BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/9/20, 9:20 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , ,

????????7️⃣4️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABUN KU

Gari ya waye mun tashi lafiya ban yi mamakin rashin taya ni da baiyi ba rana don in da sabo na saba idan yana fushi bai kallon inda nake nima kuma a yadda nake ji haka yafi mim sauki ai.
Kafin ya fito bayi na koma dakina tunda nayi sallah ina wurin zaune ina azzakar din safiya da neman cikawa da imani tare da rokon Allah abubuwan bukata ga bawa.
Na gama na tashi ina nade abin sallah lokacin khadija ta motsa inda take kwance don tana fashi sallah haka yasa bata tashi ba daga barci .
Fita nayi falo na gyara ko ina saura da kuna wanka na shiga don in gyara jikina na fito na zauna na shirya kaina ina gab da zan gama shiri naji kukan Abba daga falo nasan uncle ne ya dauko shi ya tashi daga barci yana jin yunwan safe.
Ya shigo dakin dashi na karbe shi don ihun da yake tsalawa sosai a lokacin ya fadin fuska a dake ki bashi abinci yaci ya falka yana kuka haka.
Karban yaron nayi daga hannun shi tare da fadin ina kwana uncle ya amsa min a dake ya fita na bishi da kallo ina fadin ikon Allah a raina.
Wanka na fara yiwa yaron sai da na shirya shi khadija lokacin ta mike tana hada mashi abinci tace amma anty dole ki samu yarinya da zata zauna dake ko , ?
Nace ba gaki nan ba na bata amsa a takaice.
Dariya tayi tace in na zauna ummin mu fa dawa zata zauna nace ke din zaki tabbata a dakin ummi ba zakiyi aure ba khadija ?
Dariya tayi tace ko zanyi ba yanzu ba ni sai nayi karatu ina zama saman gado da yaron tana miko min feeder shi nace kin yi sa a yanzu baba ya sauko sosai idan kin ce zakiyi karatu na san a yanzu zai iya barin ki.
Don darasin da ya samu a kaina amma in bashi ba ai da kema nasan abinda ya faru damu zai faru dake asamu wani dan uwa a laka maki.
Tab wallahi ni ba zan yarda da wanan abinda sukai maki ba ai fuskana yana ga yaron nake cewa baidai kama ba khadija.
Tace ai yanzu ba shi ba ma yarinya auren dole kullun yana fadi bai son ma ku hadu idan ya tuna da abinda yayi maki shi da su inna sai yaji ranshi na baci.
Murmushi nayi nace baba ke nan ai ubangiji yakawo muna saukin abinda da yanzu kila an manta dani ko ina nan ina wulakanta wurin yan uwa.
Shiyasa kika ga duk abinda mutumin nan yayi min khadija nake shanyewa don tuna inda rayuwana ya fito cikin kaskanci .
Matsalan shi dai shi ne wanan saurin fushi da rikon magana amma don don fitan da yake min na cewa kada na fita ni dama can ba ma,abociyar son fita bane ke kin sani yanzu ne ma ai har nake shiga mutane da ummin mu da yan uwan ta kawai muka bude ido kin ga abin ya zo min da sauki ai.
Sallaman yan matan hajiya da suka shigo muna da abin karya ne a falon muka amsa kusan a lokaci daya da khadija bayan ta aje ta leko muna ina kwana.
Nace ki cewa baaba mijin tane ya tashi da fitina ban samu shigowa da wuri ba yarinyar ta dauke shi tana fadin yau mijin hajiya ka dagawa mutane hankali ko ?
Nace wallahi idan ya tashi shi ba abinda yake nema sai abinci kamar an fada mai shi kawai ake zaman ci daukan shi tayi ta dan mai wasa nace ta ajeshi yayi kashi zan canza mai permpas din jikin shi ta fita tana mashi sheri.
Khadija ce ta shiga dashi bayi ta wanke mai jiki ta fito dashi tana saka mai wani fita nayi na barsu na je hada muna abinci ida naga sinasir sukayi da ferfesu sai tea da dankali nace a raina wanan uban abinci haka duk na karin safe.
Nasan sinasir din don uncle sukayi shi don yana son cin sa sosai ni kuma ban iya ba don haka ne ban mashi a gida amma zan koya a wurin su da birabisco din da naga sunyi ranan na gero.
