BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/29/20, 11:42 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,

????????6️⃣7️⃣????????

Ranan duk da gajiya ban samu hutawa da amsan wayan daga yan uwa da abokan arziki ba masu bugowa su na min barka da arziki.
Sai da dare samira suka bar gidan amma yar uwarta ta zauna a wurina zata taya mummy aikin jego nima naji dadin zaman nata.
Nafito bayi don yin tsarki dare saboda zan kwata a lokacin ina tsaye ina shiryawa wayana yayi kara mummy ke fadin wa kuma yakiraki yanzu kina shirin kwanciya ?
Daukan wayan nayi amma sai gabana ya fadi mummy tana ganin yadda na firgita da ganin mai kira na din a lokacin.
Waye mummy ta tambaya cikin son ji nace mata anty lagos ne bata san ina da ciki ba nassan taji zancen haihuwan ne take kirana anty tace dauka mana sai ki fada mata kin dauka ta sani ne ai.
Kiran ya katse sai ni na kirata kira biyu gana uku ta dauka nace mata anty ina bayi ne da kika kira tace yanzu nake jin wai kin haihu sulaiman yakira yana fada min.
Nace eh anty kin kyauta tace min lalai Safiya yanzu nasan yadda kika dauke ni har kiyi ciki ban sani ba sai dai inji haihuwa kawai daga sama.
Ko shekaran jiya fa kin kira ni mun gaisa dake amma baki fada min cikin ki ya tsufa ba haka sai dai inji haihuwa kawai.
Nace anty kiyi hakkuri na bansan yadda zan fada maki bane da baki na na dauka ai ya fada makine da dadewa.
Ya fada min may shine zai fada min ko ke to bari kiji kada kiyi tsamanin kiyi min kan ki kikayiwa sai ta kashe wayan kit.
Wayan nabi da kallon mamaki a hannuwan kamar ita ke gabana sai kuma na sake wani murmushi kawai.
Don nasan inda maganan ta ya dosa alokacin bai wuce zancen kudi ba ne don ko gabanin sallah na tura mata da kudi ta account din da ta turo min.
Mummy takatse da tambayan cewa may take nufi da kinyi wa kanki ko da ban san ta ba nadai san a yanzu babu abinda zata gwada maki na rayuwan duniya.
Tana miko min tea mai kauri take fadin haka nace mummy anty tayi abinda bazan iya mantawa da ita ba rayuwana .
Ta katseni da fadin don kaiwa mutun alheri ba saboda Allah kayi sai kuma mutum ya zama bawan ka saboda Allah haka Allah yace ayi taimako duniya?
Tea din na karba na shaye sai ga zufa na karyowa a jikina na aje cup din ina shirin kwanciya yaron mummy ta miko min tana fadin taba yaron ga tunda yazo duniya baiji dumin uwar shi ba.
Karban yaron nayi na rugumay shi a jikina kamar wani babba da yasan may ake nufi da haka sai naji ya sauke ajiyan zuciya a hankali a jikina.
A hankali hawaye ke zubuwa daga idanuwa na wanda ban san ina yin su ba alokacin tausayin kan mu dana yaron ne ya kamani a lokaci guda.
Mummy tace a a yaya haka kuma daga karban yaro ki kama hawaye haka don Allah kibar irin wanan dabiar mana ta mika hannu ta karbi yaron daga hannu na.
Har lokacin ban daina kuka ba wiwi badai ce min komai ba da kukan ya isheta sai kuma ta koma lalashi na tana fadin.
Haba Safiya ke da zakiwa Allah godiya sai kuma ki gode mai da kuka kamar baki gode mai da kyautar da yayi maki ba.
Tadai samu nayi shiru tare da nadewa saman godo ni kadai nasan abinda ke damun zuciyana a lokacin wanda ita mummy ba ta sani ba.
A haka barci mai nauyi ya dauke ni sai da asuba naji motsin mummy ta tashi zuwa ban dakin ta wanda acan take kewayawa bata shiga nawa har wankan yaron acan take yi mashi.
