BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:11 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , , , , , ,

????????3️⃣0️⃣????????

YAR UWA NOVEL DON NAN NA KUDI NE IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , ,

Idan nace zaman danakeyi gidan mu akwai dadi nayi karya zama dai nake yi na wacce ta rasa gatan ta da madafa saidai dadin .
Abin ban dogara da sai abin gida ba ina tsaye ina nemawa kaina mafita ga rayuwa shiya sa abin yazo min a cikin sauke,
Don ban kallon abin wani sai ma su su kalla a wuri na a nema in bayar akuma yi min gori daga karshe.
Gidan da sai an nema aci ai kin san gida ne na mawuyacin rayuwa ga bawa don ranan da bai suma ba kowa tashi fisshe shi da yaran ta.
Duk da yake mahaifi mu mutum ne mai zafin nemawa kansa bai dogara ga sana a daya ba buga nan buga can yake yi har a samu ubangiji ya rufa asiri.
Yau ma mun wayi gari baba ya wuni bai samu kudin da za ai muna girki ba har kwana biyu ga kuma Inna bakin halin nata ya motsa sosai.
Don da yar ta ta fara a daki ta nemi kudin a gunta ta rasa dan sana, an mai da takeyi jarin yana kokarin karye mata sai inna tace ta basu su sayo abinci da zasu ci tace bata da kudi.
Nan take ta fada tun tana yi a daki har ta fito waje da jidalin a bakin ta ganin ta shiga daki yasa na fito don dora muna girkin abinda zamuci a dakin mu.
Ba wani abin tsone ido nayi ba dafaduka ne na taliyan da make sayar wa na dauki biyu in dafa muna adan kau da miyau sai da dare nake son in muna tiwon masara.
Tunda ta kyala ido ta ganin a bakin murhu ta fara irin maganan ta da cewa gida ya koma muna wurin gwada tsara muda diya.
Mun koma kamar kishiyoyi a gida da mu da ku ai gara ma ke Saadatu ba a debe tsamanin aure a gare ki ba do baki da cuta amma wata kan ai haka zamu zauna muna nuna hali da mu da ita.
Tafito ba komai takeyi ba amma taje ta dawo a tsakar gida tana dauke dauke a tsakar gida kamar mai sabon hauka.
Da ummi taji abin yayi yawa sai gata ta fito waje da sauri na dago don jin motsinta nace da ita don Allah ummi kada kice zaki tanka mata.
Tai tsaye tai shiru sai taka koma daki ko ba a fada ba maganganun na Inna sun bata wa ummi rai sosai.
Yar ta Saadatu ne tafito daga dakin su tace da ita wai ke inna akan naki taba kudin mutane ne kike wanan magana har kina hadawa da Safiya may tai maki yanzu ?
Mafarin kija fitina ku kama fada da tononasiri da ummi a gidan nan ke baki taba fadan gaskiya sai ayita akare kece baki da gaskiya kulun.
Nan kuma ta juya akan Saade din tunda bata samu wace zatayi da itaba tace ke gara can shanyayya kawai an hada dake an shanye keda dan uwanki.
Nidai nagama aikina na shige dakin mu na raba na aikawa kowa gidan da nasa, muka zauna nida kanne mukaci namu.
Bayan mun gama cine nace wa ummi da take zaune tayi shiru a dakin namu tana kallon mu.
Ummi gaskiya barin gidan nan zanyi na dan kwana biyu, da sauri tace dani ina zaki tafi inda yafi maki nan din ?
Nace ba wani wuri zan tafi ba gun maman biyu zani in dan kwana biyu a can kin gama zata tace ban yada ita ba ai.
Tace dani kina ganin magafinki zai barki ki tafi kada ma ki soma wanan magana rayuka su zo su baci ga banza tsakanin mu da shi.
Nace ummi don Allah kiyi hakkuri kibar ki barni in gwada sa ata na gani ko zai yarda in tafi wallahi idan ban gusa naba inna wuri ba wata raba ana abinda ba daidai ba a gidan nan.
Ummi tace ai saidai kada akara amma kan Allah dai ya sauwaka kawai za a ce ma zancen nace amin.