Da sallama a bakina na shiga dakin shi yana saka tufafin shi a lokacin ya dan juyo ya kalle ni yana amsa sallamana.
Nace an kawo abin karyawa ne nazo fada ma oky naji yace dani yaci gaba da abinda yake yi zanin gadon na juya na yaye don canza wani don wanan yayi dauda.
Ya gama ya fice ya barni a dakin sai da na gama na fito yana zaune a gurin cin abincin yana waya cikin fada fada gurin na nufa na fara zuba mai.
Yana kallon yadda nake zuba mai yana wayan sai da yakai munzalin yadda yake so yace dani barshi haka na.
Na rufe na juya na tafi ya bini da kallo bai daiyi magana ba ina shiga na samu ta fito wanka tana zaune tana shafa mai a jikin ta.
Nace yau halin mutumun nawa ya tashi bari ya gama ci sai muje muci namu abincin tace ikon Allah haka kike fama anty ?
Murmushi nayi ina kaiwa zaune nace to yaya zanyi khadija haka kuma Allah ya jerabi ni da gani ni yanzu ma kamar kada in haihun ga sai naga fushin ya karu mai sosai wallahi.
Dariya tayi tace ko da abba yake kishi kin mayar da hankalin ki ga yaro kin daina bashi kulawan da kike bashi a baya ?
Hali ne dai kawai dama haka akace yake wai ma ya rage ne yanzu da fa da kowa bai hurda cikin yan uwan shi kowa mai laifine a gare shi.
Dariya tayi tace barin je in samay shi ai mu gaisa tun bai fita ba karasa shiri tayi a gurguje ta fita wurin shi falo inda yake kwantawa nayi kafin ta dawo.
Tare da lumshe idanuwa ina tunane duk maza halin su daya sai dai halin zamantakewar ne ya banbanta wani ya dara wani.
Mu mata a biye muke dasu komai kyautatawan mace sai namiji ya kaita iyaka da zata sauya halin ta a gare shi ko yaya ne khadija naga ta dan dade sai can gata ta shigo.
Tana fadin ya fita har na kwashe kayan kai uncle oho ya fasan abinda yake maki sarai anty haka dai halin shi yake in ba shi yace abuba ba zai yarda ayi ba.
Yanzun yake ce min wai kina fushi dashi don yace ba zaki gida idan mun koma ba to haka yace hakan kuma ya tsara abinsa tace ni dai hakkuri na bashi nace aiko baki yi fushi ba don banji kin sake maganan ba.
Can wurin baaba da ya shiga gaida ita take mai yaya gajiyan tafiya ya amsa mata ba a sake ba ta fahinci yana cikin yanayin nasa ke nan.
Take tambayan shi anyi wani abune ya zauna yana hura iska tare da fadin yarinyar nan tana son ta fito da wasu hali da ban santa da shi ba yanzu.
Ba dama ince mata ga abinda nake so sai ta kawo nata korafin akai wallahi zanyi maganin ta ne a gidan nan.
Babana may kuma ya faru a tsakanin ku ne wai haka dama kake zama da yar mutane da wanan halin nan dai ya koro mata yadda mukayi.
Murmushi tayi mai tace yanzu may ye laifin yarinyar nan a cikin zancen nan daka fada kace bata zuwa ta kara cema wani abune kuma ?
Ko taki kula kane akan maganan kai dai ne ke tsiru da wasu abu yanzu ko kana cikin mazan da dazaran mace ta haihu sai su fara kyamkyamin ta ne.
Ya dago da sauri ya kalle ta tace in ba haka bane may ya kawo wanan yawan fitina haka ko acan ma haka kake mata ne ?
Yace ina na zauna gida balle ta ganni ina wurin bidan na kaina babana ka gyara halin ka wallahi yarinyar nan tana da dadin zama ga ladabi da biyayya gare ta to may kuma ake so ga mace.
Tun ina ji har gashi na gani da idona bata da wani matsala wallahi yace ai ban ce tana da matsala ba nima ban dai son abinda take min ne kawai ina fadi tana musayawa ita wacece da ba zata abinda nake so ba wai ?
