GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate, motivate and entertain aur Reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM
????108
Kalmar Innalillahi wa’ina ilahi raji’un itace ta futo daga bakin sa, yunk’urin d’aga k’afar ya kuma yi a karo na uku, tak’i motsawa,, hannu yasa ya d’agota yaji wani Yammmmmmmm! Mara dad’i Dole tasa yayi saurin aje ta saboda ji yayi abun har tsakiyar kansa,,, zufa duk ta jik’a masa jiki kamar babu sanyi asubah,, salatin da yake ne,, ya farkar da Balaraba ta mike a zabure itama bakin ta na fad’ar kalmar Innalillahi wa’ina ilahi raji’un, saboda wani irin mumman mafarki da tayi,, hannuta ya Kamo ya rik’e tamm!! Suka tsurawa juna ido,,, gumi taga goshin sa nayi,, yana ta cije baki!! Bakinta na rawa tace”Yallab’ai baka da lafiya ne”? Da k’yar ya gyda mata kansa, yace”K’afata ta rike min” gabanta ya fad’in,, cikin zuciyarta tace”Kar dai mafarkina ya zama gaskiya,, hannu takai kafar tana shafawa idanunta har sun soma zubar da ruwan hawaye,, a hankali yace” cire hannun ki babu dad’i” da sauri ta cire hannun nata tana kallonsa,, cikin dauriya yace”Yaya za’ayi nayi sallah” tace” Ko in kama ka mik’e”? Gyad’a kai yayi yana murmushi me ciwo yace”Baza ki iya ba,, mik’omin waya ta””” sauka tayi da sauri ta d’auko wayar ta mik’a masa,,, numbar Shatima ya kira,,,, ya fada masa halin da yake ciki,, cikin tashin hankali Shatima ya futo daga gida,, kai tsaye gidan sarautar ya nufa lokacin har an idar da sallahr asubah,, Balabara na durkushe a gabansa jikinta sanye da hijab,, ba ta cire ba,, Shatima yayi sallama ya shigo,, zama yayi yana duba k’afar,, cike da alhini yace”Kurum wayar gari kayi kaji k’afar taki ta kuwa”? Sarki! Ta girgiza kai shi kadai yasan ciwon da yake ji yace”Da sauk’i ai idan kin takuwa tayi,, taki motsi fa” Shatima ya Dora hannunsa k’afar yana salati,, wayarsa ya Ciro yana kiran dector dake duba Sarki!! Yace”yazo yanzu yanzu,,, “Kamani in mik’e in kama ruwa sai in d’aura alwala inyi sallah”. Shatima ya mike yana kici-kici ya samu ya mik’e inda Allah ya rufa asiri ma k’afa d’aya ta taku itama da k’yar da dafa bango suka je toilet yayi uzirin sa, kana ya dauro alwala suka futo,, dadduma ta shimfuda masa,,, cikin zuciyarta sai tasbihi take Allah ya gajar ta musu wahala
[9/26, 8:42 PM] BintubatulBintUmarAbbale????: Da Jan k’afa suka k’araso gurin yayi nufin ya tsaya abun ya gagara,, sai ya zauna a nutse yayi sallahr sa,, duk suna tsaye suna kallonsa Balaraba sai goge hawaye take,, Shatima ko ya kira numbar Shahid yafi Sau a kirga bai d’auka mybe baya kusa,, dector ya shigo da kayan aiki,, cikin girmamawa ya gaida shi ya amsa a nutse ya fara yi masa tambayoyi,, Sarki! Ya fada masa duk abunda ya faru,,, A hankali ya kama k’afar yana dubawa,, lafiya Lou da ita a ido,, matsata yayi sarki! Ya cije baki!! Yace”Kar ka k’ara matsawa,, dector ya cire hannunsa da sauri yana neman afuwa,, yace”Yallab’ai ina ganin dole zamuje hospital dakai domin mu auna k’afar dole kuma a d’auke hoton ta, domin sanin maganin da ya dace da ita” Gyad’a kai kurum yayi,, Shatima yace” Bari insanar da Mama Halin da ake ciki,, babu Wanda yace masa komai,, yana sauka k’asa suka ci karo da Halisa ta shigo,, da fara’a ta tsaya suna gaisawa da alama batasan abunda yake faruwa ba,, Shatima ya wuce bai fada mata ba,, kai tsaye sama ta nufa cikin k’asaita! Tana shiga taga Balaraba durk’ushe gaban shi tana kuka, ga dector a tsaye a gefe yayi shiru fuskar sa ta kalla taga alamun alhini ta k’arasa da sauri kusa dashi,, cikin kid’ima tace”Hubby menene wai naga duk kuna cikin damuwa!” Kallon ta yayi zuciyarsa a dake!! Yace”Babu komai ke me kika