Yau da yake ikilima yar ta na gidan sai ta dan jima bata dawo ba haka yasa na samu daman komawa batcin dake idona.
Sai wani lokaci naji tana ta dani wai in tashi inyi wanka tun rana bai yiba sosai haka na tashi na shiga na gasa jikina a ban dakin.
Na fito na shirya cikin wasu super masu launi ja da fari dinkin shi mai daukan ido don an tsara shi dakyau da fasahan teloli na zamani.
Wayan Uncle ne ya shigo a lokacin da na gama saka sutura a jikina mun gaisa yake tambayana babu matsakan komai a tare dani ko ?
Nace lafiya kalau muke Uncle sai dai kewan ka daya cika muna zuciya baka gidan gidan babu dadi yace muyi hakkuri zamu ganshi nan da sati uku mai zuwa.
Nace haba uncle har sati uku baka zo kaga kyautan da ubagiji yayi maka ba yace karki damu ina nan ina gode ma Allah ki san a gaban shi nake ma yanzu don ina dawfin bankwana ne yanzu haka ina fitowa daga cikin kaaba ne.
Allah ya tsare nayi mashi yake tambayana mummy nace tana dakin ta da baby suna karyawa ya sake tambaya idan muna da matsala in fadawa yaya saadu nace uncle bamu da matsakan komai a tare damu.
Mukayi sallama naci gaba da shirina zuciyata cike da kewar miji na da bai kusa damu a lokaxin da muke bukatan shi a tare damu din.
Goma da rabi ma,iakatan wurin su yaya saadu suka shigo min barka bisa jagorancin yaya saadu din sun kai su goma duk kan su sun sha corth a jikin su bakake.
Wanda nake gani haka yanayin shigar wurin aikin nasu yake a falo suka girshe ni zaune dasu mummy ba hijjab a jikina kafin a dauko min hajjib duk sun kare min kallon da yaba hallitana a zukatan su.
Yaron mummy ta dauko masu nan suka shiga yaba kyawon yaron wasu na fadin wai ni ya biyo wasu kuma suna fadin ogan su yaron ya biyo.
Basu dade ba suka aje muna kyatutukan da suka zo muna dashi sukayi muna sallama suka tafi yaya saadu ne yadan tsaya fada muna samira na tafe ta tsaya gyaran gida ne yanzu zai koma ya dauko ta.
Basu zo tare ba sai gata wai wani driver yasa ya dauko ta shi ya shiga kasuwa muna zaune sai hira ake faman zubawa irin na mata idan an hadu.
Sai ga matan maikatan su Uncle sun shi su da yawa muka zauna ana gaisawa wanda duk basu sanni ba sai a wanan lokacin.
Wata daga cikin su ce ke tambayan waye mai haihuwan sai samira ta nuna na turancin yan Nigeari suka fara yi suna cewa ayyah.
Very young Lady nan hira ya kaure a tsakanin su suma dai yaba kyawon jaririn suke ta faman yi zasu tafi suka aje muna kyautan da suka zo muna dashi.
Sun fice muna masu godiya naji Samira tace shegu muna fukai kawai ina ruwansu da kurciyan ki dama sun zata ke tsohuwace ko may ?
Na da sauri nace kai Samira daga abin arziki sai zagi haka kuma tace ke baki san komai ba ina wanan maidan jan gyale wai ita mijin ki take mutuwar so kamar ta mutu.
Nace wa uncle tace shifa wallahi kyale wahalaliya wai kuma a wurin dan uwan ki take kamun kafa wai ya shawo mata kan shi.
Dariya nayi nace ashe aiki ja yagan ta kuwa sai kuma ita bakar nan mai kama da zubin arnan daji itace ta lakewa yayan ki sai da na kirata ranan naci mata mutunci sosai.
Dariya ta bamu dukan mu mummy tace ashe kina da aiki wanan zamanin idan kince zaki dinga kiran yan mata a wayan miji kina zagin su.
