BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:12 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,

????????5️⃣2️⃣????????

NOVEL DINA NA KUDI NE NA FADA MAKI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL AMANA NE GARE KI IDAN KUMA BAKI BIYA BA KIKA KARANTA ALLAH YA BI MIN HAKKINA A KAN KI DON BAN YAFE MAKI BA

Washe gari malam yayi sakon fita zuwa wani kauye da fulani da mano ma suke rikici akan gona don haka ban samu ganin shi ba ranan sai dare sosai mota ya dawo dasu har kofan gidan shi don haka ba halin in ganshi da daren nan.
Gashi washe gari zan koma don shirin taron bakin da zasu zo min anan kauyen su ummi na sayi kwan zabbi mai yawa da kuma zabbin da ransu wanda zamu gyara masu idan sunzo .
Nono har na rasa inda zan sakowa yana kawo min kyautar kwai da nono tsaraba.
Naje sallama da malam yace Allah sarki Safiya sa ar safe gashi ban samu ganin ki ba har zaku wuce nace malam ai zan dawo kafin na tare yanzu ma zan koma ne na tari bakin da zasu zo yace to ga nawa gudun mawa rago nan sai a soya masu idan sun zo Allah ya tabbatar muna da alheri yasa muce gwanma da akayi.
Nace amin a kunyace yace banyi fushi ba duk da an kasani amma in mun hadu da abokin nawa watarana zai bani kudin fansan ki a gareni.
Nayi dariya kawai na mike ina mashi sallama muka fito don mota nasa aka dauko muna shata dagani sai Shafiu kawai sai kayan mu.
Mun iso gida kafin sallah azahar aka fitar muna dakaya zuwa cikin gida na sallami driver tare da yi mashi godiya nace ya ban nombashi idan muna da sako yakai muna.
Don tunda muka kama hanya yake muna hiran yanayin kasar da sauran su shafiu ne ke bashi amsa ni sai jefi jefi nake saka masu baki ga hiran nasu.
Mun shiga gida sai bin mu akeyi da kallo Aisha ke fadin ga mutanen kauye sun dawo munko ga alama don ga tsaraban kauye nan hardasu zabbi da kwai.
Ummi ce ta buge mata baki tace kai surutu muka shiga daki na huta mama tazo ta tare mu ta tambaye mu yaya muka barsu nace lafiya suna gaida ku.
Zata juya nace mama ga nono nan da kwai da zabbi nazo dashi don bakin da zasu zo jibi sai a gyara masu.
Taji dadi tace a a baki muke dasu tafe ashe sai ta karasa shigowa dakin tana cewa yanzu yaya za ayi masu dashi don mu fara saboda akwai aiki sosai.
Nace mama yadda ya dace zakuyi dashi mana tace to yanzu bari in aika ma mamakin suzo asan abinyi kafin gobe a makara.
Ta aika kiran su mama zuwa karfe biyu sai gasu sun iso nan ta gabatar masu da komai don haka suka fara tsara abinda zasu yi na kawo kudi na basu wanda za a sai kayan aiki.
Da farko an yanka ragon da malam ya bani nan suka shiga gyara saadatu ne kawai ta fito inna cewa tayi wai ba a sata a maganan ba.
Kowa ya share ta a gidan yaya Sani yayi fada har ya gaji baba yace a kyale ta ranan asabar mi salin karfe dayan rana sai ga su kawu abu sun shigo wai babane ya aika su zo nace kai baba ho tambayan aure shine harda taso su kawu su zo kuma.
Zuwa karfe biyu saura suka iso mota biyu akai masu taron mutunci sunci sun sha sai suka gabatar da zancen neman aure da kuma suna son a yanke masu sadaki kafin su wuce.
Baba yace sadaki dubu ashirin zasu bayan ba kuma zasu wuce ba sai an daura aure don ni ba budurwa bace.
Duk yadda suka so baba yaki yarda dole suka amince za a daura kagin su wuce mu dai sai ji mukayi mai shela na sanarwa a na gaiyatan mutane kofan gidan babana.
Nan dai aka sheda daurin auren na da sulaiman akan sadaki dubu ashirin kacal ina daki kwance shafiu yazo min da labari.
Zubur na mike ina cewa yaya uncle zai min haka kuma ai ce min yayi tambaya zasu zo da kuma saka rana.
Mutane sun rage yawa sai ga bakin daya daga cikin su ya shigo na fahinci kannin Sulaiman ne don naji yana cewa ina amaryan nawa take na ganta don ban santa ba.
Nayi saurin boye sai da mama ta shigo tace in fito mu gaisa hijjab kawai na saka na fito yana zaune falin ummi yana gani na yace ba laifi shiya sa bross ya lake sai ke amma kamar na san fuskan nan taki wani wuri.
