BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

????????????????7️⃣

YAR UWA KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA DON BAA YAFE BA ONLINE NOVEL NE NA KUDI,

Yaya Sani bai da karfin da zaitare baba ya hana ai bukin nan gida ya cika da yan buki yan uwan ummi suzo sun mata kara na rufin asiri yadda ya kamata don kowa bai tsanmaci hakan ba.
An daura aure bayan sallah azahar duk masu cewa basu san angon ba sun san shi ranan.
Kowa sai albarkacin bakin sa yake fadi walima akai mun na sauka shine zance event din da akayi kawai.
Nan gidan mu na kwana acewan su washe gari run da safe zamu kama hanya zuwa ida suke.
Hakan akayi washe gari muka kama hanya bisa rakiyan mama da mama lami su kadai zaa tafi da su sai so da suka zo wurin daurin aure daga can.
Sai dare muka shiga garin don haka bazan iya cewa ga yadda garin yake ba don da dare muka shiga.
Gidan gwagona muka fara tsayawa nai mamakon ganin gidan da suke zaune ciki ana cewa suna lagas sai mitum ya dauka a cikin wani daulan duniya suke da zama ashe abin ba haka yake ba.
Dan gidane tsohon gina suke zaune ciki mai dakuna hudu gidan duk ya gage saboda tsufa.
Ashe sana, a take sosai irin na arewa irin su kamu, hura kunu mai zafi da kosai da kayan amfamin na arewa da sauran tarkace da matan hausawa za su bukata.
Kazab tan gidan kawai ya ishi mutum ya raina masu mama lami tace cikin rada lagas din kega in kaji ance mutum na kudu sai ka dauka wani dadin duniya yake can ciki.
Washe gari aka kaimu gidan da zamu zauna shi wanan gidan ba laifi don gida ne dan matsakaici dashi da daki biyu da falo ya dan sha kayan zamani an zuba ya kara haska wurin .
Muka kebe ni da mama lami tana bani shawara da cewa kin safiya ga komai a gidan mun sama don haka yan may zakiyi da su.
Nace mama ki koma dasu kawai ba abin da zan yi da sunan ni.
Tace a, a ba haka za a yi ba zan raba biyu in baki rabi ki boye in kin san gari sai ki samu dan sana a kinayi kin dai ga sarakuwa taki ita ma ba zaune take ba nema take yi.
Don yanzu bida na kai yafi komai dadi ina kin iya kitso da sannu sai ki fara dan yi sai kuma dan abin da kika ga yana karbuwa anan din.
Mama lami bata boye ma su mama yadda mukayi ba sai mama ta bada shawaran cewa ai dabaran ba ma gwogo na wani abu ace in samu sanaa na rike.
Kashi daya a bani a hannu na sauran a koma dashi gida da kudin dari biyu ne da hamsin da dan kai.
Duk da an kawoni da kayan abinci mai dan dama sai sukace mu dauka muyi amfani dashi sun kara jamin kunne a kan zaman aure mukai sallama dasu akan washe gari zasu tafi don baba yace kada su wuce kwana biyu a can.
Aka barina ni daya a gidan a garin da ban san kowa ba shiru banga shigowan shi ba gidan har bar ci ya dauke ni.
A tsorace nake sai haushin karnuka dake tashi unguwan da karan motoci jefi jefi.
Dayan dakin dake bude na shiga na rufe kaina a ciki har barci ya fara dauka na naji ana bugun gidan da karfi.
Tsoro ya kami sai da naji yana antaya min zagi na taso a tsorace daidai lokacin da aka turo kofan da karfi dama ba a rufe kofan yake ba .
Yasha yayi tatil dashi sai rangaji yake yi a tsakiyan falon na rakube gefe daya ina kallon ikon Allah yau ni safiyane a gaban dan giya.
Magana yake son yi amma layi ya hana maganan fita ya kwasa da tangadi ya shige daki da kyat ya iya bude kofan.
Shiru shiru banji ya fito ba na tashi na dan leka dakin da ya shiga kwance yake rub da ciki har takalman shi yana nasari da karfi.
Na sauke ajiyan zuciya na juya zuwa kofan na rufe da key na kashe wutan falon na dawo na takure a wuri daya a falon.
