace ta juya domin barin d’akin shi kuma ya sako kai zai shigo sukayi gware goshi da goshi, ja da baya tayi tans dafe goshin ta, cike da takaicin sa, shigowa yayi dakin sosai ya mai da k’ofar ya rufe yana bin d’akin da kallo ganin babu abunda tayi a ciki.