BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

* * *
Bike ya rage saura sati biyu duk nabi na ramay kulliyomin bani da kwaciya hankali tare dani yan gida mu sai shirin buki suke yi.
Ranan ina zaune sai ga yaya Nura da wayan shi har dakin mu wai ana magana dani a waya na karaba ina mamakin waye zai kirani da wayan shi.
Na karba da sallama na amma sai naji muryan wanda naki jini a wayan yana cewa ke yar kauye watau kina nan ga bakan ki ko.
Nagane shime a layin duk da gabana ya fadi amma a fili sai nace muna dai a bakan mu ko don kaina mayen da ka dafe min kana son shiga cikin rayuwana.
Yace ke manya na san bakomi kikewa ba sai son ace kina lagos kina aure ko ?
Nace wanan ba shine matsalan ba don ba nice farko shiga lagos daga kauye ba kafin ni wasu sun rigani.
Yace a harzuke suwa kenan kike nufi oho mahaifana kike son ki zaga ko may ?
A yadda ka dauki maganan nawa hakan nan amsa yake don bani ce farkon shiga birni ba.
Avikin tsawa yace ke dakata kiji kiyiwa bakin ki waigi ki san wanda kike magana dashi, ke har wata mace ce da zan tsaya ina bata lokacina a gare ki.
Yan mata wani iri ne ban gani ba ke har kinada abu yiwa maza feleke ne yaja tsuki yace a fusace.
To ki sani ba irin Ahmed akewa irin feleken nan ba don ni baki cikin tsarina kin sani bakuma zaki taba samu ba.
Daga kawai ana son rufa iyayyen ki asiri a taimake su da har ina macen take nan.
Nace a rifa wa iyayyena asiri taimake so ko a rufawa naka kai da ka tsufe masu awaje kar akai ga abin kunya duk barinki ya kare babu maija.
Ya kut nasan ran shi yakai kololowar baci ne da magana yace zan gwada maki yanzu nake a cikin bariki kuwa.
Kinga ni dama kiran ki nayi gwagon ki ta damay ni in akwai event din zakuyi na sani.
Nace akan wanu aure zayi event badai wanan auren kaddaran ba naka zan tsaya bata lokacina akan sa.
What ever you take it duk daya gare ni sai dai in ke baki so nasan wa yan nan mastiyatan yan uwan ki na su.
Nace dadin abin dai ba a taba canza ma tuwo suna sai dai a kira shi da tuwon abu kaza.
Au aikin banza bade za a iya saka mai suna ba ya kashe wayan shi yana jan tsuki.
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo a idona nace wannan wani irin tarbiya ya samu ko kadan muddin ba zai ragawa iyayye na bazan raga mashi ba.
Duk da kalaman da yake fada min suna da zafi kalamai ne na cin zarafin iyayye don haka na kara tsanar shi a raina.
Haka ummi ta shigo ta samay ni a cikin damuwa yanayina kadai ummi ta duba tasan raina a matukar bace yake cikin sallon hikima irin manya ta tuhumi abin dake faruwa.
Tace dani kina nan kina bata ranki ga abin da kika san ba zai hannu ba sai nace da ita ummi wannan mutumin ne baida mutunci .
Ko yaushe sai so ya zageni da iyayye na har da aibatani bai dauke shi a bakin komai ba don shi bai san darajan iyayyen shi ba.
Ummi ta jijiga kai sannan tace, abinda nake so dake yi hakkuri yi kuma tawassali da Allah in sha Allahu aniyar sa tabi shi baji a gare ki sai dai a gurin sa.
Abin da nake so dake shine kibi umurnin mahaifin ki koma maynene tsakanin shi da yar uwan shi ne bai shafe ki ba ke dai ki zage ki neme aljannan ki a gurin mijin ki zai fita masu ai in dai halin sa ne.
Kibar biye mashi ranku na baci ko banza ba saan yiki bane shi don ya girmay ki balle kuma ga aure zai shiga tsakanin ku.
Wanan magana na ummi su suka sanyaya min zuciyana take naji komai ya kawu min a rai na samu karfin gwiwan rake mashi abinda na kulla yi duk da manufar sa akaina na kuntata min.

Kamar yadda su gwago sukace basu son akaini da tarkace duk da haka an yi min kokarin wasu abubuwa wanda sam mutanen gidan mu basu zaci hakan ba.