Don haka zasu samu damar shige mai su nuna ai su na kwarai ne sai tafiya yayi nisa su fitar da halin su na boye.
Nace ni yanzu mata sun baci mummy tace bari ke dai mace fa yanzu ba abin kunya bane ta tunkari na miji da kalman son shi takeyi .
Nace ni mummy ba abinda keci mun rai da matan yanzu sai kiga mace na tafi taga mota tafe ta kasa kawar da idon ta ga mai motar.
Har ba da matan aure dabi an su ne yanzu bin namiji da kallo cikin mota ba birnin ba ba kauye ba.
Samira tace ai sai kiyi ai wanan yanzu ya zama ruwan dare a ko ina mata da sunji rurin mota basu da kwanciyan hankali sai mai motar ya wuce su.
Yaya Saadu ne ya shigo gidan yana neman Nura akace tana kitchen kiranta ikilima tayi sai gata da saurin ta ta fito yake ce mata tazo ta duba kayan kitchen abinda babu ta fadi a sawo zata koma kitchen din yace mata a a tafito suje waje suka fice tare dashi samira ta tashi ta bisu wajen.
Dariya muka kwashe mata dashi tace kuka ga abin dariya tsaron kaya yafi cigiyan shi ai nace ke dai baayi niyya ba mai zaki iya hanawa samira.
Mummy tace rabu da mahaukaciya sun dade a waje sai gasu suna shigowa da kayan abinci cikin gidan katon katon komai an sawo.
Zai fita nace haba dan uwa zauna na mana kaci abinci nasan wanan zirga zirgan da kakeyi baka tsaya kaci wani abu ba.
Mummy tace ga matar shi sai kishin hauka takeyi bata san ta tambayi lafiyan mijin ta ba.
Tace ai nasan ko nayi mai tayi bai zama yaci yana wanan zirga zigan haka mummy tace haka ake son aminin kwarai yayi maka tsaye da gidan ka idan bukatan haka ya taso bai kusa.
Abincin yaci yana ci muna hira yake fada min sunyi waya da baba yaya sani ya fada mashi kila jirgi na biyu zasu biyu don da shi suka tashi.
Mummy tace kafin su dawo ai mu mun sha bukin mu sai dai suji labari a bakin mu .
Wai yaushe shi maigidan zai dawo take tambayan yaya saadun yace basu yi waya ba don ko yabar saudiya Dubai zai tafi daga can sai dai ranan da muka gane shi.
Banji dadi ba a raina har hakan ya baiyana a fuskana yaya saadu ne yake mun sheri dan murmushi nayi kawai ban iya bashi amsa ba.
Jego ya karbe ni sai dai ina makin yadda nono na basuyi min ambaliyan ruwa ba sai na fahinci kila maganin da likita ya bani ne ya kawo hakan.
Suna saura kwana ukku muna daki da dare mu uku muna shirin kwanciya ikilima tana muna hira a dakin mu mukaji bell din gidan na kuka alaman ana sallama ke nan.
Mummy ce ta fita zuwa duba ko waye goye da yaron a bayan ta don takan goyashi kafin mu kwata don tace idan yaro yasha baya kafin ya kwanta yafi dadewa yana barci da dare.
Shiru bata dawo dakin ba yasa ikilima fita ta dubo ta sai gata ta dawo tana fadin Safiya maigidan ki ne fa ya dawo.
Gadunan dasu yaya saadu a falo ana shigo da kaya cikin gida wani iri naji gaba na ya amsa min mummy ta dawo ta sauke yaron dake bayan ta tare da kiran ikilima suka fita.
Ya shigo dakin a daidai lokacin da nake aje kofin tea saman dan drower dake gefe na dago kai nayi ina kallon shi.
Yaja yayi tsaye daga kofan dakin yana kare muna kallon cikin shaawa daga nesa tasowa nayi zuwa gare shi .
Take ya ware min hannuwan shi na shige ciki ya mayar da hanayen shi ya rungumay ni tare da matse ni cikin jikin shi.
