BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL
BAHAGON RAYUWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DUK KAN GODIYA YA TABBATA GA UBANGIJIN MU SARKIN TALIKAI DA YA KAWO MU WANAN LOKACIN TARE DA BAMU LAFIYA INGANTTACIYA A RAYUWAN MU,
YABO DA GODIYA YA TABBATA GA ALLAH WANDA YAI MUNA NUNFASHI TARE DA MA ABUBUWAN RAYUWA ACIKIN HIKIMOMIN SA YA ALLAH MUNA MASU ROKONKA DAKA BAMU IKON GODE MAKA AKODA YAUSHE MU KASANCE CIKIN BAYI MASU TSORON KA MASU MAKA BAUTA TSARKAKKE A RAYUWAN MU,
WANNAN RABARI NE MAY DAN TABA ZUCIYAR MAY KARATU TA DA WASU SAKWANI A CIKIN SAI DAI BAIDA YAWA SOSAI DON BUKATAN MAKARANTA NAYI TARE DA FATAN ZAMU AMFANA DA DAN SAKON DAKE CIKIN SA ,
NAGODE TAKU HAR KULLUN ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU GA MASU SON JIN KARSHE ZASU IYA KIRANA DA WANAN NUMBER DIN KAMAR HAKA 08036959257 DOMIN YIN REGISTER, , , ,
BAHAGON, , , , , ,
⚓1⃣
Gidane ginan kasa
wanda da ganin sa kasan akwai talauci da kauyanci a cikin sa sai dai duk da kasancewar gidan karami akwai tarin jama, a a cikin sa sosai.
Gida ne wanda ya kumshi matan aure guda uku ko wace da nata zurian don dama irin wanan gida babu komai a cikin sa sai gasar haihuwa a tsakanin matan dake gidajen.
Ba wai damuwa da rayuwa akayi ba banda bakin kishi da hassada juna a tsakani, abinda ba kai tsanmani ba shine mutum yakan riska a cikin irin wanan gidajen.
Sai dai kuma tallakawa ne fitik din su don abinda zasuci ma watarana aiki ne a gare su sai dai kowa taiwa rayuwan ta dana yayan ta dabara su sami dan abinda zasu aikawa cikin su.
Ga ko wani daki a cike da yara bi da bi irin haihuwan nan na kafin ka yaye ka samu wani.
Sai dai su matan gidan hakan ba takura bane a garesu sai dai ma jin dadin rayuwa don babu wacce aka bari a baya daga cikin su wurin saka nata irin.
Duk da uwargidan da may bi mata sunfi yawan iyali a gidan amma kuma suna kyashi da hassadan ganin Rabi amaryan su itama da ba ta dade ba da shigowa cikin su tana kokarin cin masu ga haihuwa.
Gsshi dai ba wani tallafi suke samu ba daga mijin nasu wanda zasu taimakawa rayuwan su dana yayan amma kuma kullun zance ya tashi sai su manta da nasu su shiga sake mata magana a tsakar gida.
Sai idan ta gaji ne takan mayar masu da martani da cewa haihuwa aina Allah ne kuma yaya arzikine kowa kuma na dashi batai bakin ciki da nasu ba ai.
Duk hakkurin irin na Rabi, sau da yawa takan shanye ta take irin abinda akewa diyan ta a gidan tayi kamar bata gani ba.
Sai dai tana mai bawa yayan nata shidda tarbiya sosai fiye da sauran yaran dake gidan da tarbiyan su sai a hankali.
Abu daya ne talaucin su bai hana yaran gidan yin karatun boko ba har ma da na addini wanda diyan Rabin sun fi maida hankali ga kowani fanni na karatun nasu.
Gashi bata shiga tsabaga kowa haka ma yayan nata suke a gidan zata iya zama a daki ida ba wani abin bane zai fito da ita waje.
A haka dai suke zaune a gidan da dadi ba dadi watarana aci watarana kuma a hakkura asawa sarautar Allah ido a gani.
Uwar gidan da suke kira da mama tana da diya tara mata bakwai maza biyu, sai may bi mata inna tana da diya takwas maza uku mata biyar.
Sai ita Rabi dake da diya shidda maza hudu mata biyu yar ta ta fari mace ce ana kiran ta da safiya may bi mata kuma Aisha, sai mazan issah dauda, aminu da shaibu sai karamin da take goyo da suke kira da abu.
Duk inda zaka nemi yan uwan da ke son jinunan su to yaran Rabi sun kai can don suna balain kaunar junan su sosai a rayuwan su.
