GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Haushin abunda yace yasa ta mike a fusace daga ita sai k’aramin wando da briz ta nufi toilet d’in da gudu… .. Domin tana ganin ta tsaya sanya zai kalle mata jiki
????
Ni ko nace Balaraba kenan yanzu ma ai ta kalle miki duk wayon ki Sarki! Ta fiki”

Dariya yake sosai bayan shigar ta ya mike a nutse ya sauka k’asa.Lokacin da ta futo baya d’akin cikin sauri ta sanya kayan ta, ta sauka k’asa,, yana zaune kan kujera da waya a kunnen sa, da alama waya take, da sauri ta nufi k”ofar futa tun kafin ya gama wayar ya b’ullo mata da wata tsurfar,, ba zato taji yace”Jirani mana mu tafi tare zanje mu gaisa da Mama”

Da sauri ta futa ba tare da taji karshen maganar tasa ba,yaya ma za’ayi ta jera dashi ga mutane da dama ai da kunya,, yanzu ma bata San abunda zata cewa Mama ba in ta koma.


Shamsiyya kuwa kullum tana tafe a hanyar gidan Arrama ba ta dawo wa sai dare, sai sun gama sha’aninsu kullum yana fad’a mata ta kwantar da hankalin ta, kamar ta auri Sarki ta gama ne,, Uwa yau da bakin ciki ta tashi a gidan kasancewar ko ina ta juya babu dad’i gashi bata da ko kwabo yanzu bata sai dai komai duk jarin NATA ya k’are gurin bin malamai da bokaye,, Tsarkar gida ta futo tana ta surfa bala’i ta zauna kan kujera sai durawa Lantana ashar take tana fad’in”Ban tab’a ganin tsohowar najadu ba irin wannan matar kiri-kiri ta gudu ta barni da wahalar jiyyar danta shegiya munafuka Ashe da ta karb’i asirin domin taje ta aiwatar ba abunda ya kai ta bane, to Wallahi yau sai naje na tona mata asiri a gidan,wai ni zata munafurta shigiya tsohuwar najadu”

Sallau na daki yana jin Uwa na zagin mahaifiyar shi bakin ciki kamar ya kashe shi,,, cike da taikaci yace”Uwa!! Yanzu Lantana kike zagi? itama fa a matsayin mahaifiyar ki take””

Cikin masifa tace”Rufe min baki mutsiya ci kawai Uwata ko uwarka ni wannan munafukar matar bata haife ni me halin “yan wuta”

Wani mugun tari ne ya sark’e Sallau yana daga hannusa guda yana son yayi magana ya kasa da k’yar yace”Uwa!ke ba matar rufin asiri bace kije na sake ki saki uku tunda kika zagi mahaifiya ta”

“Ahayye nanaye”!!! Ayurrrrrr” Yau Allah ya raba ni da k’aya mutan gida Ku futo Ku taya ni murna”

Sadiya da Iya duk suna jin abunda ya faru sukayi shiru suna mamakin abunda dama ya kai Lantana gidan sarauta duk Dan ta cutar da Balaraba ne, Allah yasa Allah ya tona mata asiri.. Iya bata tsinke da al’amarin ba sai da taji Sallau na fad’in ya saki Uwa saki uku sannan ta futo daga daki tana salati gami da fad’in “Assha Sallau ka yanke hukuncin da bai dace ba, Sallau ba a saki cikin fushi”

Sallau ya fashe da kuka yana fad’in “Dole In rabu da Wannan bak’ar dagar matar Atika kina ji fa tana zagin Lantana duk lalacewar ta mahaifiyar ta CE kuma itama ta haife ta tunda dai yar uwarta ce”

Iya tace”Duk da haka dai, hukuncin da ka yanke bai dace ba”

Uwa! Ta futo daga daki Cikin shiri tana fad’in “Duk naji abunda kake cewa munafuki me kashi a kwance akwai bak’ar daga irin uwarka me muguwar zuciya kawai wallahi yau sai na tona mata asiri a gidan Sarki yanda ka ganni nan a shirye nake” Waje ta futa kamar sabuwar mahaukaciya sai surutai take, Iya da Sadiya suka bita da kallo cikin mamaki.

