BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

BAHAGON RAYUWA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
9/2/20, 11:42 AM – Ummi Tandama: BAHAGGON, , , , , , , , ,

????????6️⃣9️⃣????????

Ban fasa ja maki Allah ya isa ke ko kai mai fitar min da novel waje ubangiji yayi min bakar isa akan ko waye don gangancin yayi yawa baki da tsoron Allah ko baka da tsoron Allah na roki Allah yabi min hakkina akan wanda ya fitar da wanda ya karanta bai biya ba cikin gagawa.
Allah nasan kana amsa min rokona don akan hakkina na nake magana bana wani ba ubangiji na kara kai kuka na gare ka kahana ma mai shi farin cikin da yake nema don shiga hakkina da yake yi.
Ranan da bakin mu suka tafi munyi barcin gajiya sosai a gidan sai yamma kowan mu ya ya tashi naji dadin barin khadija da akayi min don zata debe min kewa sosai a gidan.
Yaya Saadu na samu ya tsaya min akan ta tsaya din don su mama sun kafe sai da ita zasu koma don baba zaiyi fada idan ya dawo.
Sai yaya yace ace shiya ce ta tsaya din haka yasa sukai shiru suka kyale ta badon sun so ba tun dai inna da tasan zaman na ta na iya zama wani alheri a gare mu.
Samira bata shigo ba sai bayan kwana biyu da suna tazo gidan nan muka baje muna duba kyaututukan da muka samu ga bukin.
Itace da dago tana fadin yanzu ai zaki fara shiga mutane musanman matan yan wurin aikin mijin ki da sukazo maki kara kin san dole suma idan ya samay su kije masu.
Nace nasan zamu kwasa da uncle ta wanan fanin don ba ko wani zai bari naje ba tace ana dai son mutum da zumunci ba ko yaushe ki zauna sai dai azo maki ba.
Muna cikin hiran ta jefo min tambaya tace anty ki dai bata zo ba bata turo maki sako ba ko nace antyn nan nawa fushi take yi dani har yanzu samira.
Ai dole tayi fushi dake tunda baki bar masu miji sun aura ba nace ba haka na bane akwai dai kila abinda nayi mata wanda ni ban sani ba.
Samira tayi saurin cewa ga abinda kikai mata nan kuwa Allah ya kyauta nace da ita tare da fadin ni ban son komai ya fito daga wuri na don irin halarcin da tayi min a rayuwa na ba zan iya matawa da ita ba.
Ikon Allah yanzu kayan da khadija na take sakawa sai naga sun zama min na yan kyau wanda a da ni bani ko saka irin su don ban ma samay su ba.
Haka yasa na bude wardrove dina na fitar mata da duk kayan da nasan ban amfani dasu yanzu don samun ci gaban rayuwa da na samu a tare dani .
Wanda Allah yayi min gatan da ban taba zaton zan samay shi a rayuwa na sai gashi cikin hukucin Allah ya wadatani da abinda ko a mafalki ban taba mafalkin haka ba agare ni.
Yau da nayi wanka na tunkari dakin Uncle dauke da Abbati a hannu na wanda yasha kayan sanyin da mummy ta saka mai cikin kayan da muka da uncle a kasan Spain.
Kayan sun matukar karban jikin yaron don ko wa yaga kayan zai yaba da kyawon su a jikin yaron ya hade da kyau halittan da Allah yayiwa yaron.
Sallama nayi tun daga kofan dakin uana ciki kwance ya amsa min na shigo tare da kura mai ido ina mamakin ganin shi kwance har wanan lokacin.
Sai da na samu wuri na zauna na fara gaida shi da kwana ya karba min cikin dan dagowa yana kokarin mikewa zaune nace Uncle yau ba aiki ne , ?
Murmushi yayi yana kai hannun shi ga yaron haka yasa na mika mai yaron dake hannu din gaba daya ya karbe shi ya rungumay a jikin shi tare da fadin.
Bawan Allah ka yafe muna Abbana ba laifin mu bane hana maka abincin ka da mukayi son lafiyan ka ne ya kawo haka gare ka.
