BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/15/20, 10:51 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , ,

????????5️⃣7️⃣????????

NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN FITAR UBANGIJI YABI MIN HAKKINA A KAN KI/KA.

YAR UWA MAINE RIBAN KARANTA KAYAN ALLAH YA ISA KARATU FA IYAKAR SHI DUNIYA.
Karfe goma saura har lokacin ina zaune dakina na kasa zuwa dakin uncle don ban san da wani fuska zai karbe ni har nayi kamar in share shi saidai na mike na fara shirin zuwa wurin shi.
Komai na falon an an kashe alaman dai ya shige tuni dakin shi sai wutan da zai sadani da nashi part din ne kawai a kunne.
Ahankali na kwankwasa kofar tare da turawa sai najita a bude nasa kai na shiga dakin can na hango shi tsaye bakin window dake kallon wajen gidan yana tsaye ya rike labule da alama iskan dake busawa a lokacin yake shaka don yana mai dadi.
Shigowana baisa ya juyo gareni ba har na karasa inda yake tsaye batare da jin kunya ba na rungumay shi ta baya tare da zagaye hannaye na saman ruwan cikin shi.
Ajiyan zuciya naji ya sauke a sanyayye nace uncle may kake yi anan tsaye kai kadai batare da ya juyo ya kallene ba ya bani amsa da yanayin yana min dadi ne madam.
Sake shi nayi nima nakoma gefen shi na tsaya ina kallon waje sai naga motoci suna wulgaiya jefi jefi ga iska mai dadi na hurowa ta tagan dakin.
Gwaron numfashi na sauke amma a fili na kasa fadin komai sai tsayawa danayi ina kallon wajen kamar yadda shima yake kallo.
Shi ya kawar da shirun da cewa na dauka kinyi barci ne dana jiki shiru ai ajiyan zuciya na sauke nace uncle ina zan iya barci bayan miji yana fushi dani karo na farko a rayuwan mu tare.
Murmushi yayi tare da sanya hannuwanshi saman kirjin shi yace bada ke nake fushi ba sai dai maganan ki ce ta jawo min fushi na.
A marairai ce nace kayi hakkuri uncle ban san maganan zai bata maka rai ba haka da banyi ba ni gani nayi yarinyar tana zaman kane a gidan kuma bata samu sakin fuska a wurin ka ba.
Naji na gode amma ke bakuwa kike a cikin mu shiyasa zan daga maki kafa ga maganan yanzu amma indai akan zancen wanan zurian ne bani son daga yau ki kara yi min shi a gidan nan.
Ki barni da yan uwana ki zauna matsayin ki na matana a cikin su bani son ki zure masu har su samu kafar shige min haka.
Murmushi nayi na kwantar da kaina saman kafadan shi nace uncle yadda kake so haka za a yi har kullun a shirye nake da in maka biyayya a rayuwana.
Amma Uncle ina son ka zama mai yafiya ga duk wanda ya zulunce ka saboda kayi koyi da sunnan mai,akin Allah sallalahu Alaihim wassalam.
Yau uncle in har akwai abinda sukai ma rayuwan ka sai ince ya zama maka taki ayanzu don hassada ga mai rabo taki ne.
Uncle har kullun sai dai inci gaba da yima addua da fatan alheri a garemu uncle ba zan boye maka ba bantaba ganin mutum adali irin ka ba uncle.
Sai dai kuma cikar kamalan mutum baya kammals sai ya cika sharudun Allah a kan shi yanke zumuta dasu don sun taba yi ma rayuwanka illar killa can baya ba shine mafita ba a gare ka.
Kamata yayi uncle kai ka saka masu da alherin ka barsu da halin su Allah shine mai hisabi arayuwan biyan sa.
Amma uncle akan may zaka rike gawarshin wuta a hannuwan ka su kona ma aikin na alheri har ka gamu da fushin ubangiji ka ta sanadin su.
Uncle kafan Allah yana fushi da may yanke zumunci sannan na fahinci baaba tayi hakane don kawar da wani abu a gare ka.
Sannan Uncle ba, , , , ji nayi ya dora dan yatsanshi saman bakina yace ya isa haka naji na gode zanyi iya kokarina inga na fitar da abin a zuciyata.
Ina alfahiri da kasancewar ki matana a yanzu don samu mace ta gari yana haifar da alheri acikin zuri,a dawamamiya.
Ya rugumay ni zuwa bakin gadon shi sai lokacin da ya sauke ajiyan zuciya yace may kika tanadarwa tafiyan gwago ne ?
