GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Balaraba ta mike da sauri ta tsaya har suka k’araso gurin,, kallonta yayi yaga duk ta tayar da hankalin ta, ta bashi tausayi wannan alama ce da ta nuna tana cikin damuwa kuma ta damu dashi sosai,, babu yabo babu fallasa yace da ita”Wannan kukan da kike ya isa haka, cuta fa ba mutuwa bace, shikkenan ni Allah bazai jarrabe ni, ba Wannan ba yana nufin shikkenan bazan kara taka k’afafu na ba, insha Allahu inaji ajikina wannan abun na lokaci kankani ne saboda haka Wannan koke-koken da kukeyi ya Isa haka” Balaraba tayi shiru tana gyad’a kai, Azima kuwa ai batayi shiru ba sai cewa tayi “Duk ba anan take ba Yallab’ai dole muyi kuka Hak’ika an zalince ka kuma bazamu bari ba,, wallahi ka gurgunce sai mun d’auki mummanan mataki akanta ” duk jama’ar gurin suka bita da kallo cikin mamaki,,,!! Mama tace “Ku muje mu wannan tsayuwar bata da amfani,, Azima da Halisa suka rufa musu baya, Balaraba aka bari a baya tana tafiya salau-salau babu kuzari ko na kwabo a jikinta.

Buba direba ya bud’e bayan mota suka d’auke shi suka saka ciki da gyara masa zama sosai sannan kowa ya shiga ya zauna,, ganin Matan nasa na k’okarin shiga ne ya dakatar da Buba,, kallonsu yayi cikin bada umarni yace ” Ko wacce ta koma gurin ta””” umarni ya bawa Buba ya tada mota suka futa,, dake safiya CE, babu jama’a sosai a harabar gurin sai dai-dai Ku, motar na fucewa suka yo kan Balaraba da bala’i kowa na fad’in albarkacin bakinta,, Balaraba lalurar mijinta itace a gabanta shiyasa bata tanka musu ba,, wucewa tayi ta barsu a gurin suna zagin ta ta uwa ta uba.. Sun jima a gurin suna maida magana daga bisani kowa ya koma part d’insa,,, Azima labewa tayi sai da taga Halisa ta shige ta kulle kofa sannan ta futo kai tsaye b’angaran Waziri Zayyanu ta nufa…

Da futowar su da shigar su mota da futar su daga gidan sarautar duk akan idon Waziri da Tsito ,, Tsito ya kwashe da dariya yana fad’in kaga aikin Mak’asudu ko, ai inda alkawairi to da cikawa,, kai kuma sai ka kula da haradin da ya gindaya maka”

Waziri ya kece!! Da wata mahaukaciyar dariya” hahahahahaha”” Mak’asudu ka cika alk’awarina na yarda dakai akan aikin ka, daga yau zan fara mulkina cikin kwanciyar hankali da nutsuwa nasan wancan yaron ya zama musaki,, ka lalata masa k’afafu ya gama aiki, Hahahahaha”””
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION????????


We are here to educate, motivate and entertain aur Reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM

????110

Zuwan Azima gurin yasa Waziri ya bar dariyar da yake yi,ya d’ora hannunsa akanta fuskarsa cike da walwala da farin ciki yace”Kin gama min komai yarinya ta, hak’ika kin cika “yar halak d’iyar abokina aminina ya iya haihuwa ki fad’i duk abunda kike buk’ata zan yi miki”. Jiki a sanyaye Azima tace.” Nifa na soma nadamar abunda nayi gaskiya yanzu ina dana sani” Waziri da Tsito suka kalli juna, Tsito yayi wani murmushi, Yace.” Ki daina nadamar abunda kika aikata idan kuma kina jin tsoro kar sunan ki ya futo ranar da asiri ya tuno to duk ki daina, aiki inda Mak’asudu a ciki baya karyewa sai dai Idan wanda yayi aikin ne ya kar ya doka saboda kije ki kwantar da hankalin ki,babu abunda zai faru,daga yau ma zan fara aiki domin zan daure wa duk mutan gidan baki” Azima ta sauke ajiyar zuciya gaskiya halin da taga mijinta a jiki ya bata tsoro amma aikin gama ya Riga ya gama, Waziri yace”Shiga ciki ganin zuwa” simi-simi ta shige cikin gidan nasa.

