BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/21/20, 9:58 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON RAYUWA, , , , , , , , ,

????????8️⃣2️⃣????

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

NOVEL DINA NA KUDI NE IDAN KIN KARANTA BAKI BIYA BA NA BARKI DA ALLAH KE/KAI MAI FITAR WA HAKIN AMANA YA HAUKAN KU DON BAN YAFE BA.

Wasa wasa sai da uncle ya share sati daya a gida yana jinyan jikin shi wanda yawan jigilan da yake yi ya jawo mashi hakan.
Dani da yan kanne na dana dauko daga gida muke jiyan shi ida ya hana mu fadawa ko wani dan uwa nawa da shi.
Muna cikin sulilin rashin lafiyan uncle duk da yaji sauki zuwa yanzu ya dan samu sauki sosai sai dai bai fita har yanzu.
Labarin sakin anty ya zo muna inda ake fada mashi faruwa abin yau kwana biyu ke nan waya yakeyi ina sauraren shi hankalina yayi matukar tashi dajin abinda ya furta din a waya.
Take na fara maimaita innalillahi wa inna alaihim rajjiun a fili har ya gama wayan ya dago kai nace da sauri uncle anty na daddy ya saka.
A hankali ya sauke ajiyan zuciya yana fadin innalillahi shi ma cikin tashin hankali yake maganan nace may yayi zafi haka uncle ?
Tace wai kudine ya hadasu fada ya shigo da kudin aikin su gidan washe gari zai fita dasu sai ta taba yayi yayi ta fito mai dasu taki shine ya kawo masu sabani.
Nakai zaune don tsaye nake dama akan shi na dauko mai waya a daki sai na tsaya bayan kujera daga bayan shi.
Nace haba anty wai may takeyi da kudine haka don Allah kudi dai tana samun su mijin ta kuma tana samu a gare shi.
May zai sa ta daukan ma daddy kudin shi kuma har abin yakai ga jawo masu sabani haka ina magana ina girgiza kaina a hankali cikin damuwa.
Nisawa uncle yayi tare da fadin nima tunanen da nakeyi yanzu kenan a raina don son kudin maimuna yayi yawa wallahi.
Wanan labarin mutuwar auren anty ne ya kashe min jiki yinin ranan haka na wuni a lalace ina son kiranta ban san amsan da zan samu a gare ra ba.
Washe gari mummy ta dawo daga wurin yaran ta da taje gani mun yi murnan dawowan ta sosai a ranan gidan ya koma muna happy house don kowa na nan.
Nan su maimu suka koma hira da mummy dawuya su fito falo wurin mu suna wurin ta koda yaushe.
Har uncle ya fara fita aiki bai kara magana kan su anty ba kuma gashi ina son in tamabaye shi halin da ake ciki da zancen na su.
Ranan na kira hajiya baaba ina gaida ita bayan mun gaisa mun dan taba hira da ita take cewa dani sai kuka ji labari ba dadi rabuwan maimuna da mijin ta.
Nace wallahi hajiya tace manya sun zauna akan zancen ya nuna masu sam ba zai sake zama da ita ba kuma yanzun haka aure zai yi.
Don su uwa sun hada shi da wata nan abujan har anje tsayar da magana akai mutumiyar adamawa ce wacce ya samu din.
Inna lillahi nake iya maimaitawa a bakina nace hajiya yanzu shike nan su rabu da anty din tana ina yanzu hajiya ki bashi hakkuri mana da kan ki tunda daddy yana jin maganan ki sosai.
Murmushi naji tayi tace kaiyya safiya ai labarin ba dadin jine wallahi tun da abin har da zargi a ciki sosai.
Munyi sallama ina tunanen maganan hajiya din da mukayi data ce har da zargi ni dai iya sanina shine anty tana da yawan ibada kuma banga wani alama na wanan halin a gare ta ba tunda muna fita tare wani lokaci.
Da dare da uncle ya dawo nake fada mai munyi waya da baaba har nake fada mai yadda mukayi akan maganan anty din da ita.
Yace koma may ye ai zalaman ta zai iya sawa suyi mata hakan tunda ita ta yarda dasu a marairaice nace uncle kasa baki ga maganan nan don Allah.