Gaida shi nayi shiko sai sheri yake min yana fadin yau ban san yadda zai ji ba idan yaji har an daura aure gaba daya akwati biyu na gani anshigo dasu yace ga sakon baaban mu nan tace a kawo maki na mun gani muna so gashi kuma har kin zama namu gaba daya.
Na dago kai da kyat nace aimin godiya wurin baaba kafin inzo yace zata ji ya mike yana fadin zamu tafi do garin naku akwai nisa sosai wallahi ai gara da aka daura gaba daya muka huta.
Mukai sallama ya fita nan aka fara fita masu da kayan da aka hada masu na ganima suka ce harda wani dawai niya haka kuma.
Nan sukai min sallama suka tafi cike da farin cikin irin karramawan da suka samu a wurin mu sun kuma yaba da halin baba da bai yi zari ba da kwadayi ya karbi kudi kadan a sadakina.
Nan aka bude akwatin mama ta fara daga dankara dankaran zannuwan dake ciki da lece har goma sha biyar dayan akwatin sauran tarkace ne a ciki aka zuba.
Baba ya shigo har dakin ummi da kudin sadakina a hannun shi yana cewa ina Safiyan ga sadakin ki nan hakkin kine ba namu ba sai dai nayi karanbanin yake masu mafi saukin sadaki don samun albarkan aure.
Na mika hannu bibiyu na karbi kudin tare da nufan ummi na dake zaune gefe dasu tace a a rike abunki Allah yasa albarka duk wanda ke dakin yace amin.
Ya fita na koma kuryan dakin na haye gado tare da lafewa kamar mai yin barci ina jin suna watsewa da guda guda.
Ya saura sai ni kadai da yan gidan mu kowa ya kama gaban shi daga inda nake kwance na jawo waya na naji ina son kiran anty in fada mata ta ida aka hau tanan ake sauka.
Amma har ya katse bata dauki wayan ba na kara kira yan biyu ta dauka tana fadin tana sallah na kira sunan ta take ta gane ni mukai ta hira dasu har tagama ta dauki wayan.
Muryan ta ba yabo ba fallasa muka gaisa tace abubuwa sukai mata yawa shiyasa bata samu kirana ba amma tasha ganin miscall dina.
Mukai sallama nai mamakin jin bata tambaye ni Sulaiman din ba nima kuma ban mata maganan shiba.
Faiza na kira tace ke yar kasa ai na dauka ki manta danine ina son in kiraki ina jin tsoron kada ki fada ma mutumiyar tamu nace haba don kin kirani sai in fada mata kuma.
Naji ta shake murya tace dama ina son kiranki in sheda maki anty uwa nan tazo ita da yaranta sai faman shuka muna tsiya suke a gida.
Nace don Allah yaushe tazo tace yau kwananta biyu da zuwa wai may ya hadaki dasune Safiya?
Nace ni kuwa ina na san su banda wurin liyafan da muka hadu a abuja.
Tace aike gara da baki gidan don ko ita anty ta gaji da su wai kuma sati daya zasuyi a gidan nace tirkashi .
Tace ke dai ai kin auna arziki da kika tafi basu samay ki ba gani nan kamar aiki zai kashe ni yan iskan yara kawai komai basa iya yiwa kansu sai dai ai masu.
Amma kamar naji ana maganan Sulaiman da suka ganin sai sukayi shiru basu san naji abinda suke fadi ba sai dai banji ba sosai kamar suna cewa inba shi ba mai zaiyi da yar kauye ga mata birjit a birni.
Nace nice yar kauyen ke nan ko tace wa yasanar masu yan bakin ciki kawai.
Mun dauki lokaci da ita muna hira ta kashe tana cewa wai ana kiranta don haka mukai sallama tace idan taji wani abu zata kirani.
Ta barni da tunane nace a raina ashe sunzo din Allah ya taimakeni dani ce zan zama masu jakar aiki harda gaiya zasu hada min ga korar karen da sukayi niyar yi min a gidan.
Da dare na yi shirin kwanciya sai ga wayan sulaiman ya shigo min ina dauka naji ya kwashe da dariya yana fadin Allah dai ya sakawa baba da alheri.
Wanan irin halarcin haka aiba kowane zai iya ba zankadedeyar kyauta haka abin yazo min da sauki da na dawo yanzu sai kawai nazo na dauki matata mu tafi.
Nace sai kace amaryan dako yace ai itace don ko baba ya hutar dani ga komai yayi yadda sunna yace ayi saura may kuma ba in daukeki ki tare a gidana ba.
Nace kana fara yi min haka aiko dan walima ka bari muyi don Allah yace kai Safiya bansan baki da tausayi ba .
Allah ya kawo min sauki kina son kuma ki kirkiro wani abu na daban kisa ai walima ko a dakin ki kaso sai ai maki.