Tana futa Sallau ya dunga wani irin tari Wanda I n yayi sai wata majina ne kauri bak’ak’irin ta futo daga bakin sa, ga wani uban wari da take,, DA k’yar ya bud’e bakin sa yace”Atika ki yafe mun abubuwan da nayi muku ke da “yan uwanki Wanda na sani da Wanda ban sani ba ki yafe min Wannan ciwon nawa bana tashi bane, hak’ika na aikata abubwa Mara kyau don Allah ki nema min gafara gurin Balaraba da duk Wanda na batawa jikina na bani mutuwa zanyi”

Iya ta fara share hawaye tana cewa”cuta ba mutawa ba Sallau Insha Allahu zaka tashi kayi hakuri ka daina wannan maganar” Sallau yace”Kayya Atika ni nasan abunda nake ji hak’ika na zalinci Ayuba da matar shi da yarsu Balaraba don Allah ko na mutu Ku Bini da addu’a”

Kuka iya take tana bashi hakuri gami da yi masa addu’a ta kalli Sadiya dake tsaye hawaye na zuba tace”Ki kira Maman a waya yazo su gana”

Cikin dauriya tace”Kin manta “yau kwanan shi biyu da tafiya sun tafi Jalingo,zasu sauke kaya”

Iya tace”Hakane kuma kira Walidi yazo ya kai shi asibiti jikin nasa yayi tsanani yau”




Fakad’an-fakad’an Uwa! Ta shiga gidan sarautar Sai ta hau zare ido ganin wasu mutane sun yi kanta da zabgegiyar bulala sun ganta kamar mahaukaciya, Dogari yace”Keee!! Wa kike nema ne”?

Cikin rawar baki tace”Nazo gurin… Ummm gurin Balar….Balaraba Nazo”

“Wacece Balaraba”?
Yafad’a yana daga bulala zai shauda mata gani yake kamar da mahaukaciya yake magana.

Jiki na kyarma tace” Matar me Martaba Sarki! Almansur wacce a ka d’aura musu aure she karan jiya”

Nan take Dogari ya fahimci wadda take nufi cikin matan Sarki! ita ce matar Moddibo ta da, da kansa yayi mata jagora har shashen Mama Fulani, ya juya ya bar gurin ba tare da yace mata komai ba,, Harara ta bishi da ita tana tsaki kofar shiga ta nufa gadan gadan, masu tsaron gurin suka yo kanta suna zare ido suma a d’aukar su mahaukaciya CE, baya taja da sauri tana zare ido ta fara yi musu bayani nan suka gane suka bata hanya suna mamakin me ya kawo ta gurin Balaraba ko da yake sun San dama ba “yar gidan kowa bace.

Mama Fulani Jakadiya da Lantana had’e da Madabo suna zaune suna hira Lantana ta tsagalgale Sai labari take basu, kawai suka ga mace ta afko d’akin ba sallama.

A furgice suke salati domin sun d’auka mahaukaciya CE,,
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????103

Uwa! bata tsaya ko ina ba sai gaban Lantana tayi mata k’ik’am a ka tace”Yau asirin ki zai tuno yau ranar Wanka ba a b’oyan ci bi, munafukar Allah ta’ala,, kinzo da niyar ki cuci Balaraba kin samu gidin zama a gidan saboda an ga daula, da jin dad’i gami da cima me kyau da makwanci me kyau,, shine kika mak’ale kika manta da alk’awarin mu dake, to saboda haka sai ki tashi kije ki d’auko min kayan aikin da kika karb’a a hannuna”
Ta k’arasa maganar kamar zata kai mata duka.

Lantana ta mike da k’yar tana kallon ta tace”Uwa! Yaushe kika haukace ne, kawai zaki fado mana daki babu ko sallama to in kina cin k’asa ki kiyayi ta shuri nan ba gurin wasa bane, wallahi in kin saba yin rashin mutumin ki a can nan kikayi suka zaki ci”

Wani wawan mari Tayi tsalle ta tsinkawa Lantana tana hakki sai kace zakanya tace”Ni ai wa garin nan? Ni za’a yaudara wato kina so ki lauya maganar kenan munafukar tsohuwa kawai”

Cikin mamaki da al’ajabi Mama take kallon Uwa! da sauran mutanan gurin Balaraba ranta in yayi dubu ya b’aci wato sun zo suna hali ne sun zo su mata tone -tone a gida ne.
Lantana kuwa tana gefe guda hannuta rik’e da kuncin ta tana mamakin marin da tasha daga Uwa! Lallai yau ta tabbatar da cewar Uwa! Ba tada mutumci kuma bata da kunya ko kad’an wai ita ta tsinkawa mari a gaban mutane,,,

Jakadiya Shafa’atu ta buga Uwa! Tsawa tana fad’in”Hattara dai baiwar Allah nan ba gurin wasa bane idan baki da hankali nan ake koyar dashi, kar ki manta kina gaban Fulani me dakin gabas matar Sarki Almustafah, in daga turo kika futo to yanzu za’a mai dake”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button