Ban bata lokaci ba nace gwago mai za a tanadar mata dayafi jarin kuli da takeyi ba dare ba rana duk shi ya hanata zama hankalin ta na can wurin masu zuwa sarin mangyadan ta.
Kai naji yace yanzu kina nufin gwago har yanzu tana irin aikin wahalan nan na kuli nace da hannunta ko take komai wallahi.
Nisawa naji yayi yana kaiwa kwance nace Uncle kuna waya da anty kuwa ?
Yayi dan guntun murmushi tare da fadin ina jiran sai ta huce da kanta zata nemomu don yanzun ta hau sosai .
Nisawa nayi nace a kullun idan na tuna irin alherin dake tsakanina da ita ban jin dadi a raina da haka ta kasance a tsakanin mu.
Baiyi magana ba sai kamomi dayayi zuwa jikin shi muka kwanta anan labarin ya canza sallon shi.
Washe gari bayan ya gama karyawa ne alokacin gwago na da mako biyar a wurin mu kamar yadda yace kudi ya dora min saman cinya na yana fadin ku shiga kasuwa da gwago asaya mata duk abinda take so don Allah kada kibi son ranta a sai mata duk abinda ya dace da ita.
Dago fuska nayi ina kallon shi ganin yadda ya daure fuska yasa na kasa fadin abinda nayi niyar fada mai din.
Sai dai da ganin fuskana kasan so nake ince mai hidamar da yakeyi a kaina sunyi yawa haka gani nayi ya gyada min kai tare da fadin karki ce min komai indai ba so kike ki bata min rai ba.
Ajiyan zuciya na sauke tare da fadin Uncle ni may zance sai dai inci gaba da maka fatan alheri Allah ya saka da alherin sa.
Sai dai ba zan iya boye maka ba ban taba ganin mutum irin ka ba a rayuwa na har tsoro nake ji kada yan uwanka su fara zargina akan haka.
Murmushi nan nashi ya sakar min inda ya fara tafiya yana fadin yau ba zan samu rakiyan bane ?
Na mike da sauri ina fadin ban isa ba ai a tare muka fito ina rike da yar briefcase din shi har zuwa bakin motar shi inda iya nan nake tsaya dama.
Sai da yayi kissing din goshina ya fara tuki yana cewa ku fita da wuri don idan yamma yayi tafiyan ba dadin fita garin.
Na dawo ciki cike da murna a nan falo na samu Zarah ta fito ban tsaya ta kanta ba na nufi dakin gwago tabi bayana da kallo.
Zaune na samu gwago ta kura ma tv ido ga tasbaha a hannun ta tana ja tayi kyau ta kara kiba da haske sosai nace kai gwago wanan irin kyau haka karfa ki koma inji zawarori sun fara zuwa wurin ki.
Dakuwa ta nuno min tana fadin wani shegen bazawari zai zo wurina yanzu ai sunyi nacin su sun barni nan so sukeyi su dan cinye abinda muka dan gada su barmu muna leke a gidan wasu.
Don gaskiya gwago batayi tsufan da za a ce bata da aure don kunsan yadda aure yake a kauye irin auren nan na wuri atara zuria da wuri.
Sai da na zauna kusa da ita sannan na fito mata da kudin na aje a gabanta tabini da kallo sai kuma ta juya ta kalli kudin dake gaban ta tare da zaro ido.
Dariya nayi nace gwago kidin ki ne yace zamu shiga dake gari a sayo maki duk abinda kike so kuma ya ce don Allah a saya maki abinda naga zaki bukata indan kin koma gida.
Zaro ido ta karayi tare da fadin yar nan duk wanan uban kudin duka nawa ne haka gaskiya sunyiwa ki raba uku ki maida mashi da kashi biyu kice na gode.
Sauran na samu na kara jari ai sun isheni sayen buhun gyada goma nan gaba kin ga jari ya tasa ke nan nan gaba.
Da sauri nace a a gwago Allah ne ya kawo muna hutu a karkashin shi Allah ya duba wahalan mu na can baya lokacin da sai kin dauko abinci a gidan ki kin kawo muna muci da sauran abin amfani.
Don haka ma kin madaiji abinda ya fada wai na kaso maki su duka idan mun fita da sauri naji tace waneni wanan kudi yai yawa da kashewa yar nan.
Haka dai na lalabata ta shirya driver ya fita damu mu uku da zara muka fita gwago batayi niyar a sai mata abin kwarai ba so tayi ta dunkule kudinta ta koma gida dasu.
