BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/12/20, 7:42 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

????????7️⃣8️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

Muna tsaye kofan inna muna kallon yadda likitan yake mata allura zabban tausayi har ya gaba ya fito yana cire safan hannu da takunkumin da ya rufe hancin shi dashi inda ya jefa a wani leda zai fita dashi.
Nan yake fadi a gaban kowa yace a kikyayi zama kusa da ita a daina amfani da duk wani abin amfanin ta don ciwo ne mai saukin dauka ga mutum idan da hali a raba makwanci da ita.
Kuka inna ta saka mai ban tausayi tana fadin ni rakiya yau naga ta kaina na zama abin gudu har ga diyan da na haifa a duniya.
Daga kofa inda nake nake fadin cikin murya mai rauni inna kiyi hakkuri ciwo ba mutuwa bane zaki samu lafiya in Allah ya yarda adai kiyaye abin daya fada kawai.
Yaya sani yace yau bagaki ba safiya may ye ba ayiba a lokacin ciwo ki a gidan nan wanda ba kowa ya sa ai maki ba sai ke inna ina fada maki ki bari amma kamar zugaki nakeyi a gidan nan.
Har kika fara gaba dani ummi gata da ranta ita tayi min fada akan in bi maganan ki in bar fushi dake komai Safiya ta taba a gidan nan damun bi ta naki inna kona shi zamuyi a lokacin.
Likita yace ai wanan ciwon yafi kanjamau saurin kisa yanzu baga safiya ta gyagije ba kamar ba a yi ba da ta fake magani .
Ai ba a gudun mai kanjamau kamar may irin cutar nan don saurin dauke gare shi sosai ga wa yanda ke kusantan ka sai kawai mukaji inna ta saka wani irin kuka mai kama da ihu a lokaci guda duk muka rudu ga kowa na tsoron shiga dakin wurin ta don kada ya kamu da ciwon.
Nayi kundunbala na fada dakin ina bata hakkuri sai fadin take safiya dole inyi kuka cutar nan kila kasheni zaiyi safiya.
Ina naje dana dauko wanan mumunan cutar a jikina yaya sani shima ya shigo daka ciki muna bata hakkuri likitan yace idan zamu shiga wurinta mu dinga saka takukumi a hancin mu dau saukin shakan nufashin ta.
Mun fito muka sallami likitan na bashi duk wani abin bukata har zuwa lokacin da alluran zai kare.
Shigowan Saadatu ke nan gidan da goyon ta wanda yayi wayo sosai yaron ganin mu a kofan dakin inna yasa hankalin ta ya tashi bamu ko gaisa ba take tambayan mi may ke faruwa ne ta gamu cirkocirko haka tsaye ?
Bakomai na fada ina karban dan dake goye a bayan ta amma sai yaron yaki zuwa wurina don kiuya irin na yara da yake dashi.
Dakin ta shiga ta ga uwar a zaune a tsakiyan falon ta tace inna yaya jikin naki tace da sauki nan dai ta dan tsaye, tsaye jim sai ta fito waje.
Lokacin na koma bangare ummi na ina batun aika yaro yakai ma mahaifiyar Amina sokon a gidan su sai da nagama bada sokon na juyo gareta ina Saadutu an shigo ashe ?
Gaisawa mukayi tare da tambayan lafiyan su sai godiyan abincin da ta aiko min dashi daren jiya din da tayi shima nayi mata godiya akan shi.
Tace kai don Allah nasan ai bazakici ba na dai aiko ne kawai kada dan uwanka yazo gari baka aika mai da komai na sannu da zuwa ba.
Kika ce wai ba zanci ba toga ummi nan tambaya kiji sai da naci fiye da rabi nakuma shanye miyar tas wallahi taji sadi don fuskanta yanuna hakan.
Tace ikon Allah har abokiyar zama na fadin wai zan dai kawo ne amma ku yan birni ai ko kallon wanan abincin bakuyi ai haka dai na daure na kawo maki shi.
Nace aini banki ba kullun kina kawo min irin wanan din don ina son shi sosai wallahi samu dai ne ban yi a can.
Ikon Allah na katse ta da fadin yaya Adamu maigidan ki yake dariya tayi tace mutumin ki yana nan lafiya wallahi sai dai yanayin garin da muke ciki yanzu kawai amma ya daina halin nan yanzu lafiya lau muke dashi sai abinda ba a rasa ba.
Tace ai yaji dadin kudin da kika aiko mai kwanaki har ya fara sana a sai wa yanda suke sana,an tare ashe suna bishi kudi nan sukayi karan shi karshe har da na wurina muka hada aka bashi yanzu yana zaune bai komai kuma.
Na tausaya mashi nace mutum magidanci ya zauna ba sana,a haka ai abin baiyi ba wallahi tace ai yace yana nan zuwa ya gaida ke da zuwa.