Yaran nan nake tausayi wallahi yace yanzu ke duk abinda sukayi maki baki tsane ta ba saboda su fa ta gujeki har abada take fushi dake.
Nace uncle ba a duban wanan domin tayi min a rayuna yadda ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwana.
Yace yanzu yaya kike son in yi ke nan nace uncle baki ya kamata kasa a zancen anty uwa yar sherin matace sosai wallahi komai suna iya yi din su kuntatawa mutum don ba tsoraan Allah garesu ba.
Shiru yayi na dan wani lokaci tare da ci gaba da cin abincin dake gaban shi har ya gama idona yana kan shi don son jin may zaice akan maganan.
Bayan kwana uku da mukai waya da hajiya ne sai ga anty taje gidan nata duk cikin son a shawo kan daddy din take fada mata ai munyi waya nima abinda na fada mata ke nan.
Tace zatayi wani abu akan zance zata kira daddy din su zauna dashi koda tafita tunane takeyi ashe safiya har yanzu bata fita zance na ba har zata iya bada hakkuri akan magana na.
Haka yasa ta shirya washe gari sai gata ta iso abuja a lokacin mu kadai ke gida uncle yana wurin aikin shi.
Ina daki hindatu ta shigo tana ce min anty wai kinyi bakuwa tana falo nace wacece tazo tace nima ban santa ba anty na dan gyara na fito taba da baya don haka ban gane ta ba.
Nace daga bayanta sannu da zuwa ta nata bin gidan da kallo ko ina a lokacin ta juyo da sauri tana amsa wa ganin itace da sauri na karasa wurin ta ina fadin lah anty sannu da zuwa.
Yanzu kike tafe ashe duk na rude da ganin ta nayi kamar zan zauna sai kuma na nufi kitchen na hado mata abin sha.
Bayan na aje na zauna ina gaishe ta ta amsa min cikin sanyin rai ba kamar yadda take amsawa mutum da izza ba.
Nan dai nace anty kisha ruwan mana tace bari Safiya ashe kin ji abinda ya faru tsakani na da baban su yan biyu da yan uwan shi.
A sanyaye nace da ita naji anty abin baiyi dadi ba wallahi hankalina a tashe yake akan maganan tun ranan dana samu labarin.
Amma anty uwa basu kyauta maki ba anty duk irin yadda kike dasu kike kyautata masu haka zasuyi maki sakaiya dashi kuma.
Safiya bari wanan zance yanzun ai duniya ta koya min darasi sosai wallahi wai har uwa ke cewa daddy maza nake bi idan bai jan shi kuma ya yarda.
Could you believe that safiya wai uwa ke fadan haka kuma aka yarda ita ba a ce mata haka ba sai itace zata fadi haka a kaina a yarda.
Nace anty kiyi hakkuri don Allah tace ina sulaiman yana gari ko na kirashi bai dauki waya ba har sau biyu da abin ya faru.
Wayana na dauka na kirashi ina fada mashi zuwan ta yace tana ina nace gata zaune a gida wuri na yace yana zuwa ta kura min ido tana kallon yadda nake wayan cikin ladabi kamar yana gabana a lokacin.
Na sauke ajiyan zuciya nace anty wai yana zuwa ki sha wani abu don Allah ki rage wanan tunanen haka bakyau komai zai zo da sauki da yardan Allah tace safiya kina ganin hakan zai yuyu yadda daddy ya hau din nan ?
Nace anty babu abin da ya gagari ubagiji ai idan ke ce da gaskiya Allah bai basu ikon samun galaba akan ki dayardan ubangiji.
Tayi ajiyan zuciya ta dan tsiyaya ruwan ta kurba tasha mukaci gaba da maganan ya dan dauki lokaci sai gashi ya shigo gidan .
Yace madam ashe kina tafe tace ba dole ba na yanke shawars inzo wirin ku ne ku taimaka min ga abinda daddy ke shirin yi min.
Yace saki nawa ke tsakanin ku ina jin haka sai na mike uncle yace ina zaki kuma ana magana kin kuma tashi.
A marairaice nace dashi zan baku wuri ne da yace ai wanan maganan ta shafe ki tunda ta shefi anty ki ki dawo ki zauna ya fadi cikin daure fuskan shi.