Nan dai ta kara mai magana tare da nuna mashi bacin ran ta sosai akan halin da yake yi wanda ta nusar dashi da fada mai kada fa ya manta halin rayuwan da muke ciki dani dashi.
Idan bai bi a sannu bai a sannu na har na gaji da hakkuri na gudu fa yasan dai ba kimai kudi ke samuwa zai iya samun wata mace amma ba mai irin hakkuri na ba.
Wanan maganganun na baaba sun tsaya mashi a rai sosai don da zancen ta ya wuni yana mai yawo a zuciyar shi.
Ni dai naga ya dawo gida bayan la,asar ya shigo da dan sakin fuska alikacin muna falon mu zaune muna hira har da yan mata hajiya dake shirin fita gidan buki da khadija.
Mun gaida shi ya shiga dakin shi bai zauna falon ba don ganin su a part din da yayi muryan shi ya daga ya kirani na amsa na tashi zuwa gare shi.
Tsaye yake yana rage kayan jikin shi na shigo dakin daga inda yake tsaye yake magana yana fadin hada min ruwa in dan watsa ma jikina.
Ban yi magana ba na kama hanyan ban dakin kamo hannu na naji yayi na juyo ina kallon shi batare da sakin fuska ba sai naga yayi murmushi yana fadin.
Wai fushin zuwa gidan ne haka har yanzu akeyi nace fushi akan may zanyi fushi uncle idan ma kace ban zuwa gaba daya ai ba zanyi fushi ba.
Tunda nasan kana da dalilin fadin haka kawai dai idan mun koma sai gwago da khadija su wuce don ba zasu zauna har zuwa lokacin da kake son mu tafi.
Haba dai yace nace a matse suke da gida don dai kawai ba yarda zasu yi ne ina kokarin kwance hannu na daga rikon da yai mun din.
Bina yayi da kallo sai kuma na bashi tausayi sosai yaji bai kyauta min haka kawai ya hana zukatan mu samun sanyi a wani dan lokaci da ya kamata ace mun samu shakuwa sosai a tsakanin mu na zaman da mukeyi a nan din.
Har na fito daga bayin yana tsaye a idan na barshi jingine da wardrove din dakin uncle na hada ruwan, nace mai ya nisa tare da fadin nagode.
Na juyo ina kallon shi ya wani lumshe idanuwan shi ni dai na fita na barshi a wurin yana kallo na har nakai kofa yace zo nan safiya.
Na juyo gare shi ina dan kallon shi ya bude hanayen shi yana jiran in iso gare shi din nace daga inda nake ba wanka zaka shiga ba uncle ?
Idan wanka zan shiga bazaki zo ba don ina da kazanta a jikina komay ?
Dariya maganan shi ta bani har na dan murmusa kadan yace to ko ke fa duk na rasa gane kan ki kwanan har kin sa na fara zargin yan uwana ko su ke zuga ki ga abinda kike min din.
Da sauri na karaso inda yake ina fadin wallahi haram kada ka zarge su da komai idan basuce in soka ba in ma biyaya kasan dai ba zasu taba cewa in guji dan uwan su suba.
Zama lafiya kawai ke tsakanina dasu har kakai ga fahintar haka a gare mu ya rugumoni zuwa jikin shi yana fadin to ke din ce yanzu naga kina son yi min gardama ga abinda na fada.
Uncle may na fada ga maganan tunda kace ga yadda kake so ayi murmushi yayi ya rungumini kawai ban son kina min gardaman ga abinda nace.
Insha Allahu nace tare da kokarin jaye jikina daga nashi na juya kawai ban kara cewa komai ba tsayawa yayi yana bina da kallo har na fice daga dakin.
Falo na dawo na samu har sun gama shiryawa suna jira inzo in karbi Abba su fita nace ku dai kula da kan ku don Allah idan kun fita.
Insha Allahu suke cewa kusan a lokaci daya nayi masu a dawo lafiya tare da daukan yaro na nasa saman jikina.
Sai da ya gama shirin shi ya fito ina kwance saman dogon kujera da yaron da yayi barci a jikina nima barcin ne keson daukana a lokacin.
Badai barcin marace zakiyi ba kin san baida kyau nace shidai nake ji tare da dan dagowa kadan daga yadda nake kwancen.