Wani irin abu ne naji ya ziyarci zuciyana lokaci guda tausayi da damuwa nace tamu kaddaran ratuwan ke ne ubangiji ya bamu ikon ciye jerabawan mu.
Amin ya fada cikin lumshe idanuwan shi yana sauke ziciya yace duk abinda nake yi tunanen yaron nan yana cikin raina wallahi.
Uncle sai hakkuri ai tunda ma yana shan madara da sauki sosai wallahi yace yana sha sosai ko nace yana sha cikin sanyin murya.
Yace ai mu godewa Allah da ya nufe mu da rike zurian mu da hannun mu sai muyi fatan Allah ya raya munashi nace amin Uncle.
Dakata yace dani nayi saurin dago kai ina kallon shi yace ni wanan Uncle da ake kiramin ya isheni fa yanzu Allah ya bani da kamar kowa don haka akirani da sunan baban dana.
Dariya ya bani nace ai su yan biyu suka sakani kiran ka uncle da sauri yace dama ina son in tambaye ki wai ko madam ta kiraki tunda kika haihu ?
Nace eh ranan da na haihu ta kirani da yamma tana fada dani wai ban fada mata cewa ina da ciki ba sai haihuwa kawai taji a wurin daddy.
Bata ji ba fatace maki nace abinda ta fada min ke nam yace tun muna Spain na kira su na she da mata zancen cikin ki.
Wai may matar nan take nufi ne haka shiru nayi mashi ya sake cewa ko bayan maganan mu akwai abinda ya farune a tsakanin ku na kada kai tare da fadin wallahi ni matsalan komai bai taba shiga tsakani na da ita ba.
Doka tasa min in dinga tura mata kudi zata san abinda zatayi min dashi nan gaba kuma ina tura mata da kudin duk karshen wata idan kaba salary dina.
May ne ?
Ya tambaya cikin dan zaburowa daga inda yake kishingide da yaron saman kirjin shi yana dan shafan bayan yaron a hankali.
Nace a hankali ina tura mata kudin kamar yadda ta bukata yace Safiya ashe baki da wayo haka ban sani ba ?
Yanzu ko shafiu ku ko khadija suna iya yin wanan wautan da kikayi to bari kiji ni ina baki kudin nan ne don ki tare lalurar ki wanda ba sai kin fada min ba.
Na dauka gida kike tura masu suna amfani dashi ashe ke baki san ciwon kan ki ba ban sani ba to bari kiji.
Inda maimuna ko ba da ita tunda Allah ya kadara aure a tsakanin mu har da rabo ita bata isa ta hana ba ko ta sa ayi wanan abu ne nufin Allah.
Allah dai ya nufa ta dalilin ta zamu hadu idan kuma yaso zai iya hada mu ta wani dalilin bata gurin ta ba.
Daga yau na yanke duk wani hurdan dake tsakanin ki da ita har ma da kowa nata idan kina yi don ban son rainin hankali.
May ta mayar dani ne wai taga ta biyo ta hanyana bataci galaba na ba shine yanzu ta dawo gare ki .
Zan kira mijin ta yayi mata iyaka dake tun wuri ta shiga hankalin ta dani kafin rayuka su baci kada tace ko ban san abinda takeyi bane a baya na sani sarai albarkacin mijin ta da yaranta take ci gare ni.
Mun kwasa da ita akanki sosai amma ke baki sani ba don ba dole bane sai kin san yadda mukayi a kanki da ita shine ta biyo ta baya wurin ki tana min yankan baya ko ?
Ta nuna min cewa ke ba komai bane na nuna mata cewa ke wani abune mai muhinmanci a gare ni yadda take daukan ki kin wuce nan a gare ne.
Don so tayi shawaran komai dole sai da ita zanyi ban isa in ma dan uwana wani abuba ko ke ba ta hanyan ta ba.
Ranan ta jini sosai don rufe ido nayi naci mata mutunci ta yadda bata zata zan iya masu ba.
Na nuna mata kina da mahinmanci a gare ni fiye da kowa nawa a yanzu da taga hakan ta bai cin ma ruwa ba sai ta juyo tanan din dake.