Da sauri na dawo na zauna tace saki biyu ne don da cen da dadewa ya taba sakina sai kuma yanzun da ya kara daya.
Nan dai yake mata tambayoyi tana bashi amsa duk muna sauraron su yace ke ma kina da laifi wallahi.
May yasa dayace ki bashi kudi shi baki mayar mashi ba tun abin baiyi maku nisa haka ba tace sjerin shedan ne kawai ya kawo haka.
Yace ga tanan tun lokacin da muka ji zancen take bina akan in sa baki tace ban son shiga tsakanin miji da mata ne ban kula mata ba da tun tuni nayi magana akai.
Juyawa tayi ta dan kalle ni sai ta sadda kanta kasa tace nasan nayi kuskure babba a kanki safiya sherin shedan ne dana hajiya uwa da take zugani a kan ki.
To yanzu bari in kirashi inji ta bakin ki uncle yace yana lalubo wayan shi a cikin aljihu yake fadin wani yasan kin zo nan ne da zaki zo tace ba wanda na fadawa zanzo nan din.
Neman layin shi yayi kira biyu a na uku ya dauka yana fadin kadawo kenan tunda naga nomban Nigeria yace two weeks kenan da dawowa na ai na yi rashin lafiya ne dashi na dawo shiyasa baka jini ba.
Yayi mai jajen jikin yace ai bansan cewa kana kasan ba wallahi yace yana na sai dai wani magana nakeji mara dadi yana faru ?
Dariya yayi kamar a fili yake kusa damu yace may kaji kuma yace maganan ku da madam gaskiya brother banji dadin hakan ba sosai .
Daddy yace to yaya za a daurowa ne abin maimuna ta ishe ni dan uwa uncle yace dakata yaya aure ba a cewa haka abune da akeyi da fatan har mutuwa amma ba daga dan magana kadan ace rabuwa ba.
Yace na sani Sulaiman amma yanzu banjin zan iya mayar da ita gida na doni aure zanyi very soon taje ita ma ta samu wani a a dan uwa hakkuri dai zaka yi zan cen maganan auren nan don Allah kabar shi.
Sai daddy yayi murmushi wanda har muke iya jin shi yace ai magana har yai nisa yace to ni nace ka fasa tace har yanzu baka san wace zaka auro wa kan ka ba ne da bakayi ba.
Don nayi bincike a kanta bada da record mai kyau sam wallahi yace uwa fa ta sama min ita kuma ta yarda da natsuwan ta anty ta daga hannu alaman kinji ko nima da baki nayi magana irin ta kuramay nace ah tare da rike habana da mamaki.
Uncle yace kasan ba zan cuce ka ba don Allah ka janye maganan nan kayi hakuri madam ta koma dakin ta kuyi hakkuri da juna please ?
Yace to shike nan don kasa baki ne amma ka ganta ka ja mata kunne idan zata ji maganan ka don yanzu ban daukan iri halayen nan nata.
Yace insha Allahu nan dai ya gaya mashi irin halaiyan su hajiya uwa da abinda suke aikatawa a gari yace shine take son rabaka da matar ka ta hada ka da balai ko ?
Sun dan jima suna magana uncle ya kashe wayan bayan sunyi sallama da junan su ya juya wurinta yana fadin uwa yar iskan matace na sani ba yau ba shiya kika ga sam ban dauki maganan ta ko kadan da muhin manci ba don nasan kowaye uwa.
Tana share hawaye tace ni kaina nakan yi mamakin yadda tazo daga baya ta shige min jiki duk da yana fada akan in rabu da ita amma banji ba.
Ya mike yana fsdin shi zai koma sai gobe ne zaki tafi ko tace wai da yau nace zan koma yace yau kan ai dare yayi yaushe zaki isa bauchi a wanan lokacin ki bari gobe sai ki koma.
Ya fita nace ta taso ta shiga daki wani dakin na bude yana a gyara dama don baki irin haka muka gyara shi nan na sauke ta na fita na kawo mata abin bukata a dakin .
Sallah tayi na kawo mata wani dogon riga da nake ganin zai mata nace ta canza kayan jikin ta na juya zan fita daga dakin tace safiya sai na juyo da sauri.
Ganin taba da magana yasani dawo wa inda take na samu bakin gado na zauna ina sauraren abinda zata fadi a lokacin.
