BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/22/20, 5:53 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , ,

????????6️⃣1️⃣????????

NOVEL DIN NAN NA KUDI NE DON ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BA YAR UWA DON ALLAH ZAI SAKA MIN A KAN KI, , , ,

A hankali kofan ya bude shike gaba ina daga bayan shi cikin fargaban ko wa zai bude kofan a lokacin gabana sai danka yake uku uku.
Muryan Faiza ce naji tana fadin a yaya sannu da zuwa ya amsa mata kamar yadda yake amsa muna a can baya idan muna gaida shi a gidan idan ya shigo.
Fara takawa yayi don shiga gidan na bishi a baya wanda sai lokacin Faiza ta ganni taa sake dan ihu da karfi sai kuma taja bakin ta har da rikewa tace ashe tare kuke cikin washe baki tana nuna farin ciki da gani na a lokacin.
Gaba dayan su har daddy suna falo zaune a lokacin da twins din ta Fati ce kawai bata cikin su jin muryan shi da twins sukayi yasa suka mike gaba dayan su suka nufashi da murnan su.
Suna gani na kuma sai suka barshi suka nufoni tare da fadin anty safiya oyo,yo duk suka fada min a jikina nima rungumo yaran nayi zuwa jikina cikin shaukin junan mu da andade ba a hadu ba.
Daddy ke fadin kar ku karya mummy naku mana wurin murna lokacin shi har ya kai inda suke zaune yana kokarin zama.
Dayar tace anty safiya shine kika gudu kika barmu muna ta kewan ki kin dawo ke nan inji dayar take tambayana cikin kallon fuska na.
Nace na dawo yan biyu ba gani kin ganni ba ba na fadi ina kara rungumay su a jikina cikin jin dadin ganin su da nayi yau.
Mummy ga anty Safiya ta zo suke cewa uwar tasu data mayar da hankalinta ga uncle suna gaisa wa dashi bayan ya zauna.
Tace da yaran naga safiya kuda kuke kewanta sai ku tare ta nidai ba wurina tazo ba sai in wurin ku tazo hakan yasa na karasa gurin ina fadin haba anty kiyi hakkuri mana.
Dariya daddy yayi yace kin ji tun ba a kai ko ina ba ma ta baki hakkuri na karaso ina durkusawa a gaban su tare da gaishe su.
Daddy ya amsa min cikin daddin rai da sakin fuska yace yau yar gidan antyn ta ne gidan namu nayi dariya ina noke kaina a tsakiyan kafafuwa na don kunya.
Na dago kaina cikin kunya ina gaida ita ta amsa min ba wani walwala a fuskan ta da cewa lafiya lau yaya gida.
Uncle ya maiyar da bayan shi a makariyan kujeran da yake zaune yana fadin yau dai ga kaunar ki nan na kawo maki don damuna da take yawan yi akan ki.
Murmushi tayi tace aikuwa ga Safiya na gani a gabana yau ga kuma uncle nidai kaina na duke sai da daddy yace tashi mana ki zauna saman kujera Safiya nace a kunyace daddy nan ma yayi mun ai.
Na kara dukar da kaina kasa nace daddy nan ma yayi min a lokacin ne faiza ta iso wurin dauke da tire da abin sha a sama.
Ta dire a gaban mu tana cewa yau ga amarya a gidan mu anty ta ce ga fa amarya da akai muna rowan buki a gidan tazo
Daddy yace aure yayi kyau dukkan su sai wani sheki suke yi da annuri tace sulaiman ba amma itakan ai auren ma rama ya sakata yi.
Murmushi uncle yayi don yasan gatse tayi min kawai da wata manufa ta fadi maganan ta ya mika hannu ya dauki goran ruwan yana ballewa tare da kafa bakin shi akai bayan ya goge bakin goran da hannun shi.
Ga ruwan nan tace dani cikin rashin fuska a gare ta na dan dago kaina nace da ita na koshi sai dai anjima tace yayi sai ta juya ga uncle din sukaci gaba da magana dash.
Nan su yan biyu suka shiga hira dani ina dan basu amsa a hankali tana kallona ta gefen ido tana mamaki a ranta yadda na juye kamar bani bace a lokaci guda.
Kayan dake jikina kawai ma abin kallo da yadda na tsara kwalliya kamar wata balarabiya dani babu inda nake da mukusa a jikina.
