BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/3/20, 8:54 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON , , , , , , , ,

????????7️⃣0️⃣????

Tu wuce wanan yaya saadu ban tuna da zancen gwago ba sai da yake da kwana biyu da tafiya ya bugo min waya ya hada mu da gwago wai mu gaisa da ita.
Ba yadda na iya shiru ya dan biyu bayan wayan can na ce salamu alaikum ta amsa da fadin Safiya nace naam gwago kuna lafiya yaya jikin naki.
Ta cikin wani murya mai rauni ta amsa da jiki da sauki safiya yaya wajen ku kuna lafiya ko nace lafiya muke gwago tace naga sakon ki wurin dan uwan ki na gode Safiya.
Nace babu komai gwago Allah dai ya baki lafiya tace amin sai ta kama kuka tana son yin magana amma kuka ya rinjayi maganan da take son yi din.
Nikan sai na kashe waya don kada ta kashe min jijiya bayan na kashe ne yaya Saadu ya kirani ya ce kinji gwagon ki ko ga Ahmed yana gaida ke jikin nashi ne ba dadi sosai nace ka gaida shi Allah ya bashi lafiya.
Ya san ban amsan wayan shi ke nan yasa ya kyale ni bai hada ni dashi din ba ya tambaye ni yaya Abbati nace yana wurin gwago ta goya shi.
Bayan mun gama wayan khadija dake zaune gefe na da mummy suka ce wai amma kina da karfin hali wallahi.
Mummy tace ai gara da tayi masu haka na ta barsu da aniyar su ko yanzu Allah ya gwada masu abin su ai.
Ni dai murmushi nayi kawai ban ce komai ba sai dogon tunanen da nashiga tun lokacin kuma na watsar da zancen su a zuciya na gaba daya.
Haka rayuwa ke ci gaba ga duk mai rai da lafiya cikin hukuncin ubangiji har gashi nayi arbain da haihuwa yaro kuma yana cikin koshin lafiyan shi.
Yayi mulmul dashi bazaka ce bai shan nono ba idan ka ganshi don iri kulawan da yake samu na abinci da magunguna da zai bashi lafiya da kuzari.
Tun da nayi arbain nake ta shirin zuwa gida kunsan maza da jan fitina amma sai uncle yace ba zan tafi ba sai munje bauchi mun kai ma baaba yaron ta gan shi.
Naso tayar da hankali mummy da gwago suka sani gaba sukace ko murai kada na nuna mashi komai yadda yake so in bishi da hakana muje mukai ma mahaifiyar shi jikanta ta gani.
Haka yasa na daure ban nuna mashi komai ba da yake tsanmanin zan ce ban yarda ba da hakan daya tsara muna don yasan yadda nake dokin zuwa gida .
Wanda tun aure na dashi banje garin mu ba ina binshi a yadda yake sona dashi din don kawai a zauna lafiya.
Dole akalan tafiyan yacan za ta zuwa bauchi din mummy da gwago zamu barsu gida sai mun dawo da khadija kawai zamu tafi.
Mun shirya tsaba inda ranan jumma, a zamu bi jirgin safe mu tafi kamar yadda ya tsara don har da buki zamuyi na diyan wani kawon shi haka yasa na dauki kaya na alfarma don tafiya dasu.
Inda motacin shi na shiga biyu sun kama hanya da tsaraban mu da kayan mu zasu samay mu acan kamar yadda ya tsara din.
Mun sauka lafiya inda su Nafiu suka zo daukan mu zuwa gida da motaci biyu mun isa mun samu yan uwan shi mata suna gidan kaf din su sun zo tariyan mu har da Aisha da ta tafi sati daya daya wuce bukin kannen mijin ta.
Mun sauka inda suka fito waje taron mu yaron yana hannun khadija har muka isa gidan nan suka karbe shi kowa na nuna kulawan shi akan yaron sai fadi suke Abban mu Abban mu.
Suka nufi cikin gida da yaron su kuma suka tsaya muna gaisawa tun a waje part din hajiya baaba muka nufa gaba dayan mu don mika gaisuwa a gare ta.
Koda muka shiga mun samu ta karbin yaron tana fadin Allahu akbar yau jinin babana a hannu na haka ina kallo da raina da lafiya na.