Nan Ainau ta shigo gidan itama da goyon ta muka hade mu uku duk sun girmay ni amma samun wuri da kuma maganin da nake sha wanda ya hurani na danyi kiba ba sosai ba.
Anan muka wuni tare da su inda na dauko masu tsaraban su na basu sai farin ciki sukeyi da murna ga abinda na basu din.
Sai yamma suka tafi gida inda nace masu idan na huta zan shigo gidajen nasu mu gaisa na dan raka su na dawo na dibi ruwa zan watsa ma jiki sai ga shafiu ya shigo da Abba a hannun shi yana fadin wai ga Adamu nan mijin Saadatu yazo gaida ni ya shiga ya gaida inna da sauri na mayar da rigan dana cire a jikina kafin ya shigo dakin ummi din mu gaisa dashi.
Da sallama ya shigo ina saman kujera na mike ina ce mashi ga wurin zama nan ya zauna yace a a zai zauna kasa na hana shi dole ya hau kujeran ya zauna.
Ni kuma na koma daga kofan kuryan dakin ummi na fara gaida shi yace kunzo lafiya nace Alhamdullahi yace to barka da arziki ashe an sauka murmushi nayi yace bamu ba da komai ba sai kuma ga sako na gani nagode nagode kwarai Allah ya kara rufa asiri.
Nace kai haba bakomai wallahi kasuwa dai yana tafiya yanzu ko na tambaya kamar banji komai ba a kan shi yace tau Alhamdullahi zamu ce hajiya don ba a cewa komai sai hamdala.
Amma gaskiya yanzu komai ya tsaya ne cak wallahi kudin da kika turo min kwanaki na fara dauko mai jerka biyar dashi tunda wa yanda muka fara sana, a dasu sukaga na dan samu suna bina kudi sai sukayi karana dole na hada kan kudi na biyasu abinsu shine yanzu nake zaune ina zaman ba sana a .
Kin san ance wanda ya amshi kudi hannu mace yana tare da gori komai daren dadewa to abinda ya cini ke nan dama yan uwan matane suke bani yanzu kuma wanan abin daya gitta har na auri saadatu sai suka karbe dukiyan su a hannu na suga yadda zanyi watau.
Dariya nayi nace baduk mata suke haka ba ai wasu dai ne haka suke shiyasa nima banyi maganan komai da Saadatu ba har tazo ta wuce ta dai fada min kamar yadda ka fada min yanzu din yanzu a misali idan na baka dubu dari biyu zasu isheka ka fara sana,a mai dan kauri dasu.
Hajiya dari biyu ai ba karamin kudi bane yanzu nace to zan baka sai ka fara mu gani ya katseni da cewa har zuwa yaushe zan maida maki kudin ina mikewa nace a a baka nayi halal malak kaja jari dasu ba rance na baka ba ni kyautan su na baka.
Zamowa yayi saman kujeran da yake zaune da farko ya hada hannayen shi biyu a wuri daya ya fara zabga addua da fatan alheri a gare ni.
Nace ba sai ka fadawa kowa ba Adamu nidai bukatana a gareka shine ka rike min yar uwata amana don Allah ka kula dasu dukan su ukun matan kane.
Godiya ya kara min yana kokarin tura kudin da ya karba a hannu na cikin aljihun rigan shi tare da yi min sallama har yake kofa ya juyo yana fadin gobe gobe in Allah ya kaimu zanyi asubancin zuwa birni wurin saro man in sayo.
Nan dai ya fice cike da farin ciki nikan yana fita daga dakin na mike don duk zafi nake ji a jikina ina son in dan watsa ruwa inji sayi.
Kafin wani lokaci gari kowa yasan na zo wasu idan sunga mota a wajen gidan mu ne suke tambayawa a fada masu.
Wasu kuma idan na aika masu da tsaraba suke sanin na zo garin ban fara fita ba sai da na kwana uku yan uwa da abokan arziki suna zuwa gaida ni suna kuma aiko min da abinci da dan abin marmari don kulawa.
Har da makwata dana ba tsara ba sun shigo taro na da gani dan da na haifa wasu dai gulma ne ke kawo su ganina kawai suga yadda ake fadin na koma yanzu.
Gidan mummy mahaifiyar Amina kawana na fara zuwa inda musa driver ne ya kaini gidan shi da security din mu na dade gidan muna hira da mummy inda nace ai zan shiga wurin Amina kafin in koma in Allah ya yarda.
Ina fitowa na wuce gidan su mama jummai na gaida su suma duk inda naje sai na jima a gidan daga wurin su na dawo gida.
Duk abinda nasan inna naso wanda akace tace na sa yaya sani ya sayo mata inda nayiwa yaranta nasiha su kula da uwar su don Allah.