Ummi na dauka nabar zancen ne niko iya gaskiya na kenan na fada bayan kamar kwana biyu na samu baba a kofan shi zaune bayan ya gama cin abincin dare nake fada maishi kudirina nason yin tafiya zuwa wirin maman biyu.
Sai da ya kurkure baki ya watar da ruwan da ya gunda a baki yace dani anyya Safiya ba zaki hakkuri ki zauna nan ba ki barwa Allah alamarin sa yafi.
Gyara tsuguni nayi da kyau nace dashi baba ai ba zama zanje nayi ba zuwa zanyi na ganta kwana biyu sai na dawo gida.
Yace safiya bawai naki tafiyan ki bane ai wanan matar tana da mutunci da zaa gunta amma kinsan halin da kike ciki yanzu
Yan uwan ki ma da kuka fito ciki guda dasu suna nuna maki kyama balle wata can da girma da arziki ne ya hada ku kawai.
Nace baba ba haka na bane ita ta bukaci da naje gun ta, na dan kwana biyu sai in dawo don kawai nai mata alkwari ne zan zo nake son zuwa ai.
Yace Allah ya kaiki lafiya nace amin baba na gode baba yace ba koma har na mikr tsaye naji yace dake dawa zaku tafi sai na danyi shiru sai kuma nace ni kadai zan tafi baba.
Yace tau Allah ya kyauta agaida su Inna na kofar ta bata san maganan may mukeyi da baba haka hankain ta yana gurin mu .
No juya na nufi daki naji tana cewa a yanazu kuma mai cuta a jiki tafi ko wani da gidan nan samun ido , nidai wuce wa niyi ban kula taba sai magana take tana dariya.
Tun ranan da mukai magana da baba na fara shirin tafiya zuwa lagos gun mama biyu sai da na shirya tsaba na fitar da zancen tafiyan gun mutanen gidan mu.
Aiko a take inna ta kasa boye jan halinta tace zaki koma a dora daga inda aka tsaya ne na hadi wasu yawin bakin ciki nace niba wurin gwagona zan tafi ba.
Naji tana son daukan zancen da zafi daga zan tafi lagos gobe mata take ta kasa boye min bakin cikin ta a fili ta nuna hassada akan tafiyan ban tsaya kula taba washe gari na dauki hayan zuwa garin lagos.

* * *
Ban isa ba sai dare sosai na iso garin lokacin ya fara yin shiru don haka ban sha wahalan zuwa unguwar su maman biyun ba da ba don dare ne abin hawa sun rage zirga zirga a hanya lokacin .
Nazo na samu sun rufe gida sun kuma canza mai gadi kusan ma,aikatan gida duk an canza su an kawo wasu.
Don haka basu gane ni ba araina nace kodai ba gidan bane nazo sai mai gadin ne ke tambayana wurin wa nazo nace dashi madam Hauwa sai naga ya juya zuwa ciki na dan lokaci ya dawo yana tanbayan daga ina nake na fada mai sai gasu tare sun fito da ita.
Tana farin ciki da murnan gani na muka kwasa zuwa cikin gida tare farin ciki gani na duk ya cika mata zuciya.
A raina nace ikon Allah gidan mu suna kyama na wasu kuma bare na farin ciki da zuwana cikin su haka duniya ta gada.
Naga halarci agun mutanen gidan na samu kaunata tazo da kuma yar uwar mijin ta suna zaune da ita sai kuma gani na zo.
Amma duk da haka basu nuna min rashin jin dadin zuwa na ba sai ma taro na arziki da na samu a guri su.
An cika min gaba da abinci ban iya ci sosai ba don nisan tafiyan da na kwaso sai dai ina kallon abincin ina tuna su ummi da kanne na ko yanzu wani hali suke ciki oho ?
Da zan bar gida na mikawa ummi na waya na kwashe nombobi na akan idan na zo ja samu yar karamar waya in saye don wanan ta ji jiki sosai.
Ban dade zaune ba sai gata ta fito daga dakin ta dake sama take cewa dani Safiya taso akaiki dakin da zaki zauna don ki huta naga kin gaji da yawa.