Kara marairaicewa nayi nace don Allah uncle kada muyi haka dakai yace kedai zancewa kada muyi haka dake shekarana nawa ina zama gwauro yanzu kuma da aure na zaki mayar dani gwauro da karfi da yaji.
Kunyan zancen nake ji don haka nayi kokarin kawar da zancen da tambayan shi ka fada ma anty kuwa ?
Yace bari nayi sai taji ta kirani zamuyi maganan da ita don yanzu ban shirya abinda zan fada mata ba.
Ajiyan zuciya na sauke nace ashe su anty uwa sun tafi lagos din yau Faiza ke fada min yace itace info dinki a gidan ke nan nace a a magana ne ya kawo ta fada min.
Bayan muyi waya dashi ya sheda min a sati biyu yake son in tare gidan shi don haka na fara shirina da wuri zai dawo next week in Allah ya kaimu.
Bayan na kashe wayan ne na sauke ajiyan zuciya sai yaya Saadu ya fado min a rai don haka na kirashi don in sheda mashi.
Kira biyu ya dauka yana cewa yar halas yanzu muke maganan ki don ga takwaran kinan ta hanamu shakat sai kuka take muna nace subbahanallahi.
Kun bata magani kila cikin ta ke ciwo ina jin yana tambayan Samira ko an bata magani tace bata bata ba.
Ya juyo gareni yace yaya garin kina lafiya yaya logos nace ni ina gida yaya yace kina gida tun yaushe ?
Nace sati daya ke nan lafiya kika je gida yanzun Safiya kodai auren ya tashi ne ban sani ba ?
Nace aure sai dai ayi fatan dacewa da zaman lafiya yanzu yace may kike nufi tukun nace abinda na fada yanzu yaya.
Wai tsaya don Allah da gaske kikeyi ko wasa nace wallahi ko yau baba ya daura min aure daga zuwa tambaya sai daurin aure daya ni.
Yace don Allah ki bari ni ina nan ina cewa ni zan bada ke don asan ba zumuncin wasa ke tsakanin mu ba ashe baba ya rigani.
Nace wallahi yaya ni yanzu duk abin ma ya daure min kai wallahi duk na shiga rudu wallahi ban shirya komai ba yaya.
Yace Allah yasa haka yafi zama muna alheri nace amin yace yaushe ne tarewan naki yanzu nace ban sani ba yaya amma dai naji yace in two weeks yake son in tare.
Yace haka yayi yanzu ki bari zamuyi waya zan kiraki ansan abin yi kafin in zo nace yaya kada kace zaka wahal da kan ka don yace baison inje da ko tsintsiya gidan shi mata ya nema mata za a kai mashi.
Yace ayi haka bari dai mu gani zan kiraki da safe in nayi shawara mukayi sallama ya kashe wayan.
Na sauke ajiyan zuciya tare da kifa wayan nawa ina mai sauke numfashi tare da lumshe idona sai na mike zubur na fada ban daki tare da dauro alwala na fito.
Na dade zaune ina kai kukana ga ubangiji da ya tabbatar min da alheri ga wanan auren ya kawar da duk wani abin ki a gare mu.
Na dauki lokaci mai tsawo a zaune itama ummina tana nata a falo sai kanne na ne ke ta kwasan barcin su hankali kwance na shafa tare da mikewa na nade abin sallah.
Sai naji Ummi tace min kin idar na amsa mata tare da fitowa falon na samay ta na zauna anan.
Take cewa dani gashi dai yau Allah yayi ikon shi kina da aure a kan ki a gidan nan abinda kowa bai zata ba akan ki.
Don haka sai dai muyi fatan Allah yasa ma auren albarka Allah dai yanufa shine mijin ki kece matar shi kada kisa kowa a ranki ita ma wace tayi maki wanan dalilin aure kada ki yarda ki yashe ta komai ritse don ita din ba abin yaddawa bane a gare ki.
Ki manta da komai ku zauna lafiya don alaka ya sake hadaku dama duk wa yan da zaki samu a zurian shi ki zauna lafiya da kowa.
Kin daiga shi abin duniya bai rufe mai idon shi ba to kema ki zama haka na ga yan uwanshi da nasa sai a zauna lafiya.
Yanzu sai mu jira dawowan shi muji yaushe yake son ki tare dakin ki nayi saurin cewa ummi waifa a cikin sati biyu yake son in tare.
Sai naji ummi tace to shike nan mana Allah yakai mu lokacin nace ummi may aka shirya da za a biye mashi don yace cikin sati biyu yake son in tare ?
Tace akwai Allah shi zai hore muna abinda zamu kai masu a matsayin gara bashi kenan ba sai ki tare shike nan sai kuma a jira suna idan muna da sauran kwana.
Cike da jin kunya na sauke kaina kasa ina cewa kai ummi sai tayi dariya tace to may za a jira kuma yanzu bayan wanan sai maman ku ta shiga zuwa reno.