To duk wani alk’awari da Waziri yayi wa Tsito sai da yq cika masa mota guda akaiwa Tsito da tashi da ta kayan arzki ya tafi garin su, Hajiya Kulu ma tayi masa kyautar bajinta dake ba sosai take zama a gida ba shiyasa duk bata San abunda yake faruwa ba sai da Waziri ya shiga har gurin ta da sassafe ya sanar mata, murna ta dunga yi mak’iyinta ya gurgunce dama ita babban bakin cikinta shine kar yayi mulki tunda ita Allah bai bata ‘ya’ya mata ba.

Babu irin aune-aunen da ba’ayi ba, abu d’aya yake nunawa k’afafun shi lafiya suke, cike da dumbun mamaki da al’ajabi suka dawo gida suna tunanin meye abun yi,

Waziri kuwa bayan sun rabu da Tsito gida ya koma ya shiga keb’antaccen d’akinsa da ya rataye fatocin su k’adan gare, Kunama da kulb’a gami da b’eran dunka bango guda ya kafe su, tsakiyar su wani Jan yanki ne a n daure wani Abu a tsakiyar sa, shiri yayi sosai ya nufi fada yana wani irin taku na k’asaita shiga Sarki aikuwa fada na cike da mutanan sa munafukai ya zauna suka fara aikin zugashi da wasashi shi kuma yana jin dad’i.


Yanda aka futa dashi haka aka shigo dashi dama tun safe Labari yaje kunnensu Limam da Galadima da Wambai don haka suna tsaye aka futo dashi daga motar, suna kallon ikon Allah kowanne yana mamaki da tu’ajibi k’afafun Sarki! Sun kumbura sosai, ba kamar d’azu da safe ba.
A daran ranar mai girma governor yazo suka zauna da Sarki! Duk aka basu guri, dake akwai sha kuwa a tsakanin su, Governor yace.”Ina ganin wannan ciwon naka tafarar d’aya anya ba jifa bane? Nifa ka sanni da lek’e-lek’e saboda yadda yanayin al’amarin namu yake, gaskiya ina zargin jifa ne kuma duk wanda yayi maka makusancin ka ne”

Sarki! Yace.”Kaga ni kuma bana wannan tunanin kawai nafi gazgata cewar jarraba ce daga Allah” Governor ya gyad’a kai yana tunani minti biyu yace.”Shikkenan yanzu dai na sanya ayi mana vizar dani da kai dasu Shatima zamuje Saudi’a akwai k’wararun likitoci islamic a can insha Allahu kome ye zamu gane zamu samu sassauci” Gyad’a kai kurum yayi, . shiga don duk sun damu ne, amma sam baya jin wani ciwo a k’afar shi, illa kawai motsa ta da ya kasa yi duk da haka yanaji zai iya yin duk abunda mai lafiya zaiyi. Sallama sukayi governor ya mike ya futa mutanan sa suka rufa masa baya.

To a can babban falon Fulani ma Ashe tattauwar da ake kenan Liman ne ya bada sha’warar suje saudi’a wannan Asibitin dai da governor yake magana akai.

Ko da Halisa ta shiga part d’insa tun kafin ta zauna ya fattatake ta, jiki babu k’wari ta futa, tana da tasanin shirman da tayi masa d’azu.

Balaraba kuwa abunda tasan zata d’auka taje ta d’auko a part d’inta ta kullo ta dawo gurinsa, kula take dashi sosai tana jin wani irin tausayin sa, kallonta kawai yake yana mamaki ashe tana sonsa.

Yana zaune gefan gado da k’aramin littafi a hannunshi yana dubawa idonsa sanye da glass d’insa na fama ta futo daga toilet d’inshi jikinta daure da towol din sa,da wani akanta ta nannad’e kanta, had’a ido sukayi da sauri ya kauda kansa, ita yanzu kunyar sa ta ragu lafiyar sa kawai take so shiyasa bata jin kunyar saka kaya a gabansa ba, so take tagama abunda take taje gurinsa taji ko da akwai abunda zatayi masa, yau tayi Wanka tsarki dadduma ta shimfid’a ta tayar da sallahr isha’i ,, dago kansa yayi yana kallonta sosai, zuciyarsa yace”Tayi Tsarki kenan hummmm! Lallai yau akwai budiri????

Bari muga yaya za’a buga kwallon????
????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????

              _*NA*_

BINTA UMAR ABBALE
®BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUD’I
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button