GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani mugun b’acin rai! Ya turnek’e zuciyar Balaraba, tabbas Halisa taci albarkacin mijinsu da bashi da lafiya, amma da badan wannan ba, da sai ta k’ara nuna mata ita wacece, da alama ta manta karon su da ita na farko, amma taci al’washin duk randa ta k’ara yi mata magana irin wannan tabbas sai ta nuna mata kuskuran ta. Azima ce ta k’araso inda suke tsaye ta buge k’afad’ar Balaraba tana zabga tsaki! Hannun juna suka rike suka wuce ta cikin wata irin tafiya ta k’asaita. Kallo ta bisu dashi zuciyarta tana zafi,! Lallai ruwa ya daki babban zakara, ita kad’ai take fad’in haka a zuciyar ta, idan da ba haka ba wallahi da sai sun gane kuransu.
Yana zaune inda yake tun futar Balaraba, fuskarsa cike da annuri suka same shi, amsa musu sallama yayi ya nuna musu gurin zama, jiki a sanyaye ko waccen su ta zauna, babban abunda ya sa jikinsu yayi sanyi shine ganin da sukayi yana cikin farin ciki da annushuwa kamar yadda suka ga fuskar Balaraba haka, wani irin kishin Balaraba ya damu zuciyarsu, sanin halinsa na rashin d’aukar raini yasa ko wacce tayi shiru da bakin ta, gai dashi sukayi sunayi masa ya jiki, ya amsa da walwala, Azima tace.”Yau zaku tafi ne”? ” Eh insha Allahu sha biyu na rana” Shiru sukayi. Halisa tace.” Tunda ita wannan ta futa daga girkin ta, zan shiga nawa ina ganin ya kamata a tafi dani ko da wani taimakon da zanyi maka.” Harararta yayi, ta sunkuyar da kanta da sauri, a hankali yace.” Ke ko za’a tafi da wani waye zai tafi dake guri kije kiyiwa mutane shirme” Azima taji dad’in maganar sa, ji wani son kai na Halisa take fada a zuciyar ta, muryar shi sukaji yana fad’in”Duk Ku kwantar da hankalin ku babu da wanda zani, sai kace wani Yaro,ku munje ma ba wani zama za muyi ba.”
Azima tace.” Nima dai abunda nagani kenan.” Halisa kuwa sai yak’e take ta lura mutumin nata haushinta yake ji, domin yak’i sakin jiki da ita hirarasu suke da Azima tamkar babu ita a gurin. Wayar shi tafara k’ara ta mike da sauri ta d’auko masa, karb’a yayi ba tare da yace mata komai ba, Governor na ne, suka gaisa yace.” Fatan jikin da sauk’i, duk wasu shirya-shirye angama insha Allahu da kaina zan zo in d’auke ka cikin mota har filin jirgi” Sarki! Yace.” Jiki alhamdullahi ni kam bani da matsala sai ta rashin k’afafu shima na wani lokaci ne insha Allahu, zamu zauna cikin shiri insha Allahu” Governor yace.” Naji muryar ka rad’au da alama kana cikin nishadi kasan fa duk namiji da yake da mace sama da daya to mutukar suna kula dashi da kwantar masa da hankali babu Wanda ya kaishi dacewa”. Murmushi yayi yace.” maganar ka haka take, Aboki” dariya Governor yasa yace.” Dole dai na koya maka surutu ko”? Yace.” To ya na iya fa halin ka.” Haka dai sukai barkwamci kafin suyi sallama suka kashe wayar, Azima da Halisa kuwa ganin babu fuska ko wacce taje zata je tayi Wanka, suka sauka babu wacce ta kara kula ‘yar uwar ta.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????
~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LADIDI K'WADAGA
ZAMANI WRITES ASSOCIATON????????
We are here to educate motivate and entertain aur reades
JAN KUNNE⚠
Ban yarda a siyar min da d’aya daga cikin books d’in ba, duk mai buk’atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d’in ka yafi kaci da gumin wani, halak d’in ka shine mafi alkairi a gare ka.
DEDICATED
~TO~
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????113
To Balaraba ma lokacin da suka rabu dasu Halisa gurin ta, ta nufa wanka ta shiga a gurguje ta futo ta kimtsa jikinta, ta kasance mace me son atampa duk ya wanci kayan ta itace doguwar riga, da Riga da siket da zani basu da yawa, yanzu ma wata ‘yar Ghana ta saka doguwar riga ce, sosai kasa ya bud’e daga iya kwankwanson ta ya matse da kirjin rigar komai ya futa har madauri ne da ita daga baya, d’ankwali ta d’aura dai-dai misali ta shiga kicin dinta dole tana ganin sai tayi masa abu motsa baki, cake ta fara had’a ma, zuciyar ta tace ki had’a masa Dambu nama ko yana so, nan take ta futo da zallar tsokar Neman sa cikin firji ta Dora kan wuta bayan ta sanya albasa da kayan k’amshi, ta cigaba da had’a cake din ciki k’warewa.