Muka shigo da sallaman mu muna gaida ita ta juyo gare mu cikin farin ciki tana muna sannu da zuwa tare da fadin ai yanzu kin zama uwar mijina kuma wanan irin mijin da kika haifo min haka?
Murmushi nayi ina kai gwiwana kasa dukka guda biyu tare da fara gaida ita cikin girmamawa .
Amsawa take yi yayin da hankalin ta ke yaron tana fadin wanan duk gida ya kwaso wallahi ana fada ban yarda ba sai yanzu dana gani da ido na.
Uncle ya ce hajiya mun samay ku lafiya tace sannu kai dai dan Albarka ai duk na rude da ganin wanan mijin nawa da Allah ya nuna min zuwan shi da raina da lafiya na.
Sai da ta jagula yaron anty Suwaiba ta karbe shi sannan ta dawo da hankalinta gare mu sai lokacin taga khadija da muke tare tace a a da bakuwa kuke ashe ?
Da ganin wanan yar uwar Safiya ce don kama ya nuna kanshi basai antambaya ba wanan kamar uncle ne ce kaunar ta dake wurin ta ne ai tunda ta haihu suka zo suna take nan tare da mu.
Gaisawa sukayi da khadijan tare da tambayanta yaya hanya ta amsa cikin ladabi da lafiya lau hajiya.
Juyawa tayi tana fadin ku kawo masu abinci mana kun tsaya kuna shiriri ta haka suka ce hajiya baki ce a dauko masu bane ai.
Yau ga tsiya tace dasu abincin ma sai nace ku kawo masu zaku dauko masu uncle ne yace hajiya bar abincin nan yanzu a dai kai muna can part din mu zamu fi jin dadin ci acan.
Nan aka shiga kwasan abincin zuwa part din mu dashi shi kuma suka ci gaba da gaisawa da mahaifiyar tashi.
Nan na juya wurin Aisha nace mutanen bauchi ke nan ina yaran suke tace suna can gida na barsu banzo dasu ba yau.
Hiran mu muke yayin da hajiya da dan ta suna can zaune a inda muka barsu suna magana a tsakanin su.
Karshe ma sai su Aishan suka jamu zuwa cikin uwar daka nan muka shige daki guda daga cikin dakunan part din nan dai muka fara hira tana cewa ai ta godewa Allah da muka iso yau gobe ne bukin gidan su sai muje mata karan buki da sauran yan uwa.
Kiran da hajiya tayi ma suwaiba sai gata ta dawo tana fadin wai mu fito zuwa part din mu uncle yana son ya huta haka muka fito muka nufi can har lokacin yaron na wurin hajiya tana bashi madaran da khadija ta hada mashi.
Mun shiga part din komai neat kamar muna cikin shi ko yaushe yasha gyara sai kyali yake yi nan na aje handa ban dina Aisha ta biyo mu da dan troley din da muka riko.
Abincin da aka aje muna muka fara zama ci inda masa ne wanda yasha mai sai kyali yake fari tas a cikin kula sai miyar kassan rago da akayi da ganye alaihu sai kamshi ke tashi ga ferfesun kaji dayaji kayan kamshi yana tashi shima a kulan shi.
Nan dai muka taru muka fara cin abincin sai santi kowan mu keyi kan dadin masan dake gaban mu uncle ne kawai bai magana sai murmushi yake muna kawai.
Mun ci munyi kat ko dinban ferfesuf din bamuyi ba ni da uncle sai khadija ne ta dan sha kadan ta ture don ta koshi da masan da taci .
Yaron ne aka shigo dashi yana kyallara ihu kamar wanda wani abu ya sama karban shi nayi ina fadin yanzu haka fitsari yayi yake damun shi haka yake yi idan ya bata pemppers din jikin shi.
Tube shi nayi gaba daya na cire mai tufafin dake jikin shi don in sauya mashi wani na shan iska nagama shirya shi na kara mai madaran tare da bashi grive water yasha sai gyatsa na bawa khadija shi ta goya.
Kwantawa nayi don in huta don tafiyan safe da mukayi barci ne taf a idona lokacin shima uncle ya kwanta bai fita hanin kowa ba a lokacin don yace yana son dan hutawa ne .
Koda na farka khadija na kwance sunyi barci da Abba a jikin ta haka yasa na dan mike a hankali kada na tayar dasu daga barcin dakin .
Na samay shi yana barci ga sanyin AC ya karade dakin zuwa nayi wurin shi na dan taba mai huska a hankali sai ya bude ido nace lokacin zuwa masallaci yayi kada ka makara.
