BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , ,

????????2️⃣8️⃣????????

YAR UWA NOVEL DIN NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE……….

Matsala na yanzu Inna ce tabi gari tana bada labari a kaina wasu har zuwa suke yi ganina a gidan mu.
A cikin gida kuma ita da yaran ta ne suka tsan gwamay ni a gidan ko zama nayi a wurin sai sun share ko su goge zasu zauna.
Idan na taba ubu bazasu taba ba koda sunyi niyar taba abin sai su fasa.
Ga sake habaici a tsakar gida wai an kwaso cuta an zo za a lakaka masu sudai an cuci rayuwan su wallahi.
In naji su na kan yi murmushi kai a fili amma cikin raina nakan ji zafi da dacin zuciya ya kama ni.
Wani lokaci kuma idan sunyi man nakan shige daki inyi ta kuka sai ummi na tai min nasiha nakan yin shiru ko inji dan dama da sanyi.
Har aikin da kan taya ummi sai suka tsani cin abinta idan na dan taba wani abu daga ciki ko ta gama ta basu sai kaji ana kiran almajiri a juye mashi.
Da na gane hakan sai inyi zamana kawai a daki bana fitowa taya ta aikin ita ummi ta fahinci manufa na sai tace min ki zaman ki a daki yafi maki har kiji sauki.

Ranan ina daki kwance ina karatu akai sallama ina jin bakuwar suna gaisawa da mutanen gidan mu.
Sai take tambayan Safiya tana nan kuwa aka nuna mata dakin mu ta nufi can suka bita da kallon mamaki yar gayu da ita zata zo wuri.
Jin ta ambaci suna na yasa ni saurin tashi ina da sauri ina daga labulen dakin mu don in ga ko wacece take nema na din .
Bakowa bace sai Amina kawa na da mukayi karatu tare da sauri na sake labule na nufo ta muka rungumay nuna da ita sai yan gidan mu sukai tsaye cirko cirko suna kallon mu.
Na san ba komai bane suke ma mamaki sai yadda ta rugumay ni ne su gashi suna gudu na agidan suna gwada min kyama a fili.
Muka shiga dakin mu nan na aika ka sayo mata pure wata mai sanyi tana cewa a a nace ta dai bari a sayo mata bayan yaron ya fice sayen ruwan ne.
Tace dani ashe kuma haka abin ya kasan ce dake alamarin yazo da matsala haka Allah ya nufa Safiya kiyi hakkuri nima da na shigo jiya mama na ke fadamin abindake faruwa.
Safiya jiya da naji maganan nan ban iya barci ba amma kuma danaga masu shi yanzu ba a gane su a fuska sai na barwa Allah alamari .
Gaskiya naji dadi yadda nazo na samay ki baki gala baita ba gaki har jikin ki na dawo naji dadin haka kwarai da gaske.
Nan na fara bata labarin abinda ya faru tun farko sai cewa take subbahanallahi amma wanan mutum baida tausayi baida imani ko kadan.
Tana share hawaye tana fadin Safiya Allah ya duba maki alamarin ki ya tausaya maki wanan BAHAGGON rayuwan da kika taso a cikin shi.
Nace da ita amin don yanzu idona ya kyan kyashe da kukan nayi nayi nagaji sai dai na kasa daurewa ganin tana kukan nima kukan nake yi.
Sai ummi ne take bamu hakkuri tana cewa haka Allah ya nufa ba yadda banki auren nan ba amma mahaifinta da matan shi suka nace da sai tayi.
Yanzu da wahala ya cika da ita duk sun watse din sa muna ido da ni da ita a daki sun koma suna kyamatar ta a gidan.
Safiya tace ai wanan jahilci ne ba a gudun mutum sai dai ayi taka tsantsan wurin yana yin zaman takewa.
Amma in ana gudun mutum tunane sai ya shiga maishi sai ciwon ya samu galaban samun wurin yin barna da kyau.
Mun dade da ita a gidan nan ta wuni wurina nai mata dahuwa taci zata tafi na rakata bakin kofan gidan mu.
Zan shigo gida na hadu da Inna ta yafa zata fita ta wuce na shiga gida ashe tabi bayan Aminan ne ta tsaida ita.
