GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta juya baya tana jawo ruwa a rijiya Sallau ya fito daga dakin mahaifiyarsa ya hankade ta ,tayi taga taga zata Afka cikin rijiyar tayi saurin dafa bango ,Amma INA!! Santsin gurin ya kwashe tafadi ,gurin rigijff!!
Cikinta ya bugu da murfin rijiyar dake jin gine jikin bango Duk yayi tsatsa ,dalili kenan da yasa yaqi zama a rijiyar shine Lantana ta jin gine shi gurin
Suwaibah ta kwala ka!! Tana fadin wayyo Allah cikina
innaliliahi wa inna ilaiyi rajiun
Lantana tafito a suk wane tana fadin “ke lafiya ne kike yi mana ihu?
Sai taga nta zube bakin rijya gurin wanke wankensu,
Cikin zuciyarta tace Sallau ya cika ai ki kenan
Suwaiba ta dinga daga mata hannu Alamar ta temake ta,
Tabe baki lantana tayi “tace Abinda ya dame ki kenan ,nima lokacin da nake haihuwa babu wacce take te makamin ,sabida haka kije can ki karata,ta koma cikin dakinta,tana waqe waqe.
Sallau ma ficewa yayi daga gidan babu Abinda ya dame shi.
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMIBIYA BALARABA
????????????????
in kana bukatar ci gabanshi ga number nan
08089965176
[04/05, 03:09] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????Written by
BINTA UMAR
MAMAN ABDUL WAHABU
MALUKAL MULKI ZULJALALI WAL IKIRAM
????15
Suwaibah ta ruqe cikin ta tana fidda numfashi Sama Sama ,sai ko karin tashi take yi a gurin ta kasa ,sai kawai ta koma ta kwanta tana salati gami da Addu’oi tana fatan idan mutuwarta ce tazo to Allah yasa ta cika da Kalmar shahada.
Murqususu take tana jin wani mugun ciwon Mara kwankwason ta tamkar ya balle daga jikinta,tun tana iya yin Addu’ar afili har ta gazayi ta dawo yi a zuciyarta
Lantana tafito daga dakinta hannunta riqe da bota da Alama ban daki zata shiga,
Sai taga Suwaibah kwance a bakin rariyar Bandaki kamar ma bata numfashi,
Wani farin ciki ya kamata ,ta karaso gurin ta daki cikin Suwaibah da kafar ta tana dariya ,tace” shegiya “Yar mutsiyata “yar dadi miji ,yanzu shi malam din ai sai yazo ya karbar miki haihuwar ,shida ya dirka miki cikin,in sha Allahu dake da duk Dan da zaki Haifa sai kun muto kowa ya huta da jaraba”
Tafada tana kara dukan cikin a karo Na biyu ganin suwaibah bata motsa bah.
Nan ma shiru
Sai ta daga botar dake hannunta ta kwara mata ruwan ciki.
Suwaibah tasaki Ajiyar zuciya Wanda yayi dai dai da tsinkewar jini ,a jikinta kwarara yafara bin rariya
Gaban Lantana ya fadi ,ganin yadda jini yabi bin makwarara tamkar Wanda a ka kwance famfo ,tayi sauri ta tsallake Suwaibah ta shiga bandaki tayi uzirinta ,tafito da sauri ta shige dakinta ,tabar Suwaibah ,Akwan ce Rai a hannun Allah.
Atika ta shigo gidan Cikin Sallama ita ma da nata tsohun cikin,dama tare suke jerawa ,kusan kullum ta kanzo gidansu gurin suwaibah ,si ta hirarrakinsu duk a kan Haihuwa, Lantana tai tajin haushi tana zubarmusu da habaici,basa kulata
innalilahi wa’ina ilaihi rajiun!!
Shine Abinda Atika tafada ta yi kan suwaibah tana kokarin tashin ta ,Amma ina!!ina takasa sakamokon yadda jikin Suwaibah ya shika bubu kwari wuya ya langwabe,
Bakinta a bushe tace”Atika mutuwa zanyi ki cewa babanku ya gafarce ni bani da rabon kumawa ga Dan gina ,Dan Allah duk Abinda Na haifa ki riqe min shi a hannunki Na baki Amanarshi
Atika ta fashe da kuka tace”bazaki mutu ba in sha Allahu zaki goya danki da hannuki”
Suwaibah ta rimtse ido tana cije baki! Cikin Wahala jin wani Abu da yake kokarin dannowa ta kasanta ,ta riqa sakin Nushi a galabaice!!
Atika ta kwantar da ita a gurun ta mike cikin zafin Nama tayi dakin Lantana da Sauri.
Tana zaune kan tabarma da mifici a hannunta ,ta ware wakokin bar mana coge cikin redion ta sai ji take cike da Nishadi tana bin wakar cikin kwarewa ,tamkar ita ce ta rerata.