Wanda ba kowa ta jawo hakan ba ga yaran gidan mu sai inna din don batayi zoton abin zai shafe ta ba haka.
Washe gari gidan Ainau na fara zuwa tun da safe muka fita sai karfe daya na bargidan na wuce gidan saadatu .
Gidane may irin dakunan nan ajere suke guda hudu sai baranda ba wani siri da mutum zai iya yi ba a ido yan uwa ba.
Yaran gidan sun kai bakwai saadatu ne ke da daya a cikin su na samu wata mata da daure gaba tana tuka tuwo a tsakar gidan inda suke girki.
Yin sallamana yasa sauran fitowa daga dakunan su mai tuka tuwon tunda tayi muna sannu da zuwa ta mayar da kai ga aikin ta bata kara juyowa gare mu ba.
Tare da su khadija muke muka shiga dakin saadatu din daki daya ne single da gado da mirrow sai drower gadon dake gefe an dagwara mai roses guda guda da ledan kasa malale a dakin .
Kujara mai zaman mutum uku damai zaman mutum daya sune a dakin zama mukayi aka fara gaisuwa a tsakanin mu saiga wanan matar da tafita tare mu dauke da kwanon sha cike da ruwa ta kawo muna.
Tana fadin safiya ko ai yanzu bata gane ni tunda an dade ruwan na karba na sha nace wallahi kan ban gane ki ba yar uwa tayi dariya tace mune senior ku don muna gaban ku da shekara uku sai dai ni ban gama ba nayi aure lokacin mai yawo dasu Aisha sani na kusa da gidan ku.
Nan dai suka shiga min bayani ita da Saadatu saida na gane ta nace ankoyi haka tace gamu mun hade da yar uwarki muna auren miji daya yanzu.
Allah sarki nace kuna lafiya yaya yara yaron ta karba a hannun kauna na yar wurin mama da muka zo da ita tace tubarkallah yaro yayi wayo sosai.
Mun dayi hira ta fita dakin mukaci gaba da hiran mu na abinda ya shafemu na gida maigirkin taba dan tuwo kasan kwano a kawo muna mukace a maida mata a koshe muke mu.
Sai lokacin ta shigo tana fadin bazakuci abincin mu ba nace gidan Ainau muke sunci taliya acan ni kuma na koshi yanzu ganye kawai nake son in samu inci.
Ta juya ta wuce saade tace ganye kike so nace eh tace barin nemo yaro ya sayo maki sai khadija tace baga maimu na ba abata taje ta sayo bakin kasuwa mana.
Dubu daya na zaro a jakkana na bata tace na nawa nace ta sayo na duka ido suka zaro mun a lokaci daya suna fadin har ganyen dubu daya haba dai.
Na dari biyu dai ko daya nace kuba zaku ci ba ne sukace zamu ci yar uwar zaman saade ne ta shigo dakin tana fadin ko zaki sha fura ne a sayo maki nace ganye dai nake son ci ga kudi na bada a sayo min tace wa zai sayo sai khadija tace maimu zata sayo.
Ta sake tambayan da kuli zance ko soya min za ayi nace da kuli dai za a gyara min tace to ki sayo na dari biyu di sai kayan hadi sai saade tace kuje kiyi mata bayanin abinda zata sayo.
Suka fice dakin nan dai mukaci gaba da hiran mu sai ga maimu ta dawo ba, a jima ba aka gyaro ganyen sallah muka farayi muka zauna gaba dayan mu muna hada hannu muke ci a katon tire dukkan mu.
Khadija ce take fadin amma anty saade kunfi zaman lafiya da wanan matar data gyara muna ganyen nan tace ba ruwanta ai bata da fitina amma ita dayan haka take kamar innar mu wurin fitina.
Kullun sai tayi fada da wani cikin mu kan diya ko kan girki sanan tana muna kurin yan uwanta na da kudi a cikin mu har gori tayi min da muka taba fada.
Wai yar uwar tawa da nake kuri tana birni bata ko san dani ba a duniya sai ta kashe take bamu dariya nayi nace badai kina da mai kashewa ta baki din ba ai yafi babu.
Tace ina ma kika sani dana dawo wurin sunan yaron nan da naje cewa tayi kuma wai naje nayo maula ne gurin ki ai ba shiri a tsakanin mu da ya dakin ku.
Nace fita batun ta don Allah irin matan nan ne da sai su zuga ka har ka aikata abinda baka tashi yi ba tace ai na gane ta yanzu ban biye mata.
Khadija na bawa makulin mota don bamu fito da su malam musa ba mu kadai muka fito yau, nace ta je ta dauko min kayan dake bayan seat a farar leda.