Don ko yan uwan ummi sun hada kudi cas suka kawo mata tare da sauran tarkace na amfani gida.
Yayan da abokan arziki na cikin gari suma suka kawo nasu gudun mawan take kaya ya hadu ayadda baa zata ba.
Inna da ke cewa suga yaidda za ai buki uwa bata aje komai ba ta manta abin daga Allah yake don Allah shikewa bawan sa budi yadda yawo.
Yan uwan ummi sun yake shawara a tafi da kudin asai mun abin daya kamata a can idan an tafi kayan lafen dasu gwago suka kawo sai da inna tasa aka bude shi ita da diyan ta duk suka wawashe abin da suke so ciki.
Ina zaune a dakin mu don cikin gidan baimin dadin fita ina ummi sai shige da fice sukeyi na hada hada buki ni dai abin mamaki yake bani a raina.
Muryan yaya Sani naji a tsakar gidan namu yana kwala min kira na fito da sauri ina amsa kiran nashi.
Ya na kallona ganan sa ya fadi ya tsorata ainun da irin rama da ya gani tare da ni.
Ya ke Safiya lafiya irin wanan zabgewa da kikayi haka, keda ya kamata murna zakiyi aure ki huta da halin gidan nan .
Take idanuwa na suka ya kawo kwalla na dan sake mashi murmushin yake nace gani yaya.
Sai naga jikin shi yai sanyi da leda a hannun shi nasan abu yake son in dafa mashi a lokacin.
Sai ya juya dashi yana fadin barshi dai har ya taka yace dani Safiya zo nan sai nabi bayan shi muka fita.
Jikin bango na rabe a lokacin ne kuma kwalla ke zubo min a idanuwana babu kakautawa.
Na sa gefen hijjabi na ina shrewa sai naji ya sauke ajiyan zuciya dan kalle ni tausayina ya kara kama shi.
Ganin dagani sai shi a wurin kuma shi kadai ne mutum a gidan mu bayan ummi na dazan fadawa damuwa na.
Nace yaya Sani ina cikin wani hali wanda ba mai iya fitar da ni sai Allah dakuma baba.
Yace na sani Safiya karatu kike so amma baba yanuna karfin haihuwa a kan ki zai maki auren hadi na katse shi da cewa auren dole dai yaya.
Don wanda zaa bani ba ao na yakeyi baba kuma darajan iyayyen mu yake gani ba.
Ya zaro idanun shi waje alaman mamaki fa abin da na fadi din yace wa ne shi don uban shi.
Na girgiza kaina nace ko kadan baida mutunci yaya gashi kuma mashayin ne sosaiyace dani kuma baba ya san da haka din nace ban sani ba yaya.
Ki kwantar da hankalin ki zan yi bincike akai inna gane gaskiya kika fada min zan yi duk abin da zanyi in ga an fasa auren nan .
Maganan yaya sani shi kwantar min da zuciya har na dan ji sanyi a raina sai ya miko min leda da imdomei a ciki yace jeki ki dafa kici kafin in dawo.
Naji dadi a raina na ahiga nayi yadda yace na dafa indomei na shiga dakin mu muka ci da kan ne na.
Yaya sani kuma tafiya ya bincika inda yajiyo halin Ahmed babu dadi ko kadan a wurin yan uwa dake zuwa.
Yaya sani yace wanan abin duk sherin su inna ne ba komai ba nai mamaki ga su hausi yannen ta ne amma ce wai za ai mata aure ita.
Nan ya dawo gida ya ta yar da haukan shi ya kira yan uwan baba mu suka hadu ya fada masu halin da ake ciki.
Suka taru da dare akan baban mu suna fadin wanan baiyuyuwa ba ai muna auren dole ba bamuyiwa diyan mu.
Baba yai wuf yace babu mai hana wanan auren sai Allah yadda lanto ta nemi arziki a gidana haka nima zan mata shi da cewan wai gwago.
Sabada haka yadda nayi niyya haka zan yi saidai idan na kaita ta fito matsalar ta ne wannan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
8/14/20, 7:10 PM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , ,

???????? 8️⃣ ????????

YAR UWA IDAN AKWAI MASU NEMAN ACCOUNT NOBA DONA TA WURIN KI GA NOBA NA NAN SHINE 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO NOBAN WAYANA DON ALLAH KU TAIMAKA MIN.
AKWAI MASU KARBAN KUDI SUCE ZASU TURO MIN AMMA BASU BANI SAI SU RIKE A HANNUN SU IDAN NA TURA SU TURA WA MAI SHI NOVEL DON ALLAH KUJI TSORON ALLAH YAN UWA.
MASU CEWA BAN MAGANA YAUSHE ZAN TSAYA HIRA YAUSHE ZANYI TYPING SAI DAI INDAN ZAMU CIRE KWANA BIYU BA TYPING NE SAI HIRA SAI KUZABA MIN.
NAGODE NAGODE DA KASANCEWA KU TARE DANI KAUNA NE YA JAWO HAKAN SAI KUYI HAKKURI DANI YAN UWA

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button