Ya gyara zama tare da fuskantar anty din bayan ya kai duban shi gare ni yaga yadda nake zaune a takure gashi kuma matar gidan sai basar dani takeyi a wurin.
Dan uwan nashi ya fuskanta tare da fadin mu zamu koma yaya dama na kawota ne ta gaishe ku kafin mu tafi da sauri daddy din yace tun yanzu zaku tafi ba a ko gaisa ba.
Ido da ido ya kalli anty din yace matar gidan ce naga bata maraba da zuwan mata na gida so ba zan juri ganin wanan a tsakanin su ba.
Saboda may daddy yace idan bata mara ba daku ai mu da twins muna maraba daku don wurin mu kuka zo.
Yace na dauka abin da ya faru a tsakanin su ya wuce don da nasan har yanzu madam tana rike da ita a zuciyar ta ba zan kawo ta gidan nan ba.
A yadda yayi maganan ya nuna ranshi ys baci ga abinda tayi muna ya juya inda nake zaune yana fadin tare da mikewa tsaya yace tashi mu tafi.
Dago kai nayi ina kallon shi tare da dan marairaicewa nace Uncle kayi hakkuri ka bari a bata hakkuri ta yafe min.
Tare suke hada baki wurin fadin ta yafe maki da kikai mata may zaki ce ta yafe maki inji daddy ya fadi yana mai kura mata ido.
Yadda sukai mata yasa taji nauyi da kunya ta fara kamay kamay tana fadin yanzu may nace ina wanan maganan an wuce shi ko.
Uncle yace cikin girgiza kai madan bayi expecting din haka daga wajen ki ba don kece ki ka nuna mun Safiya a gidan nan duk abinda mukayi mun yi biyayya ne bisa umurnin ki.
Banji dadin yadda haka ya kasance a tsakanin ku ba a sanadiya na na dauka kin fahinci ni kowaye zuwa yanzu ni mutum ne da ban magana biyu a rayuwana.
Don , , , , daddy ne ya katse uncle da fadin ya isa haka please sulaiman dauki matar ka katafi Allah ya tsare Allah ya baku zaman lafiya.
Sulaiman don Allah kuyi hakkuri da kai da Safiya in Allah ya yarda haka ba zai sake faruwa ba ta fadi tana duban sulaiman din.
Daddy ya rausaya kai yana nuna ma uncle kujera ya zauna lokacin ne su twins ke cewa in tashi in zo inga gadon da daddy ya sake masu a dakin su.
Dole na tashi na bisu dakin nasu nan suka samu daman sakewa inda daddy yai mutaukar nuna mata bacin rai ga yadda ta tare ni.
Har yake cewa bata san Allah ne ya rufa mata asiri da anty uwa da Uncle ya yarda da auren diyar anty Uwa da kashinta ya bushe.
Karshe tace amma anan zaka barta sai dare ka dawo daukanta don karkace ban kula maka mata don naga tun yanzu ka nuna min matarka kake so dani.
Dariya suka kwashe yace ba dole ba ai safiya ta yi don yarinyar ce data san kanta wurin komai na rayuwa ya fadi hakane don ta san bada wasa yakeyi mata ba.
Ta mike tana fadin barin rafi wurin Safiyan in barku kar kuma nayi wani laifi ga mai gidan again nan ta mike ta barsu da dan uwan nashi.
Muna daki da yaranta sai gata ta shigo dakin kallon da take min yasa na dukar da kai cikin fargaban abinda zata fada min din.
Sai da ta samu wuri tavzauna take ce min Safiya kin san baki kyauta min ba don kin yaudare da sauri na dago ina kallon ta don jin kalman yaudarar da ta kiramin din.
Tace kin san kun shirya komai da Sulaiman kika boye min hakan sai jin zance buki kawai nayi gun mutane amma ke baki sanar min ba.
Nace anty bansan da auren nan ba ba fada maki tun farko daga zuwa tambaya aka daura muna aure dashi.
Nakiraki kuma in maki bayani baki saurare ni ba a lokacin kin dauki zafi dani, duk yadda na so ki fahince ni kin ki saurararona a lokacin.
Tace ai dole a daura maki aure daga zuwa tambaya tunda kuna matse ku samay shi kada ya kubce maku a hannu.
Naji wani zafi a raina nace haka ne anty don masu son su samay shi a lokacin muna da yawa da yake Allah yayi nice matar ai an daura dani ba shiri.