Ta fita sai gata ta shigo da ledan nan nanuwa saade turamay zani da sabulu nace tabawa kishiyoyin nata.
Tace duka safiya nace kada ki damu girman ki nake ja maki a hakan ai fita tayi sai nabi dakin da kallo don in san abinda zan mata a dakin nata don ace inna batai mata komai ga auren nata wai bata son auren.
Ta dawo sai gasu tare sun shigo dasu sukayi godiya suka fita khadija ke fadin dama Atikan kawai kiba wallahi nace ai ba ayin hakana kuko.
Nace saade yanzu kina ganin dakin nan yana daukan fridge da kayan kallo kuwa tace aiko bai yi zan sa afita da kuje daya sai in samu wuri nace to yayi sai ki gwada mu gani mikewa nayi nace barin shiga dakin senior dina mu gaisa na suri jakkana na fita daga dakin.
Ina jin khadija na fadi zataje tayi mata dumus ke nan tunda kinga ta dauki jakkan hannunt ban tsaya bana fice daga dakin.
Tana gani ta kama washe baki tana sannu da zuwa dakin nata gwanin ban tausayi wallahi kai mata muna cikin wani hali a rayuwan auren mu har na tuna da dakunan su ummi na da.
Sai a kai mace da kayan mutunci gidan su amma sai a kashe kayan da miji ba zai damu da ya sayawa matar wasu ba tunda a tare ake amfani dasu sai dai ita mace ne zata kama kulla kulla har ta samu ta dan saye nima nasan da ina gidan Ahmed da har yanzu da dan gadon katakon dake daki na zan ta rayuwa.
Mun dan zauna ina tambayan ta wa yanda mukai karatu a tare tana bani labarin su hannu na tura a jakka na na kirga dubu ashirin na aza mata a gadon ta nace ayi hakkuri akwai abubuwa da yawa amma wata rana zakiji sakona da yardan Allah.
Na fice tun bata fara yi min godiya ba na shiga dakin dayar mai kurin arzikin gidan itama babu komai a dakin sai wani tsohon gadon na katako da wasu rubabun kujeru manya a dakin dubu biyar na bata na fito bayan mun gaisa da ita.
Ina shiga nace ku taso mu tafi saade sai na sake dawowa maimu da hindutu ne ke rige rigen karban jakkar hannu na khadija tace naga alama mai kamar dai dake za a koma Abuja nan ko ?
Nace maimu da hindatu kan ai tashina tashin su tunda ke kin gudo ban yarda in rasa abokin hira a gida ni kadai sai mummy.
Nan suka shiga masu sheri suko yaran sai murna sukeyi zasu tafi abuja khadija na fadin kuje kuyi zaman kurkuku ai ba shiga ba fita sai zaman gida.
Na bude mota muka shiga na tayar ina masu horn duk suka daga muna hannu muka tafi sai gida tun dawowan mu na dan leka inna wacce yanzu maganin ya fara bata reaction tana yawan galabaicewa sosai na samay ta zaune yaya Sani ya sawo mata lemo mai bawa tana sha.
Na gaida ita na fito na shiga wuri mama itama na gaida ita na koma dakin ummina ina fadin wai kamar nayi wani abu yau duk na gaji ummi na sai dariya take yi cikin jin dadi da kulawa.
Mun dan taba hira wanda kusan hiran na kishiyoyin Saadatu ne sai nace maimu dake lake dani ta kira min yaya sani a waje idan yana nan tashi maimu ummi tace ashe kin samu yan rakiya Abuja ne yanzu maimu ke fada min da su za a tafi wai ?
Nace haka nake so ummi shima yayi mi maganan hakan don yaso khadija ta zauna damu amma taki kanta na rawa.
Ummi tace bar ta kawai mara hankali ba komai ya hata zama ba sai wanan sauryin nata mara mutunci da take son dauko muna wahala taki zama.
Nace nima dai ummi yaron bai kwanta min a raiba wallahi don ba yan mutunci bane ta rasa wanda zatayi soyayya dashi duk garin nan sai zurian su inna.
Gaskiya nima hadin bai min dadi ba gaskiya ummi ai ta samu wasu a bauchi da muka tafi ban dai sani ba ko har yanzu a kan shi take.
Ummi tace kinga ko bata fada ba don karnaji nayi mata fada tana tsaye daga kofan kuryan ummi tana sauraren mu ta turo baki gaba.
Ummi tace tsayin may zaki zo ki muna a kai in kina tsayawa kima kan ki fada tun wuri gara ki tsaya ga masu son ki na kwarai don dai ni ba yarda zanyi da wanan zaben naki ba.
Juyawa tayi ciki da fushi tana magana kasa kasa nace ji wawiya don Allah ana fada maki gaskiya har kina ganin laifin mutane akai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button