Allah may rufin asirin bawan sa dan karfin da Safiya ta fara kawowa ne ya ragewa Rabi wani wahala a gidan da take fuskanta na rayuwa.
Don safiya yarinya ce mai hazaka ta dauko yan kule, kulen dan abin makulasan yara tana zuwa makatan ta dashi wanda ta hakane uwar ke dan samun na sabulu daga ciki da sauran abubuwab rayuwan yau da kullun.
Wanan dan walwalan da ubangiji yai masu sai kuma hassada da kyashi yazo ya shiga cikin zukatan sauran matan gidan.
Tun dawowan su daga makaranta ta dan tsaya shago ta sayo dan madara da suga wanda take ganin zai isheta yin dan gulusuwan da zatayi gobe na zuwa makaranta dashi ta shigo ta samu kamar kullun sauran mutanen gidan suna tsakar gida suna harkokin su na yau da kullun kamar yadda suka saba.
Bata shiga dakin su ba tabi iyayyen gidsn da wasu daga cikin yayyen ta tana masu sannu da gida.
Ba wai amsawan dadi ake mata ba amma hakan bai hana ta gaida su kamar yadda ta saba a kullun suna amsa mata cikin gajewa da halinta.
Idan kuma da zata wuce bata gaidasu ba wani matsala ne hakan don har rankwashi sai tasha a gun wata a gidan ranan.
Da sallama ta shiga dakin mahaifiyar ta tana zaune ninke kayan wankin da tayi na kanne ta tun safe ta samu tanayi a dakin.
Uwar ta amsa mata sallaman ta cikin mutunci tare da fadin kun dawo tace eh tare da kokarin sauke dan jakar makaranta dake makale a kafadan ta.
Bata zauna ba ta fara kokarin ciro dan sayayyan da tayo a hanyar dawowan ta tare da ciro sauran dan kudin da ya rage tana kokarin yiwa uwar bayanin komai.
Haba yar nan bayyani kuma namay fa cire jakar ki zauna ki huta ga dan ganye nan dana gyara maku da garin rago kici kisha ruwa ki huta kafin lokacin zuwa islamiya yayi maku.
Ta zauna ke nan da niyar ta cire safan dake a kafan ta taji ana kwala mata kira a tsakar gidan da Safiya safiya da karfi.
Cikin takaici da bacin rai uwar tace dama na sani ai ba za a bari ki zauna kici dan abincin ba ma yanzu za, a nemay ki da wani aikin kuma.
Taja guntun tsaki tana cewa yar tashi kije idan kin dawo kyaci ai, cikin takaici Safiyan ta ture kwanon data bude.
Cikin ranta tana fadin kamar ni kadaice yarinya a gidan daga dawowanabza a fara kwala min kira da bakin aike ko aiki, komai sai dai a kirani ace nice zanyi ni kadai.
Kafin ta kai ga fita ta sake jin muryan Inna tana fadin wai Safiyan bata jinane ko may wai ?
Da sauri ta amsa da naam Inna gani tafe ina daura zani ne dama tafita waje tana karasa daura zanin da takeyi din.
Cikin takaici Rabi ta jawo marfin kwanon data bude don cin abincin data aje mata ta rufe tana fadi a ranta, in dai don aji ta bakinane ake wanan halin bazaku taba jina ba a kan hakan.
Duk yaran dake gidan nan wasu ma basuje ko ina ba tun safe amma ba a aike su ba sai wacce ta biyo rana ta shigo yanzu ake kwalawa kira haka.
Ko sai yaushe zasu daina wanan halin hassadan nasu a gidan nan haka oho don dai wani abin da gaiyya ma suke masu shi.
Jin muryan Inna tayi daga waje tanawa yar nata fada aka may take kiranta ta shige daki taki fitowa tun dazun.
Tace inna ina cire uniform ne a jikina dama ba kin fitowa nayi ba sai inna din tace ai dolen ki ma ki fito ga tatsin kamu can a roba yana jiran ki tun dazun har ya fara kumbura.
Safiya takai kallon ta ga inda kammun yake a bude fam ga roba sai kudajen da suka mutu a saman shi ba ako dan sakaya shi da wani abu ba.
Ta sauke ajiyan zuciya tare da cewa Inna don in dan ci abinci kafin na fara don banci komai ba tun safe dana fita gida.