gani” ? Baki na rawa tace”Tashin hankali na gani”” d’auke kansa yayi baice mata komai,, Balaraba ta kalla tace”Menene “? Kafar sa ta nuna mata, tana kuka! Halisa ta kalli k’afar da sauri,, taga ta Dan kumbura” jiki a sanyaye tace”Ciwo take masa”? Balaraba ta girgiza kai tana fad’in “Idan ciwo ne da sauk’i yau tunda ya tashi ya kasa tafiya da ita tak’i motsi d’azu da k’yar aka kai shi toilet yayi alwala ” Halisa tace”Innalillahi wa ina ilahi raji’un kuka ta fashe dashi tana k’unshe baki tace”Wannan wace irin masifa CE”???? Tsawa!! Ya daka mata yana fad’in”Bana son shashanci da koke -koke addu’a zakuyi min””””” a gigice ! Ta mike tana fad’in”Au! Da gaske ne Ashe? Sai ta kalli Balaraba Cikin daga murya tace”Ke nake zargi! Munafuka meye ribar ki anan, me yasa ranar da ya kwanta damu haka bata faru ba,, me kike nufi, bak’ar algumguma wato kina so ki kashe ki samu tumunin takaba”? Taji kamar ta watsa mata ruwan zafi,, a jiki ta dago jajayen idonta da suka rine!! Bakin ta na rawa tace”Mey…… Ka tsaye ta yayi ta hanyar daga mata hannu sai tayi shiru gami da toshe bakinta da gefen hijab dinta tana k’okarin b’oye kukan da yake k’okarin kufce mata a karo Mara adadi,,,, Halisa yake kallo cikin tsantsar b’acin rai da takaici.
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????
_*NA*_
BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????
We are here to educate, motivate and entertain aur Reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
ALHERIN ALLAH YA ZO INDA KIKE
NANA AISHATU KADUNA
Hak’ika inajin dadin comment dinki ubangiji Allah ya kara kauna da aminci nagode sosai ina miki fatan alkairi a rayuwar ki????
Kuyi hakuri yau pege din babu yawa zazzab’i ne ke damuna wallahi Ku sanya ni cikin addu’ar Ku
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM
????109
Suna had’a ido dashi ta kara rikicewa tana fad’in”Wallahi Hubby kar ka yarda da ita,, itace Silar faruwan wannan al’amari ko mara kunne ne yaji wannan abun yasan da akwai lauje cikin nadi,, shiyasa hausawa suke cewa idan takalan mutum mugun ice ne, idan ya samu guri yafi mai kudi iko,wallahi yanzu na daina ganin laifin masu kud’in da suke gudun talaka domin halin su ne ya ja mus………….”Halisaaaa!!! Rufe min bakin ki anan gurin”” ya katse ta cikin wata muguwar tsawa”” gum! Tayi da bakin ta tana shashshekar kuka,, Balaraba na durkushe a gurin kai a kasa tana zurarar da hawayen bakin ciki,, murya a cunkushe! Yace”Duk futa bana son ganin Ku” da sauri dector ya futa Halisa ta futa simi-simi,, mik’ewa tayi kwata-kwata jikinta babu lak’a, suka had’a ido saurin d’auke kansa yayi ransa a bace kalaman Halisa ba k’aramin kona masa rai sukayi ba,, wuce tayi tana waigen sa, duk yana kallonta,,, tana futa ya sauke ajiyar zuciya me zafi.
Tana sauka taga Halisa da Azima suna maganganu k’asa-k’asa suna ganinta suka hau rafka mata harara, d’auke kanta kawai tayi,, Mama ce ta shigo bayanta Jakadiya da Shatima Shahid da Madabo cikin tashin hankali ta nufi sama suka rufa mata baya,, kansa a kasa yaji shigowar su,murya Maman shi yaji a kansa, ya d’ago idonsa,, da sauri ta tsuguna kusa dashi tana masa magana,, cikin nutsuwa ya warware mata duk abunda ya faru,, cikin tawakkali tace”Allah yana ji yana kallo ko wane hali da kake ciki abunda za za’ayi yanzu muje hospital din ayi hoton kamar yadda dector ya fada insha Allahu komai mai sauk’i ne” A nutse ta ce da dector “Je ka d’auko while chair,, a d’auke shi,, da sauri ya futa, shiru dakin babu Wanda yayi magana har dector ya dawo su Shahid ne suka kama shi suka Dora shi kai, a hankali suka dunga sauka dashi, daga kafar bene, Mama na bayansu tans goge hawaye a fakaice.