Tace keko yar nan baki san may ke faruwa da Safiya bane nagan ki wurin ta har da cin girkin da tai maki.
Amina tai murmushi tace kwarai kuwa na sani shine ma ya kawo ni wurin ta ai don in mata jajen abinda ya faru da ita.
Inna tace baki gudun ki dauki wanan cutar kema a wurin ta don ance saurin yadduwa ne dashi.
Amina ta girgiza kai tace ba haka bane gaskiya a samun sa ta hanyar saduwa kamar yadda ita Safiya ta samu daga mijinta.
Sai kuma ta wurin amfani da zera ko masilar kitso ko allura idan jinin maishi ya shiga jikin ka to kaima kana iya samun wanan cutar bayan haka zaku iya hurda ko wani iri da mai wanan cutar kamar kowa.
Inna tai mata wani irin kallon rashin gamsuwa da maganan ta tace ni dai na fada maki gaskiya don naga kamar baki sani bane.
Ashe kin san komai idan iye iyen ki ya kai ki kika dauko ma kanki cuta ke kika sani ninayi nan.
Amina tace da ita dakata inna sai ta juyo ta tsaya tace da ita wanan abinda kuke yi ya kamata ku dai na wanan halin da kuke nunawa safiya.
Inna ki sani idan yarki ce ta shiga irin wanan halin yaya zakiyi sai ta tofar da miyau tace bakin ki ya sari dutse Allah yai ma diyana tsari.
Tace kin gani itama fa ba da son ranta ta samay shi ba kin sani ya kamata ku jawo ta a jiki kuna kwantar mata da hankali ba ku dinga aibanta ta kuna hattaran ta ba haka.
Don Allah Inna ku daina wanan abin da keyi sai ta tare ta dacewa mugun halin uwarta ce ya bisu ai kadan ma suka gani ai.
Allah ya kyauta Amina tace da ita ta wuce tana bakaken magana Amina dai tabita da kallo tare da girgiza kanta kawai ta wuce.
Inna ta dawo ido mirsisi tana zage zage a fakaice sai kuma ta shige daki suna magana da diyan ta kus kus kus.

* *


Ina zaune a dakin ummi tun safe da na fito van sake leko waje ba ina dai jin hayaniyar mutanen gidan mu daga waje suna harkokin su na yau da kullum.
Ba abinda nakeyi sai tunane abu biyu ne ya tsaya min a raina na farko in na tuna muamula na da mutane yadda ya ja baya yanzu.
Sai na biyu yaya rayuwa ta zata kasance a haka zan zauna dakin uwa ta in kare rayuwa na ba wani abin ci gaba da zanyi wa rayuwana.
Na lumshe idanuwa na cike da takaici take naji hawaye na zubo min ashe ummi ta shigo dakin ban sani ba tana tsaye a kaina nadan wani lokaci.
Muryan tane yasani bude idanuwa tana tsaye a kaina tana kallo na cikin bacin rai da ya baiyyana a fuskan ta.
Ta lumshe idanuwan ta cikin takaici ta juya tana neman abinda tazo dauka a dakin lokacin muryan ta yayi rauni ta fara magana ba tare da ta dubeni ba.
Watau so kike kuma ki jawa kanki sabon matsala a rayuwa baki san ciwon kan ki ba ana fada maki ko yaushe kiyi hakkuri kibar wa Allah almarin ki.
Amma sai ki zauna a daki ki ta kuka kina tunane ke kadai ana fada maki gaskiya baki dauka to maye amfanin zama na a gidan kina kara min bakin ciki ?
Ki rungumi kaddaran da ubangiji ya jarabe mu dashi sai Allah ya tausaya maki yai maki mafita ta inda baki zata ba.
Kuka nake yi sosai nace ummi ba hakana bane in na tuna da irin zaluncin da sukai min ne sai na kasa hakkuri a raina.
Tace sai kin fitar dasu a ranki ki rungumi kaddara ki mai da alamarin ki ga ubangiji kamar yadda kowa ke fada maki a kullun duk masoyin ki abinda kawai zai fada maki kenan a yanzu.
Don kaddara ya riga fata gare ki ki dinga fita kina mu amula yadda kowa keyi a gidan gida na ubanki ne babu mai koran ki cikin sa koshi bau isa ya kore ki ba tunda shi ya jefa ki a wanan halin.