To zanyi maganin ta tasan nafi karfin ta da mijin ta taci albarkacin shi wallahi da yau nasa ta dawo maki da kudin da duk ta karba daga gare ki.
Zan kara maki kashedi a kanta kada naji kada na gani na yanke duk wani alaka da ke tsakanin ki da ita daga yau din nan kinji na fada maki ko ?
A sanyaye na amsa mashi da eh ya koma ya kwanta tare da lumshe idanuwan shi ya fita batuna ranshi na bace da maganan da mukayi akan anty din.
Na dade zaune na kasa ko motsawa daga inda nake shi kuma ya fita batuna sai can na yunkura na mike na fita dakin na barshi da yaron .
Daki na koma na samu khadija kwance tana kallon tv dake aiki tana kallon wani series na yan Chaina kin dawo tace min na amsa mata rai babu dadi da eh kawai na bata amsa dashi.
Samun wuri nayi na kwanta ba tare da nakara magana ba nasan itama ta fahinci akwai matsala ne sai ta kyale ni taci gaba da kallon ta.
A idan nake har barci ya dauke ni ban sani ba ina cikin barci ne naji yana kokarin ta dani daga barcin yana dan jijigan yaron dake dan kuka a hannun shi.
Mikewa nayi zaune ina kokarin amsan yaron a hannun shi yace abashi abinci ina ganin yunwa yake ji ya fada.
Madara khadija ce ta mike da sauri ta hada ma yaron madara ta karbe shi a hannu na ta fara bashi ya karba da sauri yake jan feeder.
Uban ya dan dade tsaye yana kallin yadda yaron ke jan feeder da sauri murmushi yayi ya nufi kofan dakin yana cewa Khadija ashe kin iya reno ne haka ?
Dariya tayi kawai bata samu bashi amsa ba hankalinta na ga yaron da take ba abinci saida ya fita dakin na samun bakin magana.
Nace dama bai sha ba da akai mai wanka yayi barci shine na kai shi wurin baban shi su gaisa nasan ya tashi ya damay shi da kuka ne ya kawo shi.
Hira muka dan fara yi da ita kadan kadan har na dan sake na fitar da damuwa da nake ciki tana mi labarin yadda zaman gidan mu yake yanzu.
Nace yanzu da baki koma ba wazai dubi su wasila dake gida tace ai gwago ta fada ma su mama Jummai su koma wuri su da zama kafin ummi ta dawo.
Amma kuma nasan ko basu koma can din ba ai mama zata kula dasu a gidan don mama na kokari sosai wallahi duk da gorin da inna take mata akan abinda take yi din.
Yunwan da na fara ji yasa muka fito falo in ci abinci khadija na goye da yaron a bayan ta lokacin su gwago suka fito daga dakin da suke suka samay mu a falon.
Mummy ne ke fadin ai na dauka kuna barci ne danaji shiru nace barcin baiyi nisa ba muka tashi sallaman akayi kofan shigowa muka amsa.
Aisha ne tare da wata makwabciyar ta suka shigo gidan nan aka shiga gaisuwa ta kalle ni tace wai madam wanan irin kiba da kike narkawa fa ?
Dariya ne nace ina kiba anan duk na zube yanzu ma haka wallahi banjin dadin jiki na karfin halin kawai nake yi wallahi.
Mummy ne tace akasarin mata idan sun haihu dama sai sunyi zazzabi wanda ake kira dahuwan kassa don wahalan haihuwa da sukayi .
Kin san mace a wurin haihuwa duk sassanta jiki ta sai ya motsa to wanan motsawan shike haifarwa mata da irin wanan zazzabi daga baya.
Kayan da na ware zan bata cikin wanda muka samu daga yan uwa da abikan arxiki nabawa samira nata na Aishan ne dama ya rage shi nace khadija ta dauko mata a daki.
Basu dade suka tafi tun tafiyan su na kwanta zazzabi wasa wasa sai da ya kwantar dani dole washegari sai da muka tafi asibiti wuri likitan shi.