Wani irin tsawa ta daka mata tace kai amma lalai safiyan nan wuyar ki ya isa yanka yanzu ni zan saki aiki har ki tsaya kina cewa wai na bari ki dan ci abinci.
To ki zauna kada ki tatse idan ya gama yoyewa sai ki fito kina ca kin shige daki kuna gulman da kuka saba dake da munafukar uwar ki ko.
Haba inna gulma kuma dani da ummi ta ake bude baki zatai magana taji saukan mari a fuskan ta kayauuu, .
Daidai lokacin kuma mahaifin su da ya dawo daga wurin aikin jiman shi ya shigo gidan yana ganin ta dafe kumcin ta bai tsaya bin ba asi ba yace ke Safiya ungo nan yai mata dakuwa yana fadin.
Ashe rashin kunyar da ake fadi kina dashi yakai haka ban sani ba uwar taki ne zaki tsaya kinawa musawa a gaban ta.
Inna tace gara dai da kagani da idon ka yau idan an fadi ace an sakawa yarinya tsana don ba a kaunar su a gidan.
Safiya tana share hawaye ta wuce ta fara gyara inda zatai tatsin kullun don duk kwanonin da akaci abincin daren jiyane a gurin ba a wanke ba har lokacin.
Wanda tasan kuma karshen ta itace zata wannke su idan ta gama don haka ta mayar da hankalinta sosai ga abinda takeyi.
Sai dai har lokacin Inna na tsaye da baba suna kare mata zagi har da mama dake gefe tana kashewa yarta karama kwarkwata a kai.
Hakan bai ishi baba ba sai da yakai kofan Ummi dake ci gaba da gyaran dakin ta ya daga raggan labulen ta da ya dafe saboda dauda da tsufa dayayi.
Zagin Ummin yake sosai a kaina ina jin shi sai sharan hawaye nake ina aikin dake a gabana mai yawa ban dai san may ummi tace dashi ba naji yace da ita da karfi akan yar taki har kike son ki mun rashin kunya Rabi ?
Ban yi aune ba naji ya fada dakin ya fara dukan ummi sai ihu take kamar yadda ta saba idan yana dukan ta din don yau bashine karo na farko da naga yana dukan ta ba.
Aiki nake jikina sai tsuma yake saboda muryan ummi dake ratsa kunnuwa na a lokacin da ina da hali ko karfi a ranan babu abinda zai hana na kwatar mata hakkin ta a gidan nan.
Tun ina iya kuka ciki ciki har takai na bude murya na sosai ina fitar da sautin kukan nawa a fili kowa najiyoni a gidan .
Sai da ya gaji ya fito daga dakin yana haki ya kara nufa na da zagi da baki irin wanda bai dace mahaifi yana wa yar tashi ba.
Ina jin ya nufo ni na mike da gudu na bar wurin don nasan idan na tsaya zan sha na jaki ranan ba bisa laifin komai ba.
Sai da naga ya shige na fito inda na labe baci gaba da aikina da nakeyi inayi ina kallon kofan mu ko zanga fitowar ummina daga dakin ta amma naji shiru.
Sai da na karasa har wanke wanke na na samu daman shiga dakin namu inda na samu ummi kwance saman matatan katifan ta daya sude ta kifa ciki tana sharban hawaye.
A hankali nakai tsugunne daidai kan ta ina fadin ummi sannu kiyi hakkuri ummi nice naja maki hakan.
Ta sa hannun ta share hawayen da ya fito daga idanuwan ta ta dago da kyat ta dan motsa tana fadin ba komai yar nan akwai Allah yana kuma tare da mai gaskiya.
Tace jeki ki shirin makaranta kada ki rasa haddan na yau a wuce ki ga abincin nan ki dauka ki ci ya dai bushe ko.
Na koshi nace da ita abu ga mahaifiya sai ta manta da nata damuwan naji tace dani da sauri may kikaci maza dauki ki ci ki wuce don kin makara ko.
Ban ki ba ina ci ina shan maji har nagama na shirya a gurguje na bar gidan da sauri sai dai duk abinda nake ina tuna irin wanan cin zarafin da baban mukewa mahaifiyana.
Ina jin matan gidan na faman sakin magana a kan mu suna fadin ai kadan ma muka gani don sai mun raina kan mu a gidan.
Ban tsaya ta kan su ba nafice abina don inda sabo na saba jin wannan kalaman a gun su tun ina yar ficiciyata har zuwa yanzu.
Mun dawo daga islamiya banga Ummina a gidan ba gashi babu halin na tambayi wani inda ta tafi a lokacin.
