GIMBIYA BALARABA COMPLETE HAUSA NOVEL

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LADIDI K'WADAGA
ZAMANI WRITES ASSOCIATON????????
We are here to educate motivate and entertain aur reades
JAN KUNNE⚠
Ban yarda a siyar min da d’aya daga cikin books d’in ba, duk mai buk’atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d’in ka yafi kaci da gumin wani, halak d’in ka shine mafi alkairi a gare ka.
DEDICATED
~TO~
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????116
Waziri na zaune a fada sai bada umarni yake cike da izza! magana ma da k’yar yake yin ta,wai shi dole ga Sarki, Al’amin ya shigo cikin tashin hankali ya zube gaban mahaifinsa ya fara Sanar dashi halin da ake ciki. Hankali a tashe ya mik’e fadawansa suka rufa masa baya,kwata-kwata ya manta da alkwarinsu da Mak’asudu, yana isa ya Tarar dasu hankali a tashe mussaman Hajiya Kattime da ta kusa zautuwa domin. Bayan tafiyar Al’amin shima Ansar d’in fad’uwa kawai suka ga yayi yana rike cikin sa kafin su ankara sukaga jini na b’ulb’ulowa ta bakinsa da hancin sa,gaba ki daya sun rasa wanda taimako zasuyi masa, Khalifa kuwa tuni Allah yayi masa rasuwa kafin Waziri ya k’araso mutuwar Ansar din ta afuku a gabansa, zaman dirshan yayi a gaban gawawwakin ‘yayansa ya sunkuyar da kansa kasa yana kukan zuci,kamar daga sama yaji wata murya kamar ta Mak’asudu yana fad’in.” Kar ka manta da alk’awari mu dakai,yau na cika shi shiyasa ma na shanye jinin ‘yayan ka saka fi so da kauna.”!!! Zumbur!!! Ya mik’e tsaye idonsa yayi jazur ya kalli sauran ‘yayan nasa yace.” A shirya yi musu suttura.” Yana gama fad’in haka ya shige asirtaccan d’akinsa, Hajiya Kattime ta bishi da kallo cikin mamaki ganin bai damu ba, yanzu tafara zargin sa, Sosai take zargin wannan dakin da ya kulle ya hana kowa shiga,dole tafara bunkice a kansa.
Kafin kace kwabo mutuwar su Khalifa ta watsu a gida da waje, su Sarki! Ma labari ya same su,sunyi mamaki sosai daga bisani Sarki yace.” Ba’a mamaki da ikon Allah, Galadima da me girma governor ne suka dunga tur da halayyan Waziri domin su sun San abunda yake faruwa saboda mulki babu abunda Waziri bazai yi ba.
Mama ce ta dinga d’ebe wa Kattime kewa har akayi sadakar uku kowa ya watse Hajiya Kattime ta kudiri aniyar bibbiyar mijinta da abunda yake aikatawa tana fatan asirinsa ya tuno a duniya shine sanadin mutuwar ‘yayan ta uku, tayi da tasani data aure shi. Saboda mugun bakin halinsa.
Waziri kuwa yana shiga d’akin sirrinsa ya kulle da mukulli ya zube bakin kofar yana warware nadin dake kansa, gumi na tashin hankali kawai takeyi wasu zafaffan hawaye ne suka fara zubo masa, lokaci guda yayi rashin ‘ya’yan shi biyu lallai Mak’asudu ya shammace shi, kuka yayi sosai daga bisani ya miki ya maida rawaninsa ya futa daga dakin, yanzu yasan kuma Mak’asudu baya binsa wani bashi tunda ya biya shi. Niko nace haka kake gani Waziri aljan ba’a iya masa sai Allah
Uwa! na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tunanin rayuwa kawai take, duk ta rame ta ko jale,Shamsiyya ce ta futo daga ban daki hannunta rike da buta cikin ta ya tsofa sosai duk ta kumbura, Sadiya matar Kawu na hangota tace.” Ki dinga tafiya a a hankali da gurin nan kar ki fad’i saboda santsi.” Shamsiyya ta d’aga kanta cikin tausayin kanta taje kusa da uwarta ta zauna da k’yar.Uwa! Ta sauke ajiyar zuciya tace.” Shikkenan yanzu kamar yanda na fidda rai da Iro haka zan hak’ura da Mabaruka, anyi neman duniya ba’aganta ba.” Shamsiyya tace.” Jiya fa Walidi yake ce miki ya samu labari gurin wani abokin kasuwanci sa wai ya ganta cab portarcouht ita da saurayin ta.” Uwa! ta share hawaye tana fadin .” Allah ya dawo da ita gida ubangiji Allah ka shirye ta kasa ta gane duniya ba mattabata bace.” Cikin sanyi murya Shamsiyya tace.” Ameen” Lantana ta futo daga d’akinta ta zauna suna Tisa maganar,Lantana Duk tayi sanyi,kusan kullum tana daki tana Jan carbi sallar walha bata wuce ta, ta koma ga Allah sosai domin mutuwar Sallau ta gigirgaza ta, yanzu basa cikin k’angin rashi Walidi na tsaye a Kansu basu da yunwa,kuma daga gidan Sarauta Mama nayi musu aike duk wata.