Inata tunanen wani irin zama zamuyi dashi a gidan haka a cikin maye duk jikin shi ya baci farin kayan dake jikinshi na jeans da farar tieshirt duk sun baci da laka.
Nasan yasha faduwa ba iyaka a hanya ne yafi a kirga kafin ya iso gidan cikin maye.
Washe gari da asuba na tashi ina jin kiran sallah can nesa da mu yana tashi don haka nasan asuba yayi ke nan.
Na idar da sallah gabana sai faduwa yake yi don far gaba da tsoron shi don ban san mene zai wakana ba in mun hadu.
Na mike da kyat na fito falo na fara gyan wurin koba a fada ba kin san may zai tashi gida akan warin taba.
Ina tunanen may zan girka na shiga kitchen tsaye nayi ina kallon komai a hankali don komai akwai a kitchen din na fanin girki.
Dabara ya fado min na nagirka abu maidan ruwa ruwa tun da safiya ne yanzu.
Nan na zage na dora faten dan kali da turawa sai kunun custad dana gani na dama har na gama babu motsin shi.
Na kara gyara ko ina na shiga dayan dakin da na mayar nawa wanda babu komai sai dan gado da katifa sai yan kayana dake a gefe daya.
Na gama zan fito na debi abincin da na girkana muka gwabza karo dashi zai shiga kitchien din shima.
Ya sauya kayan jikin shi zuwa dogon jellabiya mara hannu hannushi rike da taban da ta kusa kare waba.
A tsorace naja baya kadan na rabe tare da dan tsugun nawa nace dashi ina kwana.
Kallona kawai yayi ba tare da ya amsa min ba yana zukan taban shi wanda warin shi ya banbanta da wanda na sani.
Na raba shi na wuce zuwa falon sai naji yace uban wa yace ki rufe min kofa daren jiya dana fita.
Kallon shi na dan yi nace uban wa ya rufe ma kofan har ka bude ka shigo din in an rufe ne.
Ya dauki kallon na daga sama har kasa gaba daya na rufe jikina cikin hijjabi babba har kasa.
Yace dube ki yar iska kucakan baza sai iya bakar magawa wa babba zanyi maganin ki gidan nan.
Zanyi magana kenan aka buga kofa gidan har sau biyu ya nufi kofan yana fadin who’s on the door tare da bude kofan kadan.
Lokacin na samu daman shigewa da abincin dake hannu na daki ashe kanin shi ne ya kawo muna abin karyawa daga wurin gwago.
Kiran da yake min ne nasan cewa shine ya shigo gidan ina daki na karba mashi na fito saye da hijjab dina ina gaida shi cikin ladabi naci yaya sa,adu ina kwana.
Da fara,a a fuskan shi ya amsa min tare ta zolayana na wasan tobasai yana cewa yau ga bakauya a lagos.
Murmushi nayi ina jin kunyan mayar mashi da mashi da magana.
Shiko gogan ya zauna ya harde kafa har ya kara kunna taba yana zuka a hankali sai naga annuri dan uwan yarage fara a a fuskan shi.
Da harshen turanci yake ce mashi baidace yana sha a cikin gida ba haka ko banza yaga ni karamar yarinya ce fa.
Mind your business please, don’t boader me, is my house ina da right din abin da nake so in bata so ta fita waje.
Sai ya kada kanshi yace ni zan tafi dama mummy ne tace na kawo maku breakfast nace ai muna godiya wurin gwago amma dan tsaya in zuba maka abinci mana.
Baiki ba yake cewa tou har amarya ta fara girki ashe sai ya mike yana cewa dan uwa ai dole taga kayan banza mana.
Uhmmm uhmmm naji dan uwan yace dashi da yake fadan haka ya shige yana ce ma kanin zan dan watsa ruwa ni.
Shigewan shi na kawo mama yaya saadu abincin yace tun banci ba kamshi ya buge ni da alama amaryan namu ta iya girki.
Dan murmushi nayi kawai na juya zan tafi yace ji mana sai na dawo na zauna a kujeran dake dan nisa dashi.
Ina wasa dan yatsun hannu na a hankali yace Safiya nasan cewa ba, a kyauta maki ba don baki san ko waye Ahmed ba kosu kan su iyayyen namu basu sani ba ne.