Da sannu zasu janye manufarsu a gare ki kowa a dawo daidai dama zaman gashi nan dai ne anayi har duniyan ma nawa take ga dan adam.
Ba abin mamaki bane ki mara lafiya ki rayu mai lafiyan ya mace ga Allah duk wanan sau nawa yana faruwa ga dan adam.
Don haka har kulun nake godewa Allah da ba wurin wani hanya mara kyau kika kwaso wanan cutan ba .
Har kulun ina godewa Allah daya bani yayan da suke da hankali da hangen nesa Allah ya kara shirya min ku sak na amsa mata da Amin.
Naji dadin wanan nasihan sosai na ummi kiran da a kai mata a waje ne yasata fita dakin lokacin na sauke ajiyan zuciya na mike tsaye.
Washe gari tun da safe da nai sallah ban kwanta ba na fito na share tsakar gidan mu tas baba da ya dawo massalaci ya gani ina wanke wanke yake min sannu.
Ya zuba min ido cike da tausayi ya wuce dakin shi yana tunanen a ran shi yana daya sani ya barni na auri zabi na gashi yanzu yaron ya zama wani abu a gari lokaci guda ya samu wurin aiki mai kyau yayi aure shi anan garin.
Haka naci gaba da rayuwa zaune a gida in lokacin karban magani yayi in shiga mota in je in karbo idan zan dawo na dan riko ma yaran gidan mu tsaraba.
Sai kaji suna cewa yaushe ne zan tafi birni in sayo masu abu kaza dana taba sayo masu acan.
Yanzu hankalina ya kwanta ina samun walwala sannu a hankali har nakan fita zuwa gidan gwago da yan uwan mahaifiya ta da kawaye na don sun gaji sun daina gudana.
Masu son kaya har gida sukan biyo ni don saya ko ba da sautu a sayo masu wani abin idan suna so.
Haka sai mu a mula na ya dawo daidai da mu tane ina hurda da kowa babu tsangwama ko hattaran da suke min da farko.
Na tayar da sana a ta zanga zanga dashi nake samun ina juya rayuwan mu harda na kanne a gidan don haka muka koma bamu da wata damuwa a tare damu.
Sai dai har yanzu wanan muguwar akidar ta inna nan a ranta da wasu diyanta abin yana damu na sosai yadda suke nuna min tsana a hili tundai babban yar ta da ake shirin yiwa aure.
Don da dan abu ya hada mu da ita yanzu zatai min gori da ciwon dake jiki na zata tsaya tai muna tas a tsakar gida babu kunya ko jin tausayi na ga halin da na tsinci kaina a ciki.
Yau kasuwan garin mu yaran gidan mu masu sana a suna ta sha anin sana an su da zasu fita dashi cin kasuwan.
Maganan yara ya taso sai rikici ya hada su da yaran dakin mu dana Inna da diyan dakin mu subbahanallahi ranan naji tonon asiri da ban taba ji ba a wurin inna kamar dai ta dade tana shirya muna ne.
Abin da yafi kona min rai shine irin zagin da take min da cewa naje na debo cuta don mugunta ina son in yada ma gida kowa ya samu.
Haihuwana ya zame masu bakar haihuwa a gidan da barnan suna ko fita sukayi sai ai ta nuna su basuci ba basu shaba
Wai tun auro ummi gidan ya juye masu da tsiya basu kara gane gidan nasu ba.
Tai ta fadan maganganun har tayi ta gaji karshe ta juya ga ummimu nan sukai tayi tace itama ai ba sayen shi tayi ba aure ne yaci ta .
Inna tace oho dai da ana muna sallo wai itace mai karatun boko a gidan nan anyi aure a birni, to yanzu ina bokon yake ?
Wai ina zaune a gida haka zan tabbata ina kallo yan uwanta na aure ni ko ba halin yin aure a rayuwan na.
Ummi tace Allah ya fi mu sanin daidai don yana sane da komai da kowa a rayuwa sai da baba ya shigo gidan san nan suka daina.
Watau a gaskiya tunda inna ke fada min bakar magana akan ciwon nan bai taba kona min rai irin na yau da tai min ba ni dai ina zaune ina kallon ta ina aiki na banko tanka mata ba har taci ta sude ita kadai.