Magani ya rubuta min da allura akai min yayi muna bayani cewa dole dama sai nayi ciwo saboda jinin da na zubar a wurin haihuwa saukin abin ma don ina samun kulawa yadda ya dace ne.
Sai dai in matsa da cin abubuwan da zasu kara min jini a jiki don kada na jirkita da yawa kamar yadda masu irin lalurar ke shan wahala yayin da suka haihu don jinin da ya rage a jikin su.
Duk da allurai da maganin da aka bamu sai da na wahala sosai don ba karamin jin jiki nayi ba har na ramay sosai.
Wanan raman da nayi shiya daga hankalin Uncle sosai har ya koma wurin likita yace mai babu komai zan samu lafiya haka abin yake wani lokaci.
Ai nawa matsalan yana da dama don kafin ciwon ya bugeni sosai an daukar mai matakin daya dace gashi kuma ina kula da shan magani.
Na dan fara jin saukin jikina wanda ya koma nake jin shi kamar ba jikina ba ya shigo dakin yana min sannu cikin nuna kulawan shi a gare .
Zaune nake lokacin da ya shigo dakin yake tambaya na ko ina jin wani abu yanzu a jikin nawa ?
Nadan lumshe idona a hankali na nace mashi banjin komai uncle sai dai jikin nawa ne ban jin karfin shi ko kadan.
Kina ko shan maganin kin akai akai nace ina sha na yaune ban sha ba don ban karya ba tukun yace may kike jira baki ci abinci ba har tara da rabi na safe yanzu.
Nace bakomai a hankali bakin nawa ne dai banjin dadin shi dan sunkuyowa yayi gare ni yana fadin may kike son kici sai a dafa maki.
Kunu da kosai nace mai sai naga ya daga yana murmushi yace khadija taje ta fada ma mummy asa Nura tayi min .
Tana fita yace bari ya dauko min fruits in sha kafin a gama kada yunwa yai min yawa a ciki nace uncle banjin cin komai wallahi bakin nawa ba dadi nake jin shi.
Ido ya dan tsura min sai yake kai zaune bakin gadon cikin kwantar da murya yace dani ki daure ki ci diyan icce zasu taimaka maki wurin gyaran dandanon bakin ki kai na gyada mai alaman to.
Ya mike ya fita yasa aka wanke fruits shida kanshi ya shigo min dasu dakin ina zaune a yadda ya barni lemo mai bawa ya fara bani don zai wanke min bakin nawa yace.
A haka dai har na dan ji sauki saboda kulan da nake samu ta ko wani bangare har naji sauki na murmure kamar bani ba.
Ranan ina zaune kwatsan sai ga Faiza gidana tazo nayi mamakin ganin ta kwari da gaske tace wai anan abuja ta kwana ta fito lagos zata gida bauchi ne.
Nan da nan nasa a cika mata gaban ta da abinci da abin sha muna hira tana cin abincin dake gaban ta labari take bani na anty yadda take zagina wai yanzu na guje ta don ina ganin na samu gidan miji.
Ai tasan asiri nayiwa Uncle ya aure iyayyena makwadaita ne sun ga kudi idon su ya rufe wai idan ummi na ta kira ta tana ganin kiran sai taki dauka.
Dariya nayi nace anty ke nan yanzu kuma nice na koma abin zagi a wurin ta tace tun yaushe ai na fada maki halinta tun farko shiya kike ganin ina fada maki .
Yanzu haka Fati tabar wirin ta uwarta ta dauke ta ta mayar da ita can yobe garin su don yawan matsalan da suke samu akan fati din.
Ranan dai a nan ta kwana sai dai ban yarda na fadi komai ba akan anty din don yanzu mutum abin tsoro ne washe gari ta wuce bayan na cika ta da abin arziki .
Kwana biyu sai ga yaya saadu yazo yana ce min zai tafi lagos an bugo mai waya jikin gwago da na Ahmed wai ya tsanan ta don haka zai tafi ya dubo ta.
Kudi na dauko nace ya kaiwa gwago ya gayar min da ita idan yaje yaso yaki karba amma na matsa mai sai da ya karba don sako ne na bashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92Next page

Leave a Reply

Back to top button