Kunya naji nace kai ummi tin yanzu har an fara wani maganar haihuwa can a dai samu a tare din don dazun Faiza ke fada min wai anty uwa tana lagos gidan anty kan maganan.
Sai naji ummi tace ai basuyi kamar Allah ba don aure ya riga ya dauro a tsakanin ku ko ba kuma zasu iya rabawa ba insha Allahu.
Mun dauki lokaci muna magana kafin mu kwanta barci da safe ma da muka ta shi da maganan muka tashi kuma a dakin mu.
Kiran shi ne ya shigo min na dauka da ladabi ina gaida shi bayan mun gama gaisawa yace Safiya a gidan ku wa kike ganin ta samu kebewa da Nafiu kanina da suka zo.
Gaba na ne ya fadi dam nace a gidan mu kuwa gaskiya ban sani ba don ni ina daki har suka wuce yace ki dai bincika din akwai wace ta fada masu wai.
Rufa rufa za ai min kina da cuta a jikin ki abincika kafin ki tare don kar a cuce ni da sauri nace ba kowa zai min haka ba sai inna .
Yace wacece inna nace dashi maman su yaya Sani don itace kadai zata iya yimin haka don tasha fadawa mutane hakan.
Yace subbahanallahi nan na fara bashi labarin zaman ukuban da nakeyi da ita tun tasowa na a gidan har zuwa yanzu.
Yace ok ita din ce na fada ma hajiya baaba da ta tuntube ni da zance nace ba gaskiya bane sai da mukayi gwaji dake kafin mukai ga matsaya nasan kuma ta gamsu da magana na.
Zan kuma kara yi mata bayani yadda zata fahince ni amma dai wanan matar ko bata da hali mai kyau yace zan gaya wa baba da kaina don ya dauki mataki akan ta kada yan uwa na suzo ta bata auren.
Nan dai ya kwantar min da hankalina muna gama waya na kira ummi na ina fada mata ita kuma bata tsaya ba ta kira mama tana sheda mata abinda ke faruwa.
Mama tace a bari baba ya dawo gidan ai ba kyale ta za a yi ba dole ai mata magana wanan karon.
Basu gama magana ba sai ga baba ya shigo a fusace tun daga kofan gida yake kwadawa inna kira mama tace gayacan ma shigo ko yaji ne ma ?
Inna tafito tana cewa malam wanan kira haka kamar makaho ni har gabana ya fadi ai.
Yace gaban ki ya dade bai tarwatse ba munafukan banza muna fukar wofi kawai ta Allah ba taki ba.
Munafincin ki bai ciba sai ki canza wani kafin ma ki canza badai a gida na bakan don safiya bata tarewa kina gidan.
Fadin haka yasa yaya sani dake bayan shi yana sauraren maganan baba din yace saboda may baba ?
Yace sani wanan uwar taku wani irin hali ke gareta yanzu ace duk halarcin da yarinyar nan take muna agidan nan kaf bata debe kowa ba wai amma Rakiya bata gani.
Sai tabi baya ta yi munafinci akan auren Safiya don ta kumsa muna bakinciki kawai duk a taru a lalace uwa zaune diya zaune a gida kamar yadda take da yar ta a daki.
Yaya sani ya sake fadin may ya faru ne baba may kuma innan ta sake yi ne wai ?
Yace sani wai ka diba ashe zuwan mutanen nan garin nan Rakiya ta sillace jiki ta ja daya daga cikin bakin nan ta fada masu wai ba lafiya ke ga Safiya ba ayi bincike kafin ta tare.
Sai gida ya dauki salati dama kowa ja waje cirko cirko a tsaye ana sauraren baba yaya Nura yace an ko yi haka wallahi dama nayi tunanen in ba wani abin zata fada mai ba don naga lokacin da ta fito suna alwala ta kirashi gefe ni kuma muna shagon musa mai tereda zaune wallahi na ganta.
Kai munafuki da ka ganni sai akace abinda na fada mai kenan ko may yace nidai na gan ku tsaye wallahi ba wani ya fada min ba da idona na ganki inna.
Baba yace yanzu yaron nan ya kirani yana fada min sakon da aka kaima uwarshi gida don haka ban zama da macen da bata son diyana da karuwa a gidan ki tafi gidan ku har, , ,
Yaya Sani ne yace don Allah baba kada ka karasa don Allah sai ya fashe da kuka sauran yaran suka dauki kuka gaba daya.
Ummi tace malam kayi hakkuri ko don yaran nan idan ka sallamay ta yanzu ga Saadatu da ciki ina zata yace inko ban sake ta ba yanzu bata zaka min gida sai safiya ta tare.
Nan dai gida ya dauki kuka kowa da abinda yake fada yafice yabar gidan nace gidan mu gidan danger.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button