Sai dai ance ko shiru magana ne don haka shirun da nayi sai yaci mata rai kuma wai na mayar da ita mahaukaciyan tsakar gida don nasan abinda na jajibo gidan.
Mama ne tai magana da cewa haba dai ya kamata ki tauayawa yarinyar nan kin dai yi fadan nan bata tankaki ba baki bari hakana.
Ta koma kan mama kuma wai ai ta san mama bakin ciki take da mijin da yarta tasamu don yafi na yar ta shiyasa take kyashi yar nata.
Mama tai dariya tace kuma dai an ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare .
Tace ai tun yanzu Allah ya baiyyana an sani in bashiba da ita ake zancen da zata saye ya zama nata nan dai baba ya kara shigowa ya raba su fadan.
Yaran suka fita da sanaa su gidan ya koma shiru ina kwance a dakin ummi na sai ga kanina ya dawo daga kasuwa tare da sakon dana bashi ya sayo min idan zai dawo gida.
Ina waje ina aikin miyan danyen kifi ne sai ganyen zogale na gyara ban hada ba yar wurin mama da ta dawo talla nace ta hada muna nabata kayan hadin ta gyara muna ta raba taba kowa nasa.
Na gama na shiga daki na dibarwa kowa miyan na aika masu dashi sai Inna tace a dawo min dashi.
Yaya Sani yana gida lokacin yace mata saboda may za a mayar mata ya ansa hannun yaron da na aika dashi yana ma uwar nasiha.
Shiru shiru kowa ya dawo sai yar wurin ta babban da ake shirin yiwa aure ne bata shigo ba .
Ina jin mama na tambayan ta har yanzu Saadatu bata shigo bane tace kila ta tsaya amsan kudin ta ne.
Har magariba shiru bata dawo ba nan hankalin uwar ya tashi ta yafa ta fita bata gane ta ba.
Can sai gata ta dawo tana fadin ban san ida yarinyar nan ta shiga ba na duba har layin da suke aje sana ar su ban ganta ba.
Shiru shiru an baza yara ko ina ba a gane taba nace wa ummi na bari na fita in duba ko Allah zai sa a dace.
Tace dani ki zamawa agun uwar su indai wanan matar ce barta inda kika ganta nace wa ummi aini ba don ta zani ba.
Don yar uwata ne da baba don naga hankalin shi ya tashi sosai tace sai na dawo .
Har goma da wani abu na dare muna yawon bidan ta babu labarin ta hankalin gidan mu duk ya tashi.
Muna tsaye kofan gida cirko cirko da wasu yan uguwan mu cikin zulumin ina ta shiga baban mu hankalin shi duk ya tashi na bada shawaran aje gun yan sanda a sanar dasu.
Baba da yaya sani suka nufi wurin yan sanda da daren nan suka sanar dasu abin da ake ciki har daya da wani abu na dare dole muka hakkura muka shiga gida hankali tashe.
A cikin gidan ma ba kwantawa mukayi don babu mai hankalin kwanciya sai yara kanana kawai sukai barci.
Dole baba ya hakkura suka shigo gida bayan duk an bincika gidan yan uwa da abokan arziki ba a samay ta nan ba.
Wani irin ihu da kururuwa Inna tasa da daren nan tabamu tausayi muka koma bata hakkuri amma ina bata ko sauraren mu.
Can wuraren biyu da rabi na dare mota ya tsaya kofan gidan mu da sauri baba ya bude dakin shi shi da su yaya sani suka fita don ganin ko nan ne motar ta tsaya.
Kafin sukai ma har an fara dokan kofan gidan namu da sauri baba ya bude tare da tabayan ko waye ?
Suka ce yan sandane ya bude kofan suka fice nan muka fara bude kofunan dakunan mu muna fitowa don jin may ke faruwa yan sanda gidan na mu da dare haka.
Sun ja baba gefe suna mashi bayani muna tsaye cirko cirko cikin jimay abinda ke shirin faruwa Inna baba ya kira inda suka karasa bakin motan muna biye dasu a bayan su.
Wani irin ihu Inna ta saka duk sai da muka firgice mun zaci ko gawan Saadatu inna tagani a motan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button