Salati yadan yi tare da juyawa yana fadin badon kin shigo ba da na makara don naji dadin barcin nan sosai wuce wa nayi bathroom na hada mai ruwan wanka na dawo ina fada mashi ruwa ya hadu.
Ok kawai yace na juya zan fita daga dakin yace ai na dauka za a bani goron jumma a ne kuma sai zaki fita .
Na juyo da dariya na nace kai uncle har a garin mutane ba a bakun ta na fice ina dariya don nasan in nayi sake bai da wasa wirin wanan harkan.
Wanka nayi nima na sauya kaya a lokacin sai gashi ya shigo cikin wani farin yadi mai laushi da taushi yana daukan ido da hular shi a hannu yana gyara karata da kyau.
Wayan shi ne tayi kara ya dauka su musa driver ne suka iso suke sanar dashi zuwan su tare da tambayan ina za a nufa da kayan.
Yace su shigo dashi part din shi nan ya juya zuwa wurin su yana fadin daga can zai wuce masallaci ne nayi mai a dawo lafiya.
Lokacin khadija ta falka bayan fitan shi ne tace sai yanzu masu motar suka iso garin kai amma akwai nisa ashe haka ?
Kodon da jirgin mukazo mu sai naga kamar ba nisa wallahi nace kema kin san ai da nisa mana zaki hada tafiyan mota da jirgine.
Shigo da kayan yasa na fito falon ina gwadaasu inda zasu zube muna kayan don ba karamin tsara muka lafto masu ba wanda zamu raba har uncle na fada wai kayan sunyi yawa haka.
Sallah na dawo na tayar don lokaci ya gabato ina son inyi nafila kafin jumma a din sai da na idar na juya wurin khadija dake kwance har lokacin nace hajiya sallah fa.
Ta nuna min yaron dake saman hannun ta kwance wai kada ta tashi yaron ya motsa na watsa mata harara nace yanzu don kada ya tashi ne bazaki je kiyi sallah ba.
Tana mikewa yaton na wani irin zabura ya fara dan shure shuren kafa yana dan kuka sama sama nace ashe aiki ya ganku kuda kuka koya mashi hakan ?
Nikan ba wanda zai hanani barci yanzu kuka yake sosai dole nabar adduan da nakeyi na kamashi ina lalashin shi.
Dan shiru yayi dole na goya shi a karo na farko tunda na haife kasan cewa su mummy da gwago ke faman dawainiya dashi a gida.
Ni iyaka na dashi in dan dauke shi inyayi koka kuma in mikawa mummy shi su karata can amma kasancewa yau basu kusa dole reno ya dawo kaina.
Khadija na fitowa bayi wanda nake ganin wanka ta tsaya yi ta kalle mu ta tuntsure da dariya tace ai na fada maki bai yarda wallahi ya saba da dumin mutum a jikin shi.
Idan bayaji mutum a tare dashi ba bai yarda yayi barci nace ai duk ku kuka shagwabashi dake dasu mummy yanzu gashi yazo nan yana wahalda mutane.
Sallah ta tayar muryan Aisha naji tana fadin ina matar gidan nan take ni zan tafi nawa masauki yanzi yaya gobe din in sa rain zuwan ku ne cika muna taron buki.
Allah ya kaimu nace da ita har zaki tafi ke nan gashi ko da ina son zaki tayani fitar da tsaraba wa mutane.
Sai naga ta kalle ni ta tuntsire da dariya tace yau Allah ya kamaki mummy bata kusa ai dole baban mu ya samu baya ya hau.
Dan tsaki naja nace ai uwar shi ta idar da sallah ta karbe shi su da suka saba mashi da jiki nace muje falo ki ga kayan da muka zo dashi din don yanzu su musa suka iso dasu suna can sun tafi masallaci da uncle.
Falon muka fito ta kalli kayan tare da fadin dan kari duk wanan uban tsaraba haka safiya nace to kin san mun dade bamu zo ba ai.
Nan muka fara aikin in duka yaron yace baison dukawa sai ga khadija ta fito daga daki tana zuwa ta karbe shi saman cheast din ta ta dora shi tana lalashin shi.
Nan naji dadin aikin da muke inda muka kwashe sauran zuwa wani daki tace ko da daga baya zaki tuna wani ba a bashi ba kin ga sai a diba anan.