Kallo na tayi kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru kawai ta murmusa a ranta tace eh lalai kin zama matan manya a yanzu safiya .
Amma a fili sai tace dani yaya zaman ku da yan uwan sulaiman din yake yanzu na gyara zama nace da ita lafiya kalau muke satin da ya wuce ma muna bauchi din mun tafi sallaman su kuma ya kai masu kayan azumi da na sallah.
Da sauri ta kallo ni tace what har sulaiman yayi rabon kayan azumi da sallah banda labari wa ya saka ya dauko mashi kayan da ya raba bana.
Nace yan uwanshi yaba nauyin yin hakan don sune sukayi rabon da muka je acan shiru tayi na dan lokaci sai tace zan ganshi inji yadda akayi hakan ya faru.
Nan dai muka zauna wanda duk hiran namu bugun cikina take yi amma sai in nuna mata ban san komai ba a kai har ya turo yan biyu kirana wai zamu tafi.
Tare muka fito da ita daga dakin take cewa dani kin dai san namiji ba ai mashi farar daya don haka duk abinda kike samu sai ki turo ai maki tanadin shi yafi.
Nace to anty insha Allah zan dinga turowa sai dai na fahinci uncle ba irin mazan dake ba mace kudi bane haka na amma yana kashe min kudi ga duk abinda nake so.
Tace may ye baki dashi yanzu dole ne kisan yadda zaki juyashi ya dinga sakar maki kudi kina turowa nan ana maki tanadin su.
Ina gyara gyale nace insha Allahu anty duk abinda nake samu zan dinga turowa gare ki da zaran na samu tace koke fa haka yasa muka fito muna dariya sau mazan suka dauka mun shirya a tsakanin mu ne.
Daddy ne ya nuna ma uncle din mu yace gani ba dama nace ma ai sun fi kusa kaga kamar ba yanzu muka shirya su ba.
Nan dai muka samay su tana kara jaddada min karfa ki manta da sakona nace in sha Allahu anty.
Gaban daddy nazo na durkusa gaban daddy tare da sunkuyar da kaina ina fadin daddy zamu tafi yace ubangiji ya kaiku lafiya ku dawo lafiya safiya ayi ta hakkuri shi zaman aure dan hakkuri ne.
Har waje suka rakomu muka wuce suna daga muna hannu sai da muka bar area din na sauke ajiyan zuciya a fili.
Uncle yace dani yanzu dai hankalin ki ya kwanta kun shirya da anty ki ko nace ai hakan yafi don da ba haka ba bazan taba samun kwanciyar hankali ba a raina.
Amma cikin zuciyana kuma tunanen anty din nake yi ashe dai duk rayuwan mutun sai mutane sun gane halin shi na banza mutum dai dan tara yake bai cika goma ba wallahi.
Nan dai muka isa masaukin mu kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi a lokacin bayan munyi sallah mukaci abinci bamu dade ba muka shiga barci.
Tashin asuba zamuyi don hakane muka kwanta da wuri shiya tadamu mukayi wanka karfe biyar a airport yayi muna mun gama komai kafin shidda muna cikin jirgin da zai daga.
Na dauka zuwa Canada wasa ne ashe ba karamin tafiya bane nan na jinjina ma uncle da bai jin wutan tafiye tafiyen da yake yawan yi ko yaushe sai da muka kwana washe gari muka sauka canada din.
Inda abokin shi yazo ta tare mu wani dan gida madaidaici ya kaimu nikan ban boye kauyancina sai kallon abin mamaki nakeyi a garin. .
Wanka mukayi da sallah sai abincin da mukaci nan muka kwanta ranan duk kwakwan uncle sai da ya barni shima barci yake yi sosai.
Sai wani lokaci muka tashi ko shi zuwan wanan abokin nashi da iyalinshi yasa mu tashi barci don sun kawo muna abinci irin namu na bakaken fata.
Matar shi tana gani na tashiga yaba tana fadin lalai Uncle bakayi ruwan idon banza ba wirin zaben mace haka maikyau ga tsari ga hankali.
Mijin yace na gaya maki ai mutumin nawa ruwan idon shi da dalili ya tsaya yin shi nan dai sukayi muna fatan alheri basu wani dade ba sukayi muna sallama suka tafi.