Na mike tare da daukan hand bag dina muka nufi dakin daki ne babba wanda ya kumshi gado da mirro da ban daki da tv da AC acikin sa.
Bata dade ba tafita na sauke ajiyan zuciya tare da bin dakin da kallo ina mamaki ban bata lokaci ba na fada bandakin na watso ruwa tare da dauro alwala nafito na rama sallolin da ake bina .
Daga nan na kwanta ban dade ba abu ga wanda ya gaji barci ya kwashe bani na falka sai da asuba don na saba tashi a wanan lokacin.
Na shiga ban dakin na dauro alwala nafito nai sallah ban kwanta ba na dade zaune ina addua kamar yadda na saba yi duk safe sai da gari ya haska na fito daga dakin bayan na gyara na samu mai aiki tana ta gyaran wuri sai na so taya ta amma sai ta hana.
Nan dai na taya ta aiki mikayi tare sai tabar min ta tafi hada abin karyawa muna gab da gama aikin anty tafito daga dakin ta tana cewa.
Dama nayi tuna nen hakan dake Safiya may yasa ba zaki huta ki natsu ba sai ki fito ki kama aiki.
Murmushi nayi nace da ita ai wanan duk ba aiki bane a gida duk nike wa ummina aikin da ya dace inyi na.
Murmushi tayi tace yanzu dai ki dan huta tukun kafin na san abinyi a kan ki nafi son naga kin huta kin kwantar da hankali kafin mu san abinyi a kanki.
Bayan mun yi wanka ne an fito karyawa take gabatar min da yar uwar mijin ta dake zama dasu sai kaunan ta da ke zaune dasu wai tana karatu naga tana min wani kallo na rainin wayo.
Ni dai ban kulata ba muka ci abinci inda duk hiran da ni maman biyu keyin shi akan yanayin garin mu da ta gani ina bata labarin garin namu da abubuwan da muke shukawa a karlaran mu din.
Mun gama na mike don kwashe kayan tace in barshi mai aiki ta kwashe nace haba anty kamar dai ba mata ba na kwashe naje na wanke ban dawo inda suke ba na shige don yin sallah walha.
Dana gama na dan mike don har yanzu akwai gajiya tare dani sai barci ashe ta leko dakin ta samu ina barci a inda na idar da sallah na.
Ta juya ta koma tare da jawo min kofan ban farka ba sai sha biyu da wani abu na gyara jikina na fito nan falo na same su da kauna tana mata fada ko da ban sani ba nasan a kaina don naji tana fadin.
Na dai gaya maki karki yarda ki sawa yarinyar na ido a gidan nan don ba wurin ki tazo ba indan ma tayi wani abinda ba daidaiba just ki fada min.
Don ban son abinda ya faru da dake da faiza ya kara faruwa akanta don duka daya na dauke ku don ko ita din ma ni na kawo ta nan din.
A take sai naji kuka yazo min a hankali na juya zuwa dakina da na fito din ba zan iya rike kukan ba a lokaci kuma gashi ban son suji na ji maganan su.
Sai dai a raina nasa duk yadda kaunan nata take zan iya hade bacin ran da zan gani a gurin ta don mu rabu lafiya ni da nazo cin arziki ina ni ina fada da masu gida.
Ina daki dunkule ban fito ba suma basu nemay ni ba ashrle ta fita ne gida sai shidda na yamma ta dawo gidan nan ta zube a falo inda ta samay su suna kallo.
Nan na fito cikin su tare da gaida su na samu wuri na zauna ta dago kai tana cewa Safiya kin tashi ai na leka ki har sau biyu na samu kina barci.
Nace wallahi anty sai yanzu na fito nima ban san barci ya kwashe ni ba sai tace tare da nuna kaunan mijita dake zaune ban gabatar maki da wa yan nan ba bayan tafiyan ki ne suma suka zo anan suke zaune tare damu yanzu.
Wanan ita ce faiza kaunar maigidan ne auren ta ya mutu ne tadawo nan da zama wirin mu.
Sai wanan yar uwatace itace autar mu itama anan take zaune yanzu tare dani da fatan zaku zauna a cikin aminci har kowa ta samu miji tayi auren ta.