Nai dan murmushi nace na sani yaya saadu yace kin sani fa nace eh don shi ya fada min komai kuma gashi ina gani a zahiri.
Ya ce Allah sarki safiya kiyi hakkuri karki biye mashi ku zauna lafiya duk abinda yake yi ki barshi da Allah tsakanin shi ne da mahaliccen mu.
Ke dai abinda kawai zan fada maki shi kiji ki ki jini dan ko ita mahaifiyar tamu sai hakkuri don son da take mashi yayi yawa har yakai bata iya tsayawa tai masa fada.
Don haka kar ma kice zaki dinga kai kara wurin ta don bata so, wanan zai iya kawo tsana a tsakanin ku.
Nace nagode yaya saadu yace zan dan rika lekoki jefi jefi ina duban lafiyan ki kinji ko kedai ki kula da hakkinshi da ya rataya a wuyan ki.
Godiya na kara yi mai ya mike bayan ya gama cin abincin ya tafi ya barni a cike da tunane a raina.
Ina zau ne a dakin ni daya sai gashi ya fado min kwatsan a dakin yana faman kale kalen dakin kamar bakon shi.
Hijjabi na dake gefe daya namika hannuna na dauko yace kada ki sama ki saka wanan tsunman a jiki ki yar kauye kawai.
Sai ya ja tsuki gefen gadon da na ke zaune ya samu ya zauna kadan yana may bin dakin da kallo har lokacin.
Kwata kwata na kasa sakewa a dakin don ban taba zama da namiji hana ba a rayuwana.
Sai naji yace ke baki iya gaisuwa bane ko a gidan ku ba a gaisuwa safe ne nace ai da zun na gaishe ka a falo.
Sai naji yace may kuke magana a kai da Saadu naji ya dade bai tafi ba nace abinci ya ke ci.
Ido ya kafa min bai yi magana ba na wani lokaci saidai bina da yaya da ido yana mun kallon kurulla do bai taba ganina haka babu hijjab ba sai yau.
Yace koma may ye shiya sani nida gidana ba wanda ya isa ya hanani abin da nake son yi don kawai wani yaji dadi.
Na dukar da kaina kasa idanuwa na suka kawo ruwa ya mike yana cewa common abincin ma ba a koya maki yadda zaki ba mutum shi ba.
Ya fice na sauke ajiyan zuciya a hankali tare da mikewa nabi baya shi ya zauna wurin cin abincin da aka tanadar a gidan.
Abincin da gwago ta aiko na fara budewa sai naga kosai ne da kunu mai zafi yace rufe shi wanda kika girka zaki bani nasan girki ba wani dadi sai maneji kawai.
Shi na zuba mashi na juya na dauko mashi ruwa ga kwalabe nan barkatai a cikin fridge din wanda ban san kasu ba .
Kafin wani lokaci har ya tashi da abincin a binka da mashayi dama cikin na rurin neman abin da yaci duk ya cin ye duka.
Na kwashe kayan a raina nace ka kaishi in dai gulma ne abincin da yace ba dadi gashi ya lashe duka bai bar komai a kwanon ba.
Don gatse nace ko in karo ma ne?
Ciki daka tsawa yace dani don Allah ban wuri kin ce ko dadi abincin yayi ne kawai dai don ba abin da zan ci ne shiya sa.
Kayan na kwashe na wanke na koma daki na dan kwanta do in huta saboda gajiya a jikina.
Na dan kwanta sai barci ya dauke ni ban falka ba sai wani lokaci can a cikin barci nake jin kida na tashi a gidan.
Na bude idanuwa da kyat kallon lokaci nayi idan ba ai sallah ba naga lokaci da saura don haka nace barin dan samu abin da naci don wanda na diba da safe ban ci ba sabo zuwan yaya saadu yazo gidan.
Na fito falo a zatona ya fitane yabar gidan na tashi kwatsan sai na gan shi kwace rigingine saman three seater dagashi sai gajeren wando yana busa taba sigari yana busa hayaki cike da yanga da gwanewa.
Tsoro da firgici ne suka dira min a zuciyana don ban taba ganin namiji a haka ba da sauri na juya zan koma daki naji yace ke bani son shashanci fa.
Nace may nayi kuma ?
Ya dago ya dan harareni ya koma ya kwanta yana cewa may kike nufi ne nufin ki ni zan dafa muna abinci da kika shiga daki kika kwanta.