Balaraba ta k’aware sosai gurin had’a dambun nama shiyasa sam bai bata wahala ba, nan ta had’a komai cikin abunda bai fi awa guda ba, k’amshi ne kawai yake tashi kicin d’in, zuba shi tayi cikin warmers ko wanne ta aje ta samu wani had’ad’an akushi irin na gidan sarauta ta cika shi da cake d’in da Dambu nama,wannan ta aje shi ne sai zasu tafi zata bashi, ruwa ta d’ora a wuta ta zuba kayan tea masu sa kamsh gahwa na’ana’a citta kanifari kimba da dai sauran su sai da ya gaja da tafasa sannan ta kashe gas d’in ta tace sosai ruwan tea d’in yayi kyau sai kamshi yake ta juye cikin fulas mai kyau. D’auka tayi ta kai falonta ta aje ta dawo ta gyara kicin din tas! Sannan ta dawo ta d’auki, d’auki abunda ta aje, kai tsaye part din shi ta nufa. Lokacin har su Shahid sun zo sun d’auko dashi k’asa yayi wanka shar dashi kana ganinsa kaga ango sosai yake walwala Shatima na tsokanar sa wai farin cikin me yake, shi kuma yana basarwa.
A nutse tayi sallama ta shigo, da sauri ya dago kanshi yana kallonta, saurin sunkuyar da kanta tayi, cikin mamaki ya bi hannuta da kallo, yana kallon yanayin tafiyar ta, Shatima ya amsa yana fad’in”Gimbiya sannu ki da zuw….. Katse shi yayi ta hanyar fad’in”Ka tsaya kana surutu ka karb’i abun hannuta mana,bata da lafiya” Balaraba tayi saurin kallonsa, cikin mamaki, da sauri ta wuce Shatima ya bi bayanta yana fad’in”Ayya! Gimbiya sannu da kokari kawo in aje miki daining d’in.” Murmushi k’arfin hali tayi tace.” Ka rabu dashi don ni lafiya talau fa.” ‘Yar dariya yayi yace.” Ai naga alama gashi kin sha aiki domin ki faranta ran maigidan ki mybe yana so ki huta ne shiyasa Yace in karb’e ki” Shiru kawai tayi masa tana sunkuyar da kanta cike da kunya,wato Dole dai sai ya tona mata asiri gurin abokan shi,kome amfanin fad’a musu haka oho masa. Gyara gurin tayi sosai, Shahid ya kawo shi har gurin, idonsa a kanta yace.” Wato nace kije ki huta shine kika wahalar da kanki ko.” K’asa tayi da kanta kurum domin bata so tayi wata magar ya lafto wacce zai sa har su Shatima su gane. “Jimana” yafad’a yana tsare ta da ido, a nutse ta watsa masa wani kallo, Wanda ya shiga jikinsa,amma da yake ya saba karb’arsa sa’i da lokaci a gurin ta,sai ya dake! Yace.” Bayan wahalar da kika sha jiya shine zaki na wahalar da jikin ki yanzu,wai ke bakya son hutu ne.” ? Taikacinsa ya hanata cewa komai, sai aukin futo da warmers take, Shatima ya doki kafad’arsa yana fad’in.” Kai kanai mata bak’in cikin ladan da zata samu ne, ina ruwan ka.”? Shahid ya b’oye dariya yana fad’in”Lallai hausawa da sunyi gaskiya cikin karin maganar su, inda suke fad’in”Gurgu yafi………..Sarki! Ya galla masa harara! Dariya suka saka Shatima ya bashi hannu suka taga!Balaraba kamar ta nutse don kunya, simi-simi tabar gurin tana da ta sanin dawo da tasan tonan silili zai mata da bata dawo ba, dab da zata futa sai ga Mama ta shigo da jama’ar ta, sai ta tsaya tana murmushi , itama Mama murmushi ne a fuskarta, suka zauna cikin kujera Balaraba ta durkusa har kasa ta gaishe ta, cikin sakin fuska mama ta amsa tana tambayar me jiki, tace “Jiki alhamdullahi wallahi gashi yana k’okarin Mama muna sa ran samun nasara wannan tafiyar insha Allahu, Mama tace.” Hakane dama babu abunda yafi k’arfin addu’a ai, jiya munyi waya da aminiya ta, Matar Sarkin Yalwa sosai mahaifinta dake Malami ne yasa yara ‘yan makaranta na addu’a jiya an sauke al’kurani babu adadi”