Tace kuma wanan itace safiyan da kuke ji ina fadin zata iya zuwa ko wani lokaci yar uwata ce itama zata zauna damu anan na dan wani lokaci da fatan zaku rike juna da amana.
Sai naga Fatin ta dago ta kalle ta don jin ta kirani da yar uwa nima ban san dalilin anty na fada masu haka ba.
Faizan ne tai murmushi tace kai anty lallai kina ji da wanan safiyan ai kin fada muna zuwan ta tuntuni kuma insha Allahu zaki samay mu yadda kike so a cikin amana.
Sai ta juyo gare ni tana cewa ki saki jikin ki kuma ki ja kowa ajiki saboda yanzu mun zama daya da junar mu ga gidan gidan Jamma a ne.
Wa yanda ma bamu san inda suka fito ba suna zuwa suci arziki su tafi ni dai abu daya ne ko kadan bana kaunar rashin gaskiya duk abinda zamuyi mu yi shi a cikin gaskiya da amana.
Murmushi maman biyu tayi tace indai Safiya ce to kar kiji komai a kanta, saboda komai daidai gwagwado Allah ya wadatar da ita da natsuwa da sanin ya kama ta daidai misali.
Ta nisa tace tare da cewa ai shekenan Allah ya zaunar da mu lafiya da junan mu tace aini naji dadin zuwan ta kwara don in kun watse nakan ji gidan ya koma min shiru wallahi.
Ita dai fatin tana ta charting din ta ba dago kai ta kalle mu ba balle tasan may muke fadi ma.
Na ce a raina wanan da gani zamu kwasa da ita sai dai duk abinda zata zo min da shi zan yi kokarin kawar da kaina akanta.
Muryan maman biyu ya katse min tunane na take tambaya na ko nayi waya da mutanen gida da nazo nace da ita banda waya a hannu na don wayan da zanzo na barwa su ummi shi acan don su samay ni.
Tace a a ke ko ana haka ai ya kamata ki kirasu su san kin iso lafiya yafi ke fati je daki ki dauko min wanan wayan dake saman mirro na ki kawo.
Kamar bataji yar nata ba sai da ta kara maimaita maganan nata ne ta mike zuwa dauko wayan a dakin ta.
Ta bita da kallo tare da firgiza kan ta tace kai Faiza akwai matsala wallahi sai kun ta hakkuri da ita don Allah.
Faiza tace aini yanzu nasan halin ta ba abinda zata yi ya dakay ni kuma sai dai ita Safiya da bata saba da halin ta ba.
Ta kawo wayan tana mikawa yar nata ba tare da ta kalli kowa a wurin ba ta karba tana ce min ina sim din ki yake na tashi zuwa daukowa.
Ashe bayan na tashi yar take mata fada sai tai hushi tabar falon gaba daya ta koma daki.
Koda na fito ban gane ta ba na mika wa anty sim din na samu harta cire nata dake ciki tana cewa ki fara amfani da wanan har in sayo maki naki wayan .
Ta saka min sim din tace karbi ki kirasu su san kin sauka lafiya ko hankalinsu ya kwanta idan sun jiki.
Faiza tace lalai kan do irin haka hakali baya kwanci sai kaji mutum balle lagos garin ne mai tare da hatsari sosai.
Na karba kira biyu sai kaunata dake bi mun ta dauki wayan nan dai muka gaisa nace tabawa ummi wayan muka gaisa na fada masu na iso lafiya nace ga anty.
Ta karbi wayan sun gaisa sosai ummi tai mata godiya tare da cewa don Allah don ma aikin Allah ki rike min ita amana don gidan nan ba dadi shiya sa ta zabi zuwa wirin ki ta zauna.
Tace ummi kada kiji komai zaman Safiya a guri na tankar a gida take daku saboda Allah kadai yasan abinda ke zuciya ta kuma shi ya san yadda nake jin Safiya a raina.
Ummi tai mata godiya ta bani wayan ina tambayanta sauran mutanen gidan mu tace duk suna lafiya.
Lokacin sallah da ya gabayo ne yasamu watsewa inda na kula da kowa dakin ta daban ashe a gidan sai dai duk kan mu ukun a kasa muke sai masu gidan ne ke sama da yaran su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button