Kallon wurin da kulla yake nayi sai naga alaman an cinye abincin nace ba akwai abinci ba a kulla.
Ba surutu na tsai da ke ki min ba abinci na ce ki dafa muna, ban tsaya magana ba na wuce zuwa kitchien din.
Tsaye nayi ina tunane yadda ya dora abincin nan shi kadai a cikin shi kuma wai yana neman kari.
Aiki nakeyi amma karan kidan da yasaka ya damay ni gashi babu hali nace ya dan rage ya sauke min kwandon balai a kaina.
Sai da na hada komai na fito zuwa sallah don lokaci yayi na a zahar na shiga bandaki na dauro alwala nafito na tayar da sallah.
Na koma kitchean di bayan na idar na karasa aiki na daya rage min kafin wani lokaci na hada abinci ko na aje mashi a falo nai shigewa na ciki.
Ina gama ci sai gashi cikin shirin shi do lokacin karfe biyar na yamma ya kusayi ko gabana ban da bugawa ba abin da yake yi.
Naji yace abincin fa nace dashi an gama ya dan harare ni tare da fadin ni kenan zan zubawa kai na ko.
Mikewa nayi nabi bayan shi zuwa falon yana zaune na zuzuba mai komai harda gaiyya nayi wurin zubawan amma duk haka sai da ya lasheshe kaf.
Ya mike ya dan shiga daki zuwa can ya fito ina jin lokacin da ya fita ya bar gidan.
Fitan shi gidan yasa ni sauke ajiyan zuciya namile nafito na fara dan gyaran gidan na murda kofan dakin shi na jita a kulle nace kai ka sani.
Naga komai na dawo falo na zauna ga tv amma inajin tsoron kunnawa yazo yace wayace in taba mai kaya.
Kewan gida ya dawo min a rai na zauna ina tunane ina kukan rashin yan uwana da nayi kusa dani.
Na saba a gidan mu in gari ya waye hayaniya kawai ya isheka tun safe har dare ihun yara ne zai tare ka a gidan.
Gashi yanzu nazo nan garin da bansan kowa ba ina zaman kadaici duk da unguwa guda muke dasu gwago na sin amma har dare yayi babu wanda ya sake zuwa wurina bayan yaya saad duk da kuwa tana da yara yan mata zasu girmay ni ga shekaru.
Ko da yake nasan wanan sana, a da takeyi bazai basu lokacin samun zuwa yawo ba ko wani lokaci.
In gari ya waye tun karfe hudu idan ta tashi bata da lokacin komawa kuma yi wanan sauke wancen har dare .
Jama, a sai shige da fice suke a gidan wanda akasarin su hausawa mazauna lagos da ke zuwa sayen kayan iri na arewa da babu shi a can.
Yaran ta mata ko wace nada aikin da zatayi nata cikin sana,a da take suna taimaka wa uwarsu dashi.
Suma mazan kakani ba a barsu a baya ba wurin bada nasu taimakon in ba haka ba yaro ya gane kuren sa ta hana mai kudi.
Yau ma kamar jiya bai dawo ba ina jin barci na ja kofan dakin da nake ciki na rufe kwantawa nayi na makure a wuri daya cikin tsoro.
Karfe biyu saura naji ya dawo gidan a cikin mayen shi da yasaba ina jin shi yana ta surutain shi da banke banken kaya ban dai fito ba balle.
Can nabar jin motsi haka yasani n yayi barci kenan Allah ya kyauta nace tare da gyara kwanciyana dakyau sai dai babu barcin kwarai gare ni.
Da asuba na fito in yi gyaran falo sai ganin shi nayi tirim kwace tsakiyan falon yayi amai da fitsari ya bata wurin dashi.
Take idanuwa na suka kawo hawaye nasihan da akai min ne yazo min a rai a hankali na juya zuwa ciki na dauko abin kwashewa na fara gyara wurin da ya bata nai nisa da gyara motsina ya tayar dashi.
Daga barcin naga ya mike kata kata zuwa ciki nan naji dadin tsabtace wurin da kyau ina yi ina kuka da addua a cikin bakina hawaye nata zuba min.
Nagama na shiga na dora girki abin da zamuci don nasan da ya tashi abinci zai nema in banyi kuma iyayyena su sha zagi.