Alhmdullahi yau satin su guda A k’asa me tsarki, sauk’i ya soma zuwa da izinin ubangiji duk Wannan kumburi da k’afafun sukayi ya sab’e kwanan su biyu da zuwa aka fara yi masa amfani da magunguna na islaminc masu d’auke da ayoyin Allah a ciki, yasha a shafa k’afafun nasa, dasu yanzu yana iya motsa su, amma bai iya taka su,yayi wata kib’a sosai saboda samun kulawa daga my life d’in shi Balaraba soyayyar sa yake sha sosai idan yaga babu idonsu su Shatima, dake su in Safiya tayi suna tafiya harami su yini sai yamma suke dawo wa, wannan damar da ya samu ya dinga more amarcin sa, Balaraba ta saki jiki dashi sosai tana bashi kulawa, shi kuma sai yayi tayi mata shagwaba yana lanjarewa, da dare yayi zata ga ya watsake yana Mata kallon love, tun bata gane wayon sa ba har ta gane shi, sai dai kawai tayi masa dariya, suna samun waya sosai daga gurin Mama, taji dad’i da taji jiki yayi kyau, Balaraba ta sha addu’a a gurina.
Daga Wanka ta futo daure da towol cinyoyinta duk a waje ga kanta sai d’igar ruwa yake, yana zaune gefen gado daga shi sai k’aramin wando, da alama angama love ne, bude mata hannuwan sa yayi wai ta zo. A hankali ta k’arasa amma me makon ta shiga jikinsa kamar yadda ya buk’ata sai ta zauna gefan gadon tana ya mutse fuska, Ka fad’ar ta ya kamo ya Dan matsa kad’an k’asa-k’asa yace.” Menene hummm.”? Lumshe ido tayi tace.” Bana jin dadin. Jikina yanzu na fara zargin kaina saboda banga period d’in ba, wannan lokacin nake yi shiru bai zo ba.”
????????????????????????????????????????
GIMBIYA BALARABA
????????????????????????????????????????
~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LADIDI K'WADAGA
ZAMANI WRITES ASSOCIATON????????
We are here to educate motivate and entertain aur reades
JAN KUNNE⚠
Ban yarda a siyar min da d’aya daga cikin books d’in ba, duk mai buk’atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d’in ka yafi kaci da gumin wani, halak d’in ka shine mafi alkairi a gare ka.
DEDICATED
~TO~
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????113
Hannunsa ya sanya ya rungumo k’ugunta fuskarsa d’auke da wani kyakykyawan murmushi yace.” Lallai Allah ya amsa min addu’a ta da wuri Ubangiji Allah yasa ciki ne dake, idan hakane zan yi farin ciki sosai da sosai.” Sunkuyar da kanta tayi tana jin kunyar sa a hankali tace.” Gaskiya ina zargin haka domin ban tab’a batan wata ba,ko lokaci nayi nake amma wannan kwana hud’u akai gaskiya da akwai alamun tambaya.” Cikin farin ciki yace.” Yanzu nan zan auna ki domin in tabbatar da hakan.” Towol din yake k’okarin cirewa ta rike hannunsa cike da tsoro! Kallon ta yayi yana lumshe ido,tace.” Wai kai baka gajiya ne.”? Kanne mata idonsa yayi yace.” Kece ai kamar zuma kike sam bakya gimsa ta.” Nauyin maganar sa taji yasa ya juya baya tana girgiza kai. Ya rungume ta k’am! Yana sakin ajiyar zuciya yace.” Ki barni in gaisa da babyna.” Shiru tayi, sai ya zura hannunsa yana shafo cikin tamkar Wanda yake mata tafiyar tsutsa ya dinga shafa mata mara lumshe idonta tayi tana sauke ajiyar zuciya, ni dai nan na futo na barsu.