Wurin cin abinci ya nufa yana bude kayan abincin sai wayan shi yayi kara daga cikin aljihun shi ya ciro ya duba ya dan ja tsuki tare da daukan wayan ya kara a kunnen shi.
Naji ya amsa tare da fadin ba ida zan tafi yanzu na gaji sosai yau ina son in dan huta gidana da iyalina a raina nace kamar wanda yasan damuwan iyalin nasa.
Muna zaune a falon daga ni sai shi sai dan mu dake barci a gefe na sai karan na,uran sanyi dake ta aiki a falon ya gama waya yaci abinci ya dawo saman kujerun falon ya zauna.
Khadija fa yake tambaya na nace ta fita da yan matan hajiya zuwa gidan buki rai naga ya bata baidai yi magana ba nima ban yi ba na share shi kawai.
Kwance yake yana fadin mummy tace wai kada ki manta da sakon ta ko may ye sakon nace ai nayiwa anty suwaiba magana masan bauchi take so azo masu dashi idan zamu koma.
Yace masa kuma ba ko kirdamo ba nayiwa mutanen gidan gona na magana su sama muna kindarmo da zai wadace mu idan mun koma.
Nace amma ko naji dadi tundai da nazo nan na koyi shan shi da shinkafa yana min dadi sosai wallahi yace au ashe kina so ke nan ?
Ai kullun sai na tsiyayo a falon hajiya don akwaishi koda yaushe mutum ke so dama ita hajiya tana son shi sosai awurin ta ma muka koyi shan sa.
Sallama akayi muryan namiji ne daga kofan shigowa falon ya amsa mai da fadin mustapha shigo mana na fara dan kamay kamay jikina don nasan ba abu mai wuya bane hakan ya hada mu.
Yace ki zauna abin ki baki san mustapha ba ko kanin yayana ne mijin anty ki ai bakon ke fadin bamu taba haduwa ba da ita ko kin sanni ya juyo yana tambaya na.
Kai na girgiza mai alaman ban san shi ba mike wa nayi ina fadin bari na leka baaba na dawo nan na fice na barsu sai yaron dake barci.
Ita kadai a wurin ta sai tv dake ta faman aiki tana zaune tana waya na shigo ganin tana waya yasa na mayar da hankalina ga tv dake aiki a falon.
Hankalina naga tv naji ta ce dani maryam tace a fada maki wai gobe zata zo damai gyaran jiki a gyara maki kan ki da kumshi dariya nayi nace wai data barshi ai don na kaina bai dade ba ma tace sunyi magana don itama ina gani za ai matane.
Allah ya kaimu nace tace ai ku yara gyara jiki gareku baya baci balle wanan miji nake dake da saka ido dole ki mayar da hankali ga gyara don shi dan korafi ne.
Nasan shi sarai da son gyara ga mace don yaran nan shike basu kudi suje kitso suna kanana kin ga ko yanzu a kan ki zai koma ke matar shi.
Dariya nayi tace nasan halin shi sarai wurin tsabta indai babana nace wallahi ko baaba haka ma yake ko acan ina da matar dake zuwa har gida tayi min kitso ko wanke kai tace bakaji ba baida wasa wirin tsabata shi.
Alhamdullahi duk abin da nake jiye mashi ya samu a wurin ki tunda ba wanda ya taba jin kan ku ai kin ga an zauna kalau ba korafi.
Sai dai abinda nake so dake shine ki kara hakkuri nasan kina da da baki da shi da yanzu anji kan ku da wanan fushin nashi nayi mai magana kan zuwa gida da kike son yi shikuma yana son hanawa.
Da sauri na dago kai na dan kalle ta ina mamaki a raina ina taji wanan zancen don dai ni ban fadawa wani ba ko kuma wurin khadija yan matan hajiya sukaji suka kwarmata mata.
Kai khadija bata fadi na sani to a ina taji nake tambayan kai kamar tasan abinda nake tunane naji tace nan yazo da safe yake fada min na nuna mashi kuskuren shi.
Nan dai ta shiga yimi fada nima tana kara lurar dani zaman takewan zama tare da yadda hakkuri ke jawa mutum riban aure a rayuwa.
Shi ya shigo yana fadin Abba ya tashi yana dauke da yaron a kafadan shi ya miko min shi tashi nayi na fita don abincin shi nacan part din mu don haka na koma can.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button