Kwana biyu uncle baya fita ko ina muna gida acewan shi yanzu ne yake more amatcin shi dariya nayi nace wani amarci ya saura amarya wata shidda a dakin ta kuma.
Yace ai wuyan aiki ba a fara ba don ni so nake kafin mu bar nan din sai kin samo ma hajiya baaba dan jikan da tace tana son dauka nawa.
Daya fara fita ko saida na raina kaina naji dama ya barni a gida ne yafi don ko yaya muna dan hira da zara ko Nuratu mai aikin mu.
Amma nan haka zan wuni sai kallo sai ko kwanciya ban tsinana komai a rayuwa tunda safe in yafita sai dare sosai yake dawowa gidan.
Haka kuma idan gari ya waye zai sa kafa ya fice gidan sai kuma dare kwana zai dawo duk suna wurin harkan kasuwancin su.
A kasan muka fara azumi duk da ba musulmi a kasan sai jefi jefi wani lokaci zai dawo gida da wuri tunda azumi ya fara.
Mukan dan fita idan ya dawo da wuri yadan nuna min garin mu dan yi sayayya mu dawo gida bai kara fita sai kuma gobe.
Ranan ya dawo gida da wuri ya shigo da sallaman shi da gani a gajiye ya shigo gidan don yanayin shi kawai zai nuna hakan.
Kwance nake saman carpet ban ko iya daga kai in mashi sannu da dawo ba a lokacin don tun cikin dare nake jin jiki kuma ga azumi a bakina.
Ya cire takalmanshi akofa kamar yadda mukeyi acan tare da rataye rigar sanyin da ya dora saman kayan jikin shi.
Ya tako har inda nake tare da sunkuyowa gaba yana fadin madam yau lafiya kike kuwa da kyat na iya dago kai na dan dube shi da idanuwa na da sukayi min ja saboda wahala.
Na mayar dakai na kasa ina wani irin numfashin wahala nace da kyat uncle sannu da dawowa.
Kasa yakai zaune a inda nake don ya tabbatar da ba lafiya nake ba a lokacin zama yayi saman carpet din tare da dan tallabo kaina yana fadin may ke damun ki ne haka ?
Na runtse idanuwa tare da cije baki na nace uncle banda lafiya ne tun da dare nake jin zazzabi yana damuna sai kuma amai ya biyo baya bayan fitar ka gidan.
Dan taba jikina ya shiga yi yazo daidai wuyana yaji yadda jikina yayi zafi ya gashe sosai a lokacin yace shine baki kirani ba ana wasa da ciwo ne komai karantar shi akace maki.
Ya ce ki tashi muje asibiti yanzu a duba ki ansan abinda za a baki na cije baki nace uncle bari in ansha ruwa mu tafi don yanzu ina dauke da azumi.
Ya katse ni da cewa wani azumi kina haraswa haka sai ya mike tea mai zafi ya shiga ya hado min ya dawo inda nake yana min sannu ya mikar dani ya matsa min sai da na sha ina runtse idanuwa don ba dadin tea din nakeji ba.
Ina sha yana min sannu da fadin dan kara dai ko kadan ne na cije baki na kara amsar cup din ina kurbawa da gudu na mike zuwa bandaki sai da na amaye shi kaf na samu saida a raina.
Yana tsaye a bayana yana min sannu na dago cikin cije baki ina maida numfashina dakyat ya rungumoni muka dawo falo daki ya shiga ya dauko min hajjab dina na sa.
Sai faman cije baki nake yi haka ya kamani zuwa waje inda muka shiga motar da yake amfani dashi a kasar wani asibiti mukaje.
Nan ya yaki kati inda babu dadewa suka shiga yimin gwaje gwajen su na likitoci tare da yan tambayoyi.
A karshe da result ya fito likitan yayi mashi albishir ina dauke da juna biyu na wata biyu a jikina hakan ya nuna tun a gida nageria nike dauke da cikin a jikina bamu sani ba.
Tun fitowan mu yake faman washe baki shi yana jin wani irin dadi a ranshi yana yi yana dan kamoni tare da fadin Allah ya karba adduan mu dana hajiya baaba.
Ni dai ban iya ce mashi komai ba har muka shigo gida har na haye kujera na kara lafewa kafin ya shigo yakkule ko ina na gidan haka yasa na fahinci bai kara fita ko ina ke nan ranan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button