Amma naki yarda sai da na sai mata abinda naga zasuyi mata amfani idan ta koma da tsaraban da zata kai ma mutanen gida.
A gajiye muka dawo gidan sai dan abin motsa baki da muka sawo muka zauna nan mukaci muka kora da drinks zarah ta mike ta shiga dakin ta tare da abinda na sayo mata a fitar namu.
Bayan mun huta na dora girki na dawo wurin gwago na dubata tare da dan taba hira na koma ban sake dawowa wurin ta ba saida dare bayan na gama komai kafin ya dawo don ranan yayi dare bai dawo da wuri ba na fara hada mata kayan ina mata bayanin komai da wanda na sayo masu mama Jummai zata kai masu tsara da yaran su.
Sulaiman ya dawo gidan da alamun a gajiya ya dawo don tun bai shigo gidan ba ya rage sassauta tie di wuyan shi tare da balle rabin anineyan gaban rigan shi.
Sannu da zuwa muke mai daga ni har gwago yana amsawa da kyat yana kaiwa zaune yace gwago ana nan anashiri ko tace kaidai dan Albarka sannu da kokari wanan irin abin arziki haka mai yawa baka gajiya da dawainiya damu ?
Yace kai gwago ai albarka ku muke nema ko yaushe don abinda muke nema yayi albarka tace haka nane ubangiji ya kara rufa asiri Allah ya kara daukaka da nisan kwana .
Ya amsa cikin jin dadi da amin gwago abinda muke nema ke nan gare ku addua da fatan alheri ya juya inda nake tsaye ina saurare su bayan na gama hada mata kayan.
Yace madam yaya gida yana mikewa tsaye yake fadin haka nace Alhamdullahi yaya gajiya aiki yace not bad nabi bayan shi muka fita tare har zuwa dakin shi dauke da briefcase din sa dana karba.
Muna shiga dakin ya zube saman gado gaba dayan shi na aje na juyo ina kallon shi bayan na aje jakkan a ma ajiyar shi takowa nayi zuwa wurin na duka a hankali na fara cire mai takalman dake kafan shi tare da safa sai naji ya sauke ajiyan zuci bandaki na shiga na hada mai ruwan wanka.
Na fito still yana kwance a yadda na barshi ga ruwa can ya hadu uncle na fada mashi ina kokarin fita dakin don na dora ruwa a kattle.
A lalace naji muryan shi yace madam na juyo da ina kallon shi yace da wanan yarinyar kuka fita sayayya dazun ?
Nace eh zarah ko ?
Sai naji yayi gajeriyar murmushi yace I know it dama mikewa yayi zaune bai bi ta kaina ba ya fara kokarin cire kayan shi.
Ya barni tsaye ina jimamay tambayan shi gare ganin baita kaina yasa na fita dakin naje yin tsabgan gabana.
Bayan ya fito yaci abinci bai dade ba ya koma dakin shi tun bayan gama kallon news da yayi tare da cin abinci.
Nima sai banyi nawa ba na gama na samay shi a dakin amma yana waya a lokacin ga yadda na fahinta kafin in shigo fada yakeyi a waya amma ina shigowa sai ya rage sautin fadan shi tare da fadin na fada maku bazan dauki wanan halin ba.
Wuce shi nayi na dauki flask din na tafi daga dakin har na dawo waya yake na aje na samu wuri na zauna a bakin gado wayan ya kashe yana mai sauke numfashi tare da wurga wayan saman gado ya shiga ban daki nikan kwaciya nayi kafin ya fito.
Banji fitowan shi ba sai muryan shi da naji yana fadi daga bayana don may kika dauki yarinyar na kuka je sayayya da ita?
Na juyo da sauri yana goge jikin shi da towel nace uncle naga zamu barta gida ita kadai ne yace a harzuke ku barta mana sai may?
Ai dama bari nayi kisan halin su da kanki basai nayi warning dinki ba yanzu kin ji abinda tayi ta buga waya tana cewa wai kudi nake sakar maki kamar may don ko gwago da zata tafi wai ba karamin kudi na bayar ba akatafi kasuwa mata sayayya.
Ban san lokacin da na mike zaune ba yace yes dama na sani kadan daga cikin aikin su ne wanan.
A mairaraice nace uncle wani abu yafaru ne ?
Ya faru mana daidai lokacin da yake hawa saman gadon yace waya tayi gida wai take fada masu a hankali nace Zarah din yace dama may ya kawo ta ?