Ajiyan zuciya kowan mu ke saukewa a lokacin babu abin da nake tunawa sai haihuwan wahalan danayi na farko babu muji babu aike shi.
Allah mai yin yadda yaso ga bayin shi na furta a raina yanzu gani gidan akwai gidan mutunci inda akasan daraja na da kimana ana tarairariyana kamar kwai.
Sake juna mukayi tare da jana zuwa wurin gadon da yaron yake kwance yana barci acikin net din jarirai .
Hannu na ya sake ya duka ya dauko yaron dake ta barcin shi hankali kwance ya rugumay shi a jikin shi.
A hankali bayan yagama mai adduan da yake mai a duka bangarorin jikin shi ya dago yana kallona inda nake zaune a bakin gado na zuba masu ido.
Sannu madam yace tare da sake min murmushi mai ma,anoni da yawa a zuciyar shi nima murmushi nayi mai kamar yadda yake min.
Yace wanan katon baby haka yaya kika iya haihuwan shi a gida nace da taimakon Allah da na nurse Lidia na haife shi uncle.
Zama yayi da yaron a hannun shi yana mai kura mai ido babu ko kiftawa nace uncle shine baka fada muna zaka dawo yau ba mu sani a shirya ma abinci.
Yace aini akoshe nake ganin ku ya kosar dani da komai yanzu ya sake dago kai yace sannu safiya ubangiji ya raya muna wanan yaron yasa mashi albarka a rayuwan shi kin min komai tunda kin haifar min baba na a yau.
Nace sunan Abba ke nan zaici yace ba dole ba Safiya ina matukar son mahaifina shima yana sona amma mutuwa ta raba mu alokacin da muke jin dadin junan mu.
Allah ya gafarta masu na furta yace amin yau ki dawo min da tsohona dana rasa wanda har yau cikin yan uwana babu wanda ya taba min kara yace zai saka sunan shi.
Nace ai gashi Allah ya baka yanzu ka huce haushin hakan yace wallahi na dade ina jiran wanan ranan a raina har da na cire tsaman sumun shi a rayuwa na.
Sai gashi a lokacin da ban taba zato ba ubangiji ya dawo min dashi a rayuwa safiya zan so yaron nan kamar yadda nima mahaifina yaso ni a rayuwan shi ki taimake ni ki tayani sin shi don Allah.
Nace har ma zan fika ni da yake babana kuma sukina ina kewar rashin shi a lokacin da muke bukatan shi a tare damu a lokacin da ya kamata ya kasance dakai yaji dadin haihuwan ka.
Mummy ne ta leko dakin tana fadin Alhaji ga abinci can an hada maka yace mummy sannu da kokari ina jin labarin kokarin da kikewa babana sosai a wurin safiya.
Murmushi mummy tayi tace masha Allah tsohon gida ne ya dawo ashe?
Ya na aje yaron yake cewa baba na ya dawo mummy ku tayani farin cikin samun wanan daman da ubangij yayi min .
Ya aje yaron yana kallona yace zan je in watsa ruwa sai da safe idan Allah ya kai mu don naga kuna shirin barci ne yanzu.
Nace barin taso in hada ma ruwan wanka don ban hada heater ba yace na hutar dake yi zaman ki sai da safe ma hadu ai mummy sun kawar da komai yadda ya dace.
Yana fita mummy ta shigo dakin tana cewa kin ga kyautar ubangiji watau sunan tsoho yaro ci ubangiji ya raya muna shi nace amin mummy.
Nace da alama akwai shakuwa mai tsanani tsakanin shi da mahaifin shi tace ai da ganin yadda yake yi akan yaron kin sani kema.
Yanzu aiki ya samay ki yadda yake ji da yaron nan sai ki taimaka ku bashi kulawa yadda ya dace in kina cire wanan filancin da kike yi yanzu sai ki cire don haka zai iya kawo matsaka a tsakanin ku.
Murmushi nayi ina gyara kwanciya na nace mummy ai naga alama nasan akwai aiki a gabana sosai haka ta kashe wutan dakin muka kwanta asuba ta gari yan uwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button