Sai bayan mun gama ne ta wuce har waje muka fito rakiyan ta da motar ta tazo don haka a ciki muka saka mata nata tsaraban nan muka tsaya take fada min kishiyar ta lami tazo tana nan sun hada kai da uwar gidan ta suna kulla mata muna funchi.
Nace rabu dasu Allah ya fiso duk abinda zasuyi basuyi kamar Allah ba ai tace wallahi da da yaya baya kulamu an samu abin fada yanzu kuma da yake muna ance ina muka fito
Mun dauki lokaci muna magana tsaye a waje nace taje ta kama yaranta dake gida tace wallahi nasan suna can yamzu wuri wuri suna nema na mukayi sallama badon mun gama gulman mu ba ta wuce tana jaddamin batun zuwa na gidan su gobe.
Ciki muka koma muka kwaso ma hajiya tsaraban ta zuwa part din ta su kuma su anty suwaiba duk wanda zai tafi na bashi nashi tsaraban.
Sai dare su uncle suka dawo gidan lokacin muna falon hajiya baaba muna hira don gidan an watse sai mu da tsirarun mutane wa yanda ke gidan wurin ta muka rage a gidan.
Yashi alokacin ya cire babban rigar dake jikin shi ya rage daga shi sai yar ciki a jikin shi tafiyan shi kawai ya isa ka gane a gajiye yake a lokacin.
Sannu da zuwa mukayi mashi ya isa gaban mahaifiyar shi yana gaida ita inda ya juyo gare ni yana fadin .
Madam yaya bakunta nayi dan murmushi nace ai mun sauke shi yanzu mun zama yan gari ko dariya yayi yace yana zama na gaji wallahi.
Hajiya ta tambaye shi ina ya shiga haka shiru shiru yace yarima ya jani muka dinga zuwa ziyara tsufin abokan mu har yamma yayi muna haka.
Tace ai hakan na dakyau ba karamin lada kuka samu ba wallahi ai ziyara nada kyau mutane ne basu gane ba.
Ban iya magana ba don hajiya na wurin ina jin kunyanta don haka ma sai na kawar da kaina gare su muna hira da su khadija mikewa nayi.
Abinci na mike na dauko mai tare da aje mai komi da zai bukata a wurin shegewa mukayi can wurin yaran hajiya don mu basu wuri su tatauna da mahaifiyar shi.
Muna shiga tace mashi babana harda wani uban tsaraba haka mai yawa kuka zo wa mutane dashi bayan kullun dawainiyar ka bai karewa gare mu.
Yace hajiya ban ko san ta hada tsaraban nan ba sai gani nayi ana sakawa a mota tace yanzu duk itace da wanan dawainiyar haka , ?
Shiyasa ake son samun mace tagari wacce zata dinga kare wa mutum mutuncin shi dana yan uwan shi wanan yarinyar gata dai karama amma kuma tana da wayau wallahi tasan darajan mutane sosai.
Sai bayan goma na dare muka fito zuwa shiyan mu bayan mun yi shirin kwanciya ne nake fada mai zancen zuwa gidan su Aisha buki da muke son yi gobe.
Yace mantawa nayi Aisha na garin nan dana dage tafiyan mu sai wani lokaci don nasan yawo zata jaki ku dinga yi a nan niko kin san ban bukatan hakan ko.
Shiru nayi don idan na tanka zai samu hanyan da zai hana fitan gobe wanda ba zaimin dadi ba har Aishan bayan nayi mata alkawari.
Jin nayi shiru ne ya kyale baici gaba da maganan ba sai ji nayi ya jawo ni zuwa jikin shi nace a raina nan kafi auki dama.
Yana fafin kima ganin khadija zata iya kwana da yaron nan kuwa nace ita tace ai a barshi tunda ba nono yake sha ba.
Yace tana da kokari wallahi shine hikimar da nayi ai wirin cewa a barta don nasan zata temaka maki ta hanyoyi da dama.
Washe gari tun tashin mu gyaran part din mu mukayi muka fita zuwa gaida hajiya din mun dan jima wurin ta har da karyawa mukayi kafin mu dawo mu fara shirin zuwa gidan Aisha wurin buki inda yan uwa zasu taro sai mu dunguma mu tafi gaba dayan mu gidan bukin da abinda za a kai mata don da autar dakin su maigida cikin bukin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button