Tace nasan nayi maki ba daidai ba a cikin zaman mu amma duk da haka ke kina bina da alheri har yanzu banta dana sanin rabuwa dake a rayuwana ba sai yanzu da na shiga wanan halin.
Uwa ta cuce ni safiya ta cuci rayuwana wanda nasan ba banza ta barni ba a yanzu da nake tuna irin yaudara na da taitayi ita da diya ta da sunan zasu taimaka min.
Ashe ha,inta na sukeyi ban sani ba ni na dauka so ne ance ka samu dangin miji ka rike mutum guda a ciki shine na riketa ashe ita bada zuciya daya take zaune dani ba.
Ni dai hakkuri nake bata kawai don ban ma san may zance da ita ba a wanan lokacin sai bata hakkuri nake kawai dakin su mummy na shiga don in duba su.
Yaran suna kallo nace mummy kuna ciki ne tace eh ai dazun zan fito naga kuna da bakuwa bakuwa kukayi ne a gidan nace eh mummy anty ce tazo.
Wata anty ta tambaya cikin son sani ko wanake nufi nace anty na da nayi zama a wurinta lagos itace tazo dazun .
Allah sarki ashe da rabin zan santa bata taba zuwa ba nake gani ai nace ko yanzu ma ba zuwan lafiya tayi ba na zauna ina bata labarin abinda ke faruwa.
Sai dana gama fada mata tace ikon Allah haka abin Allah yake fa gashi tun ba a je ko ina ba Allah ya fitar maki da hakkin ki baki da Alhakin ta ke nan.
Ai wanan zamanin ana abu wallahi da karfi da yaji akeson tubbuke ka a gidan auren ka don kawai wani ta shiga ko idan shi yashiga alhaki zai barshi ya zauna ne shi ?
Mata kyashi da hassada yayi muna yawa yanzu sai kiga ko da yan uwa na jini da nine yanzu suna kyashin junan tun dai idan an ga daya ya dara daya sai hassada yazo ya shiga tsakani.
Ke dai fita batun yan duniya ki rungumi mijin ki tunda bai raga ki da komai ba na bukata kuyi zaman ku lafiya ba fita kike yi balle ki ga wani abun a kan shi.
Shine amfanin zama guri daya yau idan baka kula mutane ka huta ma rayuwan ka sai zuciyar ka ta zauna lafiya da kowa ba abinda ya damay ka.
Amma kinga yawan kwashe kwashen na babu abinda bai haifarwa shi nake guje wa mutumiyar ki ai kullun ina kan bakina da ita samira bata san ciwo kan ta ba wallahi.
Nace mummy may tayi kuma tace waya san iyaka yar nan gashi yanzu yar uwanta ke fadin dawowan nan danayi tace wai sabbin abaikai tayi ko yaushe idan su basu zo ba ta taje wirin su.
Kinga ai irin haka mutum ke gudu wa rayuwanshi don ba a gane mugu a goshi tunda ba zuciyar mutane ake gani ba wanan abin na yarinyar nan yana damu na wallahi.
Nace ni mummy sai yanzu nake ganun fa,idar barina in fita da uncle bai yawan yi koma wani wuri zan tafi in ba wurin Aisha ko samira zan tafi sai dai mu fita tare sai kuma idan wani abu zan fita in sawo mai muhinmanci a gare ni.
Mun dauki lokaci muna hira da ita nafito daga dakin don magariba ya kawo jiki a lokacin don haka na fito don zuwa sallah.
Ko da uncle ya dawo da dare tafito sun dan taba hira dashi ta koma daki ni dai sai haba haba nakeyi da ita a gidan in samu mu rabu lafiya ina mai kara bata hakkuri.
Washe gari ta wuce da safe tana matukar bani tausayi tace don Allah in kara yiwa uncle magana akan zancen nace insha Allahu anty zanyi bayan tafiyan ta muka zauna nan da mummy a falo muna hira.
Duk jikina yayi sanyi wai yau anty ne take kumsan bakin cikin da na miji a kanta matar da suke gwanin ban sha,awa agidan su ita da mijin ta da yayan ta a gida har damu da mu kaje cin arziki a gidan.