Har nayi na gama ban ji motsin shi ba na shige nai wanka na fito bayan na gama gyaran jikina na fito do in debi abinci in ci ga dai abincin na diba sai na tasa shi a gaba na kasa cin koda cibi daya ne.
Nai zurfi ga tunane najiyo motsin shi daga dakin shi lokacin har karfe takwas da rabi saura na safe rana ya soma fitowa a gurguje ya fito yana sauri.
Ina kwana nai mashi ya amsa a dakile kamar wanda baya son amsawa bani abinci na yace dani ya nufi wurin cin abincin kai tsaye a ranan nasan wai ashe yana aiki ya makara saboda ya bugu a daren jiya.
Nidai na zuba mai na koma daki yana ci ya fice a gidan ban sake jin duriyan shiba kuma har rana ina zaune ni kadai a gidan nace barin leka waje inga yanayin uguwan.
Uguwa ne irin mai jamma, a din nan da yawa kowa na harkan gaban shi ba ruwan wani da wani kowa tashi ta fisshe shi din nan.
Na dan duba yanayin na koma ciki tare da jan kofa na rufe kwantawa nayi sai barci ban tashi ba sai biyu da rabi.
Na tashi ina salati don makaran da nayi wurin yin sallah na dade zaune ina adduoi na neman tsari da mafita ga Allah.
Na tashi nafito duk da akwai dan sauran abinci amma sai da na girka wani na rufe.
Don ina gudun ya dawo ya hauni da masifan don ni yanzu tsoranshi nake ji sosai gani nake zai zo ya samay ni da duka idan ya je ya shawo.
Na gyara gida na dawo falo na zauna can dai nace barin kuna tv in kallo ina kunnawa yana a wani tasha da aka badala iskancin filin Allah maza da mata.
Da sauri na kashe karshe ma a mike daga falon na koma daki na zauna ba wani aiki a gareni sai na tunane.
Sati na guda a kidan muna wanan zaman in ya fita run safe baya dawo gida sai dara ya raba idan zai shigo kuma a buge zai dawo gidan.
Tun ina tsoro har na fara sakin jikin na na saba da zaman kadaci ba mashigowa nima bana zuwa wurin kowa.
Duk da zaman da muke yi dashi tun ranan da yai mai da fitsari nakwashe ta rage zagina da tattara sai dai ba sakin fuska ko kadan a wurin shi.
Nima dai hakan ne a wurina daga gaisuwan safe zan ja bakina na tsuka sai kuma wata goben in Allah ya kamu lafiya.
Yau ma zai fita na gyara gidan nake rokon shi da ya kunna min tv zaman kadaici ya isheni har zai yi magana komay ya tuna sai da ya gama jan rai ya hada ya nuna min yadda zanyi.
Ya fita ina zaune ko ina zaune ni daya kallo ya dauke min hankali wani indiya ake yi mai ban tausayi kofa naji ana bugawa.
Nai mamakin jin bugun kofa a lokacin na tashi na saurara kofan ake bugu a hankali na bude kofan.
Sisters din shine su biyu tsaye a kofan na tare su da mutunci sai naga suna amsawa dakyat suna wani yamutse fuska.
Nace sai yau anty ?
Naji sadiya tace min tauuu,
Na sake cewa ina su gwago suna lafiya ?
Ta amsa da lafiya kalau.
Nace dasu ku zauna mana.
Sai naga sun kalli junna su kamar ba zasu zauna ba sai dai suka zauna din kitchean na wuce na fito da cups da goran ruwa na kawo masu.
Ita dai habiban ko magana bata son yimin nace dasu bissimillah ga ruwa sai naga sun kalli juna sun tabe fuska .
Sadiyan tace bar ruwanki dama mu hanya ya biyu damu nan muka ce bari mu biyu magani ko yaya yana gida mu gaisheshi.
Nace yana wurin aiki sai daren ya shigowa habiban tace ke sadiya mu tafi don Allah hakan haka auka fice nabisu da idanuwa cike da mamaki yan uwan nawa kenan kuma yan uwan miji na.
Da wani zanji a raina wai da nashi ko da nasu tsiyar da naga sun fara nuna min ina ce wurin su zan ji dadi ashe abin ba hakana yake ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button