Shiru nayi a raina nace wai rufin kofa da barawo ke nan ashe idon su hajiya ce Zarah ban sani ba ashe da munafuka muke zaune a gida aiko nawa ya ya samay ni.
Tunanen may kike yi dama baki san ma,anan zuwa da ita da uwarta ta matsa ma hajiya sai munyi da ita ba.
Aisha ta fada min komai tun can hannatu ta fada min komai amma tunda naga ke kina da raayin zama da ita yasa na kyale sai tayi maki.
Da wanan bakin cikin na kwana a raina na Zarah da safe da na tashi bayan nayi sallah naje muka gaisa da gwago ban tsaya ba kitchen na shiga don dora breakfast.
Sai na samu har Jonh ya shigo yana yayanka kifin da zaiyi ferfesu dashi don shine mai muna abinci ni kuma kazantar cin abincin shi nakeyi shiko uncle bai damu ba cin abinsa yake yi.
Na gaisawa mukayi da shi tare da fada mai ya barshi zanyi baiso ba amma ban bashi fuskan tsayawa ba ya fita daga kitchen din.
Bai dade da fita ba sai ga zarah tashigo muryan ta naji daga bayana tana fadin anty ina kwana ?
Dan juyowa nayi ina amsa mata tace dani may zan kama maki anty ?
Nayi mamakin jin tambayan don bata fitowa haka da safe sai idan mun gama tace barci ne ya dauke ta bata san gari ya wayewa ba.
Yau kuma ko tafito ganin wani abin ne ta sake fada ban sani ba sai nace da ita ki barshi kawai ba wani aiki mai yawa zanyi ba ai.
Tayi dan jimmm sai naga ta nufi wurin dankali nace ki barshi yau ba zan soya dankali ba ai nan naci gaba da aiki na share ta.
Ta dan jima atsaye sai ta juya ta fita daga kitchen din na gaba na ba kowa nasa wanka nayi kafin ya fito na shirya cikin wasu atamfan Super mai launin makuba na fito zuwa wurin shi.
A tare muka fito dashi daya gama shiri tana falo wanan lokacin ganin mu yasa ta zamo daga saman kujera duk ta daburce da ganin ta bata da gaskiya ko kadan ta na gaishe shi a daure ya amsa mata.
Bayan kwana biyu gwago ta koma gida tare da abin arziki mai yawa da ta samu wurin maigida don har injin din tatsar mai ashe ya saya mata duk bamu sani ba sai da ta koma nakejin labari.
Naso bayan tafiyan gwago in daure ma zarah amma sai nayi shawara na fasa nuna mata nayi ban san komai ba gaba na da yawa ai.
Sai dai na bar yin komai a gaban ta yanzu na kuma rage bata fuskan da nakeyi sosai so nake ita da kanta tabar gidan batare da wani abu ya fito daga gare mu ba.
Wata na biyu cur a gidan uncle na canza acikin dan kankanin lokaci saboda abin more rayuwan da nake samu a gidan shi.
Don babu abinda ya rage ni dashi na fannin rayuwa duk wanda ya ganni sai yayi maganan canzawa na ni kaina nasan ina daga cikin matan da suka dace da gidan miji.
Banda tunanen komai a raina in ma ina da bai wuce na ciwon dake jikin mu ba kuma Alhamdullahi muna samun kula yadda ya dace sosai dama abinda ciwon ke bukata kenan.
Haka zai sawo abubuwan kara jini ya sakani a gaba sai munci tare magani kuma idan yana gari a tare muke sha kullum kafin mu kwanta don ka,idar shan shi ke nan.
Yaya Saadu yazo sau biyu a lokacin don ba a gama gyaran gidan da zai zauna ba sai yake zuwa yana komawa.
Ranan ina daki kwance dakina da yamma daidai lokacin dawowan uncle gida ta kusa sai ga zarah ta shigo da sallaman ta dakin tayi sallama na amsa mata ta shigo ba kasafai take shigo min daki ba sai idan da wani dalili.
Anty kin yi baki tace min na dago daga kwancen da nake ina fadin baki tace eh suna falo zaune suna jiran ki.
Dama bani zama babu kwaliya a gida tsab nake banda wani kushe a jikina kara dan gyarawa nayi dakyau na fito don ganin ko su waye suka zo.
Mata na hango zaune su hudu a falo sai dai ban sheda ko su waye ba daga nesa sai da na karso wurin ina fadin sannu ku da zuwa gaba daya suka juyo sai da gabana ya fadi.
Fon ganin bakin nawa don ba kowa bane anty Uwa ce da yaranta uku gaba daya a gidan namu, , ,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button