Yau sai gashi wai sun samu sabanin mai muni a tsakanin su dole mata mu rika taka tsamtsam da maje komai dadewan mu a gidan miji.
Haka rayuwa ke guda yau dadi gobe madaci ga bawa watarana kuma a dara uncle yayi kokari ya mayar da anty dakin ta tare da basu hakkuri daga ita har daddy din.
Haka yasa anty uwa da kawar ta suga shiga tashin hankali don komai sunyi na shirin buki a lokaci da bincike da komai suka gano uncle ne yayi sanadin komawan anty gidan daddy din.
Haka yasa suka niko gari zuwa gidan namu uncle ya shawo kan daddy ya yarda a tsayar da zancen auren su da sahura.
Muna zaune a falo duk da safiya ne amma hakan baisa sun shigo sun samay muda shirin mu a gidan bamu da wani makusa sai kanshi ke tashi yana kwance saman dogon kujera don ranan babu aiki.
Abba yana saman jikin shi yana mai wasa sai ni dasu maimu dake zaune muna mashi hiran shirmay su don yace zai saka su islamiya shine suke biya inda suke.
Sallaman su mukaji daga sama shigowa falon gidan kai tsaye da mamaki nake kallon su don shi yana kwance a lokacin.
Baiga fuskokin su ba sai dai yana kokarin mikewa zaune a lokacin gane su da yayi yasa ya daure fuskan shi yana cewa uwa kune tafe ?
Tace eh gamu mun shigo yau ziyara sannu ku dazuwa kawai nace dasu ban kara bita kan su ba kuma ban bar wurin ba sai cewa dani dasu hindu su shige ciki.
Ban kuma mike zuwa dauko masu abinsha ba na zauna tare da harde hannuwana wuri guda jikina yana gugan na shi a yanayin zaman da muka dashi.
Bayan su gaisa dashi anty uwa ta dan dube ni tace don Allah bamu wuri magana mukazo yi dashi kallon ta nayi na cewa ni tare da nuna kai na ?
Tace eh magana ya kawo mu wirin shi mukazo kafin ince wani abu don yau nayi niyar mata rashin mutunci sosai sai naji uncle yace da ita.
A, a bakizo ganina bakan duk abinda zaki fada min idan baki iya fada a gaban matana ai ba alheri ya kawo ki ba ke nan.
So idan kinyi niyar gani na ba idan zata tafi don gidan ta kika shigo kinga ko baki da right din cewa ta baki wuri ki fadi maganan ki kai tsaye kawai naji.
Don ni mata itace abokiyar rayuwa abokiyar shawarana gaba daya don ko kin fada a bayan ta ma fada mata zanyi tsab.
Nisawa tayi tace dama bawani abu ya kawo mu ba sai zancen yayana da kawana sahura gata har an saka lokacin aure yanzu kuma yace wai ya fasa komawar wanan macuciyar matar tashi da ta shiga ta fi, , , ,
Dakata uwa don Allah ban son sha shanci kin sani ke har zaki iya dauko kafa kizo min gida da wanan zancen naku na banza .
Yanzu don baku da kunya kuke kokari shiga tsakanin mijin da matan da suka shafe sheru goma sha wani abu da aure kina kokarin cusa mashi wata bare can.
To bari kiji ban cikin wanan magana naki na hauka kuma aure yaya ba zai taba kara aure ba muddin maimuna na gidan nan.
Tashi tayi da fushi tana fadin don munzo wurin ka neman taimakon bawai yana nufin munzo roko ko maula ba balle kayi kokarin fada min magana haka ?
Dole yasa ka ga mun zo wurin ka don kawai ka dafa muna ba wai wani abu ba yace oho gani mahaukacin daure kun kwaso kafan ku kunzo a hada kai ayi cuta to ban iya ba ku bace min da ga tun raina bai baci ba na kira maki yan sanda yanzu.
Sai da ta watsa min hara nima na mayar mata daga inda nake zaune ta fita fuuuuu sauran suna biye da ita a baya.
Yaci gaba da fada a falon yana fadin wanan matar tana da hankali kuwa ko abin nata ya zama hauka ne wai ?
Naji dadi sosai har cikin raina yadda uncle bai raga masu ba ya kore su ya kira wayan daddy yana fada mashi abinda ke faruwa a gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button