Atika taga labule fuskarta jike da ruwan hawaye Ciki tashin Hankali tace”Lantana ki kawo temako Dan girman Allah,ga suwaibah can zata haihu jini yana kwarara a jikinta”
Lantana tayi mata kwallon banza tace”ke Fice min A daki munafukar banza da wofi ni ce nai Mata cikin zaki zo kice in temaka mata kowa ai da haka ya haihu,lokacin da nake haihuwa Uwarki! Ta taya ni ne”?
Da sauri Atika ta fita daga dakin tana Mamakin Rashin Imanin Lantana
Ta yi hanyar waje da sauri domin taje ta kira Gwaggo Shattu matar Liman,
Ita ko Lantana tana jin ficeawr Atika daga gidan ,sai ta mike ta je ta daga labulenta tana keqen Suwaibah a kwance har yanzu batasan Wanda ke kanta ba
Taja tsaki!! Ta saki labulen ta har da sake gyarashi sosai ta zauna ta cigaba da jin wakokinta,babu Abinda ya dameta.
BINTA UMAR ABBALE
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
????????????????
08089965176
[04/05, 03:10] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
????GIMBIYA BALARABA????
????♀????♀????♀????♀????♀????♀
✍????writting by
BINTA UMAR
MAMAN ABDUL WAHABU
ZAMANI WRTES ASSOCIATON????????
ALLAH KAI MANA MAGANIN ABINDA YA DAME MU ,MUGUN JI DA MUGUN GANI ALLAH KA TSARE MU
????16
Bissimillahi
Gwaggo shatu da Atika suka shigo cikin tashin hankali, Haryanzu suwaibah Na kwance bakin rariya, jini Na fita ta kasanta, Numfashinta sai kaiwa yake yana kawowa,tana ganin zuwan gwago shatu ,ta daga mata hannu tana motsa bakinta,da sauri Gwaggo ta karasa gurin da take kwance ta dago,sosai tana nanata innaliliahi a fili tace”Atika maza zo ki kama min ita mu shiga daki haihu zatai yanzu,
Atika tazo suka kama suwaiba suka shiga da’ita dakinta sai nishi! Take cikin garari da Tsabar wahala ga kan da yafito ya Amma tsabar galabaita ya hanshi yunkurin fitowa ,ita ma Suwaiba duk wani qarfinta ya kare nishin wahala kawai take,
Lantana Na dakinta sake da labule tana jin wake-waken ta babu Abinda ya dame ta
Gwaggo tace”Atika jeki karbo Rubutun gurin Malam Nasan yanzu ya gama”
Atika Na kuka ta fita daga dakin tana tausawa Suwaibah ganin yadda take shan wuya ,tace dama haka mata suke wahala gurin haihuwa, ita sai tafara jin tsoran ranar da tata zata zo
Ta Na fita suka ci karo da Sallau ya shigo gidan ,saura kadan ya buge ta ta kauce,
Sallau ya ja ya tsaya yana dura mata Ashar!! Yace”ni ba wanki bane da bazaki gaishe ni ba”
Tace”Sallau suwaibah babu Lafiya zata haihu kaje ka kira babanmu”
Dariya Sallau ya fashe dashi cikin mugunta yace “Allah yasa ta mutu in dai sai naje Na kirashi ne ai kema kinsan gurin Aikinshi kije ki kirashi,mana”
Yayi wucewarsa ciki ya barta tsaye,
Sai ta fita da sauri tana share hawaye tana tur! Da Bakin Hali irin Na lantana da yaranta,
Tuni Malam ya kammala rubutun Na kuda ya fito da kanshi ,ganin yara zasu bata masa lokaci,sai ya hangi Lantana ya tsaya ta karaso,ta gaishe shi,yasan Rubutun zata karba sai ya mika mata yace maza a je bata in sha Allahu zata sauka lafiya”
Atika ta kar6i rubutun ta Na godiya,har ta joya zata tafi sai ta tsaya ta ce”Malam Babanmu yana gurin Aiki bai San halin da ake ciki ba”
“Ashsha””! Malam yafada yana jinjina Kai yace”yanzo zan tashi yara suje su fada masa ko in je da kai na,kedai maza jeki kai rubutun”
Da sauri Atika tatafi tana taiwa Suwaibah Addu’a Allah ya sauke ta Lafiya
Gwaggo shattu sai gumi take sharbawa ganin duk iya bakin kokarinta tayi Akan Suwaiba tayi wani yunkuri!! Ko yaron ya fado Ta kasayi Asabili da qarfinta ya kare, ita dai tana kwance Batasan wace duniyar take ba,sosai Gwaggo ta firgita,ganin yadda jini yake fita har yanzu gashi ba a haihuba,tabbas fitar jini ga mace mai naquda hadari ne,ba’aso Anfison in mace ta haihu sai jinin ya fita,duk da a lokacin da qaracin wayewar kai,Gwaggo shatu ta fahimci Suwaibah tana cikin hadari ba karami ba shiyasa ta tsinke da Almarin ,sai addu’oi take tofa mata,ta mike ta fita domin baza ta iya aikin ita daya ba,tanajin tsoran fita taje ta kira unguwar zoma, Sai ta daga labulen dakin Lantana,