Waje na fita na yayo dan kirorin da zan hura wutan da zan yi madarana dashi har lokacin ummi bata dawo ba gidan.
Na hada ina kokarin tukawa ne naji mama ta kwala min kira nasan ba komai bane abincin dakin mu take kirana na dauka gashi idan na bar madaran zai iya konewa.
Ba yadda na iya dole na sauke shi a hakana na tafi bata barni na dawo gurin aikina ba sai dana kawar wa kowa da abincin shi na koma lokacin har ya sandare ko a haka rai a bace na juye ina nifin dakin mu naji sallaman ummina ta dawo gidan.
Sai dai fuskanta yana a kumbure har lokacin sannu da zuwa nake mata a cikin zakuwa da ganin ta ta amsa min a dararare ta shiga dakin gidan ba wanda yai mata kin dawo.
Itace ta fara shiga daki nabi baya ta kofi na dauko na dibar mata ruwan sha don ban tsanmanin ta sha ko ruwa har wanan lokaci nan naji matan gidan suna dariya suna fadin.
Mutum ma da wani gata gare shi da har zaiyi yaji don baisan kunya ba ya juyo babu ko dan rakiya zikau ya dawo shi kadai.
In mutum ya isa ya nuna shi din dan gatane mana muga tsomamun iyayyen mutum sun dawo dashi.
A haka dai za a kare uwa lalace diyan ma haka na sai bakar wahalan banza kawai a duniya.
Ban tsaya karasa sauraren su ba na debi ruwana na shige na sake fitowa na hada kan nannena suje suci abincin da aka samu dafawa a ranan don ranan girkin Inna ce ranan da wuya a rasa dan abin tsakurawa idan tana girki a gidan.
Ni dai ina zaune ina zubawa yan kannena abinda zasu ci ina jiyo dariyan su da yaran su wanda nasan akan zance guda suke yin sa.
Ranan dai a haka muka kwana da ummi ba tako iya magana sai idan ya kama nice nai ta controling din kanne na har sukai barci.
Fita nayi duk da dare ya soma na karbo mata magani a gurin mai shagon uguwar mu ta hadein.
Zan shigo gida na hade da uwale yar wurin mama take cewa ke kuma daga ina haka ko har kin fara fitan dare ne bamu sani ba.
Nace a marairaice haba uwale sheri kuma zaki min daga ganina najuya naji ta shako bayana tana fadin wake sherin yar iskan banza kawai dake.
Nace to yanzu may nai maki kuma tace ko zaki zage ni ne yanzu ki koma daki irin na uwarki jiki yai tsami.
Nace saukin abin dai ai ba uwata kawai ake duka a gidan ba sai ko naji ta shake ni da karfi tana fadin da uwar wa ake duka in ba uwar ki ba kawai.
Ta fara duka na sai ga dan wurin inna ya zai shigo yaya haruna don shi ba ruwan shi da harkan kishin gidan mu duk daukan kanne yake muna gaba dayan mu bai biyo sauran yaran gidan ba.
Yace ke sake ta mana may tai maki tace dashi cikin hasala wai fa uwata take zagi don kawai nai mata magana daga ina take yanzu.
Yace ke din daga ina kike ko wani ya baki gadin ta ne a gidan ku dai wanan bakin dan ubancin naku shi zai cuce ku wata ranna a gidan nan.
Ta ture ni da karfi sai da na bugu ga rubaben bangon katangar gidan mu na dafe goshina ina kuka na shige ciki.
Ina mamaki irin wanan bakar tsanar da mutanen gidan mu sukai muna mu da mahaifiyar mu.
Wanda har hakan ya shafi wasu daga cikin dangin mahaifina suma basu kaunar mu ko kadan magana kadan in dai ya shafe mu yanzu zagi ko duka ne zai biyo baya.
A yadda na samu ummi ta zauna daga kofa nasan duk abin da muke yana a kunnen ta kasancewar gidan namu ba wani babba bane a haka muke rayuwa a matse a cikin sa.
Nabawa ummi maganin ta tare da debo ruwan da zata sha dashi na jawo dan keson tabar man roban da nake kwana a sama na kwanta daga gefen yan kanne na wanda kafin gari ya waye duk sun jika ni da bolin su.
Sai idan babana yana dakin ummi ne nakan je dakin mama na kwanta daga kofa makure babu wuri a kasa wai babu inda zan saka mata tabar ma a dakin ta.